daki kud'in sa, tsaki yayi tace " ok nagode, mai ruwan ne ya bata tausayi a hankali ta kalli Sadik ta marairace face tace " please dear muje mu taimake shi, tayi maganar kamar zatayi kuka, murmushi yayi mata yace " Dear muje mu biya kudin, a kansa yana jin dadin halinta na tausayi da taimako, a ranta yake godewa Allah daya bashi daya a matsayin matar da zai aura, motar yaja zuwa wajen, glass din motar ya sauke yana hangen wanda zai aika, rasa wanda zai aika yayi dan haka ya kalleta yace " My love sai dai fa naje nadawo, mak'e Kafad'a tayi cikin shagwab'a tace " nidai a'a sai dai mu tafi tare, "ok yace, fita yayi motar ya zagaya ya bud'e mata motar ta fito a hankali, tun kafin ta gama fitowa sukayi ido hud'u da Fa'iz, kallon ta Fa'iz yayi ya bud'e baki zaiyi mata magana yaran ya wawuri kwalbar lemo ya kad'awa Fa'iz aka,gaba daya ganin sa ya d'auke, numfashinsa ma ya d'auke ya tafi luuuuuuu da k'arfi Fauziyyah tayi wata mahaukaciyar k'ara ta saki ihu tayi kansa tana kiran sunan sa FA'IZ!!!!!!!! kamar mahaukacin..........




*Alhamdulilah*



*MOMYN ZARAH*



BYE
[05/09, 20:33] Frd Din Fatima Saudia: ```K'ADDARA TAH!!!```

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹


~NAH~


*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_



_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_



*EDITING BY MOMYN ZARAH*


```DEDICATED TO FA'IZA ANFA```



175-180



Tayi kansa tana kiran sunan sa "FA'IZ!!! kamar mahaukaciya,da gudu tayi kansa tana zuwa ta faɗa jiknsa tana " please Fa'iz karka mutu kuka take sosai tana jijjiga shi, sandarewa Sadik yayi a tsaye ya kasa koda motsi saboda mamaki, wani baƙi kishi yaji yazo ya tokare masa ƙirjinsa, ya kasa koda ɗaga ƙafarsa balle yayi magana, wani irin yake gani baya jin maganar kowa a wajen sai maganar Fauza tana cewa " please Fa'iz karka mutu, ɗago kai Fauza tayi tana bin mutanen wajen da kallo tana kuka tace " dan Allah ku taimaka min karya mutu, ganin bamai niyyar taimakonta ne yasa ta rungume Fa'iz ta ƙara tsandara mahaukaciya ƙara ta ƙamƙame shi tana ihu, ƙarar da Fauza tayi ce ta dawo da Sadik daga duniyar tunanin daya tafi.



Da sauri yayi wajenta cikin sanyin jiki ya durƙusa ya rungumi Fa'iz haɗi da taimakon wasu mutane suka saka shi a mota bayan motar Fauziyyah ta shiga ta rungume Fa'iz tana kuka sai sambatu take ita bama tasan me take cewa ba, cikin mutuwar jiki Sadik yake tuƙin motar, kallon sa tayi ta daga mai tsawa tace " dallah Malam idan bazaka ja motar ba ka tsaya mu fita, cikin kuka da tsiwa tace " wallahi idan ya mutu bazan taɓa yafe maka ba, shiko Sadik jikin sa duk ya mutu, in banda faɗuwa babu abinda gabansa, wai yau shi Fauziyyah ke yiwa tsawa da faɗa akan wani ɗa namiji, ita ko in banda faman kuka babu abinda takeyi, ita bama tasan me takeyi ba, balle tasan tayi masa tsawa, a ƙofar wani private hospital yayi parking, kafin motar ta ƙarasa tsayawa ita har ta buɗe ta fita, a gigice ta shiga cikin asibitin tana kiran nurses, abaya suka biyo ta ɗauke da gadon turan marassa lafiya.



Da kyar Fauziyyah ta bari aka shigar da Fa'iz Emergency, tana kuka Sadik ya janye ta aka shigar dashi, shi duk jikinsa sa yayi sanyi, tsoro da fargaba sun dirar masa in banda kallon ta babu abinda yake shi ya kasa cewa komai da ido kawai yake binta, gana ganin yadda ta koma a cikin 'yan muntuna duk ta fita haiyacinta ta koma kamar zararriya, a ransa yace " tabbasa akwai al'amari mai girma tsakanin Fa'iz da Fauziyyah, kansa ya tambaya " koda soyayya suke, dan tabbas ko yaro yaga abinda Fauziyyah keyi sai ya tabbar tana yi masa mugun so, akwai tsantsar so da ƙauna a tsakanin su, a fili yace " no hakan ba baza ta taɓa yiyiwa ba Fauza tawa ce ni kaɗai, Fauza matata ce, haka dai yayi ta zance zuci.




Kasa jurewa kukanta yayi a hanakali ya janyo ta jikinsa ya rungume ta, kanta ya shiga shafa mata yana ɗan bubbuga bayan yana bata haƙuri, " kiyi haƙuri My Fauza in sha Allah zai warke bazai mutu ba kinji, a hankali ta ɗago jajayen idonunta ta kalle shi tace " please Yaya karya mutu bana san ya mutu idan ya mutu nima mutuwa zanyi, dammmmmm!!!!!!! gaban sa yayi muguwar faɗuwa, cikin rawar baki yace " in sha Allah bazai mutu ba zai rayu, sake kallan sa tayi tace " yawwa ka tabba ta zai rayu, bazai mutu ba? tayi maganar kamar an fizge ta daga bakin ta, kansa kawai ya iya ɗaga mata alamar eh, lamo tayi a ƙirjinsa tana sauke ajiyar zuciya, Doctor ne yazo yace " kece matar sa ko? ƙura mata ido Sadik yayi dan jin amsar da zata bayar, ji yayi kamar daga sama tace " eh nice, yace " ok to biyoni, kafin ya rufe bakin sa tayi gaba ta bishi, ɗakin da aka kwantar da Fa'iz ya nuna mata yace " Alhamdulillahi ya rayu, ba wasu cewuka sosai kawai dai kansa ya fashe, a hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga kwance ta iske, ido ta ƙura masa sai a lokacin ta lura yayi baƙi ga wata muguwar rama da yayi, duk ya janja kamanni kamar ba Fa'iz ba, kuka ta ƙara fashewa dashi ta faɗa kansa, ta rungume, ji tayi an dafa ta a hankali ta ɗago ganin Sadik tayi tsaye a kanta idonsa yayi mugun yin ja kai da gani kasan ransa yayi mugun ɓaci, kallon mamaki kawai yake yi mata, da ganin kallon da yake yi mata kasan na alamar tambaya ne , sai a lokacin ta rinƙa tuno irin abubuwan tayi ji tayi jiknta yayi sanyi, kuma taji bata kyauta ba, tasa lalle tayiwa Sadik babban laifi, kwata-kwata sai taji bata kyuta masa ba, tausayin sa ya kamata, dan ita batasan tayi wasu abubuwan ba dan bata cikin haiyacinta sai yanzu take tuno su,cikin jin kunyar sa, ta miƙe a hankli tace " muta f.... caraf Fa'iz ya riƙe mata hannu a hankali ya buɗe idon sa, ya kafe ta dasu rai ta ɓata ta goge hawayen dan ita bama tasan ya farka ba, tace " dalla sake ni, karka ƙara taɓa min jiki,ɗan iska kawai.



Ƙoƙarin miƙewa Fa'iz yayi amma ya kasa, komawa yayi ya kwanta dole badan yaso ba, yace " please karki tafi ki barni idan kika tafi kika barni a halin da nake ciki mutuwa zanyi Fauziyyah kece rayuwa kece gatana, kece komai nawa, please my Fauza kallon sa tayi, ta ɗanyi murmushi tace " aiko indai nice rayuwarka zaka mutu dan ni ina da miji, Allah ya bani miji na gari, wanda yasan ya kamata wanda yasan ciwon kansa da darajar kansa ya kuma san ƙimar 'ya'ya mata, kallon Sadik tayi, tayi masa murmushi tace "nagodewa Allah daya bani kai a matsayin miji na kuma uban yara na, ta juya ta kalli Fa'iz ta nuna masa Sadik tace" ni kuma wannan shine rayuwata, farin cikina, kuma shine komai nawa nima idan bashi mutuwa zanyi dan bazan iya rayuwa ba, yanzu ma da kaga mun taimake ka, ba'a san rai na bane, shine ya taimakeka dan idan tani ce abarka ka mutu kayi mutuwar titi mutuwar karnika, mugu kawai tana kaiwa nan ta kama hannun Sadik taja shi sukayi waje, Fa'iz ya fashe da kuka yana kiran sunanta, amma kota juya, ya rinƙa ƙoƙarin tashi amma ya kasa, yana ji yana ta tafi ta barshi.



Cikin sanyin jiki yake tuƙin motar, babu wanda yake cewa kowa komai motar tayi shiru, kowa da abunda yake saƙawa a ransa, ita Fauziyyah babu abunda ya dame ta sai kunyar abinda tayi sai satar kallon Sadik take taga ya shiga damuwa, shi kuma tunani yake abubuwan da tayi da kuma abunda ta faɗawa Fa'iz akan shi, a ransa yace "shin da gaske Fauza tana so na, da gaske tana alfahari dani, kuma wai nine rayuwarta, gabansa ne ya ƙara faɗuwa daya tuno abubuwan da tayi akan Fa'iz da kuma maganganun taka rinƙayi, da yadda ta koma zararriya, mahaukaciya, duk sai yaji bai gamsu da abubuwan ba, shi yanzu babu abinda yake so irin suyi magana ta fahimta ta buɗe masa komai ta kuma yi masa bayani dan babu mai fitar dashi daga cikin duhu sai ita.




A haka dai har suka ƙarasa gida a ƙofar fidan su yayi parking tayi mishi sallama cikin sanyi, ta shiga gida tana zuwa direct ɗakinta ta wuce ta faɗa gado ta saki kuka, a hankali tace " am so sorry Sadik nima ban san meke damuna ba, shima ɗakinsa ya wuce ya kwanta yana tunani daga ƙarshe dayaga bashi da mafita sai ya miƙa gaba ɗaya lamurran sa ga Allah, amma duk da haka yayi masifar tausayawa Fa'iz.



*BAYAN SATI ƊAYA*


Haka dai rayuwa tayi ta tafiya lokaci na ƙurewa Fauziyyah ta rayuwarta cikin farin ciki, sai dai bata cikin walwal tana cikin damuwa, ga bikin su na matsowa saura 3weeks, a ɓangaren Fa'iz kuwa kwanan shi uku a asibiti aka sallame shi, ya warke sumul, babu abunda ke samun sa sai matsananciyar damuwar Fauziyyah, kwata-kwata baya cikin farin ciki da kwaciyar hankali musamman ma tana faɗa masa Sadik ne mijin ta kuma har an saka musu ranar aure, kullum yana cikin kuka kamar ransa zai fita, baya iya ci baya iya sha, ya ƙara lalacewa, ya fita hayyacinsa, saboda tsabar tunani da damuwa koyaushe yana cikin matsanancin ciwon kai da ƙirji, sannu-sannu ciwon ya rinƙa yin gaba yana shiga jikin sa sosai.



Sadik kasa haƙuri yayi shi so yake kawai ya keɓe yayi magana da ita, ƙofar gidan su yaje ya kira ta a waya tana ɗagawa yace " ki fito ina waje, ya kashe wayar da sauri ta miƙe ta zuba hijab dan tunda wannan al'amarin ya faru bata ƙara ganin sa ba, cikin motar da shiga da sallarta, sallamar kawai ya amsa amma ko kallan ta baiyi ba yayiwa motar key, kallan sa tayi taga ya haɗa rai, bakinta ta kama bata ce komai ba, a ƙofar gidan sa yayi parking yace " Bissimillah, cikin sanyin jiki ta fito dan ba hali tayi mishi musu, saboda kwata-kwata face ɗinsa babu annuri.



Falon gidan suka shiga ya zauna, ƙin zama tayi takai wajen 7mnt a tsaye sannan ya kalle ta yace " ki zauna magana nake san muyi dake, cikin sanyi jiki ta zauna, shiru babu wanda yayi magana sai can yace " zan tambaye ki wani abu amma ina so kiyi man alƙawar zaki faɗa min iyakar gaskiyarki, bazaki ɓoye man komai ba, zaki sanar dani komai tsakanin ki da Allah, cikin sanyi tace " in sha Allah zan yi, "a'a ba haka zaki ce, cewa zakiyi nayi maka alƙawari zan faɗa gaskiya akan duk abinda ka tambayeni, shiru tayi kamar bazata amsa, sai kuma tace " nayi maka alƙawari duk abinda ka tambaye ni zan sanar da kai gaskiya, ajiyar zuciya yayi, cikin nutsuwa ya kalle ta yacd " waye Fa'iz? da sauri ta ɗago kai ta kalle shi ido suka haɗa dan shima ita yake kallo, yaci gaba da cewa " meye alaƙarki dashi, a ina kika sanshi wace irin dangantaka ce ke tsakanin ku, meye ainahin lamarin dake tsakanin ku?



Shiru bata bashi amsa ba, sake maimaita mata tambayar yayi amma taƙi yin magana, Fauziyyah ya kira sunanta amma bata amsa ba tashi yayi daga inda yake zaune ya durƙusa a gabanta yace " waye Fa'iz, waye shi a wajenki, meye dangantakar ku? kukan da take ƙoƙarin ɓoyewa ne ya kufce mata, kukan take sosai, tashi yayi ya koma inda yake zaune ya ƙura mata ido, sai da suka yi 30mnt a haka sannan ya sake yin ƙasa da murya yace " please ki faɗa min gaskiya, kinga da farko sai da kika ɗau alƙawarin faɗar gaskiya kuma kin san mahimmanci alƙawari, shiru dai tayi bata ce komai ba sai faman kukan da takeyi, miƙewa yayi tsaye yace " ok tunda bazaki faɗa ba, zanje na faɗawa Abba da Baba cewar kince baki so na kuma baki aure na ke Fa'iz kike so kuka shi zaki aura yana magnar yana fita daga falon, aiko da sauri ta miƙe ta riƙo shi tace " a'a please karkayi man haka zan faɗa maka, " ok yace ya dawo ya zauna, Shiru tayi bata yi magana ba sai kuka daya ci ƙarfinta, ƙoƙarin miƙewa ya somayi da sauri tace " Allah zan faɗa mamaka amma please kayi man alƙawarin baka taɓa gudu na iya wuya kana tare dani please ta faɗa riƙe da hannunsa tana durƙushe a gabansa, cikin mutuwar jiki ya daga mata kai, dan bai iya magana saboda gaba ɗaya jikinsa ya mutu ga gabana dayake ta faman faɗuwa yan bugawa da sauri, ya matsu yaji labarin, cikin kuka ta fara magana..................




*Alhamdulillahi*


*MOMYN ZARAH*



~PLEASE COMMENTS~🙏🏻
~PLEASE COMMENTS~🙏🏻
~PLEASE COMMENTS~🙏🏻



BYE
[05/09, 20:33] Frd Din Fatima Saudia: ```K'ADDARA TAH!!!```

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹


~NAH~


*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_



_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_



_DEDICATED TO_

*FATIMA MUKTHAR*
*(FATY'N KIYAWA)*

```MOMY NA TA KAINA ALLAH YA BAR ƘAUNA, UWA MABADA MAMA, INA ALFAHARI DAKE MUTANEN CHINA```

```INA MUGUN YUNKI SOSAI, IYA WUYA ANA MUGUN TARE```


~ONE LOVE~

❤❤❤❤❤



*EDITING BY MOMYN ZARAH*



180-185



Cikin kuka tace " he is my first love, shi na fara so arayuwata shine namiji na farko dana fara so na kuma fara saurara, at back time i really love him so much,I love him with all my heart, ban haɗa soyayyar shi data kowa ba, amma at the end he deceive me, & he cheating me, and he put me in the biggest troubles, but now I hate him, I really hate him, ta fad'a cikin kuka, jikin sa duk ya mutu yace " wanne irin abu yayi maki haka?



Kuka take sosai kamar ranta zai fita tace " please let past be past don't remember me, my previous life, I bag you, kasa magana yayi dan ya tambatar komeye yana da girma, cikin sanyin murya yace " please dear let me knew yours, ina san muyi sharing any problems between us, bata iya cemai komai ba illa kukan daya ci k'arfin ta, gaba d'aga kukan ta yasa shi fita daga haiyacin sa a gaban ta ya durk'usa ya ruk'o hannayenta yace.



" koma meye ya riga da ya wuce, yanzu raguwar mu ta gaba ya kamata muyi facing, & please dear you promise me, you can ever live me along we can also life 2geder and die, please dear karki barni bazan iya rayuwa bake ba please karki barni ya fad'a hawaye na zubowa daga idon sa, a hankali ta d'ago face ta kalle shi, sai tausayinsa ya kamata, cikin Kuka tace "I promis......., ji tayi gaban ta yayi muguwar fad'uwa, abinda ta tuno ne ya hana ta k'arasa maganar, muryar Momyn Fa'iz ta jiyo tana ce mata.



_Fauziyyah na baki amanar Fa'iz, kiyi min alk'awari zaki kula dashi har iya kar rayuwar ku, kiyi min alk'awari zaki zame mishi uwa kuma uba aranar daya rasa mu gaba d'aya, kiyi min alk'awari zaki raba shi da munayen halayen sa da munayen abokanan sa, da matan banza da shaye-shaye, kiyi min alk'awari zaki duk runtsi duk wuya bazaki taba rabuwa dashi ba, zaki zauna dashi zaki kula da rayuwar sa_


Fauziyyah ta tuno maganar ta da Momyn Fa'iz a ranar da taje gidan su Fa'iz yiwa Momy gaisuwa.



Cikin tunanin taji Sadik ya k'ara matse hannun shi cikin nata yace " please baby said it, hankali ta mik'e tsaye tana kuka sosai ta shiga girgiza masa kai tace " I cant zumbur shima ya mik'e binta yake da wani irin kallo na tuhuma yace " baby are you still love him? No kawai tace masa ta fita daga falon da sauri ya biyo bayan ta yana cewa please dear karkiyi min haka nima you are my first love, I don't want miss you please da gudu-gudu sauri-sauri take tafiya harta fita daga gidan, binta yayi ganin tayi mai nisa ne yasa shi dawowa ya d'auki key din mota ya bi bayanta, ita sosai take gudu tana Kuka.



A ganta yayi parking car dinshi ya fita da sauri bai tsaya yi mata magana ba ya rik'o hannunta ya danna ta a mota, ya figi motar, a wani silent place ya tsaya, shiru yayi baice mata komai ba,ya kura mata ido, sai da ya bari taci kukan ta sannan yace " dan Allah kiyi shiru kin san ban san Kuka ko?



Bata bashi amsa ba, Da kyar Sadik ya shawo kanta tayi shiru tabar kuka, sai da suka yi yawo sosai sannan ya tambatar hankalin ta ya kwanta, ya saka ta dariya da nishad'i sannan ya maida ta gida.



********************************


Su Fa'iza iskanci yafi uban nada dan yazo ya k'ara wayewa sosai ta samu bud'ewar ido, dan yanzu sun san manya sosai a k'asa suna da alfarmar ganin duk wani shege a k'asa kai tsaye, yan Nigeria ke basu kwangilar kisan kai ko kidnapping wani, idan mutan yana da matsala da wani har gida ake bawa su Fa'iza aiki suje su kashe shi, ko suyi masa kashedi, ko su b'atar da mutum b'at, aneme shi a rasa, babu kwangilar da ba'a basu, idan ka fito takarar siyasa wani ma ya fito to yanzu za'a basu aiki a b'atar
Showing 51001 words to 54000 words out of 70679 words