amsa masa, Aysha tarok'a kuma ya amsa mata, datasamu damar k'aratu batayi wasa da damarba tanutsu tayi, cikin wad'anda ba k'abilarsu d'ayabama, amma bataji shayi ko burin kasancewar gazawarta ba agaba-gaba ba wajen nuna kwazonta da jajircewa_.
_sannan kuma taginu akan wani k'yak'k'yawan buri nason ku6tar damata dayawa dasuka tsinci Kansu cikin irin rayuwar datake, walau dasaninsu, koda tirsasawar wasunsu, ahakan hartasamu ceto rayuwar meerah, wadda tafidda rai dagama shiriya baki d'aya, alokacin kuma data samu damar k'arfafa mijinta saitazama mai k'arfafashin, da nuna fushinta wajen son yataimaki matan wannan al'ummar damuka kasance cikin gararin rayuwa, bayan addininmu yamana gata, amma wasu tsiraru acikinmu suke nuna zalinci da k'arfa-k'arfa akan hakan._
_yakamata 'yan uwana mata muyi koyi da Aysha, muzama masu kishin junanmu dasanin darajar juna, muzama masu k'arfafa zukatanmu wajan fallasa asirin wasu 'yan jari hujja dake wargaza rayuwarmu komin kusancinmu dasu kuwa, da wannan jarumtar Aysha tasamu damar fallasa asirin su momy har aka d'auki hukunci akansu, datayi shiru tsoro yahanata haka rayuwar zatayita tafiya da walagigi da sauran mata. Kuma wlhy abinda su momyn nan suke aikatawa agaske yana faruwane yanzun, saidai shugabanninmu sunyi burus da lamarin😭._
Mata muzama Aysha, koda k'ar6ama rayuwarku 'yancinta🤷🏽‍♀.


_Mama, mama ta birgeni kwarai da gaske, zan iya cemukuma tafi kowa birgeni, Dan bata d'auki kishin banza da wofi mara amfani da amfanar da matan wannan zamaninba ta yafama kanta, tazama adalar abokiyar zama, mai mutunta mutuncin zaman tare, danuna adalci irinna koyarwar addininmu, uwa tagari, maiso ceto wasu 'ya'yan dasuka shiga gararin rayuwa, tayi tawakkali dayin abinda bakowacce uwa bace zata iya, wajen hana cutar da 'ya'yan wasu, ta sadaukar da rayuwar tata d'iya._
_ALLAH mai alkairi, saiya dubi k'yak'k'yawar zuciyarta yatsare mata tata d'iyar kuwa, abinda yay k'aranci awannan zamanin kenan, wanima bai Isa tsawatarma d'an waniba, bare har takai ga sadaukarwar cutar kai wajan ceto wasu, iyaye mugyara Dan ALLAH, mudunga duba gobenmu bawai jiyanmuba, Dan tarigada tawuce saidai labarinta, ALLAH yabamu k'yak'yk'yawar zuciya irin ta mama, mai sauk'ak'ama kanta kishi da bak'inciki, dawatace saitace INA ruwanta, aii khaleel ba d'anta baneba, d'an kishiyane, idanma ya salwanta batada asara, amma baiwar ALLAH batayi hakaba, saita jajirce har saida tamaidashi hannun mahaifiyarsa._


_dolene Mamie ta birge kowa, kodan hak'urinta da kawaici akan cinkashi da hajia baba taita mata, sai bata zamo tanamata rashin kunyaba, komin zafin abinda Tamata bata daina girmamataba, amatsayin uwargidan mijinsu, tahad'a 'ya'yan agidan tarik'e baki d'aya, vata Nuna banbanci agaresu, hakan yasaka taita bama d'anta kulawa batareda tasaniba, tarage masa rad'ad'in rashin samun kulawar daga momy wadda yakema kallon mahaifiya, dabata jasa ajikiba koda gaskiya tafito bazaiji soyayyartaba aransa, saboda zaicigaba da kallonta amatsayin kishiyar uwane.._
_saimu gyara 'yan uwana mata, mudinga lura, idan Kane agidan miji amatsayin amarya karmu hantari 'ya'yan Uwargida, bakasan ranar dazasumakaba anan gaba, Dan doledai 'ya'yankane zasuzo amatsayin k'anana, idan Kana cutar da 'ya'yan Uwargida, sumafa zasu ringa huce haushinsune akan 'ya'yanka, ko bayan idonkane kuwa, please saimu kiyaye, kowacce Matsala kagani akwai tushen k'irk'irarta wlhy, mata muyi koyi da wannan baiwa Anty Mamie, ALLAH yasa Mugane amin._


_dolene ayabama Ummi amarya itama, Dan awannan zamanin bakowane zai iya abinda tayiba gaskiya, musamman idan mukayi dubi da yanda kishi yake awannan zamanin, yarinya kafin tashiga gida tafara kishin iyayen agidan, hakan ba daidai baneba, Ummie amarya tayarda da Auren baffah domin taimakon mama akan manufarta mai k'yau, mata masu irin zuciyar ummi amarya sunyi k'aranci, burin kowa ya Auri mai dukiya yazauna shikad'ai babu kishiya, please mugyara kafin lokaci ya k'ure mana_.


_samun iyaye irin baffah awannan zamanin kad'anne, musamman idan akwai wasu 'yan canji a hannunka, zakiga kullum Baka maida hankali akan tarbiyyar 'ya'yanka, uzurinka yafi kulada familie naka, aganinka karigada katara musu dukiya, shikenan buk'atunsu da nauyinsu akanka yak'are, gobe kana waccan k'asa jibi kana wancan taro, bakada lokacin iyalinka ko kad'an, dasunzo maka da buk'atar kud'i sai zaka biya musu awuce wajen, maganar tarbiyyarsu kuma kabarma matan gidanka, bayan kuma hannu d'aya bayan d'aukar jinka, musamman awannan zamanin da duniyar tarikid'e gaba d'aya, iyaye Dan ALLAH kunutsu akan tarbiyyar 'ya'yanku, walau kaid'in talakane komai kud'in, Dan wannan zamanin bawai 'ya'yan masu kud'i bane kad'ai lalatattu, wlhy tawani fanninma 'ya'yan talakawa sunfi 'ya'yan masu kud'in lalacewar, Dan haka ko'ina akwai Na kirki akwai Na banza, ALLAH dai ya gyara mana kawai, ALLAH ka shiryemu dai baki d'aya._



_idan muka d'auki jigon labarin baki d'aya ZAMU kula yatafine akan hassada baki d'aya, domin hassada itace tazama tushen komai._

_badan innah jummai tatashi da hassadar Ammah ba da komai baikasance hakaba,, hasaada tasakata gur6ata tarbiyyar 'yarta d'aya tilo, hassada yasaka d'ora momy a keken 6era Na burin zama wani Abu wajen Tara dukiya domin akirata da suna hamshak'iyar mace, badan wannan dalilinba da momy bata Shiga k'ungiyar ('ya'yan kunama ba), datayi hak'uri tazauna agidan mijinta lafiya, dabatayi tunanin cin gadon Alhaji Abdallah jigawaba, bare harta dinga kallon haihuwar mata amatsayin dakushewar komanta, har takaita ga sace d'an abokiyar zamanta, domin kawai yazama jari a burinta, wannan hassadar Ce hartakai ga shafar mufeedah batajiba bata ganiba._
_hassada masiface wlhy, domin kunga innah jummaice kawai taginata, amma tacigaba da zagaye mutane masu d'unbin yawa acikin masifa, innah jummai ta Reni momy akan hassada, momy kuma tareni 'ya'yan ta gallabar rayuwar wasunta irinsu mama da Anty Mamie, hartazama sanadin salwantar wasu mutane dayawa._
_Amma abin kaico, dukkan abinda suke burin akansa ALLAH yabasu, daga k'arshe kuma saiya zama rugzajje, Mara amfani agaresu, saima yazame musu sanadin nadama da Dana Sani, k'ask'anci da d'umbin kunyar rayuwa, Yakamata Mugane hassada tamkar tubalin toka take, koda kaginata danisa watarana saita ruguzo idan tatashi da mutuncinka kuma zata rushe. Hassada babu k'arama babu babba acikinta, komin samanka kuma saika fad'o idan kakasance mutum mai hassada, koda bakayi k'arshe irinnasu innh jummaiba kuwa, kuma mafi yawan mai hassadama wlhy sanadin bugawar zuciya yake mutuwa, ko hawan jini._

_a wannan zamanin ko kishi damata keyi hassada tafi yawa aciki, Dan ba'a kishi irinna matan manzon ALLAH (s,a,w), wannan nabama kowacce mace dama tazauna tayi nazari akan hakan kuma._🤷🏽‍♀

_soyayyar Khaleel da Aysha abin birgewa, kowacce mace tana burin samun irin wannan rayuwa, gashi kuma itace tayi k'aranci, Dan mazajenmu sunfi fifita Neman kud'i akan iyalinsu, k'alilanne acikinsu ke bama matan kulawa, amma da anyi aure wata uku tayi yawa soyyaya tazama tarihi saikuma zaman hak'uri dana 'ya'ya, wlhy ko kar6uwar novels damaida hankali wajen son karatun buks Na soyayyar damukeyi yasamo asaline daga k'aranci kulawa ta mazajenmu akanmu, towatama batasan irin wannan soyayyarba sai novels, shiyyasa idan muka saka tayi yawa saikiji ana k'aryatamu, Dan ALLAH maza kugyara, ko yawaitar zinace-zinace da buri irin Na mata yana tafiyane wajen k'arancin kulawar damuke samu, kishin kansa damata keyi harda rashin kulawa, domin ita kanuna mata soyayyar awaje, amma tana shigowa gidan sai komai ya canja, kakuma koma hangen wata awaje, kana bata kulawar dabaka bama wannan tagidan, kaga kuwa kataro March wlhy, amma muma matan dazamu nutsu muyi hak'uri dasaikiga abin mamaki, itamafa tana shigowa gidan rabin shekara yayi yawa zata fara kwasan makamancin d'acin dakika d'iba sanadin shigowarta, Dan itama kwanaki kad'an idonsa zai fara komawa kan shinshino wata kuma awaje😂🤭, bulalar data doki uwargidafa, itace zata jibgi amarya watan watarana._
_mun kasa fahimtane kawai, amma maza sun maidamu sakarkaru wlhy, ahanaki zaman lfy da jituwa tsakaninki da 'Yar uwarki jinsinki, sannan sukuma kullum suna gefe suna dariya dakiranku mahaukata baki d'aya🤕._
Saimu farka idan munga zamu gane, idan bazamu ganeba kuma muyitayi, muke tareda wahala, sudai babu ruwansu.



_kobabu komai Ammah jar wuya tsohuwar arzik'i ta nishad'antar daku😂, kowa zaiso yasamu kaka irin Ammah😉👍🏻🤣._



Bara nabarku haka, badan nagajiba, saidan watarana cikakken sharhin wannan labari zai iya zuwa muku kaitsaye daga k'ungiyar haske, bayan antaceshi an tankad'e kuma an rairaye.

Takuce har kullum, mai sonku da k'aunarku.

Bilkisa Ibrahim
(Bilyn Abdul)


Marubuciyar.✍🏻

*_Rashin sani!!._*
*_auren k'addara ko biyayya?_*
*_k'anwar uwace ko kishiyar uwa?_*
*_Nida aminiyata!!_*
*_Nawaff!!_*
*_Sabon al'aree!!_*
*_kukan kurciya....!!_*
*_Ban saketaba!!_*.
*_Abdul-maleek bobi!!_*
*_Karayar arzeek'i!!_*
*_sanadin bikin sallah!!_*
*_ciki da gaskiya!!_*.


_duk zaku iya nemansu Ku karanta, karkuma kiji tsoro ko kunyar tunasar dani wani kuskure danayi acikinsu, kifad'amin ta k'yak'yk'yawar sigar dazan fahimceki vatareda cin zarafiba._


_banyi ciki da gaskiya domin cin zarafin kowaba, hakama sauran buks d'inna, saboda yanayin rayuwama nak'i fad'ar wani matsayi daga 6angaren aikin khaleel, shikansa ban fad'i girman igiyar kakinsaba, so hakan yafi sauk'i._
Idan kin karanta saiki gyara abinda kikeyi Mara k'yau, kodan gudun fad'awa hanya Mara k'yau, idankuma burin yi ne dake saiki cireshi aranki.


ALLAH yasa Mugane, mu anfana da abinda muka samu aciki, Wanda yazama kuskure ALLAH ka yafe mana baki d'aya.



ALLAH ka gafartama iyayenmu dadukkan musulmai dasuka rigamu gidan gaskiya.


Duk Wanda na6atamawa ayayin rubutun wannan labarin ya gafarceni, nayine akan rashin sani, ALLAH ya yafe mana baki d'aya.



Abaya nace next novel d'inna ABINDA KASHUKA.... Tom yanzun naga ana rubuta abinda ka Shika, so watak'il zan iya canja sunan nawa labarine idan hali yazo da hakan, idankuma naga babu sunan daya dace dashi to zanyi amfani da wannan sunan nafarko.


Insha ALLAH a next year zakuga Sabon buk d'inna.


Inama kowa fatan alkairi.




Bilyn Abdul Ce.😉👍🏻👍🏻👍🏻


Ngd kwarai da gaske💋💋💋💋💋💋💋💋❤❤❤❤❤*_📲Typing_*


🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......_*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_


*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*


*_HASKE WRITERS ASS......._*
_(Home of expert and perfect writers)_


*_part 2_*
_(littafi Na biyu📙)_

_alkairin ALLAH ya iso gareku kuma, bilyn Abdul bata manta dakuba._
*DUNIYAR MAKARANTA group & ATK hausa novels, Momiskoh hutu.*


5⃣1⃣


Kwana biyu kenan da dawowar khaleel Nigeria, har yanzu kuma fushi yakeyi da Aysha, zaidai shigo yad'auki junior yafita, Ammah ma baya kulata, yana dai gaisheta amma babu hira.


Yau takasance monday, dawuri khaleel yay shirin office, ko cikin gida bai shigaba yafice da hanzari.
Adams yabud'e masa mota yashiga, bayan sunyi salute nashi.
Tafiyar mintuna k'alilance takaisu.

Zamansa babu dad'ewa a office saiga kira yashigo wayarsa, dubawa yayi kasancewar wayar office ce, ganin ogansa yasakashi d'agawa da hanzari.
Cikin girmamawa ya gaidashi.
Saikuma naji yana fad'in "OK sir, ganinan zuwa to".
Yana Yanke wayar yamik'e yad'auki wasu takardu yafice.
Saida yayi knocking aka bashi izinin shiga sannan yatura k'ofar yashiga, ya k'ame tareda salute na ogansa.
Fuskar Oga d'aukeda murmushi yanuna masa wajen zama bayan yamaida masa murtanin salute d'in.

" J! Ya iyali?, da abokina Abdallah?".
Murmushi ya khaleel yayi, yace, "yana nan lfy sir".
" to ALLAH ya albarkaci rayuwarsa, ALLAH yasa yafika jarumta da kwazo".
Murmushi sosai khaleel yakumayi, Wanda har hakwaransa suka bayyana, yanason ayaba masa d'an Abdallansa😃👍🏻.
Yace, "to ALLAH ya amince sir".
Oga yay 'Yar dariya, tareda mik'ama khaleel wata Leda mai azabar k'yau.
"Ga wannan j!, gobe idan ALLAH ya kaimu su zaka saka, kuma kaida madam zakazo".
Cikeda mamaki khaleel yakar6i ledan, yad'an lek'a cikinta sannan yakalli ogan nasa.
" sir! wani abune za'ayi?".
"A'a, kaidai kasaka kawai, kuma sai around 11 za'azo a d'aukeku insha ALLAH".

kasa cewa komai khaleel yayi, sai jinjina kai yake tamkar k'adan gare.
Oga yayi murmushi, tareda basar da zancen yace, " so ina takardun danace kazo dasu?".
Mik'a masa khaleel yayi.
Oga yakar6a yad'an dudduba, sannan yad'ago yakalli khaleel d'in, " ehm j akwai wani aiki daya taso mana again, so zamuyi meeting akan batun next week insha ALLAH, kuma aikin gaskiya dolene kaine keda zarrar yinsa, Dan wad'anda za'a kamad'in saida irinku awajen, amma gawad'annan kaduba wani 6angarene nabayanan, zan turo maka sauran ta network".
"OK sir!".
" zaka iya tafiya abinka".
Mik'ewa yayi tareda k'amewa dayin salute na ogan, sannan yafice.


**********

Tunda yadawo office yaketa juya maganar ogan nasu, baidai bud'e kayanba, yamaida hankalinsa akan binciken bayanan da oga yabashi akan aikin kuma dayake tunkarosu.
Yaja tsawon lokaci a binciken yaji alamar shigiwar massage a wayarsa.
Kamar bazai dubaba dai yad'auka.
Number Aysha yagani, yasaki guntun murmushi sannan yabud'e sak'on.

_"Amincin ALLAH ya tabbata agareka yakai sanadin farincikina, inafatan kana cikin kwanciyar hankali da walwala ahalin yanzu?, Alkairin ALLAH yacigaba da yalwatuwa aduniyarka, ALLAH yatsareminkai daga idon mata🤕, masu k'arema mazan mutane kallo😏."_
_"junior yace dadynsa yakasance cikin kwazon aiki da farinciki, gefe kuma yaringa tuna mamansa, yamata uzuri, adaina fushi da ita, ba laifinta bane, itama tana kewar bakandamiyar rayuwarta Abban junior💋."_

Baisan sanda wani murmushi ya su6uce masaba, yakuma maimaita sak'on sannan ya tuntsure da dariya, kai yarinyarnan sai'a barta, 'yar k'arama da ita ta'iya kishi.
Cikin lumshe idanu ya sumbaci massage d'in, shikansa fushin dayakeyi dauriya kawai yakeyi, amma yana kewarta, yanaso kod'an kissing d'inta yayai, amma Ammah takafa tatsare.
Bud'e idanunsa yayi, sannan yay dealing d'in number d'inta, harta katse bata d'agaba, kasa hak'uri yayi yakuma kira, bugu biyu kuwa tad'aga.

Murya can k'asan mak'oshi tace,
"Hii my lollipop".
Lumshe idanun yakumayi, da k'yar ya iya furta " A'eesha kin rainani ko? kimin laifi amma kimaidashi wasa?".
_"Ooo! my god, ni na'isa wasa da jarumi mai zarrah irin j!, karfa ka manta j! Ne, kuma j!! Bayason raini, amin afuwa, komai akaga nayi, akan kuskurene, amma bazan sakeba, junior nataya Amminsa bada hak'uri, kagama kuka yake shirinyi, harya fara ta6e baki"._
"Kai haba dai?".
" ALLAH kuwa". "tayi maganar tana kara wayar kusada Junior".
Aikam tamkar jira yake yafashe da kuka😂

" kai, dama da gaske kikeyi? Please banason jin kukansa, kibasa abincinsa".
Shagwa6e murya Aysha tayi. tace, "to kadaina fushin dani please?".
" ai wancan laifin daban, bamu abincinmu kuma daban".
"Naji, to amma naci albarkacin junior".
" sarkin wayo, shikenan na yafe miki, komai yawuce, amma saiki shirya tarbata yau ko?".

"Lah Sadaukina, banfamuyi arba'inba".
"uhm nasani aii, amma koda bazanje city ba, sai'a barni nad'an rage zafi".
Kamar Aysha na gabansa tarufe idonta, ''kai ya khaleel, ALLAH kaima wani lokacin bakada kunya.
" hhh ko sholyna?".
"Eh mana".
" tom nazama mai kunya, kibarni nayi aiki inba sokike nazabga musu shirmeba wlhy, duk kin wani narkar dani".
"Wata 'Yar dariyar kissa Aysha tayi, tayimasa siririn kiss sannan tayanke wayar batareda yashiryaba, saidai yaji d'iifff."
Da sauri yakalli wayar, yakoma yalafe jikin kujerar yana fad'in ya salam yarinyarnan zata karni wlhy🤦🏻‍♂.


🤣🤣🤣😜.
Kina aljanna sholy, muna binki da addu'a, nida fans🤸🏻‍♀🤸🏻‍♀.

ALLAH yaba Xoxo irin khaleel kodan........🤭, bazan fad'aba to😜, su o e har an kasa kunne aji kanun labari😏.



_______________________
Sai bayan isha'i yadawo gidan, 6angarensu yashiga yay wanka yakimtsa sannan yazura jallabiya kalan ash, yad'an fesa turare yad'auki ledar da ogansa yabasa dawata ledan dayad'an yima Aysha siyayyar toshin baki😂 yafito.

Da sallama yashiga falon na Ammah, babu kowa aciki sai mufeedah dake barci a doguwar kujera, da'alama bada shiri barcin ya kwashetaba, Dan harda waya a hanunta.
Jiyo Ammah yayi tana karad'i itakad'ai a waya, da'alama waya yakeyi da uncle ma'aruff kokuma wani.
Sad'af-sad'af yashige d'akinta, yana k'yautata zaton Aysha nacan.
Aikam kan gadon AMMAH yahangota zaune tana k'ok'arin sakama junior pampas.
K'ofar yasakama key sannan yak'arasa gareta.
Tad'ago ido tana masa sannu.
Zama kusada ita yayi yana amsawa, tareda saka d'an yatsansa cikin hannun junior, shikam yakama yarik'e gam kamar yasan miye.
"My sweet kawuni lfy?".
Aysha data gama saka masa pampas d'in tad'agosa tad'ora masa acinya tana fad'in " k'alau ya wuni, saidai kewar Abbah ko baffanmu?".
Ya khaleel yakar6esa yana murmushi, ya sumbaci fuskar yaron, "to nima nadawo inata kewarku".
" humm yaronafa sai k'ara k'iba yakeyi, ALLAH nononki yanada k'yau 'yammatana, masha ALLAH, ingani".
'Yay maganar yanakai hannunsa kanta'.
Baya tamatsa tana dariya.
Shima dariyar yayi ya cafkota, jikinsa tafad'o, yana rungume da Junior yamatseta itama, kissing d'in wuyanta yafarayi, bata hanashiba, saima wani salo data fara masa.
Aikam dandanan mutumin naku ya afka.
Suna tsaka da hutawarsu Ammah taita buga k'ofar, shiru sukai mata kuwa, sukacigaba da faranta ran junansu.
Dama tea takawoma Aysha, falo takoma tana mita, saikuma tayi shiru tana d'aga hanci
Showing 174001 words to 177000 words out of 181849 words