musu, sannan yayi musu bayanin da yayiwa Fa'iza na zubewar ciki, daga k'arshe yakai su har d'akin da aka kwantar da ita, yace "tun jiya bata farka ba, ina san ran nan da few minutes zata iya farkawa, yana kaiwa nan ya fita.



Ganin halin da Fauziyyah ke ciki ba k'aramin d'aga musu hankali yayi ba, musamman da duk fuskarta an rufe mata ne da bandegi, kuka sosai Mama da Aisha suke, shiko Abba kukan zuci yake, nan suka zauna suka saba gaba suna kallo Mama na sharar wahaye, a ranta kuma tana mai godewa Allah a bisa zubewar cikin.



Sai da su Mama sukayi 43mnts sannan ta farka tana cewa "wallahi baku isa ku keta min haddi ba, Fa'iza tsakani na dake Allah ya isa, muguwa azzaluma, wallahi dakuyi zina dani gwara na mutu, tana maganar tana haure-haure, can kuma sai ta fashe da kuka tana kiran Mama da Abba, Aisha tana cewa " ku yafe man, mutuwa zanyi wallahi ba laifi na bane, makirci aka shirya man, da sauri dukkan suka mik'e suka nufi wajenta, suna bin junan su da kallan mamaki da jin abinda Fauziyyah ke cewa, a hankali Mama ta rik'e hannunta wata irin ajiyar zuciya ta saki, a hankali Mama ta fara yi mata magana "Fauziyyah mune bud'e idonki ki gan mu, meke faruwa dake, Abba cikin rawar murya ya rungume Fauziyyah yace " bakiyi mana komai ba, mun yafe miki duniya da lahira, Allah yayi miki Albarka, jin maganar iyayen ta a kusa da ita yasa ta bud'e idon ta a hankali, dishi-dishi take kallon komai kafin idonta ya k'arasa bud'ewa.



Ido ta zubawa iyayen nata, sai kuma ta saka kuka, ganin haka ya tabbatar wa Mama da Abba akwai abinda ke faruwa, a hankali Mama ta zauna kusa da ita ta lallashe tayi shiru, Abba kuma ya kira doctor ya sanar dashi ta farka, duddubata yayi yacewa nurse din dake niye dashi " ki saka bata magungunanta, ya fuce, magungunan ta bata ta d'an tada ta zaune ta jingina mata pillow ta fita, Fauziyyah ta fara magana cikin muryar marasa lafiya "Mama ashe Fa'iza shaid'aniya ce muguwa ce ta k'ara fashewa da saban kuka, Mama da Abba duk ido suka zuba mata can Mama tace "yi shiru ki sanar damu abinda ke faruwa, a hankali Fauziyyah ta kwashe komai tun daga ranar da suka fara had'uwa da Fa'iz, har had'uwar ya Fa'iza, da labarin da Fa'iza ta bata na duk makircin da suka shirya mata, har zuwa kai ta gidan maza da tayi jiya, ta fad'a musu, kowa mamakin abun yake, cikin kuka da jirin da yake d'iban ta fara shin mik'ewa da sauri Abban ya mik'e ya zaunar da ita yace "me kike so?



"Abba wata alfarma zan rok'eka, "ina jinki Fauziyyah ya fad'a cikin muryar tausayi, hannunshi duka biyun ta rik'e tace " Abba dan Allah mubar garin nan, please Abba karka ce a'a, wallahi Abba bazasu tab'a kyale min rayuwa ta ta zauna lafiya ba, bazasu kyale mu mu rayu cikin farin ciki da walwala ba, basu kyale mana kwanciyar hankalin mu ba, sunta samu a cikin masiba kenan, please Abba mu canja gari, rayuwa, komai namu, jikin Abba da Mama ne yayi sanyi, Abba ya juya kalli Mama dake ta faman kuka, sunkuyar da kanta tayi, juyowa yayi ya maida hankalinsa kan Fauziyyah, a hankali ya fara zame hannun sa daga cikin nata, aiko gam ta k'ara rik'e hannun tace "dan Allah, wallahi wata rana gawa ta za'a kawo muku, karki damu Fauziyyah zamuyi magana da Mamanki tukunna.



A hankali ta saki hannun mahaifin nata ta koma ta kwanta idonta na zubar da hawaye,Aisha taje tana goge mata itama tana kukan idonta ta bud'e tana halin da Aishan ke ciki, cikin muryar kuka ta shiga girgiza mata kai tana cewa " please sister karkiyi kuka itama tana goge mata hawayen dake zubo mata, " to Aunty idan kina so na daina kukan kema ki daina, cikin kukan Fauziyyah ta rungume ta saki saban kuka, tace " please sister karkiyi irin abinda nayi nasa iyayen mu cikin damuwa, please kona mutu ke ki zame musu 1 tamkar da 10, ki share musu hawayen dana zubar musu please sister, iyayen na kallon su suma zuciyar su kamar zata fashe.



*BAYAN SATI D'AYA*


Kwana biyu kenan da sallamar Fauziyyah ta warke sumul, mahaifinta ya yarda da shawarata ta su canja gari da rayuwa, sun sayar da gidan su, da duk wani abu da suka mallaka a garin katsina kayan sawar su kawai suka bari, suka had'a kayan su, sun yanke shawarar komawa garin kano ta dabo tumbin giya, an sai gidan da daraja har 2.5 daya had'a da kayan daya sayar sai kud'in suka tashi 3 millions naira,kasancewar yau ne wa'adin su damai gidan zai cika yasa su shiryawa suka nufi bakin titi dan neman abin hawa zuwa tasha.



Fa'iz zaune gaban Momy duk ya fita haiyacin sa, dan tun ranar daya kawo ta hospital bata farka ba har yau, kasancewar basu da kowa shine zaune wajen ta ko yaushe baya fita ko nan a can, tari Momy ta fara yi tana kiran ruwa da gudu Fa'iz ya fita ya nufi office din doctor, shiga yayi ko sallama babu ya kira shi, shima doctor a guje ya fito, sai da suka k'ara duba ta sosai sannan, doctor ya bada umarnin a bata ruwa, a hankali Fa'iz ya d'ago ta ya shiga bata ruwan, sai da tasha sosai ya ishe ta sannan ya maida ruwan ya ajiye, yana ajiye ruwan sai ta fara tari da aman jini na fitar hankali, da gudu Fa'iz ya yunk'ura zai fita kirar doctor ta rik'e shi, a hankali ya dawo ya durk'usa a gabanta yace " Momy doctor zan kira, "no need ta fashi amsa, a hankali ta saita tarinta tace"Fa'iz ni tawa ta k'are, zan tafi inda kaima wata rana dole zaka je, Fa'iz kaji tsoran Allah, Fa'iz kaji tsoran Allah idan ka tuna da ni da mahaifinka dakai muke rayuwa yanzu duk ina muke, ka tuna mutuwa ka tuna kwanciyar kabari da hisabi.



Dan tarin ta k'arayi sannan taci gaba " idan mu mun fad'a maka gaskiya kak'i yarda to duniya zata fad'a maka, kuma fad'awar duniya bata da dad'i, Fa'iz ka tuna komai daren dad'ewa wata rana kai uba ne, kuma inba mutuwa da tsofa, Fa'iz ina baka shawara Fauziyyah ita ce matar data dace kai, itace matar da zata kaika aljanna, ita ce matar da zata fitar mana da jikoki d'aiyaban, itace hanyar shiriyarka zuwa ga mahaliccenka, domin Fauziyyah macen kwarai ce, duk wuya duk runtsi karka sake ka bari Fauziyyah ta kufce maka, duk wahalar da zaka sha karka rabu da ita, karka yarda wani ya shigo tsakanin ku balle har ya samu damar rabaku, Fa'iz babban buri na a duniya shine naga ka aure Fauziyyah ka mallaketa a matsayin mata, please son kayimin alk'awarin cika min birina yana kuka yace " nayi miki mom, murmushin k'arfin halin tayi tace " nagode son Allah yayi maka albarka, Ubangiji ya kare min kai ya tsare min kai ya shirya min, sai kuma ta d'an b'ata rai "me? Yace cikin muryar kuka.



" son sakan bana san shaye-shaye da neman matan da kake yi ko? kai ya d'aga mata saboda kukan sayaci k'arfinsa, shima kayi min promise har abada naka k'ara yin zina da shaye-shaye, cikin kuka yace "nayi miki alk'awarin ban k'ara d'aya daga cikinsu mom never after, murmushin jin dad'i tayi sannan taci gaba da kwad'aita mishi auren Fauziyyah, tana nuna masa amfanin auren.



"Itace mace ta gari da kowanne namiji ke burin samu, mace mai nutsuwa, kamala, hankali, hak'uri, juriya tunani, sanin ya kamata, kawaici, wallahi Fa'iz idan kabari kayi asarar Fauziyyah a matsayi matar aure kayi babbar asara, kuma wallahi sai kayi kuka da idonka ba baki nayi maka ba, Allah yayi maka Albarka, Ubangiji ya shiryeka kan tafarki na gaskiya, Allah ya baka mata ta gari, 'ya'ya na gari zuri'a ta gari, Allah ya sanya albarka a cikin rayuwarka, Allah ya nutsar min dakai, yasa maka hankali da sanin yakamata a cikin ruhinka. Nasiha mai ratsa zuciya da shiga da rai tayi masa sosai.



Tana cikin magana tarin yaci karfinta da gudu ya fita, amma kafin ya kira doctor rai yayi halinsa, ihu sosai yake yana buga kansa a bango, yadda kasan mahaukaci haka ya koma ya rungume gawar Momy a kirjinsa yana kuka kamar ransa zai fita.



Fa'iz na cikin 'yan zaman makoki bayan an kai Momy makwancin ta, sanye yake da farin yadi, idonsa yayi ja, saboda tsabar kuka, wani ya shigo yace " Fa'iz yanzu naga su Fauziyyah zasu bar gari wai har sun sai da gidan su ma, wata irin zabura yayi ya fita a guje ko takalmi babu yadda kasan mahauci gudu yake sosai a titin Allah........




*Alhamdulilah*



*MOMY'N ZARAH*



BYE
[05/09, 20:33] Frd Din Fatima Saudia: ```K'ADDARA TAH!!!```

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹


~NAH~


*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_



_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin Ζ™ai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_



*ZUWAIRAT (UMMU MARYAM)* πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£πŸ—£

```PLEASE INA CIKIYAR TA DUK WANDA YA GANTA YA TAIMAKA YA SANAR DANI```



_PLEASE KIYI HAK'URI HORON YA ISA HAKA MUN HORO, JIKIN MU YA GAYA MANA MUN TUBA, AYI MANA AFUWA PLEASE_ πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»



~NAYI MISSING NAKI~
😭😭😭😭😭



```I LOVE YOU SO MUCH FOR NO REASON, LUV YOU MORE MOST```❀😍❀😍❀❀


~AYI MANA AFUWA A BAMU~

*NA CUCE TA PLEASE*





*EDITING BY MOMYN ZARAH*



130-135



" Assalamu Alaikum cikin rawar murya ya amsa sallamar, bayan sun gama gaiwasa ne Fa'iz ya sanar da Director buk'atarsa, shiru Director yayi na wani d'an lokaci sai yace "maganar gaskiya Fa'iz bazamu iya baka Admission ba, saboda abubuwan da suka faru, nan Fa'iz ya shiga rok'onsa, yana had'a shi da Allah, "ok to in sha Allah zanyi maka k'ok'ari in sama maka admission a BUK dayake abokina na Director makarantar, "nagode sosai Allah yasa da alkhairi, Amin yace ya kashe wayar.



Malam kullum bashi da wata magana sai ta damun Abba akan yabar Fauziyyah taci gaba da karatu, shi kuma Abba ya kafi fir yak'i yarda, Malam Bala yayi da Abba amma Abba yak'i har Malam Bala yayi fushi dashi, shi kuma Abba ba abun ya fad'awa Malam Bala abinda ya faru ba, idan yayi haka kamar ya tonawa kansa asiri ne, hakan ne yasa dole ya kama bakin yayi shiru, amma ya k'uduri niyyar komai Malam Bala zaiyi bazai tab'a barin Fauziyyah ta k'ara ci gaba da karatu ba, Abba nan k'ofar shagonsa yana zancen zuci Malam Bala yazo zai wuce amma ko kallan Abba baiyi da sauri Abba ya mik'e ya bishi.



Rik'e hannunsa yayi yace " d'an uwa na fishi kake dani, kallon sa Malam Bala yayi yace " ina ni ina fishi akan abinda ba nawa ba, ba kuma ni da iko akai, Abba ya fahimci maganar Malam Bala murmushi yayi yace " kai ko kake da iko dashi, duk garin kano akwai wanda yafika iko da gida da iyalina, da sauri Malam Bala yace " bani da iko inda ina da iko na nemi alfarma a wajenka ka hana ni, Abba yace " wai ita Fauziyyahn ce tace maka tana san ci gaba da karatu?



"A'a ko d'aya ni naga ya dace da hakan saboda kewa da damuwa sai yayi mata yawa, ajiyar zuciya Abba yayi yace " ni da a san rai na nafi san nayi mata aure idan taje gidan mijinta sai tayi karatun acan, Malam Bala yace "kana da tabbacin auren wannan zamanin? da anyi haihuwa d'aya shikenan, mazan yanzu mayaudara ne, shiru Abba yayi, Malam Malam yaci gaba yanzu babu gatan da zakayiwa yaranka daya wuce ka basu ilimi mai zurfi, ga ba 'yan uwanta nan su Fatima ba, mai ya same su, Abba ko a zuciyar magana yake "hmmmm dazaka san meya faru damu dakaima ka tsorata, Malam Bala yace "inata magana ka kyale ni, Abba yace " ba shuru nayi ba ina jinka, ai matsalar ni ban san kowa anan ba bani da hanyar da zan samata , murmushi Malam Bala yayi yace " bakomai ka bani takardunta in sha Allah zanyi iya k'ok'ari na, "to kawai Abba yace yana share gumi Malam Bala ya lura da hakan amma yayi kamar bai gani ba.



Malam Bala yace " ai yanzu zamuje ka bani," to Abba ya k'ara cewa, ya wuce Malam Bala na biye dashi, sai da Abba ya shiga gidan shi kuma ya tsaya a k'ofar shagon saboda bai rufe ba, takardun Abba ya d'auko ya mik'awa Malam Bala hannu na rawa badan yaso ba, ya karb'a yana murmushi yayi Abba yace "nagode abisa mutumtani dakayi ka bani ragamar iyalinka, in sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi, kuma zakayi alfahari da hakan, shi dai Abba shiru yayi baice komai ba.



Malam Bala na tafiya Abba ya rufe shagon ya koma cikin gida a kicin ya samu Fauziyyah tana girki ya wuce parlor ya iske Momy zama yayi a gefenta ya zauna ya fad'a mata duk abinda ya faru tsakanin sa da Malam Bala cikin sanyin jiki tace " to Allah ya zab'a mana abinda yafi alkhairi, Ubangiji ya tsare mana ita ya kare ta, "Amin Abba yace, sai kuma ya kalli Mama yace " kema kin goyi bayan hakan!? cikin sanyin murya tace " a'a ba haka bane kawai ina jin tausayinta ne, in banda islamiyya da take bin su Aisha bata zuwa ko ina, kuma kasan ajin 'yan hadda take da'an gama karb'ar hadda shikenan idan ta dawo gida ta shige d'aki bata fitowa, mu kammu iyayenta kunyar mu take ji akan abinda ya same ta, shiru Abba yana sauraron Mama sai yace " bakomai K'ADDARAR TAH ce haka babu yadda zamuyi muyi, illa mu dage mu taya ta da addu'a.



Duk maganar da Abba da Mama keyi Fauziyyah najin su, wani irin farin ciki marar misaltuwa taji, nan take tayi sujjada ta godewa Allah, haka nan kuma ta dage da sallar dare da karatun Qur'an tana addu'ar Allah yasa a samu admission d'in, haka kuma ta dage da addu'a akan Allah ya tsare ta da fad'awa mugun hannu a karo na biyu, tun abinda Fa'iza tayi mata taji ta tsani k'awaye da maza kwata-kwata aure ko soyyaya basa gabanta, sai abu d'aya duk irin tsanar da tayiwa Fa'iz ta kasa mantawa dashi, da ta tuna maganar su da Momy sai taji gabanta yayi muguwar fad'uwa, sai dai kuma Sadik d'an Malam Bala ya hana ta sakat, tun ranar da Sadik ya ganta Allah ya d'ora masa bala'il santa, zuciyar sa ta hana shi sakewa, babu abinda Fa'iz zai nunawa Sadik sai dai farar fata da lulu eyes, sai dimples, amma shima Sadik ruwan tarwad'a ne dogo mai dogon hanci yana da k'irar zaki, irin su mata ke kira da handsome guy, dan shima kyakykyawa ne ajin farko, gaba d'aya ya hana ta sakewa da samun nutsuwa, da baya zuwa weekend sai k'arshen wata amma yanzu duk ranar Fridays yake zuwa, ko yaushe yana gidan su sallah kawai ke fitar dashi.



Sadik yaro ne nutsatstse ga hankali da wadatacciyar tarbiyya ga sanin ya kamata,ga wadataccen illimi boko da arabi, tunda Sadik yake bai tab'a soyayya ba sai akan Fauziyyah, Ita kuma tak'i bashi fuska, dayake 'ya'yana Malam Bala basu da iya da gidan Abba ya kama su Fauziyyah basu da iya a gidan Malam Bala, dayake akwai kyakykyawar fahimta a tsanin iyayen nasu, duk duniya Abba da Mama basu da wani d'an uwa daya wuce Malam Bala da Matar sa basu da wani dangi daya wuce 'yaran Malam Bala, haka ma Malam Bala da Ramatu basu da kowa sai Mama da Abba, kuma kowa yana ganin mutuncin kowa, duk hukuncin da wani ya yanke a gidan wani to ya yanku babu wanda ya isa ya canja.



*BAYAN WATA BIYU*



Cikin ikon Allah, Malam Bala ya samowa Fauziyyah admission a ABU ZARI'A, an bata low zata karanci BARRISTER, tayi farin ciki sosai duk da ba course din da take so aka bata ba, Fauziyyah na kwance a d'akin su, taji wayar ta tana ringing tayi mamaki sosai ganin bak'uwar number tunda ta canja layi babu wanda yasan layin ta daga Zainab sai Farouk dayake shi abokin tsamar tane, suna wasa sosai, dan idan kaji dariyar Fauziyyah to tana tare da Farouk ne, dan wani lokaci idan ya shigo gidan tun safe sai dare, idan kuma yana makaranta ya dame ta da waya, sai kuma Fatima ('yar malam bala dan yanzu itace k'awarta itama da kyar Mama ta shawo kanta ta yarda saboda nacin da Fatima keyi mata, dita yanzu Allah ya sani tsoran k'awaye takeji) sai da mama tayi mata fad'a sosai, sannan ta fara d'an kulata sama2.



Da sallama ta d'aga wayar jin muryar ta yasa shi lumshe ido, bai amsa sallamar ba sai da ta k'aratana jin muryar sa ta gane, ido ta d'aga ta kalli Mama aiko karaf suka had'a ganin Mama na kallanta ne ya hana ta kashe wayar, "ina yini? "lafiya lau my love, fuska ta k'ara b'atawa tace "ina jinka, nan fa ya shiga yi mata hira sosai, ita dai ta rasa yadda zatayi ita ba abin ta kashe ba Mama tayi mata fad'a shi kuma ya dameta zancen soyyaya duk sanda yace mata my Fauza sai taji gabanta ya fad'a dan haka Fa'iz yake kiranta, shiko ya dage sai zuba mata soyyaya yake yana yi mata shagwab'a wai bata sanshi bata kula shi, dan ya kyale ta tace "to yanzu me kake so ya Sadik, da sauri yace "zuciyar!!! Pls ki so ni, shiru tayi ta kasa magana dan yadda yake yi mata magana duk ya kashe mata jiki, cikin sanyin murya tace " to ya Sadik, yace" ai ba shikenan ba, kiyi min promise duk sanda nakira ki zakiyi picking call d'ina,
Showing 33001 words to 36000 words out of 70679 words