harma tana ganin jiri, gashi tak'i cin abinci har 4 Na yamma, shine nasake kiransa, hak'uri yabani akan bara ya bincika text d'in daya mata, saiyazo da sakamakon, dakuma maganin daya dace tasha.
Nacemasa shikenan ngd.
Wajen misalin 8:30 saigashi yazo, saidai duk yanayinsa ya nuna a sanyaye jikinsa yake, kirana gefe yayi yabani result d'in. wlhy baffa Dana bud'e saida juwa ta kwasheni, saida doctor Ameer yarik'eni saboda tashin hankalin abinda ke ciki.
Dana dawo dai-dai nahaushi da masifa akan baisan aikinsaba, yanata bani hak'uri dason fahimtar dani amma nak'i saurarensa, saina d'auketa mukaje Rahma especial hospital, amma bayan gama dubata result d'in duk d'ayane dana doctor ameer, saidai saboda bushewar zuciya irinna mufeeda ta dage akan k'aryane wlhy, tun a asibiti muka fara fad'a, ganin abin zaiyi tsamari karnaje Na daketa Na illatata nakira ummi Na Na sanarmata komai, tun a Daren sukaje suka taho da mufeeda nan maitama, anan gidanmu takwana".
"Humm mi result d'in ya nunane Aminu?".
Farar takarda Aminu yamik'ama baffah kansa ak'asa.
Baffah ya kar6a zuciyarsa Na harbawa, jikinsa a sanyaye yamik'ama Ya sultan, Dan bazaiso yafara ganiba, gudun karyaga abinda zai saka zuciyarsa bugawa.
Ya Sultan yabud'e takardar yafara dubawa, saida yamik'e tsaye Dan tashin hankali, har zufa saida tafito kan goshinsa, murya Na rawa yace, " mufeeda kin 6ata sunan gidanmu, da girmanki kije wani yamiki cikin shege harna tsawon watanni uku, kuma kinssan da hakan amma kika bari aka d'aura miki aure dawani?".
Duk falon kowa sallallami ya d'auka, baffah kam yakasa koda motsi, hajia babba kanta ture mufeeda tayi daga jikinta, ta fisge takardar daga hannun ya Sultan tana dubawa, jikinta sai 6ari yakeyi kuwa, aii batakai k'arsheba tazube awajen.
Zuwaira da ya sultan dasu mama duk sukai kanta, ya mujahedeen kam sarkin zuciya aii kan mufeedah kawai yayi yahau duka kamar ALLAH ya aikoshi.
Da k'yar Aminuddin ya kwaceta a hannunsa, please ya mujahedeen kayi hak'uri kasan ba ita kad'ai baceba, kar dukan yajawo wata matsalar".
"Kabarni Ameenu, sainama yarinyarnan dukan mutuwa tafad'i yanda akayi, munafuka afuska kamar bazata iyaba, idanma ka hanani dukanta wlhy ya khaleel yadawo saiya kusan kasheta agidannan".
Duk da hakadai kayi hak'uri Dan ALLAH, nima danya zama dolene asani shiyyasa nafad'a wlhy".
Ammah da hankalinta nakan d'anta baffah tace Ameenu kabarsa yadaka fitsararriyarnan, Mujahed kiramin Babanku Ma'aruff awaya.
Ya mujahedeen yana huci yakira uncle Ma'aruff dayaje gidan wani abokinsa.


____________________________

Lokacin da ake bak'incikin cikin dake jikin Mufeey baby🀣, ya khaleel nacan Na farincikin result d'in kazarsa da Aysha taci tabiya a asibiti.
Gwajin farko doctor Faisal ya tabbatar musu Aysha ta harbu, cikin watanni biyu da sati πŸ‘†πŸ»πŸ˜€.
Wayyo zokaga bidiri wajensu anty Shukurah da Ama...
Oga kwata-kwata kam rungume Aysha yayi dukda tana barci ansaka mata k'arin ruwa, hawayen farincikine ke zirara a kumatunsa, wai yau shine za'a haifama d'a, gudan jininsa, wanda dole akakira sunan d'an ahad'a da nasa sunan, duk inda 'yar ko d'an yaje za'ace d'an/'yar Ibraheem khaleel ce, wayyo ya ubangijina, kaike bada k'yautar da kud'i ko mulki bazasu sayaba, kaike bada abinda babu wani mahaluki aduniya dake ikon bama mutum ko hanashi sai kai kad'ai ubangijin talikai, ngd maka godiya mara adadin k'ididdiga, godiya irin wadda tafi k'arfin harshe, saidai zuciya taita ayyanawa.
Duk su Hafiz cirko-cirko sukayi suna kallonsa, kowa fuska d'aukeda murmushi, yau sunga farincikin d'an uwansu.
Cikin tsokana hafiz ya kirashi, "ya khaleel tunda nina kawota asibiti idan ta haifi namiji sunana za'a samasa".
Dariya duk sukayi, harda ya khaleel da idanunsa ke a lumshe, ya kwantar Aysha ahankali yana kallon Hafiz, " Hafiz ko sunan 'yan gidanmune duka zan iya sanya masa ko mata kaji".
Nanma duk dariya sukayi, Hafiz yaciro waya zai kira gida yayi kwarmato Anty shikurah ta dakatar dashi, "A'a Hafiz dakata, dolenefa mufad'a yanda za'a bamu goron Albishir, wayakamata afara kira?".
"Anty!, baffah ko Ammah".
" yes akirah Ammah, tunda itace tushen kowa".
Hafiz ne yakira Ammah, dukda yanda ta amsa sallamarsa bai damuba, Dan zumud'i baisa yagane muryar tata da damuwaba, "Ammah Albishirinki".
Cikin dakewa amma ta amsa da goro, Dan batason katsema Hafiz farincikinsa, dantaga azumud'i yakirata".
" mizaki bani to?".
"Duk abinda kakeso bayan kafad'amin kaza6a".
" anzo wajen, Anty Ayshan ya khaleel tanada ciki".
Da sauri Ammah tamik'e tsaye tana fad'in Alhmdllh, yanzu kuna inane?".
"Muna asibitin doctor Faisal, ansaka mata k'arin ruwa tana barci".
Duk jama'ar falon suna kallon Ammah ne, jira kawai suke tagama wayar ta sanar dasu abinda yasakata farinciki, dukda suna cikin bak'inciki.
Tana yanke wayar kuwa tayi gud'a, dafad'in "Alhmdllh. Dama wani Na haddasa maka damuwa wani yana yaye maka, matar iroce da ciki".
kowa saida yafurta Alhamdllh, banda hajia babba data farfad'o yanzu, hakama Anty zuwairah bak'inciki kamar zai karta.
Tuni kowa yadaina damuwa da cikin mufeedah yakoma murnar Na Aysha, mama dai batace komaiba itama, saboda kara.
Bayan uncle ma'aruff ya iso akabama dangin Aminu hak'uri, aka kuma sanar dasu za'azo har gida ak'ara bada hak'urin.
Annakuma take Aminuddin cikin jin kunya yabama mufeedah saki d'aya.
Babu Wanda yaji haushi, saidai mufeedarce ta rushe da kuka, momyma kukan zuci takeyi.
Sudai su Aminu sukayi sallama suka tafi, bayan sunmusu murnar cikin Aysha.
Babu wanda yasake bi takan mufeedah, Dan hukunci kuma sai'an zauna, baffah ya sallami kowa, suka d'unguma zuwa asibiti.
Momy dai da Anty zuwaira basubiba.🀣.lol.


********

Labarin cikin Aysha dana mufeeda yakarad'e gida, harda result d'in saki d'aya.
Kowa saidai yace ALLAH ya k'yauta, Na Aysha kam sai murna sukeyi, musammanma 'yan Kano.
Amma da baffah dawasu cikin 'yan Kano da uncle ma'aruff dasu Sultan, Anty Mamie duk suka d'unguma zuwa asibitin.
Har lokacin dai Aysha bata farkaba, ya khaleel yana manne kusada ita yak'i ya matsa konan dacan, jiyake yana matsawa wani Abu zai iya samun matarsa da cikinsa.
Su Anty Ama....... Sai dariya suke masa kuwa, INA ko'a jikinsa, dama ya khaleel da son yaran tsiya, barekuma yau ganashi😁.
Su baffah sun iso anatama juna barka da addu'ar ALLAH ya sauketa lfy, ya khaleel kuma duk sai kunya tad'an kamashi, sai sinne kai yakeyi kuwa.
Harma abin yabasu dariya, Ammah ta tasashi gaba da tsiya kuwa, shiru yayi yakasa maida mata, saidai su ya Sultan ke karemishi da uncle Ma'aruff.


____________________________
Sai kusan 1 Aysha ta farka, lokacin su ya khaleel sun fita sallah, Anty Mamie Ce kawai da Ammah, saisu Anty Shukurah dawasu daga bak'in Kano da gwaggo bintu, duk suma sallar sukeyi..

Aysha tabud'e idanu da kyar, ledan ruwan tabi da kallo har k'arshe, ta lumshe ido tareda maida kallonta Kansu Anty Mamie dake sallah, aranta tace ni Aysha nice da kwoncia asibiti? Banta6a ciwon daya kwantar dani asibitiba, ta yunk'ura danta tashi amma saida kasa, saboda jikinta babu kwari, kusan tun shekaran jiya rabon Aysha dacin abinci, saidai taci wannan taci wancan, shima 'yan yame-yamene, bawai abincin kirkiba.
Komawa tayi takwanta tana sauke numfashi da k'yar, Anty Mamie ce tafara hangota, da Sauri tamik'e ta k'arasa gareta, ''Aysha kin tashi?".
Kanta ta iya d'agama Anty Mamie da k'yar, sannu kinji, mike miki ciwo yanzun?".
"Anty Mamie yunwa nakeji wlhy".
" ok... To mizakici?".
Shigowarsu ya khaleel yakatsema Aysha bada amsa, duk suka k'araso gaban gadon da sauri, suma su Ammah sun idar.
Sannu duk suketa mata, ya khaleel kam yakasa cewa komai, sai kafe Aysha yayi da idanu, jiyake kamar ya tsaga jikinsa yasakata. Itadai sau d'aya ta saci kallonsa. Anty Mamie takuma cewa ''fad'i mikikeson ci a nemomiki?".
Saida tad'an yatsine fuska sannan tace, "Anty Mamie kaza gasashshe, da papcorn, da waina masa, sai kuma ice-Cream da shinkafa da wake, garau-garaufa irin adafata daga attarugu sai manja kad'an da daddawa".

Kutttt miza'ayi inba dariyaba🀣🀣🀣, har baffah dariya yake mata.
Ya khaleel kansa harda jingina da bango saboda dariya.
Itako ta turo baki, danmi za'a mata dariya, itafa da gaske yakeyi duk zata iya cinyewa🀣🀣🀣🀣.


Ho sholyn sadauki, nimafa kinbani dariya, nasan dolene fans ma su dara🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣.

Saida suka gama cin dariyarsu sannan uncle ma'aruff yace, '" karki damu d'iyata, yanzunnan zaki samu duk abinda kikeso, amma bara afara siyo miki abinda ke kusa ko?".
Kanta ta gyad'a masa tana murmushi.
Ya khaleel aransa yace lallai ba'a biyani kazata abanzaba ashe.πŸ˜‰πŸ˜‚


Babu dad'ewa saiga ya Mujahedeen yadawo da kaza, harma dawasu abubuwan.
Sanda yadawo nurse tashigo tacirema Aysha k'arin ruwan, aka kawo mata wata tasa ta wanke bakinta, sannan Anty Mamie dakanta tadinga bata kazar, saidai kuma bataci ta kirkiba labarin ya canja, tafara yunk'urin amai, kafin abata wani taimako tafara kwarashi.
Duk kuma sai tausayita yakamasu, kowa fuskarsa ta canja, saida tagama sannan nurse suka shigo suka gyara wajen, ya khaleel kamar zaiyi kuka.
Doctor Faisal dakansa yashigo yakuma dubata.
Cikin damuwa ya khaleel yace, "yanzu nan doctor haka zatayita amayar dad'an abinda tasamu taci?".
" saidai hak'uri j!, amma inaganin kawai mutafi gida da ita saina saka mata wani k'arin ruwan a can, zaima taimaka mata akan cin abincin, koya kukagani?".
"Hakan yayi doctor". 'cewar baffah'.
Kowa yayi na'am da zancen.

Saida doctor yayma Aysha Allurar barci sannan suka tattara suka fito, ya khaleel ya d'auketa kamar wata 'Yar babie, to dama tsawonne kawai, garama cikinnan yasakata 'Yar k'iba.
Koda suka Isa gida sai Ammah tadage akan 6angarenta za'akai Aysha, dole aka yarda a hakan saboda jarabar Ammah, inba hakaba kuma ta buwayi kowaπŸ˜‚.


πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€sai Ammarmu ko k'asar ba kowa wlhyπŸ€£πŸ€.

Ya khaleel kam baiso wannan tsari Na Ammah ba, yaso yabama matarsa kulawa da kansa, dukda dai yasan dawuya aikinsa yabarsa, ballema yanzu da aiki yagama rinca6e musu, cases sunyi yawa a hannunsa, wasu ana kan shari'a a Cote, wasu kuma anakan bincike, wasuma basu kamasuba.
Hakadai yadire Aysha a doguwar kujerar falon Ammah mai taushin tsiya, πŸ˜‰komaifa Na Ammah Na musamman ne😜.

Saida doctor Faisal yagama d'aura mata ruwa yatafi sannan 'yan uwa sukaita shigowa dubiya, 'yan Kano dai tafiyarsu saikuma gobe.
Mamaki yacika zuciyar ya khaleel danbaiga giccin Momy da sauran k'annensaba, Anty shukirah ce kawa. Ficewa yayi yanufi 6angarenta dam duba ko lafiya?................✍🏻





*_kuzo mu yanka cake tawan (Xoxo) tasamu lafiya,πŸ˜€πŸ‘―β€β™€πŸ”ͺπŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚πŸŽ‚, kowa dai yamaida kwad'ayinsa saita faraciπŸ˜‰πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€_*




*_ina Reefat yahaya 'Yar team d'in Hajia babba? Yakamata kimatso kusafa, takusa 6arewa dakuπŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ˜‚_*
Koya kukace fans?πŸ€·πŸ½β€β™€πŸ€£.






😍😍😍😍😍😘😘😘😘?*_TypingπŸ“²_*


🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_


*_Bilyn Abdul ceπŸ€™πŸ»_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyuπŸ“˜)_

_Tab, aii yau kowa yamatsa gefe, gaisuwar ta manya-manya ce, duk wata mai suna *MARYAM* tasaka a ranta wannan page d'in natane, saboda darajar sunan (uwa😘) Alkairin ALLAH yakai muku masu sunan girma, *Maryam A.I gital & Maryam Ibrahim (maman hanan)* ALLAH yak'ara girma my dears momys😘😘😘😘😍😍😍😍❀❀❀._

3⃣1⃣

Cirko-cirko yatadda sauran bak'in dasuka rage basu tafiba, daka gansu kasan arikice suke, batareda da neman ba'asiba yanufi d'akin Momy da hanzari, inda yakejiyo kakari tamkar namai shirin mutuwa.
Nanma zamu iya cewa kusan cike yake da mutane, sai k'ok'arin d'aga Momy akeyi daga kan mufeedah data shak'e akan saita fad'a mata Wanda yamata ciki (itace mai kakarin mutuwar).
Da sauri yafara ture mutane yaje har Gaban momy, k'arfin namiji dana mace ba d'ayaba, sannan sabon jini da tsohon jini akwai banbanci. Da k'yar yasamu damar fincike mufeeda daga shak'ar momy. Dagashi har momyn hakki sukeyi, mufeedah kuwa tuni ta sulale k'asa saboda wahala, da sauri Aleeya da kubrah suka Tallafeta.
Cikin hakki yace, "Haba momy minene yayi zafi haka? zaki kasheta."
''Aigara nakasheta Ibraheem, danasan irin mufeedah zan Haifa wlhy da tun bata wuce wata d'aya acikinaba zanje amin raga-raga da ita aciki ajuye amasai."
Tafashe da kuka tana fad'in "kin cuceni mufeedah!".
" mufeedah kuma!?". 'Ya khaleel ya ambata yana juyawa yakalli mufeedah, shifama duk zatonsa Hasnah Ce ko Husnah. dukda tabbas yaga mufeedah tashigo gida lokacin zasu tafi asibiti, amma farincikin daya tsinci kansa aciki yasakashi mantawa da ita.
Baice komaiba yajuya yafice daga d'akin, kowa da kallo yabishi.


6angaren baffah yaje, suna zaune shida uncle ma'aruff, abinci sukagama ci, suketa hirarsu ta zuminci.
Uncle ma'aruff mutumne mai yawan barkwanci, kuma har 'ya'yansa bai bariba, ya kalli ya khaleel daya shigo da sallama yace, "inye kaga d'ana anzama baba, harfa kakuma wani girma yau".
Dukda damuwar daya tsinto a 6angaren momy, hakan baihanashi yin murmushiba ga uncle ma'aruff.
Baffah yace, " ALLAH Ma'aruff karink'a girma dai."
"Hhhh Yaya kenan, aii ko kura da 'ya'yanta take wasa a daji, idan banyi danawa 'ya'yanba dawa zanyi?."
Baffah baice komaiba, sai 'Yar dariya dayayi, idonsa nakan khaleel d'in, Dan tun shigowarsa ya hango damuwa k'arara afuskarsa.
"Mu'azzam lafiya dai?".

Da k'yar ya khaleel ya had'iye yawu, " baffah miya dawo da mufeedah gidane? Na taras momy Na Neman kasheta yamzun".
"Kisa kuma? Yanzu ina mufeedah d'in?".
''Tanacan".
Waya baffah yad'auka yakira Ammah, ya sanar mata yakamata suzo su zauna, kuma ta aika akiramata mufeedah suzo tare.
Yana katsewa yace, " mu'azzam kiramin sultan da mujahedeen ".
Jin jina kai ya khaleel yayi kawai.
Baffah kuma yakira mama, Anty Mamie da umme amarya.
Babu dad'ewa saiga mufeedah da ammah, harma da momy da Anty zuwairah. Saikuma su mama ma suka shigo dasu sultan.
Kowa waje yasamu ya zauna, falon yayi tsit, sai shashshekan kukan mufeedah kawai.
Baffa zaiyi magana wayar ya khaleel tayi Ring, Ciro wayar yayi yaduba, cikin hikima yabi mutanen falon da kallo, saida ya tabbatar babu maijin French acikinsu sannan ya canja harshe.
Taheerne yakirashi, bayan sun gaisa yace, "sir matarfa damuke bibiya tana nan acikin gidanku, kuma tabbas duk yanda mai email d'innan ya musalta haka mukabi, yau kwannata uku anan gidan".
" gidanmu kuma?". 'Ya khaleel yayi tambayar da mamaki'.
"Yes sir".
Taheer to ad'an k'ara mata lokaci muga idan zata bar gidan zuwa gobe, Dan gaskiya banason akamata agidanmu, hakan zai zama rud'ani sosai, mak'iyana kuma zasu sami hanyar ruguza mana aiikinmu, Dan dolene nabi cikin hikima wajen duba mai alak'a da ita acikin gidanmu, sannan kubar matar Alhaji mustapha itama karku kamata, tunda har yazamto wannan matar Nada Alak'a da gidanmu dolene nabi ta hanyar matar Alhaji mustapha d'in Nagano komai".
"OK sir, babu damuwa, saikajini".
" aha kukula".

Babu Wanda yafahimci inda maganar ya khaleel ta nufa, tunda basajin French, saidai haka kawai momy tatsargu, duk saitaji damuwarta tak'aru.
"Ammah tace, " d'an nema iro, katasamu gaba kanamana yaren aljannu, kaiwai kanka Abu nawa yake d'auka? Yare nawa kakejine?".
Kusan duk saida aka dara.
Showing 87001 words to 90000 words out of 181849 words