" ai dama na fad'a maka ka guji sharrin mace musamman ma 'yar bariki, kai da a tunaninka na kyaleka ko na manta da abubuwan da suka faru ko ka d'auka nima Fauziyyah ce da babu abinda zan iya sai canja gari , Fa'iz ai dama na fad'a maka akwai ranar kin tashi lafiya k'in dillacin ,maganar Fauziyyah ce ta fad'o masa


_"Allah ya isa tsakani na dakai Fa'iz,in sha Allah sai kayi danasi a ranar da bata da amfani ,in sha Allah sai ka wulak'anta ta yadda kai kanka bazaka iya gane kanka ba, wad'annan abokanan naka da suke zagaye dakai duk kansu munafukanka ne,azzalumanka, babu komai a zuciyar su sai munafurci da mugun abu........_


Wani mahaucin k'arfe Salim ya buga masa a kansa,nan da nan kan ya fashe jini yayi tsartuwa,kamar jira suke gaba d'ayan su suka rufe shi da duka ta ko'ina basu kyale shi ba sai da kuka yi mai tsinannan duka sukaga baya motsi,sunkuyawa Salim yayi ya kara hannunsa a hancin Fa'iz yaji baya nunfashi kunne yasa a k'irjinsa yaji zuciyarsa bata buguwa yace " mun kashe shi,zubar da makaman hannunsu sukayi suka shige mota sukayi tafiyar su suka bar gawarsa anan...........



*Alhamdulillah*



*MOMYN ZARA*



*ZAN TSAYAR DA TYPING NA KWANA 2 SAKAMAKON RASHIN COMMENTS D'INKU DA BANA SAMU NASO K'ARASA MUKU LABARIN KAFIN HAJJI,AMMA ALLAH YA SANI KUN B'ATAMIN RAI NAYI MAGANA HAR NA GAJI KAD'AN KE KAWAI KE COMMENTS*



~MASU YIN COMMENTS NAGODE SOSAI~


BYE
[05/09, 20:33] Frd Din Fatima Saudia: ```K'ADDARA TAH!!!```

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹


~NAH~


*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_



_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_



*EDITING BY MOMYN ZARAH*



140-145



Abba na driving yayi zashi gida ,fitilar motar sa ce ta haska masa wani abu a kwance cikin jini kamar mutum ,har ya wuce sai yaga kamar abin yana motsi a hankali yayi parking motar sa ya fito ,mutum ya gani yayi jina-jina cikin jini,d'an ja da baya Abba yayi gaban sa ya fad'i dan ya d'an tsorata ,motar sa ya koma yaja ya tafi ,har yayi d'an nisa sai yaji gaban sa na fad'uwa sai yaga kamar bai kyauta ace yaga mutum cikin jini halin rai ko mutuwa amma yak'i taimakarsa sai ya tuna ranar daya fara shigowa kano shima ,a hankali ya karya kan motar sa ya koma ,da kyar da taimakon wasu mutane suka saka Fa'iz a mota,Abba yace "pls kuma ku shiga muje hospital d'in tare dan kuyi min shaida "ah to bakomai inji wani mutum daga cikin mutanan,dakyar Doctors suka karb'i Fa'iz,aka shigar dashi Emergency room,godiya Abba yayiwa mutanan,sannan suka tafi,wayarsa ya zaro ya kira Baba yake shaida masa abinda ya faru.



Anan Baba yazo ya sami Abba jikinsa shima duk jini,da gudu Baba ya k'arasa inda Abba yake yana k'ara tambayar abinda ya faru,ya bud'e baki zai bashi amsa aka fito da Fa'iz daga emergency aka tura gadon zuwa wani d'akin a baya suka busu,Doctor ya kira su Abba zuwa office,anan doctor yake shaida musu ya samu buguwa sosai amma sun bashi duk wani taimakon gaggawa daya kamata ,amma bazai farfad'o ba sai nan da bayan sati d'aya, "innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Abba yace ,Baba yace " to yanzu wazai zauna a wajen sa ? " a'a badamuwa acikin ma'aikatan mu zamu samu wanda zai rinka kwana dashi in sha Allah,duk wani abu da ake buk'ata su Abba ne suka biya kud'in sannan suka tafi gidan,a hanya ne Abba yake bawa Baba labarin duk abinda ya faru,bayan sunje gida nan ma yake bawa Mama labarin komai.



Washe gari da misalin k'arfe 11:30am Abba,Baba,Mama,Umma suka shirya gaba d'ayan su suka nufi hospital ,direct d'akin da aka kwantar da Fa'iz suka wuce Doctor da nurses suka samu suna duba shi ,aka yi masa allura aka saka masa k'arin jini,hunnu Doctor ya mik'awa Abba da Baba suka gaisa sannan suka ya fita ,da yake jiya da daddare akayi komai Abba bai ga fuskarsa ba sai yau ,ji yayi tausayin Fa'iz ya kama shi farat d'aya kuma yaji k'aunarsa ta shige shi a hankali ya shafa kansa yace " Allah ya baka lafiya,"Amin ,amma duk yadda akayi yaron nan ba bahaushe bane,dan yafi kamata da Indian,cewar Baba ," gaskiya nima haka nake tunani kuma duk inda ya fito daga babban gida yake dan da ganinsa kasan daga gidan arziki yake ba gidan tsiya ba ,sun kai 30mts sannan suka tafi.



Rayuwa na tafiyarwa Barrister Fauza da Farhan yadda ya kamata,yani mugun so da kulawa Farhan yake bata ,ko k'uda bai kaunar ya tab'a masa BFauzan sa itama a hankali taji ya fara shiga ranta yana ratsa mata ko'ina na jikin ta kai har cikin jininta tana jinsa da yake Farhan mutum ne mai surutu da barkwanci ga wasa da dariya gashi da kyawawan halaye bashi da girman kai ko nuna isa idan ka ganshi bazaka tab'a cewa d'an gwamna bane, dan rayuwar sa yake cikin hankali da nutsuwa,haka ma a b'angaren Sadik kullum sai sun yi waya kusan sau 3 ,wani mugun so yake mata wanda ita kanta ta kasa gane wanne irin so Sadik ke yi mata,kusan kullum sai yayi mata kuka wai ta kular mishi da kanta ,wai ga missing d'inta yana samunsa in banda ta hana shi da tuni yayi zuwa yafi a irga,ita kanta ta kasa gane wa tafi so tsakanin Sadik da Farhan,amma acan k'ark'ashin zuciyarta tana jin wani abu wanda ta rasa menene data tuno Sadik ko Farhan sai taji gabanta yayi muguwar fad'uwa kirjinta na bugawa da sauri ta rasa mai yasa take jin haka.



Haka zalika da wani daga cikin so ya kira ta da suna FAUZA MY ko FAUZA ko idan wani daga cikin su yayi mata maganar soyayya (dad'ad'an kalamai) sai taji gaba d'aya ta rasa mai yake yi mata dad'i hankalinta ya tashi wani abu yana taso mata daga zuciyarta ta rink'a jin k'unci tana san sanin dalili amma ta rasa,data rasa dalili sai ta mik'a lamuranta ga Allah ta dage da addu'a,dan gaba d'aya a 'yan kwanakin nan ta rasa mai ke damunta tana yawan jin fad'uwar gaba,tanaji a jikin ta kamar wani abu ya faru da ita.



" _TO MUDAI SAI DAI MUCE ALLAH YA KYAUTA,KO ME YAKE DAMUN BARRISTER FAUZA OHO_



Haka ma a b'angaren Sadik shima yana jin irin yanayin da Fauziyyah ke ji,haka yana cikin irin halin da take ciki gaba d'aya ya rasa mai ke damunsa kwata-kwata baya cikin kwanciyar hankali ga wasu mugayen mafarkai da yake yi akanta, yana yawan yin mafarkin wani ya kwace masa Fauzansa ko kuma suna zaune a wani lambu mai kyau suna hira wani yazo ya tsaya a kansu sai yaci gaba da tafiya kawai itama B FAUZA sai ta mik'e tabi bayansa, ko yana wayan ganin taran d'auren auren Fauza amma wai bashi bane angon ba kuma duk mutum d'aya yake gani amma ya kasa gane fuskarsa.



Yaune wa'adin Doctor zai cika,tun safe Abba da Baba suka zo amma har wajen 4:00pm Fa'iz bai farka shima doctor yayi mamaki kwarai da gaske,allurai akayi masa aka saka masa oxygen ba'afi 1hr da samai oxygen ba hannunsa ya fara motsi da gudu Abba ya ruga ya kira doctor tare suka shigo da doctor d'in a hankali Doctor ya cire masa oxygen,aiko nan take ya fara tari sai da tarin ya lafa sannan ya bud'e idonsa a hankali yake bin d'akin da kallo kamar marar hankali,wani irin abu yake yi daka kalle shi kasan baya cikin hankalin sa,ba'afi 1hr da farkawarsa ba ya fara surutai marasa kan kan gado,kasa motsi Abba yayi sai Baba ne yayi k'arfin halin zuwa kiran doctor ,bayan doctor yazo ya dudduba shi ne ya kalli su Abba yace " please kuyi hak'uri ya samu tab'in hankali "kamar ?ya cewar Abba " kwantar da hankalinka inyi muku bayani, sakamakon dukan da akayi masa da k'arfe akai shine ya jawo masa haukacewa mu godewa Allah ma da bai mutu ba dan da gani san kashe shi akayi ba,bawai a iya illatawar aka so tsayawa ba gaskiya.



" Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un yanzu doctor meye abinyi ? "Eh to gaskiya yanzu bazamu iya sani ba ,amma zamuyi iya k'ok'arin mu dan ganin ya dawo hankalin sa, "nan da wane lokacin kenan? " magana ta gaskiya bazamu iya sani ba amma a kalla zai iya kaiwa 6mnts, kuma koda anyi hakan ma dakyar zai dawo normal kamar yadda yake a baya, "to yanzu doctor ina zamu nemo iyayensa ko danginsa?



"Sai dai ku d'auki photo nasa ku kai gida TV da radio ku bada cikiya ko Allah zai sa a dace,cikin sanyin jiki Baba yace " anan asibitin zaku barshi ko zaku kai shi na mahaukata? " a'a anan zamu barshi muma muna da secretary's (asibitin mahaukata),jiki ba gwari su Abba suka koma gida,kamar yadda Doctor yace haka su Abba sukayi amma an rasa iyaye ko dangin Fa'iz.


Su Fa'iz kuwa an samu duniya ana cin duniya da tsinke ita da abokanan Fa'iz na da rayuwar su sukeyi cikin jin dad'i da kwanciyar hankali in banda k'ara'in hulewa babu abinda suke yi ansanya dukiya gaba anacinta ba kama hannun yaro,yau ana Abuja gobe ana Lagos kullum ana yawan clubs asha giya fa kayan maye mazan su nemi mata ita kuma ta nemi maza in banda yad'a fasadi da anfasha babu abinda sukeyi a doran k'asa da mahaifinta ma ya nemi takura mata rashin kunya tayi mishi ta tara mishi mutane sannan ta kwashe kayanta ta bar gidan mahaifiyarta na kuka tana kama k'afarta ta fisge tayi ball da ita tayi tafiyar ta tabar iyayenta cikin k'unci da takaici ga kunyar jama'ar unguwa,haka dai Fa'iza ke rayuwa cikin jin dad'i da kwanciyar hankali ga daula an samu yanzu ta zama big gal ga kud'i ga kyau ga iskanci.




*BAYAN WATA SHIDA*
_(6 MONTHS LETTER)_



*Alhamdulillah*



*MOMYN ZARAH*



```LOVE YOU SO MUCH MY FANS```💋💋💋


_ONE LOVE ME & YOU_❤❤❤


💋💋💋💞💞💞



~BYE~
[05/09, 20:33] Frd Din Fatima Saudia: ```K'ADDARA TAH!!!```

🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹


~NAH~


*HAUWA A USMAN*
_(JIDDARH)_



*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
_(DASHEN ALLAH)_



_Bismillahir rahamanir rahim, da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai, godiya da yabo sun tabbata ga Ubangijin sammai da K'assai_



*SADAUKARWA GA*


*MAIMUNA MATAR ABDULLAHI*

*' YAR MUTAN NIGER*


*IYA WUYA ANA MUGUN TARE*


_ONE LOVE MATAR ABDULLAHI_



*EDITING BY MOMYN ZARAH*



145-150



*AFTER SIX MONTHS*



BFauza ana rayuwa mai dad'i sai dai missing d'in gida daya dameta kullum tana cikin waya da 'yan gida,ga Sadik daya sako ta a gaba kullum bashi da wata magana sai ta auren su ,kullum cikin gaya mata irin sanda yake mata yake ,yana bata amanar kanta,haka ma abin yake a b'angaren Farhan yana bata kulawa ta musamman duk inda zasu ce tare suke zuwa sai dai shi har yanzu ya kasa difowa ya fad'a mata yana Santa.



Yau da misalin k'arfe 11:30am na k'asar America BFauza na kwance sanye da 3quarter da best mara hannu tana waya da Sadik yana tayi mata rigima kamar k'aramin yaro tace " please habibty kayi hak'uri ba sai ka zo ba yanzu fa nayi 7mnts " to wai mai yasa baki san nazo kullum nace miki zanzo sai ki rink'a hanani why? sweet ba haka bane ina duba maka wajenka aikin kane nima ina san ganinka amma kodan su Abba da Baba ai mayi kawaici ko? " ni dai ba wani nan ya fad'a da muryar shagwab'a,dariya tayi tace "please habibty kayi hak'uri ni wallahi kunyar su Baba nake ji ,kuma ace ni ka biyo ni ban san iyayen mu su zarge mu kasan zuciya bata da k'ashi.



"Ba wani nan kedai wayau kawai kike san yi man,dariya tayi ta gyara kwanciyar ta da gani kasan tana jin dad'in wayar tace " to naji my love ni dai ka bari ban so , " dariya shima yayi yace " ko kina gudun kar nazo na maimaita abin nan da nayi miki? dariya tayi ta kashe wayar ,wayar yabi da kallo yayi dariya yace "matsoraciya kawai,itama dariya tayi tana kallon wayar ,tana d'aga kanta suka had'a ido da Farhan idonsa yayi ja kamar wuta duk da A.c. dake d'akin gumi yake yi ita kanta ta yi muguwar tsorata da ganin yanayin daya shiga da sauri ta mik'e ta nufe shi ita ta manta da kayan dake jikin ta ,ta manta da kashedin shigo mata d'aki kai tsaye ba excuse.



"Lafiya Friend da yake haka suke kiran junan su,ji yayi kansa ya sara a ransa yace " yanzu ta gama cewa wani habibty,my love,sweet amma ni wai Friend d'ago jajayen idonsa yayi ya kalle ta yace " dawa kike waya ya fad'a kamar an fizgi maganar ,kallonshi tayi tace " kamar ya dawa nake waya ,tsawa ya daka mata yace " ba tambayar ki nake ba ,nace dawa kike waya ? gabanta ne ya fad'i tsoro ya kamata jirin ya d'auki rawa da sauri ta ja baya ,biyo ta yayi tana baya yana binta har suka kai bango yace "bazaki ban amsa ba ?



Murya na rawa saboda tsoro idonta yayi ja itama tace "Ya Sadik ne' "waye shi a wajenki? shiru tayi ,shak'o wuyanta yayi ya matse ta a bango yace " bazaki ban amsa ba?"shi ne wanda zan aur.........! ai bata k'arasa ba ya sake ta yayi baya taga-taga zai fad'i da sauri tayi wajen sa zata rik'e shi ya sake daka mata tsawa yace "stop ur rubbish,don't ever try to touch me,a firgice tayi baya ta rab'e a jikin bango ,kansa ya jingina da bango sai ya naushi kansa ya buga kansa da bango ,kamar an tsikare shi yayi wajenta ya durk'usa a gabanta yace "do you knew who u are in my life? shiru bata bashi amsa ba , yace " do you know how much I love you? a razane ta d'ago ido ta kalle shi "yes & u never knew my feelings 2 u ,u are my first love,tun ranar dana fara d'ora ido na akanki naji na fara sanki, amma bakomai i miss my 1st love ya fad'a kamar zaiyi kuka ,sai kuma ya riko hannunta ya mik'ar da ita tsaye yace "I really love you more most, wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata,kai ya girgiza mata yace " no karki kiyi kuka i don't wanna see you cry,yana maganar yana goge mata hawayen dake zubo mata.



A hankali tace "am so sorry please,rungumeta yayi gam a k'irjinsa yana sauke ajiyar zuciya ,a hankali ya sake ta yace "kiyi wanka ki sameni zamu fita lessons,kai kawai ta iya d'aga masa yana tangadi ya fice,bayansa tafi da kallo ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta fashe da kuka saboda tausaya masa dan ta hango tsantsar santa a kwayar idonsa,wayar tace ta fara ringing a hankali ta duba taga My life,shiru tayi ta rasa abinyi idan ta d'aga zai gane tana kuka idan kuma batayi picking ba hankalinsa ne zai tashi ,k'in picking tayi tayi dayi mata 5miss call sannan ta sai ta kanta ta d'aga tana dagawa yace "I don't want to miss you in my life ,I love you forever and ever, idan na rasaki bazan iya ci gaba da rayuwa wallahi Fauziyyah mutuwa zanyi yayi mata hot kiss ya kashe wayar ,wani irin kallo take wa wayar sai ta sake fashewa da kuka.



Ta rasa wa zata zaba tsakanin Sadik da Farhan ,kowa yana mata mugun so ,ta rasa wa tafi so,tun tuni Farhan ya gama course d'in daya kawoshi amma saboda ita yaki komawa Nigeria wajen iyayensa da ' yan uwansa ya tare a America saboda ita wai sai ta gama zasu tafi tare.



*********************************



Wata shidan da Doctor ya d'ibar wa Fa'iz ta cika kuma cikin ikon Allah da taimakon Ubangiji ya samu sauk'i ya warke sumul kamar ba shi ba ,yau Doctor zai sallemeshi duk su Abba sun zo,Doctor ya kalle Fa'iz yace "masa ya sunanka? "Kallo kawai yabi doctor dashi sai can yace "waye kai please? murmushi Doctor yayi yace " ni likitan ka ne ya nuna su Abba yace "wad'annan kuma su suka tsince ka suka kawo asibiti dabadan sun kawo ka ba ka rasa rayuwarka ,kallon Baba da Abba yayi godiya yayi musu sosai har k'asa ya durk'usa yayi musu godiya ,hankali da tarbiyyar Fa'iz tayi matuk'ar burge Abba da Baba,a hankali Baba yace " tashi ka zauna ,amma yak'i sai da da kyar Abba yasa shi ya zauna ,kallon sa Baba yayi yace "ya sunanka,daga ina kake,su waye iyayenka?



A hankali Fa'iz ya d'ago kai ya kalli Baba da Abba yayi shiru amma ya kasa tuna komai ya kasa tuna waye shi,cikin sanyin murya yace "ban san kowaye ni ba na kasa tuna komai nawa, "what that is impossible,Doctor ya fad'a a razane ,kansa ya sunkuyo kusa da Fa'iz yace "k'ara tunani mai zurfi please ,shiru Fa'iz ya k'ara yi yayi-yayi ya tuna wani abu nashi amma ya kasa kai d'ago ya sake kallon Doctor yace "bazan iya tuna koda sunana ba,cikin tashin hankali kuwa yake kallansa Baba yace "Doctor mai yake faruwa ne ?



Shima Doctor kallan su yayi yace "yanzu bazan iya cewa komai ba sai mun gwada shi zamu iya gano komai,yana kaiwa nan ya fita baifi 3mnts da fitar sa ba nurses suka shigo suka tura Fa'iz zuwa wani d'aki ,sai da aka shafe 2hrs sannan aka fito dashi su Abba na nan duk sunyi jigum-jigum suna jiran tsammani,likitan na fitowa ya kira su zuwa office d'insa ,anan ya kalli Abba yace "gaskiya akwai matsala dan mun gano ya samu losing memory (cutar mantau) a halin yanzu ya manta komai nasa iyayensa,gidan su koda shi kansa ma bazai iya tuna waye shi ba ,Baba kasa magana yayi saboda tsabar tashin hankali sai Abba ne yayi k'arfin halin cewa "yanzu doctor meye
Showing 39001 words to 42000 words out of 70679 words