sosai karatun ya shiga kanta sannan ya kyaleta.




Tunda Director ya fara yi mata bayani ta fahimta sosai ta kuma gane Fa'iz yaudararta yayi wani irin kuka mai ban tausayi Fauziyyah ta saka, jikin sa a sanyaye ya kalleta yace " Fauziyyah kiyi hak'uri babu yadda zamuyi da K'ADDARA, dan ta riga fata, sannan ni kaina da da yadda zanyi da nayi, gaskiya ba k'aramar cuta Fa'iz yayi miki ba, dan kinga yanzu ya jawo miki barin makaranta dole, dole ne kumar makaranta ta d'auki mataki a kanku, shi ya riga ya gama karatunsa, ke kuwa dole ne a koreki, saboda horo, da kuma sauran students suma su hankalta su k'ara shiga hankalin su, kamar a mafarki taji Director yana cewa " FAUZIYYAH HUKUMAR MAKARANTA TA SALLAMEKI DAGA MAKARANTA MA'ANA AN KORE KI!!!!! wata irin k'ara ta saki dami da ihu daga nan bata k'ara sanin inda kanta yake ba.




Ko kallanta Abban su baiyi ba sai Director ne ya mik'e cikin tashin hankali yana Subhanallahi, cak ya d'auke ta yayi mota da ita.



*************************



Fa'iz na shiga d'aki ya wuce bathroom kansa ya sakarwa shower ko kayan jikin sa bai cire ba, yana tunanin maganganun Mom

_( "yarinya nitsatstsiya gata da hankali da tarbiyya, ina matuk'ar san yarinyar zan so had'a jini da ita ko dan nasamu zuri'a ingantacciya)_


A gaba d'aya wunin ranar babu abinda Fa'iz yake tunani kamar maganar Mom, ya kasa sukuni, da dai yaga tunanin na neman damun sa ya shirya ya nufi night club, yana cikin tuk'i yaji wayar sa na ringing da dai kamar bazai d'aga ba, daga baya kuma ya d'aga, Director ne ya kira shi, sanar dashi duk abunda ya faru yayi tun daga farrko har k'arshe har korar da akayiwa Fauziyyah daga makaranta, yace" wallahi kaji tsoran Allah kabar ganin babu abinda suka isa suyi maka dan iyayen ta bamasu hali ba, Allah bazai tab'a kyaleka kaci bulus ba sai ya jarrabeka ta inda bakayi tunani ko tsammani ba, wallahi Allah Fa'iz hak'k'in yarinyar nan bazai tab'a kyale ka ba yata bibiyarka kenan, sai ya hana maka kwanciyar hankali da jin dad'in duniya kasan illar cirewa budurwa budurcinta a titi kuwa, ka kuka da kanka duk abinda ya sameka kar kayi kuka da wani, ya kashe wayar.



Tunda Fa'iz yake rayuwar bai tab'a aika ta wani abu marar kyau yaji babu dad'i ba sai yau, sosai yaji abun ya dake shi musamman maganganun da Director ya sanar dashi, zuciyar sa ba k'aramar harzuk'a tayi ba da yaji abinda Fai'za tayi ba, dan shi ya tabbatar itace, zuciyar shi kamar zata tsaga k'irjinsa ta fito, har bibbiyu yake gani a haukace ya nufi gidan su.



Cikin sauri Fai'za ta gama shirin ta na makaranta dan yau a k'agare take dataje makaranta dan taga abinda za'ayiwa Fa'iz da Fauziyyah, a hanzarce ta fito daga gida ta tare d'an a daidaita, ko ciniki babu ta hau, dan tsabar sauri, yana kaita ta sauka ta bud'e jakarta ta biyashi ita kuma tayi cikin makaranta, tana shiga makarantar ta bud'e jaka da nufin ciro wayar ta ta kira Fauziyyah dan taji komai, ga mamakinta taga babu waya, da sauri ta zazzage jakar taga ba waya,tunawa tayi da tayi waya da acikin adaidaitan, tana gama wayar ta ajiyeta a gefe, aiko da sauri tayi class wani ta samu ta karb'i a aran waya ta kira wayinta, a kashe taji wayar, wani irin bak'in ciki ne ya ziyarci zuciyarta data tuna da video su Fa'iz da Fauziyyah dake cikin wayar, shikenan dama ta kufce mata wani ne zai samu a banza, tasan duk wanda yaga video shima kud'i zai nema, "hmmmmm tace had'i dayin murmushi kome ta tuna oho............




*Alhamdulillah*



*MOMYN ZARAH*



KUCI GABA DA BINA DAN JIN K'ARSHEN FA'IZA DA FA'IZ, DA RAYUWAR DA FAUZIYYAH ZATAYI A GIDAN SU, SHIN YA MAHAIFIYAR FAUZIYYAH TAJI IDAN TA SAMU LABARIN ABINDA TAYI, MAI FA'IZA TA TUNA WANDA YASATA DARIYA, MEYE DALILIN SUMAN FAUZIYYAH, A IRIN SAN DA MOM D'IN FA'IZ KE YIWA FAUZIYYAH WANE MATAKI. ZATA D'AUKA IDAN TAJI LABARIN ABINDA FA'IZ YAYI MATA, IDAN FA'IZ DA FA'IZA SUKA HAD'U MAI ZAI FARU........
[05/09, 20:32] Frd Din Fatima Saudia: ```K'ADDARA TAH!!!```

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹


~NAH~


*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_



_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_



105-110



Tunawa tayi wayar ta akwai security baza ta bud'u ba dole sai anyi restarting d'inta, idan kuma akayi restarting komai nakan wayar zai zama babu, amma duk da haka taji ba dad'i musamman ma data tunayi losing abubuwa da dama kenan har abada, har dai ta zauna a class har suka gama lectures amma baji ko ta ga wani abu ya faru ba, ba dan taso ba ta koma gida.



Fa'iz na zuwa k'ofar gidan su Fa'iza ya tura yaro yayi masa sallama da ita, yaran bai dad'e ba ya fito ya sanar dashi bata nan, dama yasan mawoyacin abu ne a sameta a gida, yadda yake cin zuciyar sa na tafasa bai iya barin k'ofar gidan ba batare da yayi maganinta ba, waje ya samu ya gyara parking dan ya sawa ransa ko kwana zatayi saiya jirata.




Yakai 4hrs yana jiranta tun da dama sallah ba damunsa tayi ba, bata cikin jerin rokunan rayuwarsa, can ya jiranta ya hango d'an adai-daita sahu ya ajiyeta, da sauri ya bud'e motar ya fita, cikin takunsa na k'asaita ya k'arasa gabanta, dammmmm!!!!!! taji gabansa ya fad'i dan da ganinsa tasan ba Alkhairi bane ya kawo shi ba, cikin dakewar zuciya tayi banza dashi ta rab'a ta gefensa zata wuce, shak'o wuyanta yayi ya dawo da ita gabansa.




Bata kula shi ba duk da irin tsoratar da tayi da kuma muguwar fad'uwar da gabanta ke yi amma ta dake ta b'ata fuska tace" malam lafiya ne? Kauuuuuuu!!!!!! taji wasu wawayen marika a jere sun dira a fuskarta,k'arar marin da zafinsu sai da yasa jinta da ganinta suka d'auke, sai da takai wajen 15mnts sannan ta dawo haiyafinta, bata kulashi ba ta, gida take k'ok'arin ta shige dan idan ta biyewa Fa'iz zai tona mata asiri ne ya kuma zubar mata da mutunci a unguwar su da gidan su, bayan duk unguwar suna d'aukarta mutuniyar kirki mai mutuci salihar mace ta gari babu wanda yake mata kallon watsatstsiya.



Ganin take-taken sa shiya hanata kula shi, k'ara fizgo ta yayi, ya yaga mata hijab d'in jikinta auko sai ga help best da short nekeer sun bai ya na, " please Fa'iz karkayi man haka dan Allah komai zamuyi muyi shi a can gefe kaga kaima ban tab'a binka unguwarku ba, bai kula ta ba illa ma d'aga murya da yayi yace " banza karuwa basik'a 'yar maye, aiko nan da nan jama'a suka fara taruwa mahaifinta dake gida yajiyo hayaniya yayiyo waje, sai da Fa'iz ya tara jama'a mak'il sannan ya tuna mata asiri, yayi mata bankad'e da tunon silili, duk abinda Fa'iza keyi bai rage ko ya b'oye wani abu ba sai da ya fad'a, sannan yahau motar sa yayi gaba.



Cikin bak'in mahaifinta ya kalle ta yana zubar da kwalla yace " ni dai Allah isa tsakani da ke domin kin yaudare ni kije ga duniyar nan ya tsallake ta yayi tafiyarsa,



*************************



Fauziyyah bata farka ba sai ta kai wajen 5hrs, da kuka ta farka ta ganta a gidan su a d'aki Aisha na zaune a gefenta, Aisha na ganin ta farka da gudu ta fita ta Kira Mama, tare suka shigo da maman, da ganin fuskar maman taci kuka har ta gaji, a hankali ta zauna a kusa da Fauziyyah ta kura mata ido, ita ko Fauziyyah in banda kuka babu abinda take, duk fuskarta ta kumbura, Mama tace" kingani ko, dama na fad'i duk duniya ni kad'ai ce daga ni babu wani ko wata, Fauziyyah kin cuce mu kin watsar da ingantacciyar tarbiyyar da muka baki, ta fashe ta kuka ita maman cikin kukan taci gaba " Allah ma shaida ne ba irin tarbiyyar da muka baki ba kenan, yanzu da wanne ido zamu kalli duniya, da wanne ido zamu kalli dangin mahaifinki, da wanne ido zamu kalli mijin da zai aure ki a matsayin budurwa, ina zamu kai wannan abin kunyar abin gori, abinda ba'a tab'a yinsa a zuri'ar ba, Fauziyyah da wanne ido zamu kalli duniya muyi ikirarin mu iyaye na gari ne, kin kunya tamu, kin cire mana yak'in mu akan ku Fauziyyah ta k'ara fashewa da kuka.



Shima Abban nasu cikin tashin hankali ya shigo, ganin Mama na kuka bak'in cikinsa ya k'aru kallanta yayi cike da tsana yace " yanzu ina amfanin wannan kinsa mahaifanki kuka mu duka biyun shima ya k'ara fashewa da matsanancin kuka yace " Allah ya sani ban tab'a zina da 'yar wani ba, na kuma baki tarbiyyar da cikekken ilimi,Fauziyyah mun d'auki dukkan burin mu mun d'ora shi a kanki, mun baki yarda, mun baki kulawa, mun baki damarki, babban kuskuren danayi shine na yarda dake da kuma sakarmiki rayuwarki.



Cikin kukan da har muryarta ta dishi ta zube a k'asa tana kuka tana bawa iyayen nata hak'uri " Abbah dan Allah ka yafe min fushinku ba k'aramar masiba bace a gare bare kuma hawayenku, nasan nayi laifi nayi babban kuskure, dan Allah kuyi hak'uri ku yafe man, kuka take sosai tana maimaita ku yafe min.



Abu wasa-wasa yau har wata d'aya amma kullum abu gaba yakeyi, tun iyayen Fauziyyah suna fushi da ita har kuka dawo fad'a yanzu gashi sun dawo lallashi amma a banza, kullum cikin kuka bavci ba sha, bata cin komai duk tabi ta zafge ta rame ta koje kamar ba ita, ta zama kamar wata tab'abbiya bata komai sai kuka ko wanka batayi ganshin kanta duk yayi buzu-buzu, sallah kawai da karatun Qur'an su a gaba, kullum tana cikin kai kukan ta ga mahaliccinta, dan shi kad'ai zai sama mata mafita, ko bacci bata iya yi sai dai idan ya sace ta cikin baccin zakaji tana cewa Maman mu Abba Aisha ku yafe min.



Gidan kowa cikin bak'in ciki yake babu wanda hankalinsa yake a kwance a cikin su, hatta Aisha da take k'arama ita ganin halin da 'yar uwarta ta ke ciki, duk yasa ta fita hankali ta, kullum tana tare da Fauziyyah, Allah sarki rayuwa gidan da ake rayuwa ta farin ciki da kwanciyar hankali shine yau aka wayi gari yakoma kamar gidan mutuwa kowa ga gani yayi jugum, ita kuwa kullum tana d'aki, tana sa'ar tata dan ko karatun Qur'an take bata fasa kukan, har sallah tanayi tana kuka.



Director yana zaune a office dinsa yasa phone dinsa a caji ya fita sallah, yana dawo daga sallahr ne yaga hayaki na firowa daga windows din office dinsa aiko da gudu ya karasa yana bud'e office din yaga wayar sa daya bari a caji ce ta k'one k'ormus har cajar, saboda tsabar takaice kasa yin komai yayi ya zauna kawai yana ganin ikon Allah.



Duk yadda kaso ka tunawa mutum asiri idan Allah ya rufa shikenan, babu yadda Fa'iza batayi ba dan ta yad'a video ba amma Allah ya kare Fauziyyah, daga k'arshe ma aka sace wayar tata, shi kuma Director wayar sa ta k'one, dama kuma duk duniya su biyu ne kawai masu video, yanzu kunga babu mai shi kenan



*BAYAN WATA D'AYA*



Halin da Fauziyyah ke ciki ne ya jawo mata matsananciyar rashin lafiyar da har sai da aka dangana da asibiti run kwajin farko da likita yayi ya tabbatar wa da iyayen ta tana da shigar ciki na wata biyu da sati biyu.............




*Alhamdulilah*



*MOMYN ZARAH*



```Please ku rink'a yin comment, wallahi Allah ina jin haushi sosai na rashin comment dinku, da harna yanks shawarar tsayar da typing dan gani nake kamar sakon baya iya gare ku ko baki jin dad'in novel din```



~Please comment~
~Please comment~
~Please comment~



_Yau nasan zakuga typing error da yawa ayi hak'uri please_ 🙏


Bye
[05/09, 20:32] Frd Din Fatima Saudia: ```K'ADDARA TAH!!!```

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹


~NAH~


*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_



_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_



*EDITING BY MOMYN ZARAH*



110-115


"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un abinda kowannen su yake dad'e kenan, jin jiri na d'ibarta ne yasa dole Mama ta zaune shiko Abba gumi ne kawai ke keto masa, shi kansa likitan ganin irin tashin hankalin da suka shiga ne yasa shi fuskantar lalle akwai wani abu a k'asa, kasa hak'uri yayi yace " lafiya kuwa naga duk kun shiga damuwa naga ai abin farin ciki ne, ina mijin ta?



Cikin k'arfin hali Mama tayi murmushi tace " tsabar farin ciki ne yasa mu shiga wannna halin daka gannu, mijinta ya mutu kuma bamuyi tsammanin an samu rabo, murmushi shima yayi yace " ikon Allah kenan, haka dama Allah yake ikon sa, shiru suka yi su duka babu wanda ya k'ara cewa k'ala, magaunguna ya rubuta musu yace" idan kun fita ku siya.



Suna komawa gida kowa yayi d'aki tana shiga d'aki ta fad'a gado ta saki kuka mai ban tausayi da k'ona zuciya, tana cewa "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, Allah wannan wacce irin mummunar k'addara ce, Allah kai kace baka d'orawa bawanka abinda bazai iya, ya Allah ka bani ikon cinye jarabawar nan, ya Allah ya taimakamin ka d'auki rai.




K'ara fashewa tayi da wani kuka tana ta surutan ta ita kad'ai, Mama na shiga d'aki ta sami Abba zaune a k'asa ya had'a kai da gwiwa yayi tagumi sai zufa ke zubo masa kusa dashi Mama ta zauna ta dafa shi, sai kuma ta fashe da kuka mai k'ona rai.



A hankali ya d'aha kansa sama ya kalleta, ba kad'an yake jin zafin kukanta a ransa ba, yace " haba Maman yara ke kiyi kuka suma suyi kuka ya kike san nayi, idan suma yaran suka ga kukan ki ai sai ki karya musu zuciya, ki dubi girman Allah kiyi shiru, sautin kukan nata ta rage sai shashsheka dake fita a hankali, yaci gaba, ki yarda da K'ADDARA mai kyau ko marar kyau mana, Allah baya tab'a barin d'ayanmu ba tare daya jarrabe mu ba, mu irin tamu K'ADDARA kenan kin san ta wasu, kin san wace irin jarabaawa Ubangiji yayiwa wasu? kai ta girgiza alamar a'a, murmushin k'arfin hali yayi yaci gaba" to ki goge hawayenki, ki godewa Allah a bisa jarabawar da yayi mana, mu daure muci jarabaawar nan, ni yanzu zuciya ta tayi sanyi, saboda yawan kiran Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, da hasbunallahu wani'imal wakil, subhanallah Alhamdulilah Allahu Akbar, na yarda da K'ADDARA, duba da irin halin da Fauziyyah ta shiga, na yarda da jarabaawa ta Ubangiji, na d'auka, Allah ya bani ikon cinye ta, a hankali tace" Amin.



"Ni dai abu d'aya na sani idan duniya zata tashi baza'a tab'a zubar da cikin nan ba, wallahi Allah sai ta haife abinda ke cikin ta, wani irin mummunar fad'uwa gaban Mama yayi, a ranta tace " shikenan abinda nake gudu ya faru, yanzu sai munyi shege, jin shirun da tayi yasa Abba tab'a ta yace " ya akayi ne Maman yara? sanin halin Abba shiyasa ta b'oye halin da take ciki, dan yanzu itama sai ya shafe ta, murmushin k'arfin hali tayi tace " hakan yayi, "yawwa Maman mu, ya fad'a da alamun tsokana dariya tayi, sai da Abban ya kwantar mana da hankali sosai, sannan yace " maza jeki lallashi Fauziyyah dan nasan yanzu tana can tana sana'ar tata.



A hankali Mama ta shiga d'akin a kife ta samu Fauziyyah tana ta faman kuka tana ta sambatu, ita kanta bata san me take cewa ba, ba k'aramin tausawa 'yar tata tayi ba, a hankali ta zauna kusa da Fauziyyah ta dafa ta, a hankali ta d'ago kai, idonta duk ya kumbura ta zube a k'asa tana kuka tace " Mama na jawo muku magana na jawo muku kunyar duniya, dangin Abban mu sun samu abin fad'a burin su ya cika, dan Allah Mama ku yafe min ko naga haske a rayuwa ta ta gaba, Mama ki bawa Abban hak'uri, wallahi na gwammaci mutuwa ta da na saku cikin wannan mummunan halin, Mama na gwammaci ciwo mai tsanani ko hauka da ganin halin dana saku, Mama dan Allah ku rok'a min Allah ya d'au rai n.........


Da sauri Mama ta ta katse ta ta jawo ta jikinta ta rungume gaba d'ayan su suka saki kuka, abin ban tausayi, sun dad'e a haka sannan Mama tayi k'arfin halin yin magana ta daina kukan tace " bakomai Fauziyyah mu mun yarda da K'ADDARA, mun yarda da jarabaawar Ubangiji, dan kin shiga wannan halin bazamu tab'a kyamatarki ba, iya kaci dai mu nuna miki kuskuren ki, to Alhamdulilah mun nuna miki kuma ke da kanki kin gane hakan, haka dai mama taita fad'a mata kalamai masu dad'i har ta kwantar mata da hankali



*************************************



Tun abinda Fa'iz yayiwa Fa'iza tsanar shi ta k'ara k'aruwa a zuciyar ta, babu abinda ke yi mata yawo a zuciya sai wutar d'aukar fansa dake ruruwa a zuciyar ta, ta zama cikekkiyar 'yar maye kullum tana cikin shaye-shaye da maye saboda tsabar takaicin abinda Fa'iz yayi mata ta haukace saboda tsabar neman hanyar d'aukar fansa ta kasa samun sukuni da kwanciyar hankali burinta kawai ta d'au fansa a kansa, so take taga tayi masa abinda har ya mutu bazai manta ba, so take taga ya wulak'anta ya tozarta ya zama abin tausayi ko a wajen mak'iyin sa ma balle kuma masoyansa, wannan tunani ne yayi mata yawa ganin ta rasa mafita ne yasa ta yawan shan kayan maye.



Fa'iz ne zaune da Gan's d'insa yana basu labarin irin ni'imar daya
Showing 24001 words to 27000 words out of 70679 words