sauri yace " I will try my best doctor, so please help me, murmushin jin dad'i doctor yayi yace " in sha Allah zan taimakeka, yanzu tashi in taimaka maka kayi wanka, da taimakon sa yayi wanka yayi sallah yaci abinci.



Kafin 1 week da taimakon doctor Fa'iz ya murje yayi kyau yayi sumul, doctor ya zama tight friend din Fa'iz, dan tare suke yawa doctor yana d'auke masa kewa sosai, yana bala'il k'ok'arin akan Fa'iz, bayan Fa'iz ya warke an sallame shi, doctor ya tambaye shi ina ne gidan su, nan Fa'iz ya bashi labarin sa tun daga farko har k'arshe, amma bai gaya masa abinda ya shiga tsakaninsa da Fauza ba, doctor ya tausaya masa sosai, bayan ya tashi daga aiki ne, ya d'auki Fa'iz ya kaishi gidan su yayiwa Momyn sa bayanin komai, ita ta tausaya masa sosaiTa kuma k'arb'eshi hannu bibbiyu, da yake Momyn Doctor Adam mutance mai mutunci da sanin darajar dan Adam, sosai ta mutunta Fa'iz, yadda takeyiwa Adam haka take yi masa, in dai Doctor baya office to suna tare da Fa'iz tare suke zuwa ko'ina wani tym din ma har office, sosai Fa'iz yake jin dad'in zaman gidan su Adam.



Tunda abinda ya faru gidan ya zama kamar gidan makoki, kowa yana d'aki yayi jugum, ganin halin da gidan yake yasa Abba yanke hukuncin d'aura auren Sadik da Fauziyyah, Baba ya samu yake sanar dashi hukuncin daya yanke, murmushi Baba yayi yace " bakomai ai duk 'ya'yan ka ne, Abba yace " idan ka shiga ya sanar dasu za'ayi meeting bayan sallar la'asar, "to kawai Baba yace jikinsa a mace, Abba ya lura da yanayin Baban amma yayi kamar bai ma san yana yi ba.



Kowa ya hallara a babban parlon, Abba ya kalle Sadik yace " bud'e mana taro da addu'a, addu'a Sadik yayi suka shafa, Abba ya kalli Baba yace " Bissimillah, kayi musu bayani, gyaran murya Baba yayi yace " mun yanke hukuncin d'aura auren Sadik Da Fauziyyah, Aisha da Farouk, ranar asabar din nan mai zuwa in Allah ya yarda, yau lahadi kunga kenan saura kwana shida, satar kallon Fauziyyah Sadik yayi yaga ta zabura gaba daya ta gama fita hayyacinta, ya lura bata cikin farin ciki, duk ta zare, gashi tayi muguwar rama wayi bak'i sosai, ita ko Baba na sanar da d'aurin aurenta da Sadik gabanta yayi muguwar fad'uwa, da sauri ta d'ago kai ta kalli Baba, tayi rau-rau da ido zatayi kuka, Mama ma ita take kallo gaba d'aya hankalinta yana kan Fauziyyah, Aisha da Farouk duk sun sadda kai k'asa, alamar jin kunya.



Shiko Sadik ya k'urawa Fauziyyah ido, baya ko k'iftawa aiko karaf suka had'a ido, k'ok'arin kuka take a hankali ya shiga girgiza mata kai alamar kar tayi kuka, itama kai ya d'aga masa tayi masa murmushin k'arfin halin, duk abinda ke faruwa tsakanin su Abba da Baba na lura, ita ko Umma hankalin ta yana kan su Aisha, Baba yace " kunji ko? Duk suka amsa da " eh!, yace " idan da mai magana yayi, kowa yayi shiru, Abba yace " Shikenan ku tashi kuje Allah yayi maku albarka, duk suka ce " Amin, Fauziyyah na fita da sauri-sauri ta shiga d'aki ta fad'a gado ta saki kukan da take dannewa, a hankali ya shigo d'akin, zama yayi a bakin gado ya kasa cewa komai sai da yayi kusan 20 munute, itama bata daina kukan ba, ajiyar zuciya yayi ya kira sunan ta a hankali "Fauziyyah!!! Wani irin yarrrr taji dan Sadik bai tab'a kiran sunan ta kai tsaye ba, shiru tayi bata amsa ba, a hankali yace " please if u don't love me, just tell me, babu komai zan kuma fahimceki, dan ina sanki bazai sa na tauye miki hakki ki ba, zan baki damar ki ki rayu cikin farin ciki da wanda kike so, so please tell me d true, bata iya ce masa komai ba, illa kukan ta data ci gaba dayi, " fauza hakan ma amsa ce, na kuma tabbar da baki so na, in sha Allah zanje nayiwa su Abba bayani yadda ya kamata kuma nasan zasu fahimta.



Mik'ewa yana shirin fita da sauri ta mik'e tace" no yaya please karka fad'a musu komai nifa bance ban sanka ba, ta fad'a kanta a k'asa, hab'arta ya tallabo ya sunkuyo da faskarsa dai-dai tata ta kwaikwayi maganarta yace " to me kika ce? Murmushi tayi tace" kawai ina kuka rubuwa da Mama da Aisha ne fa, ta fad'a tana langwabar da kai gefe, " to kice kina so, " I love you dear, ta fad'a hawaye na zubo mata, murmushi yayi yace " I love you too baby, ya share mata hawayen yace " please stop cry, its pain me, ya fad'a yana dafe saitin zuciyar sa, dariya tayi tace " na daina, sai da ya lallab'e ta sannan ya fita zuwa masjid.



Yana fita ta k'ara fashewa d saban kuka ta durk'ushe, duk abinda ya faruwa tsakanin su Baba na kallon su kuma yana jin su, tausayin yaran ne ya kamashi, amma babu yadda zaiyi, bayan Sadik ya fito daga masallaci ya kira abokansa yana sanar dasu d'aurin auren sa, haka ma a watsa a media, a shafin sa na Facebook, Instagram, Twitter, WhatsApp, duk ya saka ya sanar yana gaiyatar jama'a, nan fa Mama da Umma suka shiga shirya Aisha da Fauziyyah magunguna sosai Mama ke ba Fauziyyah saboda tana matuk'ar tausaya mata da K'ADDARAR TAH, shiyasa ta dage dan ganin ta share mata hawaye, maganin matsi, maganin ni'ima, laushin da santsin fata, Umma ko 'yan maiduguri tayiwa magana suka zo har gida suka shiga gyara, ga abu yazo a kurarran lokaci dan ma da kud'i a hannu duk abinda kake so zaka samu duk yawansa, aiko nan da nan Fauziyyah ta canja tayi wani mugun kyau na fitar hankali ga fari, dama abinka da farar fata dirinta ya k'ara fitowa sosai, musamman hips da breast dinta, sosai kamarta da Ashwariyya rai ta fito.



Haka ma Aisha duk abinda akeyiwa Fauziyyah itama anayi mata maganin matsi ne kawai ba'a bata, saboda ita cikekkiyar budurwa ce, su kansu amaran sun san sun canja ga wata muguwar zuba da sukeyi wani lokacin ma Fauziyyah har pad (Always) take sawa, ga wani tsumi da Mama ke basu kullum, suma 'yan maiduguri suna bala'il k'ok'ari akan aikin su dan turare bak'aramin kama jikin su Fauziyyah yayi ba duk inda suka zaun ko suka shiga sai kaji yana kamshi, haka ma ko abu suka tab'a kamshin yake, suma sosai suke basu maganin mata.


Ranar juma'a ana gobe d'aurin auren, Fa'iz na kwance yana chart yaga abinda Sadik yayi posting a Facebook, aiko da sauri ya mik'e ya duba sosai, tabbas idonsa ba k'arya yayi masa ba gobe ne, d'aurin auren Fauzan sa da Sadik, da sauri ya duba Instagram, nan ma yaga yayi posting haka ma a Twitter, aiko zumbur ya mik'e yana cewa " ina dat is impossible, Fauza tawace ni kad'ai wallahi baki isa ki auri wani d'a namiji ba sai dai in bana raye, kai da ganin sa kasan kwata-kwata baya cikin hayyacin sa, da nutsuwarsa, jin abinda yake fad'a ne yasa Dr Adam mik'ewa yana cewa " what is going on abokina? kasa bashi amsa yayi sai wani dube-dube yake kamar zararre duk ya wani haukace, sosai hankalin Dr ya tashi, fita Fa'iz yayi Dr yabi bayanshi yana tambayar sa meke faruwa bai iya bashi amsa ba sai wayarsa daya mik'a masa, shima Dr ya firgita sosai da ganin gobe d'aurin auren Fauziyyah, gashi yanzu dare yayi wajen 9:30pm, kallon Fa'iz yayi yace " subhanallah, dare yayi yanzu gobe kuma 10:00am za'a d'aura aure, we are too late friend, ai Dr na fad'ar haka yaji kamar an zubure shi yayi waje yana sambatu da gudu, dan ji yayi kamar Dr ya watsa masa Acid, bin bayansa Dr yayi, duk kiran da Dr yayi masa bai tsaya ba sai a k'ofar gidan su Fauziyyah, Aisha da Farouk ya samu a k'ofar gida, da sauri ya nufe ta, yana zuwa ko sallama babu yace " where is she? kallan sa Aisha kawai tayi, bata ce masa komai ba, yace " please sister help me to call her, I need 2 see her please, sosai ya shiga rok'on Aisha akan ta kira masa Fauzan sa, kallon Farouk tayi , yayi mata kallon ok no problem, kallan Fa'iz tayi tace " kasan dai idan Abba ya sani bazai barta ta fito ba, so u hv 2 be take care, dan yanzu ma k'arya zanyi ince inji mijinta ne Sadik, ji yayi kamar saukar aradu a k'irjinsa jin an kira Fauzansa matar wani a gabansa, a tsakar gida ta wuce Abba da Baba suna cin abunci kasancewar ba nefa.




D'aki ta shiga ta samu Fauziyyah tace " Aunty wai kizo inji Yaya, "to kawai Fauziyyah tace dan ita a zaton ta Sadik ne tace " yana ina? yana waje, tare suka fito tana fitowa wata mota ta dalle mata fuska, ai ba Fa'iz ba kad'ai har Dr sai da gabasa ya fad'i dan sun tsorata da mugun kyan da tayi, dan shi Dr a zaton sama aljana ce, ganin Fa'iz na nufarta yasa Dr rik'e yace " kai wai baka da hankali ne aljana ce fa, tunda kake ka tab'a ganin mai irin kyanta a zahiri, murmushi Fa'iz yayi yace " she my Fauza, she d 1 I love, kamar dolo Dr ya saki Fa'iz shi bai ma san mai yake ba baki bud'e yana kallon Fauza ajiyar zuciya ya sauke yace " wowwwwww she so beautiful, Fa'iz dole ka haukace a kanta harka kamu da ciwon zuciya.



A gabanta ya zube da sauri ta sunya ta tallafo shi tace " dear lafiy........ Maganar ce ta mak'ale mata had'i da muguwar fad'uwar gaba a lakacin da tayi arba da fuskar Fa'iz.......


*Alhamdulillah*



*MOMYN ZARAH*


BYE
[05/09, 20:33] Frd Din Fatima Saudia: ```K'ADDARA TAH!!!```

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹


~NAH~


*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_



_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_



```DEDICATED TO```


*SAMEENAH ALIYOU*
_(A DUNIYAR MU)_



*EDITING BY MOMYN ZARAH*



190-195


Wani mahaukacin ihu Aisha tayi, tayi kansa tana kuka " please karka mutu idan ka mutu Aunty na bazata iya jure rashin ka ba, itama mutuwa zatayi, ganin baiko motsa ba illa dafarar dake zuba a bakin sa, yasa yin waje tana ihu, " Abba please ku taimake wallahi mutuwa zaiyi idan ya mutu Aunty ma mutuwa zatayi, ko kallan ta Abba baiyi ba, sai Baba ne yace " subhanallah ya juya direct doctor office ya nufa, da gudu nurses suka d'auke a gadon marasa lafiya sai Emergency.



Da kyar Aisha ta bar asibitin sai da Abba ya b'ata mata sannan suna shiga gida Fauziyyah ta jiyo kukan Aisha da gudu ta fito, tana tambayar ta lafiya, cikin kuka Aisha ta fad'a jikin ta, murya na rawa tace " Aunty Fa'iz ya mutu..... Wani irin ihu ta saka wanda kusan duk unguwar kowa yaji, kanta ba d'an kwali tayi waje da gudu tana ihu kamar zararriya, duk ta fita haiyacinta Abba da Baba, Mama, Umma ido kawai suk bita dashi duk sun kasa magana shiko Sadik mutuwar tsaye yayi, saboda tsabar rud'ewa,dakyar yake iya jan numfashi, gaba d'aya duniyar tayi masa nauyi, kansa sai juywa yake, bibbiyu yake gannin komai, baya jin komai a kunnuwsa sai shuuuuuuuu.



Kafad'ar Sadik Aisha ta kama ta shiga girgiza shi tana kuka" please yaya ka taimaka Aunty fa ta fita kar tayi wani wajen takai 3mnts tana yi masa magana amma bai ma san tana yi ba, sai data girgiza shi karfi ta sakar masa kuka sannan ya dawo haiyacinsa, cikin firgice yake kallon Aisha yana jin abinda take fada yana kuma tuno abunda ya faru, Aiko da gudu ya fita ya bi bayan ta, dakyar ya gano ta a titi tana ta shara gudu kamar mahaukaciya bata san inda kanta yake ba, batasan inda take nufa ba, saura kiris mutu tabi ta kanta cikin zafin nama Sadik ya rik'o ta ta fada jikinsa, suka zube a k'asa, k'uuuuuuu mai motar ya taka birki, a hankali ya mik'e rik'e da hannunta yayi gida da ita, itako binshi kawai take dan kwata-kwata bata cikin haiyacinta.



Yana shiga gida rik'e da hannunta bai tsaya ko ina ba sai da d'akinta a bakin gado ya zaunar da ita, ya mik'e ya d'auko mata ruwa ya bata tasha ta sauke ajiyar zuciyar, kusa da ita ya zauna ya jawo ta jikinsa ya rungume ya kwantar da kanta a kan kirjinsa, kawai shima sai ya fara kuka, dan sai yanzu ya tabbatarwa kansa san masu wani yake, sai yanzu yasan kwata-kwata Fauziyyah bata sanshi, gangan jikinta kawai ke tare dashi ruhinta yana ga Fa'iz, sai ya tausayawa kansa, a hankali ta d'ago kai ta kalle shi, cikin sanyin murya tace" yaya kuka kake?


Murmushin k'arfin hali ya k'ak'aro, ya girgiza mata kai alamar a'a, kanta ta k'ara mayarwa cikin k'irjinsa ta kwantar tace " yanzu yaya shike nan Fa'iz ya mutu tayi magana kamar ana fisgarta daga bakin ta, shiru yayi dan bai san amsar da zai bata ba, dan shi kanshi bashi da tambaci akan rayuwar Fa'iz ko mutuwar sa, kanta ya shiga shafa mata yana d'an bubbuga mata bayan ta, a haka har wani wahalallan barci yayi gaba da ita badan ta so ba, yana ganin tayi barcin ya mik'e ya kwantar da ita a hankali ya fita.




Yadda yabar kowa haka ya same su, illa Umma data tafi gida sai Mama data shiga d'aki, anan ya iske Abba da Baba sai Aisha dake ta faman kuka, a tsaye, kai ya sunkuyar zai fita, a hankali Abba ya kira sunanta, tsayawa yayi cak, dan shi kwata-kwata bai so hakan ba so yayi a kyale shi kawai ya tafi yayi jinyar zuciyar sa, da kyar ya amsa Abba yace" kayi hak'uri Sadik nasan kana da mutuk'ar hak'uri kuma kana mugun san Fauziyyah in sha Allah Fauziyyah bata da wani miji dana wuce kai koda bayan rainane, na baka amanarta, ka kula da ita, karka kula da duk wannan abubuwan dake faruwa, ni ne dai mahaifin Fauziyyah kuma na baka ita duniya da lahira idan Fauziyyah ta auri wani namiji bakai ban yafe mata ba, sai dai idan kaine kace ka fasa aurenta ko baka santa, cikin sanyin jiki yace " nagode Abba, ya fita shima Baba jiki ba kwari ya fita yayi gida, koda Sadik ya shiga gida d'akinsa ya wuce ya fad'a katifarsa ya saki kuka mai ban tausayi.



Jikin Mama a sanyaye ta zauna kusa da Abba, shima cikin mutuwar jiki ta d'ago kai ya kalle ta yace " Maman yara ya akayi ne? shiru ta d'anyi sai tayi ajiyar zuciya tace" Abba ni kuma sai nake kamar muyi tunani kar muyi gaggawa kar muyi abinda zai dame mu, "kamar me fa? cewar Abba, " ina ganin kamar idan akayi auren Fauziyyah da Sadik a halin da ake ciki akwai matsala, kar muyi abinda zai zo ya damemu daga baya, kaga mune masu 'ya mace duk abinda zai faru mune a k'asa, kuma mutanen nan sunyi mana halaccin da ko d'an uwan mu bai mana ba, kar mu had'a auren Fauziyyah da Sadik azo asamu matsala zumunci yazo ya lalace tunda ni da kai da shi kanshi Sadik da kowa ya tabbatar da Fauziyyah bata san Sadik, Fa'iz take so, kada azo ayi aure a rink'a samun matsaloli har komai ya lalace.



Kuma ni ina ganin yanzu Fa'iz ya shiryu, duk inda ake neman mutumin kirki yakai, ya zama malami makaranci kuma kowa shaida ne akan irin mugun son da yake yiwa Fauziyyah, ji fa mawuyacin halin daya shiga akan 'yar mu, mu tausaya masa mana, mu duba yadda ya koma, duk a kanta yace bashi da kowa sai mu sai Fauziyyah yace ita ce kowa da komai nasa, ni dai a gaskiya ina ganin gwara a bashi a barsa ya k'arasa b'arnar da yayi, ba sai mun tonawa kanmu asiri ba, hakan ma kad'ai na iya haifar da matsala, rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a zaman takewar auren su, kasan fa budurci mahimmin abu ne mafi girma arayuwar mace da aurenta, amma dai yadda ka gani ni dai shawara ce tawa, duk maganar da Mama keyi Abba ya k'ura mata ido baya ko k'iftawa, ita ko tak'i fasawa harda saida takai aya, shiru duk sukayi sai Mama ce tace " Abban yara ko baka ji nane, murmushin su na manya yayi yace " duk naji, amma indai ni ne mahaifin Fauziyyah to bata da wani miji sai Sadik,Shiko Fa'iz abinda yayi ne a rayuwar sa yake girbar abinsa, ai dama ita duniya ta gaji haka, kamar yadda Fa'iz yake tak'amar yana san Fauziyyah haka Sadik yake santa shima, haka ma ya fad'a masa a gaban mu (duk yadda kake ji akanta nima ina jin fiye da haka) ki duba halin daya shiga yanzu duk ya fita haiyacinsa, kuma ma ai da kunya na kalli idon Malam Bala nace masa na fasa bawa d'ansa auren 'yata Fauziyyah, dan dai ku mata baku da hankali da kara akan 'ya'yan ku, ai mu muna dashi, wallahi koda mutuwa zatayi idan ta aure saita aure shi sai dai ta mutu,wallahi Allah koda shi da kansa Sadik din ne yace ya fasa bai isa ba, Mama zata k'ara yin magana Abba ya d'aga mata hannu ya dakatar da ita yace " ya isa na riga na gama yanke hukunci.



Shiru Mama tayi bata kuma magana ba, ta mike ta fita tabar mai dakin ya bita da kallo a ransa yana mamakin irin sankai na mata a kan yaran su, saboda san da iyaye mata suke
Showing 57001 words to 60000 words out of 70679 words