"Ammah badai jikin Aysha ya matsanta mataba ko? Naga dukga yaran amma ita babu ita?"..
Cikin shan k'amshi Ammah Tace, " a'a jikinta da sauk'i, tanacan tareda mijinta a 6angarensu, da safennan yazo ya saceta".
Duk falon saida akayi dariya, amma banda Momy dataji kamar Ammah ta soka mata mashi.
Tayi dariyar yak'e "ayya amma, dama meatpia ne namata datacemin tanasonci, kuma ganaku, bara aina aiki hasnah Takai musu".
''A to kin k'yauta gaskiya, sunacan".
Ajiye musu Nasu tayi tafice, babu Wanda yazargi komai suka faraci, sai Santi sukeyi, yayi dad'i, dama Momy ta iya kayan snacks d'innan muguntace kawai Dason jiki ke hanatayi.
Bata zame ko inaba sai 6angarensu ya khaleel.
*******
Sun fito wanka kenan Aysha tace masa yunwa takeji wlhy, Dan harta fara ganin jiri, k'arasawa yayi kusada ita ajikin madubi, ya rungumota tabaya, hannayensa duka nakan cikinta, kansa yad'ora gefen kafad'arta suna kallon juna ta madubi, my sholy kinfa zama consumer, kad'an-kad'an saici".
"Kai sadauki, duk yaufa banci komaiba sai rake, nidai kaje kasamomin abinci acikin gida, ALLAH harna farajin tashin zuciya".
Sumbatar gefen wuyanta yayi, cikin kunnenta yace, " idan naje aikennan nikuma miye tukuycina?, hannu tasaka ta shafo kumatunsa, sannan tad'aga masa gira🤨, saika dawo zaka gani".
"Wata sassanyar dariya yasaki acikin kunnenta, yana shinshinar wuyanta yace, ''yanzu kuwa zan samo abinci, kuma duk kukanki saina kar6i tukuycina".
Baijira cewarta ba yasaketa yafice.
Murmushi Aysha tayi tana binsa da kallo ta madubi, akan la66anta tafirta I love you so much sadaukina, kabani farinci yau d'innan, bakuma zanta6a mantawa da hakanba😊".
Shima abinda yake ayyanawa aransa kenan, fuskarsa d'aukeda murmushi sukayi karo da Momy afalo zaune.
" Momy kece?".
Juyowa tayi ta kalleshi, bak'incikin ganin fusakarsa a farinciki yadaki zuciyarta, amma saita dake, "nine my lovely son, zonan mana, kwana biyu ana fushi da Momy ko?".
Murmushi yayi, yak'arasa gefenta ya zauna tareda d'ora kansa a kafad'arta, yace, ''I miss you momyna".
" miss you 2 my dealing, ykk?".
"Alhmdllh momyn, saidai missing naki danayi, kiyi hak'uri kidaina fushi dani, ranarma sharrin shaid'anne, kinsan banida kamarki duk duniyarnan".
"Karka damu kaji Ibrahim, komai ya wuce, ina d'iyata d'in Aysha".
Kunyace takamashi, yad'an Sosa kansa yana murmushi, da hannu yanuna mata d'aki.
Murmushin yak'e Momy tayi.
Khaleel yace, ''dama zanje cikin gidane samo mata abinci, wai yunwa takeji".
" ayya gama meat pia na kawo muku, dama itace tacemin tanaso jiya, shine nayishi yau, kamaji da zafinsa saika kaimata taci, ni bara naje, Dan zuwairah na shirin tafiya".
Dad'ine ya lullu6e khaleel Dan ganin momy tafara basu kulawa shida matarsa, yamata godiya tafice, shikuma yanufi d'akinsa, tararwa yayi Aysha kwance bakin gado, yunwa tahanata ta6uka komai.
Kwanon tangaran d'in kawai yamika mata, jikinta har rawa yakeyi tatshi zaune, kusan tare suka d'auka, amma tarigashi gutsura, harta fara taunawa tatsaya, waini Sadauki inama kasamo meat pia ne haka? da zafinsa.
Harzai gutsura yatsaya bata amsa, momyce takawoshi yanzu, tace dama jiya kikace mata tamiki". (Acikin d'oki yake gaya mata).
Da sauri Aysha ta furzar dana bakinta, shima tayi saurin ka6e na hannunsa daya gutsura, bayi dasauri, fuskarsa a murtike yace, "k miye haka?".
Hankad'a kwanon Aysha tayi yafad'o k'asa ya tarwatse, Aysha tayi azamar tura hannu cikin bakin khaleel tana kwakulo Wanda ya 6allah, dama ko taunawa bayyiba.
Hankad'ata yayi tabigi gado, bata damuba, tunda tasami nasarar Ciro na bakin nasa.
" waike wane irin iskancine sannan? Uwatafa nace takawo ba uban waniba!!!".
Itama Aysha a tsawace tace, "ko itad'ince takawo bazakacishiba, kasan miye cikinsa?!!! To gubace ta kasheka inbaka sanib...........
Bai bari ta k'arasaba ya d'auketa da mari, ''k!!! Karfa kiga ina wasa dake kiringa kawomin iskanci, kina nufin uwata data tsugunna ta haifenice zata kawo guba tabani naci na mutu!!!!!?".
Hannun Aysha dafe da kuncinta tana kuka tace, " wlhy koda zaka kasheni saina fad'a, nace gubace aciki, bai dameni da matsayin Momy agarekaba, inma bakai tayi nufin kashewaba nitazo kashew........
Da sauri yamatsota, itakuma tamatsa baya, duka takuma kaimata ta kauce, ya wawurita tafice da gudu, shima binta yayi har cikin gida.
Basu zame ko inaba sai 6angaren Ammah, yanda Aysha tashigo aguje yasaka kowa mik'ewa, saiga ya khaleel shima, Ammah ce tayi jarumtar tareshi, sai huci yakeyi tamkar kurar daji.
Aysha da bakinta bai mutuba, saboda rud'ewar datayi, cikin kuka takuma fad'in wlhy koda zaka kasheni yau agidannan saina fad'a, gubace Momy tabamu muci a meat pia muci mu mutu, idankuma bahaka baneba tazo ta gardama mana.......
Kuma yunk'urowa yayi kanta, baffah daya shigo yanzu yay saurin rik'eshi, dandanan 6angaren Ammah yacika daduk Ahalin gidan.
Daga Aysha har ya khaleel sunkasa nutsuwar da za'a tambayesu, sai Aysha daketa fad'in ko khaleel zai kasheta saita fad'a guba Momy tabasu suci su mutu, kuma inba haka bane tazo ta Musa zancen.
Shikuma ya khaleel sai fisgewa yakeyi daga rik'on baffah, burinsa kawai Yakama Aysha yamata dukan mutuwa, tunda har tsaurin idonta yakai taringa yima mahaifiyarsa sharri haka.
"Tsawa baffah yadakamusu, yace, " kai duk banason rashin hankali, minene yahad'aku?".
Aysha zatayi magana ya khaleel yay saurin tareta ta hanyar fara fad'e.............✍
Hummm sannu-sannu bata hana zuwa, saidai adad'e ba'a zoba🐢🐢🐢🐢🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🤸🏻♀🚴♀🤣.
🤾🏿♀🤾🏿♀🤾🏿♀🤾🏿♀🤾🏿♀🦂
*_Typing📲_*
🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_
*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*
*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_
*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_
3⃣5⃣
Dogon d'akine, saidai anyi kananun d'akuna aciki tamkar na prison, yawancin d'akunnan dukda mutane aciki, matane kuma zallah awajen.
d'akin dake can k'arshe suka k'arasa, kubrah Na zaune tacusa kanta tsakanin cinyoyinta, sai kuka takeyi, bata ta6a tunanin shiga wanga haliba, musamman yanda ta'iya takunta.
K'arar bud'e k'ofarce tasanyata d'agowa da sauri dukta fita hayyacinta, kamar wata sabuwar kamu a hauka.
Ganin khaleel yasakata mik'ewa zumbur zata nufosa, wata uwar tsawa Taheer yadaka mata, babu shiri tayi baya ta zauna da6ar.
Lumshe ido khaleel yayi yana girgiza kansa, Samuel dake binsu abaya ya ajiyema ya khaleel kujera, zama yayi idonsa akan kubrah data koma jikin bango ta raku6e.
Saida yamata kallon minti 2 sannan yajuyo yakalli Sam... Da Taheer batareda yayi maganaba.
Ficewa sukayi, Dan sungane miyake nufi.
Suna fita yadawo da kallonsa kanta, itama dataga daga ita saishi saita fashe da kuka, tana fad'in "Dan ALLAH khaleel kafitar dani, wlhy bammusu komaiba, zalincine yasakasu kamani".
K'asaitaccen murmushi ya khaleel yayi, Wanda yadad'e baiyi irinsaba saboda damuwa, cikin turo iska daga hancinsa yace, " nima abinda yakawoni kenan kubrah, nasan ked'in mutuniyar kirkice, banta6a ganinki kina aikata Abu mara k'yauba, zan ku6tar dake ammafa saikin bani had'inkai".
Har taune harshe takeyi wajen fad'in "wane irin had'inkai?".
Nanma murmushin yasaki, muryarsa can k'asa yace, "kwantar min da hankalinki mana my Sweet".
Wani dad'i yaratsa kubrah, khaleel yacemata Sweet.
Shima murmushin yayi danya hango matakan nasara.
" kubrah wanne kasuwanci kikeyi ak'asashe daban-daban Na duniya?, dannaga bak'ya kulla watanni biyu a Nigeria ".
Tashin hankali, jikin kubrah ne yafara 6ari. Khaleel yace, " yahaka kuma da rawar jiki? Tambayacefa bawani abuba, saikace wata mara gaskiya?".
"A...a'a wlhy, inada gaskiya khaleel, dama dai tambayarce tazomin a bazata, shi....shin...shinefa kawai".
"Uhyimm, Sorry fa kinji".🤨
Khaleel yay maganar yana d'age gira d'aya sama.
" ina jiran amsarki".
"To khaleel mizance maka, kasan ina business ne aii".
" Nasan business kikeyi, amma wane iri nufina?".
Gumin da keta tsatstsafo mata ajiki tashare da hannun doguwar rigar atanfarta, amma takasa furta komai.
Shikam khaleel yayi masifar tsura mata idanu, zuwacan yace "shikenan, shikenan, barma waccan tambayar Nagano amsarta, miye alak'arki da hajia khaltum?".
"Kamar Yaya take a wajena".
"OK".
" akwai wadda kuka ta6a zuwa gidanmu da ita, lokacin bikina, itakuma wacece? A INA kuma take?".
"Kamar zata fasa kuka tace k'awatace".
"Tana ina yanzun?".
" kwanaki tayi had'arin mota tama rasu".
"Ayya, lalai ta iya mutuwa, amma nikuma naganta kwanakin baya a Lagos, zataje America".
Afirgice kubrah tace, "glory d'in?, itafa a Islands UK takema".
K'aramar dariya ya khaleel yasaki, danya samo amsar tambayarsa, yace, "kwarai kuwa, saidai inaga bayan dawowarta tamutu ko?, waccan dai kamar sunanta glory Zamani, koba ita baceba?".
Kubrah tasaki ajiyar zuciya, "A'a ba ita baceba, k'awata sunanta glory maba".
" dak'yau 'Yar gari, kin gamamin komai, tabbas ba ita baceba, amma ina jajanta miki mutuwar k'awarki, zanje muyi magana da habeeb dan yazo ya kar6eki, idan ni nanemi haka baza'a baniba, za'aga kamar munhad'a bakine".
Godiya kubrah tamasa, dad'i yakamata baigano komaiba, gashima har yana shirin k'ubtar da ita.
Harya mik'e Yakoma ya zauna, af kinga kuma Na manta, a INA zan samu habeeb?, Dan inaso yazo gobe, jibi inada tafiya zuwa London ".
"Ito habeeb d'inne sai a slow, amma hanya mafi sauk'i kaje Cinema, yau za'a haska film, Na tabbatar zaije".
"OK thanks, angama, gobe ki saurari sakamako, bye my Sweet😉".
Dad'i kamar yakashe kubrah, haka Sam...yashigo ya d'auki kujera yafice, aransa yace banza, bakisan halin boss bane, dagani wayo yamiki.
______________________________
Tunda ya khaleel yadawo office yaketa tunane-tunane, ta hanyar dazaibi yaje Cinema yau, ga tunanin binciken glory, ta inama zai fara?, kiran wayarsa da'akayi yakatse masa tunani.
Wayar ya d'auka yaga Aysha Ce.
Guntun murmushin yayi, danya kula kwana biyunnan tashiga damuwa da sharetan dayakeyi, saida takatse yakirata, bugu biyu kuwa ta d'aga.
Muryarta can k'asa akuma galabaice tayi sallama, komawa yayi yajingina da kujera, shima murya can k'asa ya amsa mata, yace, " gimbiya yajikinne?".
"Ga shinandai, ya aikin?". 'Duk a shagwa6e take maganar'.
Saida ya furzar da huci sannan ya amsa mata da Alhmdllh, yaudai babu zazza6in ko?".
" akwai mana, yanzuma nagama amai".
"Wannan amai bazai tausayaminba, yabarki kid'anyi k'ibama, mikikaci to?".
"Kunun gyad'ane".
" sannu kinji sholyna, babies suna wahalarmin dake, dolene idan sunzo duniya namusu bulala, Saboda wahalarmin dake dasukayi, kona dawo gidane?".
'Yar dariya tayi, wadda tadad'e batayiba, tace, _''A'a Sadauki, gara kazauna a office, kullum burina bai wuce kakawo k'arshen azalumaiba, idan kayi hak'an 'ya'yankama zasuyi alfahari dakai, hakan zaikuma tabbatar musu mahaifinsu jarumin jarumaine, 100% nimai k'arfafakace, bamai raunanakaba, koda yaushe addu'ata nanan biye dakai, nidai Burina kada kabar Azzalumai suyi barci mai dad'i, kahanasu dariya da farinciki, ALLAH ya dafa maka mijina abin alfaharina nida al'umma💋💋._
d'ifff takashe wayar.
Zabura ya khaleel yayi daga kwancen dayake yana saurarenta, "please karki kash......"
Ina harta kashe, cikin hanzari yake dialing d'in number, amma ance switch up, yagwada yakai sau hud'u amma maganar d'ayace akashe take. Maida akalar Kiran yayi kan Ammah, cikin kwakwazonta ta amsa, dama Amman bata iya waya ahankaliba🤣.
Kowacce Lamba da alamar datama mutum yanda zata gane, Dan haka khaleel Na kira taganeshi, iro!! Kaine da rana tsakarnan? toya ofishin nakune?".
Dafe Kansa yayi, afili yace, ''wayyo nafa kira uwar kwarmato, yanzun saita had'amin mutanene gidan duka".
"Wai iro Baka jinane?! Allo iro!, nifa banajinka, inaga natuwok ne, kasake kirana kawai ta ajiye batareada ta Yanke wayarba.
tsaki yaja ya Yanke wayar, afili yace, " kai tsohuwarnan akwai kwakwazo, zubaina kenan, tuni Ammah zata saka kwalwar mutum harmutsewa, shi kawai inda yake sonta akwai tsage gaskiya".
Komawa yayi Yakuma lafewa jikin kujerar, kalaman Aysha sai kai kawo suke a zuciyarsa, yarasa mitake nufi? Yakuma kasa fassarasu? Amma tabbas kalaman NATA sunfi kama dana mai gugar zana.
"O my god, waimike faruwane?".🤦🏻♂
*********
Gaba d'aya yau haka yaraba hankalinsa biyu a office, rabi kan aiki rabi wajen FASA kalaman Aysha Dason fassarasu, amma har kusan 11 Na dare dayakai baisamu fashin bak'i ko d'ayaba.
____________________________
Wajen k'arfe d'aya Na rana saiga hajia khaltum tazo yima Momy barka da tashin bak'i, batasan abinda yafaruba ita, saboda tayi tafiya zuwa Benue state tun washe garin bikinsu mufeedah, wani aikin k'ungiyane yakaita.
Tunda tashigo falon taga sauyin fuska ga aminiyar tata, bata damuba tazauna suka gaisa, Momy tajata suka tafi k'uryar d'aki kamar yanda suka saba, saboda bataso yaranta su fahimci komai, babuma kowa daga ita sai zuwairah da mashi'a mai aiki, ganinma tayi bak'uwa Anty zuwairah tad'auki gyalenta tafita nan makwaftansu gidan wata k'awarta Tamata sallama.
Mashi'a ce kawai a kichin, itama ganin Anty zuwairah tafita sukuma shunshige bedroom saita turama Aysha message akan tazo.
Aysha nakwance ciwon ciki ya isheta taga message d'in mashi'a, amma dan k'arfin hali haka tasato jiki tafito.
Hajia babba da hajia khaltum na shiga d'aki suka zauna a bakin gado, hajia khaltum ta kalleta, "umm aminiya barka da tashin bak'i fa, Ashe 'yan biki duksun kama gabansu?, kai Alhmdllh, daganan kuma sainasu babie na, kisan kuwa yanda aiki yayi k'yau a Benue? Yara kusan 13 nasamo mana, kuma zagad'a-zagad'a, wannan karon kubrah ce zata tafi dashu UK, munsami sabon dila ma bayan john, hhhhh aikifa na k'yau aminiya, kud'i sai k'ara zama sukeyi, shiyyasa ban damu da account d'ina da Ibrahim yarufeba, saboda k'aramine, nidama bana zuba zunzurutun kud'i a banki aii."
Itadai Momy batace k'alaba, duk uban surutunnan da hajia khaltum kezubawa, bata kula Momy tayi kicin-kicin da fuskaba, saida takusa kai k'arshen aya sannan talura.
" a'a aminiya waishin lafiya kuwa?".
"Da sauk'i dai khaltum".
"Mike faruwa to?".
" mufeeda tadawo gida tun kwana biyar dasuka wuce".
Wata zabura hajia khaltum tayi, tagyara zamanta sosai tana fuskantar hajiya babba, "ki min dallah-dallah mana yanda zan fahimta".
Afad'ace hajia babba tace, " aii dolene namiki dallah-dallah kuwa khaltum, domin tasilar habibu aka sakkomin d'iya, habibu ya yaudare Mufeedah ya d'irka mata ciki, wannan ne dalilin dawowarta gida harda saki".
"Habibu kuma? Habibuna daine ya yaudari mufeeda da girmanta? Shekarun mufeeda nawa aduniya hajia laurah? Ince 27? Yanzu mai shekaru 27 ne aduniya za'ace an yaudareshi?, please babu wannan tsakaninmu, idan har cikin ya bayyana jikin mufeeda, kuma yakasance Na habibune to tabbas da had'in kanta, amma babu batun ya yaudareta anan, idanma gaskiya kikeso kawai mu jingina laifin Kansu su duka, amma bawai shikad'aiba......."
"K!!! Hajia khaltum!, wlhy ki iya bakinki, zan d'auki komai arayuwa amma banda wulak'anta rayuwar 'ya'yana, ya ina gaya miki magana zakina gayamin babu dad'i? Kema kinsan wanene bunsurun k'aninki aii........
" laurah!! Maza sakama bakinki linzami wlhy, inhar habibu bunsurune aii mufeeda ma akuyace, tunda ba har ciki gida yazo yamata fyad'eba, kum.........
Aysha data shigo d'akin da sauri tace, "kai Sirikata kuyi ahabkali, kuna d'aga murya dayawafa, gashi ya khaleel yana gida, kuyi maganar k'asa-k'asa surukata🤭. Saikuma Aysha ta shek'e da dariya.🤣
Daga hajia khaltum har hajia babba mutuwar tsaye sukayi, suma kasa cema Aysha uffan
Showing 105001 words to 108000 words out of 181849 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36 Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61