NAPPY SAULAWA
SHATUUU
LITTLE MISS
MAMAN TWINS



90-95



*EDITING BY MOMYN ZARAH*



Da kyar ta iya mik'ewa tsaye tayi bakin get, da kyar take iya jan k'afarta, adai-dai ta sahu ta hau direct tayi gida, tayi sa'a tsakar gidan ba kowa d'akin su ta wuce ta fad'a kan gado ta saki kuka mai ban tausayi, da karya zuciyar mai. "



Tun 10:30 ta dawo gida take ta faman aikin kuka babu wanda yasan ta dawo, har 2:00pm Aisha ta dawo daga makaranta ta iske Mama ta gama aikin gidan tas, har abinci ta gama, a gajiya ta dawo dan haka bata tsaya a tsakar gida ko d'akin Mama ba, d'akin su ta wuce, Fauziyyah najin ta tayi saurin kifa kanta kamar bacci take, tana shigowa ta ganta a kwance, kanta ta fad'a tana "Aunty yau kin riga ni dawowa, kamar mai bacci ta farka, tana murza ido muryar ta a dishe tace " eh kai na yake ciwo, ta mai da kanta gefe ta rufe ido dan tasan Aisha da surutun tsiya ga tambaya, shiyasa tayi mata haka. "



Aiko da gudu Aisha tayi d'akin Maman tana cewa " Mama wai Aunty bata da lafiya? itama Maman da sauri tace "wacce Autyn? "Aunty Fauziyyah mana, "tana ina? "d'aki, "au ta dawo ne? " nima yanzu dana dawo na ganta, wucewa Mama tayi d'akin, Mama na shiga d'akin ta iske ta kwance kamar mai bacci, tsayawa Mama tayi a kanta ta k'ura mata ido tana san gano wani abu tattare da 'yar ta ta.



"Ganin ta kasa gano komai ne yasa ta fita daga d'akin, Aisha ta kwalawa, tace "idan Auntyn ki ta tashi ki kira ni, "idan kuma bata tashi ba fa?, "ki tashe ta nan da awa d'aya, "to Maman mu. "



Shiko Fa'iz bayan ya gama yiwa Fauziyyah wulak'anci gida ya wuce, cikin maye ya shiga gidan, ya iske Momy a falo, yana ganinta yayi k'ok'arin saita kansa baiyi mata magana ba ya wuce d'akinsa, itama bata yi masa maganar ba, ido ta k'ura masa, ta gane a halinsa da yake, bayan sallar magrib tana zaune a d'akin ta ya shigo da T-shirt da 3 quarter a jikinsa, bakin gado ya zauna harta gama lazimin ta, kallonsa tayi da alamon tambaya, yagane kallon tambaya take masa. "




Sumar kansa ya shafa yace " Momy akwai abinci a gidan ne? "Eh tace masa kawai ta juyar da kanta gefe, "Momy lafiya ko laifi nayi miki ne? " a'a baka yi man komai ba, Momy idan nayi miki wani abu koda akan rashin sani ne kiyi hak'uri, (duk iskancin Fa'iz yana matuk'ar yiwa iyayensa biyayya, baya tab'a tsallake umarninsu)



"Fa'iz ta kira sunansa "Na'am momy, "karka k'ara shigowa gidan nan cikin maye, cikin sanyin jiki yace " Momy maye kuma? "Eh kasan dai nasan maye ko, tunda naka 30yrs ina zaune da d'an maye, pls ka barni ma da bak'in cikin baya, "mom...., "kadai ji abinda na gaya maka bana san musu, "to yace cikin karyayyar mura. "



Abinci tasa 'yan aikin gidan suka jera musu akan dianing table, suna cin abincin suna hira, dan ita Momy mace mai hak'uri duk girman laifin dakayi ata daka bata hak'uri shikenan ya wuce kwata-kwata bata ruk'o, cikin wasa da dariya suke kallan sa tayi tace " Fa'iz ina Fauziyyah, dammmmm!!!!!! yaji gabansa ya fad'i, shiru yayi bai bata amsa ba, taci gaba da cewa " Yarinya nitsatstsiya ce gata da hankali da tarbiyya, yarinyar ta shiga raina sosai ina matuk'ar santa, zan so na had'a jini da ita ko dan na samu zuri'a ingantacciyah, yanaji kayi shiru ne?




Ciikn rawar baki yace "oh! Fauziyyah yarinya mai hankali kam tanan lafiya, yana kawowa nan ya mik'e yana "Mom my phone is ring, da ido kawai ta bishi tana kallan ikon Allah, " tabbab akwai wani abu ta fad'a jiki ba kwari, nidai Allah yasa bai lalata musu 'ya ba. "




Ita ko Fa'iza tana tashi daga bacci, ko mik'ewa batayi ba daga inda take kwance, ta bud'e YouTube, taga video data d'ora, takai 1hrs tana dubawa amma babu, ganin bai hau bane yasata yin cilli da wayar, wata irin dariya ta saki dan tuno da wani abu, wayar ta d'auka ta had'a, wani malami ta kira wanda suke holewar su, yana d'agawa yace " hello yau manyan mata an nemeni, murmushi tayi kamar yana kalloanta ta kashe murya tace" ai kone manya, ya garin? "Alhamdulillah, ya akayi ne? Baban mu ne wai yake san number san number Director na makarantar mu, "ok jirani in turo miki, " a'a ka fad'a min yanzu nayi dialing "ok yace ya bata number, sukayi sallama. "



Tashi tayi, tayi wanka sannan ta fita, saban layi ta siya ta bud'e WhatsApp account dashi, tana duba number Director ta ganshi a online tayi murmushin jin dad'i ta tura masa video, sai ta tabbar ya shiga kuma ya gani sannan tayi masa typing kamar haka÷



_Assalamu Alaikum_

_Ni d'aya daga cikin d'aliban makarantar kace, wannan wanne irin mummunan abun kunya ne, ace a k'asar musulmai, jahar musulunci, makarantar musulmai a rink'a aika irin wanna mummuna fasadin, ka godewa Allah daya sakance ni na gani, dan inda wani ne ya gani da tuni an d'ora shi a kan YouTube kai ma da sai ya shafe ka_


_Sunayen d'aliban sune_


_Fauziyyah Muhammad Ahmad tana Microbiology level 2 1st semester_

_Fa'iz Abbakar gama makarantar this year, y shigowa ne kawai b'ata yaran mutane_



Tana tura sak'on ta kwanta kanta yana kallon sama, fuskarta a sake da alamun jin dad'i tana cikin tunani taji an kira wayar, tana dubawa taga Director dinsu ne katse wayar tayi ta karya layin........



*Alhamdulillah*



*MOMYN ZARAH*
[05/09, 20:32] Frd Din Fatima Saudia: ```K'ADDARA TAH!!!```

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹


~NAH~


*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_



_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da Kasai_



BAN MANTA DAKU BA, HAR KULLUM KUNA CIKIN RAINA


AUNTY FAUZA ('YAR AMANA)
AUNTY BATUL ADAM JATTKO
MARYAM AHMAD PAKI (KANWA TA)
KHRTY
NUSSEE



95-100


*EDITING BY MOMYN ZARAH*



Tunda Fauziyyah ta kwanta ba bacci takeyi ba, idon ta biyu, in banda kuka babu abinda yake yi, jikin ta duk ya mutu ga kanta dayakeyi mata masifar ciwo kamar zai tsage, tana cikin kuka Aisha ta shigo tsayawa tayi akanta tana kallanta sai can tace " Aunty mai akayi miki?



Kamar daga sama taji muryar Aisha dan bata san shigowarta ba sai kawai maganar ta taji, cikin zafin nama Fauziyyah ta goge fuskarta tacewa Aisha" bakomai kaina ne kawai yake man ciwo, Aisha batace mata komai ba sai fita datayi, dan kiran Mama, saboda Maman tace idan ta farka ta kira.



Da sauri Maman ta shigo d'akin a bakin gado ta zauna kallon Fauziyyah take kamar bazata daina ba, ajiyar zuciya Mama ta sauke tacewa Fauziyyah tashi kiyi wanka kiyi sallah, sai da Maman ta taimaka mata sannan ta iya mik'ewa, Aisha Mama ta saka takai mata ruwan wankan, bayan ta fito daga wanka ta shirya sannan ta shiga jero salloli, cikin nutsuwa take karatun Qur'aninta tanayi tana zubar da kwalla.




Har sai da akayi kiran sallar ishsha sannan ta rufe Qur'anin ta mik'e ta gabatar da sallar, tana idarwa Aisha ta shigo d'auke da farantin abinci ta dire a gabanta, fita ta kuma yi ta d'ebo mata ruwa ta kawo, itama waje ta samu ta zauna a gefen ta, sai da Fauziyyah ta gama azkar d'inta, ta ninke hijab d'in, ganin tana shirin komawa ta kwanta ne yasa Aisha cewa " Aunty ga abincinki nan fa na kawo, " na k'oshi ta bata amsa adak'ile, " Aunty dan Allah kitashi kici ko kad'an ne, " nace miki nak'oshi ko.



Bata kuma yi mata magana ba ta fita ta nufi d'akin Mama, ko sallama babu ta danna kanta d'akin, "Mama wai Aunty bata cin abincin, ta fad'a cikin shagwab'a, d'akin Mama ta shiga, Aisha na biye da ita a baya, tun daga k'ofar d'akin Mama ke jiyo shashshekar kukan ta, da sauri ta k'arasa d'akin tana kiran sunan ta, saurin goge hawayen fuskarta tayi, bata iya amsawa Mama kiran da take mata ba, saboda tana bud'e bakinta kuka zai biyo baya.




bakin gadon ta kuma zama batayi mata magana ba ido kawai ta zuba mata "Fauziyyah ta kira sunanta a hankali"Na'am kawai tace, shiru Mama tayi sai can tace " Fauziyyah wai mai yasa kike da zurfin ciki ne, nayi2 dake ki fad'amin damuwarki da matsalarki amma kink'i, ya kamata ace kin san ni kad'ai nafi kowa kusanci dake ni nafi cancanta dana san matsalarki ko sirrinki, saboda ni zan iya rufa miki asirin da duk duniya ba mai iya rufa miki shi.



Nice fa mahaifiyarki, ni na d'auki cikin ki wata tara da kwana tara, na shayar dake na yaye ki ban tab'a bawa kowa ruk'onki ba, ni na raineki, kin fi kusanci da sabawa dani fiye da kowa, ki fad'amin abinda yake damunki tun wuri mu tare shi da zafin addu'a kin san addu'ar mahaifi, kin san bakin mahaifi,saban kuka Fauziyyah ta saka tana cewa " Mama ni kaina na rasa meke damuna na rasa meye matsalata ban san meke damuna ba, kawai dai ina jin bak'in ciki araina ne, shiru Maman ta kuma yi can tace " Fauziyyah tunda kink'i fad'amin damuwarki shikenan rainan danayi muku baiyi min amfanin komai ba, kin san tashin hankalin ko fushin su bak'aramar masifa bace a rayuwar d'a ba, na dad'e ina tambayar ki matsalarki amma kinyi biris dani, in banda kuka babu abinda Fauziyyah ke yi, jikin Mama ne yayi sanyi dan ganin halin da 'yar tata ke ciki, tasan koma meye ba k'ara mun abu bane, amma bakomai in sha Allah zata taya ta da addu'a. "



Fuska Mama ta b'ata tace " idan bakya san fushi na a kanki ki d'auki abincin nan ki cinye tas ki mik'o min kwanan yanzu, "to tace badan ta so amma yaza tayi haka tamik'e, jin abincin take kamar magani, " Aisha jeki d'aki kan kobet ki d'auko min paracetamol, "to Aisha tace, cikin sanyin jiki, dan itama ta damu sosai ganin halin da 'yar uwartata ke ciki, dan ba k'aramar shak'uwa ce a tsakanin su ba, "gashi Maman mu, karb'ar maganin tayi ta b'allar mata biyu ta mik'a mata, sai da ta cinye abincin tas, ta shanye maganin ta kwanta Mama ta kalle ta tace, bazan matsa miki lalle sai kin sanar dani damuwarki ba, idan kinga na cancance hakan kya sanar dani, ta fice daga d'akin, bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita ba tare data sani ba.




Director ne zaune a office d'insa sai gumi ne ke keto masa yana gogewa, sai tunane yake ya kasa sanin mafita, yakai wajen 2hrs, ya rasa mafita, dafarko yace idan har ya bari video ya fita to tabbas sai ta shafe shi, kuma ya zubar da mutuncin makarantar da d'aliban sa, idan kuma yace meeting zaiyi da gaba d'aya lecturers d'in makarantar nan ma dai bai tsira dan asirin ne zai tuno, da kyar dai ya nemo mafita, takarda ya rubuta ta neman mahaifin Fauziyyah da ita kanta Fauziyyah, takas ya tashi d'an aike har gidan su Fauziyyah, d'an aiken na zuwa yaci sa'a ya sami Abban su Fauziyyah a k'ofar gida yana alwala, hannu ya mik'a masa suka gaisa daga bisani ya sanar dashi daga inda yake da kuma sak'on dake tafe dashi, takardar ya amsa yayi masa godiya ya wuce.



Gida ya shiga ya sanar da Maman su Fauziyyah cewar ana neman sa gobe k'arfe 10:00am, jikin ta sanyaye tace "Allah yasa alkhairi ne, amma tabbas jikinta ya bata akwai wani abu a k'asa duba da yanayin da Fauziyyah ke ciki, "Amin shima yace, duk abinda ke faruwa akan kunnen Fauziyyah amma jikinta bai bata komai ba.




*WASHE GARI K'ARFE 10:00am A OFFICE D'IN DIRECTOR*




*ALHAMDULILLAH*



*MOMYN ZARAH*



```KU BIYO NI DAN JIN YADDA ZATA KAYA YANZU AKA FARA WASAN```
[05/09, 20:32] Frd Din Fatima Saudia: ```K'ADDARA TAH!!!```

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹


~NAH~


*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_



_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_



```INA MATUK'AR JI DA KU, I REALLY LOVE SO MUCH```

*K'ADDARA TAH FANS GROUPS*

*KAINUWA WRITERS FANS GROUPS*

~IYA WUYA ANA MUGUN TARE~
```LUV U MORE MOST```

*COMPUTER SCIENCE GIRLS RONI EX-STUDENTS 2012 GROUP*


~I NEED UR PLAYER AM NOT FEELING WELL (AM SICK) SERIOUSLY~



```MY DEAR ALLAH YA BAWA OGA LAFIYA UBANGIJI YASA KAFFARA NE KARKI DAMU ALLAH NA NAN```
*(MRS MAKAMA❤❤)*



100-105



*EDITING BY MOMYN ZARAH*



Director ne zauna a office d'insa, daga gabansa kuma Abban Fauziyyah ne zaune, gefensa Fauziyyah ce zaune, ta sunkuyar da kanta k'asa gyara murya yayi ya kalli Abban yace " a zahirin gaskiya ban so sanar da kai halin da ake ciki ba, amma dole ne sai ka sani saboda kai mahaifinta ne, a hankali ya zaro wayar sa ya kunna masa video ya mik'a masa tunda Abban Fauziyyah ya fara kallon video zufa ke karyo masa fuskar sa ta jik'e sharkaf da hawaye kasa k'arasa kallon video yayi da sauri ya mik'awa Director wayar sa, yana cewa " Fauziyyah kin cuce mu, kin b'atawa zuri'ar mu suna har abada, kin kunya ta mu, kin watsar da tarbiyyar danayi miki, kin sa na yarda dake, ashe ke fasik'a ce, mazinaciya ce, kin yaudare mu ni da mahaifiyarki, da ganin wannan rana gwamma mutuwa t...... kasa k'arasa maganar yayi saboda kukan dayaci k'arfinsa.




Duk abinda akeyi Fauziyyah bata san ainahin laifin datayi ba, ba kuma tasan cewar ba aure sukayi da Fa'iz ba, cikin alamun mamaki fuskarta d'auke da alamar tambaya ta d'ago kanta ta kalli Abban ta da Director tace "meke faruwa ne? zubur mahaifin ta ya mik'e gami da shak'ar wuyanta, ya hau dukanta ta ko ina yana cewa " shegiya gwamma na kasheki na huta, ni zaki rainawa wayau, ni kike san k'ara yaudara, shegiya butulu, duk iyakacin k'ok'arina dana ke yi a kanku a she duk a banza ne, ganin yana niyar yin kisan kai ne yasa Director saurin mik'ewa ya rik'e shi " haba malam baka da hankali ne kabar ganin 'yarka ce wallahi idan ka kashe ta hukuma bazata kyale ka ba.




"To sai me? ai gwamma na kashe ta nima a kashe ni, wannan lalatacciyar yarinyar ina amfanin rayuwarta, " haba bawan Allah saikace dai ba musulmi ba, kamata yayi ka zauna muji ta bakinta, dan gaskiya a hankalin yarinyar na da tarbiyyarta baza ta tab'ayin aikin irin wannan ba, dan nayi bincike sosai a kanta babu wani d'alibi ko malami daya fad'i aibu ko wani mummunan abu a kanta, kowa ma yabanta yake, ni gaskiya ina ganin kamar akwai wata k'ullalliya a k'asa ka sani ma ko ba'a cikin haiyacin ta take ba, ko saida aka bugar da ita sannan.



Shiru Abban Fauziyyah yayi, kallanta Director yayi ya kira sunan ta, da kyar ta iya amsawa saboda kuka, tun shak'ar da Abban su yayi mata ta tsora ta, ta koma gefe ta rakub'e tana ta faman kuka, k'ara kiran sunan ta yayi, ya amsa yace " zo nan, a hankali cikin tsoro da rawar jiki ta je, video ya kunna mata ya mik'a mata, hankali kwance ta gama Kalan video tas, babu wani alamar tashin hankali a fuskarta, mamakinta d'aya yadda akayi har aka d'au video, kallanta Director yayi yace " kin san wannan yaron? " eh tace, "meye alak'ar ki dashi? a hankali tace "miji nane ta bada amsa kanta tsaye.




Da sauri Abban ta ya d'ago kai yace what!!! mijin ki? hannu Director ya d'agawa Abban Fauziyyah alamar yayi shiru, murmushi yayi irin na manya, alamar yasan da wani abu a k'asa, yace mijin ki, kamar yaya, ta ya akayi ya zama mijin ki? tun daga farkon had'uwarsu da Fa'iz ta kwashe ta fad'a musu, bata rage komai ba, kaf ta basu labari, har marin da tayi mishi, da kuma yadda ta ganshi 2days ago, "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai Abban ta yake maimaitawa, shiko Director kasa magana yayi, sai can ya d'ago kai yace " kaji ko ni dama nasan ruwa baya tsami banza, cikin tsananin b'acin rai da fushi Abban ta ya d'ago kai yace " ashe ke jahila ce, jaka, akuya tunkiya, iliminki na addini bai yi miki amfani ba bai k'are mu da komai ba, still Director ne ya k'ara dakatar dashi yace " haba yarinya ce fa she is 17yrs, kuma yayi amfani da basira, wayo, da tsoran da take dashi ne, shegen yaro ne yasan kansa sosai, kuma duk wanda ya girmeka ya riga ya girmeka, yayi amfani da basira ya cusa mata sanshi a ranta, kasan kuma so ko abu ba dai-dai bane yakan nuna dai2 ne, sannan yayi amfani da yarintar ta, yayi wasa da hankali ta da tunanin ta, ya had'a abin nana Hauwa'u da Adamu , ko babba ne za'a iya yi masa yawo da hankali, duk hankalin ko ilimin mutum idan akace maka yaro ne to kayi shiru kawai, musamman ma idan muka duba K'ADDARA.



Fauziyyah yarinya ce k'arama bata da wayewa ko gogewa irin ta yaran yanzu, shi kuma babbane tunda yakai 27yrs kuma wayayye ne d'an duniya ne, cikekken d'an bariki, ya fita komai na rayuwa ya kuwa zai kasa yi mata wayau, kallan Fauziyyah yayi yace " ya cuce ki, ya yaudare yayi miki illa yabar miki taban da har abada bazai gogu daga zuciyar ki, Fa'iz yaudararki yayi Fauziyyah ba aure kukayi ba wayo yayi miki yayi zina dake, ya cimma burinsa a kanki tsakanin ku babu aure, k'arya yayi, haka yayi tayi mata bayani yana kawo mata hadith gami da ayoyin Qur'an dan ta fahimmata sosai, sai da ya tabbatar ta fahimta
Showing 21001 words to 24000 words out of 70679 words