Ya khaleel yamata harar wasa, kajimin tsohuwarnan, aii duk abinda kika zuba akaina saiya zauna, wuyarta dai ki zubad'in".
''Kai dallah rufamin baki, aiko wataran sai kanka yabuga saboda ajiye-ajiyen tsiyarka, shikenan an maida kwalwa kamar container".
Nanma dai saida aka dara, amma banda momy da Mufeedah.
Babuma Wanda yadamu dasunyi kobasuyiba, baffah yay gyaran murya da sallama, sannan ya maimaita dukkan abinda yafaru d'azun, dama ya khaleel ne kawai babu, aka mik'a masa takardar result d'in yagani, aikam cikin fushi yamik'e, saida yayma mufeedah Marika har hud'u, sannan uncle ma'aruff ya tsaidashi, "ya isa haka Ibrahim, barta saboda ba ita kad'ai baceba.''
" kabarni uncle, Na jigata ga6o6in jikin dabbar yarinyarnan, yanzunan dama akwai wata yarinya 'Yar gidannan dazata iya aikata wannan aikin?", yakuma kaimata halbi.
Da k'yar uncle ma'aruff yajanyesa, yamaidashi ya zauna.
Cikin shashshekar kuka momy tace, "Alhaji kawai azubar da cikinnan".
Kafinma baffah yayi magana ya khaleel yace, " wlhy saita haifeshi, muba jahilai baneba".
To dan ubanka nice jahilar? Ibrahim ka kiyayenifa".
Shiru yayi, Dan kalmar jahilcin nan su6utowa tayi daga bakinsa, baimasan yafad'aba, Yakuma mance momyce tayi maganar.
Ganin tanata banbamin masifa, tana Neman sauke fishinta akan ya khaleel, Anty Mamie dake bayansa zaune akujera ta zungureshi da k'afa.
Waigowa yayi yadubeta, tace, "bata hak'uri mana, karka sake furta hakan ga mahaifiyarka babu k'yau".
" wlhyn Anty Mamie su6ucemin maganar tayi, ammah momy kiyi hak'uri".
Tsaki kawai tayi amma bata tankaba.
Baffah yace, "maganar Mu'azzam gaskiyace, bazamu zubar da cikiba, dolene ta haifeshi sannan a dank'ama mahaifinsa. Saidai kafin sannan ''k mufeedah wanene mahaifinsa?".
Kuka sisai mufeedah tafashe dashi, saida mujahedeen ya daka mata tsawa, 'Yar iska kimana shiru kona dakaki wlhy, ubanwaye ubansa? Ko 'yan iskan naki sunwuce d'ayane?".
Sosai mufeedah take kuka, takasa cewa komai, aikam Ammah ta zuba mata rankwashi mai zafi akanta, Dan ubanki bazakiyi maganaba saina saka mujahedeen ko iro sun sassafaki anan?".
Rankwashin yashigi mufeedah sosai, tadafe kai tana k'ara k'arfin kukanta, cikin shashsheka tace, " Habeeb ne".
"Wane habeeb d'in?". 'Sultan ya tanbayeta cikin taushin murya, shidama baicika zafiba sosai'.
Saida ta saci kallon momy sannan tace, "k'anin Ammi".
" bantan ubannan, mufeedah kina nufin habeeb d'in hajia khaltum!!? ". 'Momy tayi tambayar a tsawace'.
Mufeedah Na matsawa baya tana kuka tace eh.
Sallalallami aka fara kuwa, banda ya khaleel dayakasa ko motsi, yama rasa wane hasashe zaiyi akan yaron, yasonshi kam, amma ya manta kamanninsa gaba d'aya, kafin tunaninsa yadawo yaji fad'uwar momy.
Kowa kanta yayi.



*_Bayan wasu hours_*

Momy na a kwance cikin d'akinta, an saka mata k'arin ruwa, barci takeyi, su khaleel Na zagaye da ita, tuno da Aysha dayayi yasakashi mik'ewa.
Anty zuwairah takalleshi, "ina kuma zakaje khaleel?."
"Zan duba A'eesha kota tashine".
Shiru Anty zuwairah yayi, Anty shukurah tace, " yakamata kan adubata itama, dukda Ammah Tanacan".
Baice komaiba yafice.


Ya Tatar har yanzu Aysha tanata barcinta, Dan ruwan an sakashi can k'asane, yana d'iga d'is-d'is.
Yazauna kusada ita, idonsa kan k'yak'yk'yawan face nata, tayi fari tas da ita, amma yau saiyaga ta rame masa, hannu yasaka yana shafa kwantaccen gashin kanta.
"Tofa sannu jananu kuke cewa ko janinu?".
'Dago manyan idanunsa dasuka koma jajaye yayi yakalli Ammah, guntun murmushi yayi saboda maganarta tabashi dariya, yasan tanaso tace (majnun) ne, shinefa taketa wannan kame-kamen wai jananu da janinu😊.
Itama kusada k'afafun Aysha ta zauna tana kallon khaleel.
Iro! Nikuwa ga wata shawara.
"Inajinki Ammah".

"mizai hana itama mufeedah tadawo nan wajena, idan kuma ba hakaba tofa uwarka tana samun lafiya zatasa a 6arar da cikin jikin yarinyarnan, Dan naji ta goyi da bayan jimmai, jimmai k'anwatace ciki d'aya, nasan halayenta sarai kuma, zata iya fiyema da hakan".
Gaskiyane Ammah, nima Na yarda da maganarki, kawai zuwa anjima kije da kanki ki izo k'eyarta".
"A'a a'a, kaizaka kawota da kanka iro, kasandai sungama rainani, dannima dai d'in jar wuyaceπŸ˜‚ shiyyasa wani lokacin suke shakkata".
Kasa daurewa ya khaleel yayi, saida yadara, wai jar wuyaπŸ˜†, kai tsohuwarnan saidai abarta kawai.
Saida yagama dariyar sannan yace shikenan zan kawo miki ita kinji Jar wuya".
" yo iro, idanma da shak'iyanci kake fad'ar jar wuyar aikayi tabanza, kowannan jarumtar dakake tak'ama da ita awajenwa kasamu albarkaci? Aii a wajenace da dattijon mijina m. Rufa'i".
"Gaskiyane Ammah jar wuya, aini dagama yau jar wuya zan ke cemiki, tunda nima kink'i daina fad'amin iron".
" naka wasane yaro, aii iro har 'ya'yanka babu fashi, baridai wannan farar komon matar taka ta haihu".
Fuska ya had'e yana Harar Ammah Da wasa, ALLAH jar wuya kifa iya bakinki, matar tawaje farar komo? Saikace wata faraπŸ¦—?".
"Yo daga fad'ar gaskiya, ba farar komon baceba, yanzufa saika tattarata kubarmin waje".
" aini dai-dai kenan jar wuya, dama zakiyi haka har k'yauta zan miki, dama aii iyayinkine yasa kikace akawota nan".
"Fitsararre, to bazan badatanba, salon kaje ka antayar dad'an cikin damuketa faman murna, tashi kaficemin anan dogon banza maikama da bishiyar giginya".
" kema kikasan giginyar, idanma baki bani da arzik'iba ainazo Na saceta, haka kawai da matarka amaidakai gwauro, gaskiya jar wuya bak'ya k'yautawa da irin wannan mulkin naki".
Murfin kwanon data bud'e fura tad'akko.
Yasan kad'an daga aikin Ammah ta kwala masa, aiko da gudu yafice.🀣
Murfin kwanon ta ajiye tana fad'in "d'an nema, wlhy d'an kwal uban yaronnan iro yagama rainani, dogon banza kawai".
"Kai dogo matarka doguwa, haka zakuyita haifama mutane shantalin yara".



🀣wayyo ammarmu.




Kuyi hak'uri da wannan, yau kaina ciwoπŸ€¦β€β™€ yakeyi, danma karna barku hakanan nasamu nad'anyi wannan d'in.








*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu baki d'ayaπŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ™πŸ»πŸ˜­_*?😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘😘?😘😘?πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“*_TypingπŸ“²_*


🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_


*_Bilyn Abdul ceπŸ€™πŸ»_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyuπŸ“˜)_

_Gaisuwa da fatan alkairi agareki takwarata, Bilkisu, *(Ummie Garkuwa writer d'in JENNIFER)* ALLAH yabar zuminci, ina godiya agareki har babu adadi, I love you so much wlhy my Sister._
β€β€β€β€πŸ’ƒπŸ»


3⃣2⃣

Da dariya ya isa 6angarensu, yacire kaya yashiga wanka, can k'asan zuciyarsa kuwa tana cikin nishad'i, yayinda gefe guda kuma yake tunani akan matar da taheer ya tabbatar masa tana cikin gidansu, dadai Aleeya zuciyarsa ke zargi, amma idan yatuna da cewar ance kwannanta uku agidan saiyaja tsaki, afili yace, "to wacece wannan?".
Haka yayta sak'awa da kwancewa harya kammala wankan yafito, gaba d'aya kwakwalwarsa a dagule take, abubuwa biyu sun gitta masa a ranar farin cikinsa, ranar data kasance yadace yayta murmushi har washe garinta.
K'aramin tsaki yaja, sannan yahaye gado yakwanta danya d'an huta.


____________________

Farkawar Aysha tasaka ammah saurin isowa gareta, sai sannu take mata, Aysha kuma tana d'aga kai da k'yar, ta yunk'ura zata tashi taji hannunta yamata nauyi, dakatawa tayi tabi hannun da kallo.
Ammah tace, "karki tashi. Bara nakira iro yazo yacire miki, shima nazata bama zaiyi nisaba aii".
Aysha dai batacewa Amman komaiba.
Kiran ya khaleel Ammah tayi, bayan tagano Alamar data sakama number sa da k'yar, harta yanke bai d'aukaba, kunsan dai Ammah babu sauk'i, tacigaba da doka masa kira babuji babu gani.

Tun yanajan k'aramin tsaki cikin yanayin barci, harya bud'e idonsa ahankali, sosai kirannan yatakurasa, batareda yaduba wake kiransaba yad'aga yakara akkune, a muryar barci yace, "hallo! Please wanene".
''Iro nice, kazo kacirema Jikata wannan ruwan ta farka".
Da sauri yatashi zaune, ''Ammah kina nufin A'eesha ta farka?".
"Eh, kana inane?".
" ganinan zuwa".
Bai jira cewartaba ya yanke wayar, sakkowa yayi daga gadon yashiga bathroom, mintuna kusan 5 yafito.

*******
Da sallama yashigo, haryanzu Aysha Na kwance Ammah ta hanata tatshi, yak'araso da saurinsa, gaban kujerar ya durkusa saitin fuskar Aysha, idonta Na a lumshe yasaka hannu yana shafa kwantaccen gashin goshinta, ahankali ta bud'e shanyayyun idanunta, wad'anda ciwo yasakasu komawa k'ananu kuma sunyi d'anja.
Sassanyan murmushi yasakar mata, sannan ya sumbaci goshinta, ta kuma lumshe idanunta tabud'e ahankali bisa fuskarsa.
"Babiena ya jikin?".
Cikin mamakin sunan daya kirata dashi, muryarta can k'asa tace, "Alhmdllh."
" masha ALLAH, bara kiga acire ruwan tunda yak'are" kanta ta jinjina masa kwai.
Yacire ruwan sannan ya taimaka mata tatashi zaune, daidainan Ammah tafito daga kichin d'aukeda kula k'arama. Sannu itama tama Aysha, sannan tazauna gefenta tana tambayarta ina kemata ciwo yanzu?.
Aysha tace babu komai, saidai bakinta d'aci.
"Karki damu shima zai daina watarana?".
Nanma kanta kawai ta d'agama Ammah.
Ya khaleel yad'an murza hannunta dake cikin nasa, tajuyo ta kallesa. Gira d'aya yad'age mata, yace, " mizakici yanzu to?".
Janye idanunta tayi daga kansa, tad'an jingina kanta da gefen hannunsa, Dan zaman yafara gundurarta, cikin dadishewar murya tace, "dama zan samu dafaffen gyad'a".
Murmushi yayi yace, " saikuma mi?".
"Shikad'ai ya isheni ya Sadauki".
Yashafe fuskarta da hannunsa Na haggu, " haba my Sholy kidai fad'i wani abun bayan gyad'an, kinsan bakici komaiba".
Ta d'ago idanunta tana kallonsa, fuskarta a yamutse tace, nidai gyad'an is OK, idan kuma za'a samu zogale ahad'amin dashi to".
Ammah dake kallonsu cikeda sha'awa dajin dad'i tace, "Abu mai sauk'ima kuwa, bara ajenan gidansu Ameenu arok'o zogalan tunda sunadashi, barama dakaina zanje aii".
"Yauwa Ammah jar wuya, shiyyasafa nake yinki akoda yaushe, dolene nasiya miki motafa".
Baki ammah tawashe. "Lah iro gaske ko wasa?".
" ahaf aii dagaske nakeyi ammah, amma sai nanda k'arshen shekara idan ALLAH ya kaimu, yanzu abubuwa sunmin yawa".
"Yo konanda shekara biyune aii zanhak'ura iro, kaidai kawai kacika alk'awari idan munkai daranmu".
"Insha ALLAH zancika ammah".
Ammah tafita anata washe hakwara ya khaleel zai saya mata mota.

Tana fita ya khaleel yamaida kallonsa ga Aysha yana murmushi, A'eesha kinfaji Ammah tsohuwa, ko INA ita INA mota?".
Murmushi Ayshan tayimasa, tace, " Yaya kacika alk'awari kawai".
Harar yazuba mata.
tace, "o, sorry sadauki, tayi maganar tana rufe bakinta da hannu.
guntun murmushi yayi, sanna yamik'e da Aysha ajikinsa yana fad'in muje kiyi wanka, kafin Ammah takawo zogalan ko, tunda kinsan saita dafa tukunna.
Cikin 6ata fuska Aysha tace, "to gyad'anfa kuma?".
Yatsansa guda d'aya yasaka ya d'alli bakinta.
Zafi yasakata dafe bakin da sauri.
Shikuma yay murmushi yakaita toilet d'in Ammah.
Dak'yar ya yarda yafito tayi wankan da kanta bayan yahad'a mata ruwa maid'an zafi, amma da ya dage saiya mata wankan dakansa.
Ganin shagwa6ar datake zuba masa zata sakashi ya narke, yasakashi hak'ura yafita.

Tanayi tana hutawa, haka tagama wankan, saboda jikinta duk babu k'wari, ga ko INA ciwo yake mata, musammanma mararta wlhy.
Koda tafito abakin gadon Amman ta iskeshi zaune, yabud'emata hannayensa alamar tazo gareshi.
Akunyace tak'arasa tashige kuwa, ya rungumeta tareda gyara mata zama acinyarsa, ahankali ya sumbaci goshinta, murya k'asa-k'asa cikin kunne yace, " nizan shiryaki ko? Tunda kin hana namiki wanka".
"kai ya khaleel wai bakajin kunya? Ammah fa zata iya shigowa ta ganmu".
Hannu biyu yasaka ya tallafe kumatunta, sai raba idanu yakeyi a fuskarta, itakam takasa kallon cikin idonsa, saikawai ta lumshe idanu, ganin haka yayi murmushi tareda d'ora bakinsa akan NATA yashiga abubuwa.
Tun tana k'ok'arin kwace kanta harta hak'ura ta mik'a wuya. Saida ya sumbaceta San ransa sannan yacire bakinsa suna sauke numfashi.
Kunya ta lullu6e Aysha, tayunk'ura ahankali zata tashi Yakuma rik'eta da k'yau, "kinga Izamanki, bara Na shafa miki man, nasan jikinki babu kwari sosai".
Dole Aysha tahak'ura ya shafa mata man, amma idonta arufe akayi komai.
Kwantar da ita yayi agadon Ammah yace, " kwanta kihuta inazuwa".
Ta gyad'a masa kai tana wani lumshe idanu, jinta takeyi wani fayau da ita yau d'inan wlhy.
Fitar ya khaleel babu dad'ewa saiga Anty Ama.. Tashigo, k'arasowa tayi Indaa Aysha take tana mata sannu, Aysha ta amsa kanta tsaye, harda cema Anty Ama wai mi doctor yace yana damunta?".
'Yar dariya Anty Ama tayi, tace, "ya khaleel nasan aii zai fad'a miki, yasan kin tashine?".
Aysha ta gyad'a kanta ahankali, kamar wata k'adan garuwa..
Babu dad'ewa ya khaleel yakawoma Aysha da doguwar riga Arabian gown, Anty Ama tatashi tafita.
Yanzuma dakansa yasakama Aysha kayan, duk kuwa kunyarsa ta gallabeta, harzai d'auketa tace, "please Anty Ama batatafiba fa".
Yad'an d'age gira yana ta6e baki, harya mik'o hannu zai d'auketa yajiyo sallamar Anty mamie a falo.
Dole ya dakata, yadai taimaka mata tamik'e zaune, dad'an rangajin rashin kwarin jiki ta isa falon, Anty Mamie tayi saurin tararta tana mata sannu, a kujera doguwa ta zaunar da ita ta jinginata da jikinta, yanzu ina ke miki ciwo?".
"Wlhy Anty Mamie dukdai banajin dad'in jikina, gakuma bakina d'aci".
"Sannu, Duk zasu daina kinji."
Ya khaleel kallonsu yakeyi cikeda sha'awa, saiyaji inama momyce kebama matarsa kulawa haka? kwallah suka cika idanunsa, karo Na farko dayafajin d'acin rashin kulawar Momy akansa, da k'yar ya maida kwallan, saidai tuni Anty Mamie tagani, ita kanta saida ranta ya sosu, Dan koba'a fad'aba tasan mi khaleel keyima kewa, (kulawar mahaifiya), amma yaza'ayi, haka ALLAH ya tsara masa.
Sallamar da Ammah ta doka yasakasu duk maida hankalinsu kanta, Anty Ama...tamik'e ta kar6i kayan hannunta tana mata sannu, "a'a Ammah mi'aka samomana kuma?".
" uhm mizan samo nikuwa, zogalene da gyad'a, wai Indo kesonci".
"Kai Ammah waye indo kuma?".
Da hannu Ammah ta nuna Aysha, "matar iro mana".
Mi Anty Mamie kuwa zatayi inba dariyaba, ya khaleel kam 6ata fuska yayi, Amma baice komaiba.
Zogalan Aysha tafaraci, babu laifi ansamu ya zauna, harma tad'anci gyad'ar.
Daganan akaita shigowa dubata, mama ma tazo, hakama bak'in 6angaren Momy da Anty shukurah tamusu jagora, Amma banda Aleeya da Anty zuwairah da kubrah, dama mufeedah ba'a sakata a lissafi, su Hasnah kuwa suna makaranta.


*****
Momy kuwa sai bayan magriba ta farka, bayan k'arin ruwan yak'are Aleeya ta cire mata.
Ya khaleel baije wajenba saida yadawo sallar isha'i, yatarar Momy zaune akan gadonta ta jingina da fuskar gadon, shayi takesha Wanda Hasnah ta had'a mata.
Yazauna kusada ita gefen k'afafunta, " momyna
Showing 90001 words to 93000 words out of 181849 words