yana ahaka sannan ahankali komai yadawo masa sabo fil, tamkar mafarki kokuwa film, wai Momy ba mahaifiyarsa bacebaπŸ€”, shiyyasa take masa duk abinda tagadama kenan?, kai wannan lamari akwai d'aurewar kai, ya tsurama Aysha idanu tamkar ajikinta yakeson gano gaskiya maganar.
Yaja mintuna masu tsayo sannan yatashi ahankali zaune, cire k'arin ruwan da'aka saka masa yayi, k'afafunsa yaziro k'asa ya sakko ahankali, dabin bango ya iso gadonda Aysha take kwance, yaja kujerar plastic fara yazauna, awahalce ya feso iska daga bakinsa, sannan yad'ora Kansa asaman shafaffen cikinta, maikama da babu wata halittar mutum acikinsa, ahankali yasaki kuka mai ta6a zuciya da ruhin mai sauraro, shikansa baisan dalilin kukan nasaba, bashida wani za6in daya wuce yayi kukad'in, Dan hakan shine mafi sauk'i agaresa, kwakwalwarsa takasa d'aukar abinda yafaru, Ajiyakam yamanta shikansa wane jinsine, namiji kokuwa mace?, Dan bashida wata aba jarumta ahalin dayake yanzun.
Acikin barci Aysha taringa jiyo kuka sama-sama, ahankali tabud'e idanunta tasauke akan d'an kufan gashin sumarsa, gabantane yashiga fad'uwa ganin ya khaleel yana kuka, saidai batada wani kuzarin tambayarsa kokuwa matsawa jikinsa, saikawai tazuba masa idanu tana kallonsa.

Da k'yar ta iya d'aga hannunta Na dama dababu k'arin ruwan tad'ora saman kansa, ahankali take shafa kwantacciyar sumar dabatada yawa, saboda askewa dayakeyi, itama hawayenne take zirararwa, tausayin ya khaleel yakamata, wannan wace iriyar rayuwace? Mi hajia laurah kenema itakuwa aduniyarnan? Miye dalilinta naraba d'a da mahaifiyarsa aranar datagama shan nak'udar haihuwarsa, bayan watanni Tara data d'auka Na azabar rainon cikinsa, amma saboda rashin tausayi atsige matashi batareda ta ko kallishiba taji sanyi aranta.
Yanzu da ALLAH baisa hankali ajikin khaleel ba, dahaka kullum zaita cin zarafin mahaifiyarsa amatsayin kishiyar uwa? Wanda hakan hajia babba taso yakasance, takan takali Anty mamie tsiya kodan khaleel yaci mutincin Anty mamie, Amma ubangiji gafurun rahimun saiya dakatar dahakan, yasaka kunya daganin mutuncin juna tsakaninsu, tareda k'arfin soyayya irinta uwa da d'anta.
Dr Faisal ne yaturo k'ofar, dasauri yak'arso inda suke, tausayinsu yakamashi, dukda baisan miya faruba, yafahimci tun ajiya family d'in suna cikin tashin hankali, yadad'e tare dasu, har ankai matsayin dazai iya sanin farincikinsu ko akasin hakan.
Dabaya yakoma, yakira baffah.
Jin sun farka yasaka su mama ma mik'ewa da sauri, saidai dole su suka tsaya ajikin window, baffah kad'ai yashigo.
Jiyayi kwalla tacika masa idanu, jarumin d'ansa mai k'ok'ari da dakakkiyar zuciyar tunkarar kowanne irin had'ari shine ke kuka, shikansa sometimes yakan jinjina jarumtar Mu'azzam, saboda mutumne shi mara tsoro, komai girman mulkinka zai fad'amaka gaskiyane awuce wajen, shiyace bashida lokacin zaman gulmar wani, amma kalla yaushine ke kuka, kuka ajikin mace, kuka irin Wanda Duk Wanda yagani zaisan kukan bak'incikine da k'unar zuciya.
Bayansa baffah yadafa shima yana k'ok'arin maida kwallar data cika masa nasa idon.
Jin k'amshin turaren baffah yasaka khaleel d'ago kansa, dasauri yafad'a jikin baffah yakuma sakin kukan.
Huci babbafa yafurzar daga bakinsa, yana shafa bayan khaleel da hannayensa, alamar lallashi.
Aysha kallonsu takeyi cikeda tausayawa, itama har sannan kukan takeyi.
Anty mamie tashigo itama, inda Aysha take kwance tak'arasa, ta zauna bakin gadon tareda d'aukar kanta tad'ora bisa cinyarta, tasaka hannayenta tana share mata hawayen.
"Ya Isa kinji d'iyata, daina kukan hakanan, kinga bake kad'ai baceba, ba'a son mai juna biyu da 6acinrai kinji.
Jinjina kai kawai Aysha ta iya yi, amma batace komaiba.
Shima baffah yanata lallashin khaleel, saida yasamu yayi shiru sanan, saman gadon baffah yamaidashi ya zaunar, yasaka masa filo yajingina da bango.
Dr Faisal yad'an duddubasu yace, " Alhmdllh. Yanzudai jikinsu normal, sai abasu abinci suci, ga magani susha, idanma ALLAH yataimaka k'ila mu sallamesu zuwa dare.
Hamdala duk sukayi taredama Dr Faisal godiya.

Mama da Anty zuwairah da Anty shikurah suka shigo, duk jikinsu asanyaye yake, sannu sukai musu, khaleel yad'ago ido ya kafe Anty zuwairah dasu, kallonta yakeyi tamkar Momy, Dan ita tana kama da ita sosai.
Jikin Anty zuwairah saiya kuma yin sanyi, Dan ganin kallon da khaleel kemata, kusadashi tak'arasa, takama hannunsa ta rumtse anata, hawaye masu zafi suka ziraro akumatunta.
Takasa magana, Dan batasan mizata cema khaleel d'inba, batada bakin furta komai, harshenta yamata nauyi.
Ya khaleel yasaka hannunsa ahankaki yashiga share mata hawayen.
Baffah dake kallonsu cikeda tausayi yayi murmushi, hakama mama da Anty Mamie.
Mamace tazo ta janyeta tana lallashi, ya isa haka zuwairah, kukan ya isa haka, tunjiya aketa Abu d'aya, dolene muyi hak'uri, bamuda dalilin canja k'addara, abinda yafaru yarigada yafarun, saidai mu kiyaye Wanda zai faru anan gaba kuma.
Ku sakama zukatanku hak'uri, muyimasu addu'ar samun lafiya kawai kunji.
Duk Kansu suka d'aga mata.

Anty shikurah tahad'amusu shayi, tamik'ama Anty Mamie dake tareda Aysha, Anty zuwairah kuma takar6i na khaleel, dakanta taringa bashi, baiyi musuba yakar6a tamkar wani k'aramin yaro😺.
Aysha dai dafarko tace bazata shaba, saida Anty Mamie da baffah sukaita lalla6ata sannan tad'ansha, kur6artama baifi hud'uba tafara yunk'urin amai, da sauri Dr Faisal yakawo wata tasa, aikam saida ta amayar dashi tas sannan aka samu sassauci, dukta gama galabaita, sai numfashi take fitarwa da k'yar.
Ya khaleel jiyakeyi tamkar yamata kuka, tausayi take bashi ainun, laulayin ciki yana bata wahala, gashi yazo ga6ar tashin hankalin dasuka tsinci Kansu aciki, duk Aysha tagama canja kamanni, tarame sosai, sai uban haske datayi, ko mak'iyinta dolene ya tausaya mata.
Shima daganan daina shan tea d'in yayi, duk lallashinsa da Anty zuwairah keyi itada mama k'insha yayi, hankalinsa gaba d'aya yanakan Aysha.
Bayan Anty Mamie ta taimakama Aysha ta wanke bakinta ta rungumeta ajikinta, saida tad'an huta sannan tashiga tambayarta mitake sha'awar ci yanzun?.
Shiru nad'an wani lokaci, sannan Aysha tace, "Anty Mamie zan iya samun fura".
" da guduma kuwa d'iyata, furama abu mai sauk'i".
Anty shikurah tace, "bara naje nasiya miki kinji sholyn khaleel". 'Tayi maganar cikin 'Yar tsokana'.
Saida kowa yayi murmushi kuwa, har khaleel d'inma, Aysha kam kanta ta 6oye ajikin Anty Mamie.

Bayan Anty Shikurah tasayo furarne a Shop d'in dake cikin asibitin tadawo tagamu dasu meerah sunzo dubasu.
Atare suka rankayo d'akin.
Nanfa aka shiga gaishe-gaishe da tambayar masu jiki, harda Aleeya akazo.
Sosai Aysha tasha furarnan, ALLAH kuma yataimaka ta zauna, batayi amanba.
Babu dad'ewa kuma saigasu Amal amare, Adams yakawota, saikuma gasu Hamdiyya, kowa mijinta yakawota yatafi, bayan sunshigo sun duba masu jiki, har Ammah, Adams dai anan aka barsa, Dan baigama hutun amarciba, amma yanaji aransa dolene yakoma aiki kam.
Bayan sun gaisa da kowa saisuka ragu, wasu suka tafi d'akin Ammah jar wuya, aikam tiryan-tiryan saida Ammah tabama su Shahuda labarin duk abinda yafaru ajiya, sunsha kuka kuwa, da tausayin khaleel da Anty Mamie, tareda jinjinama k'ok'arin mama da ummi amarya da gwaggo bintu, badai suce komai Akan momyba, kowa yabar tsinuwar dayake mata azuciyarsa.

************

Kowa yayi shiru, d'akin tsit idonsu akan TV suna kallon labarai a tashar NTA da ake maimaitawa Na jiya, labaran kamasu hajia babba dasu khaleel sukayine afarko.
An nuna inda aka kamasu, dakuma makamai dawasu abubuwa irinsu kwayoyi da cocaine da'aka kamasu da'ita, sai yara kusan 64 da'aka samo awani gida, wad'anda an ajiyesune ana shirin kaisu wasu k'asashe.
Saikuma aka nuno youseef yana tattaunawa da 'yan jarida. Yace.
"Kwarai da gaske, mundad'e Muna musu tsinci d'ai-d'ai, saidai bamusan gawurtarsu hartakai hakaba, abin bak'incikinma shine samun manya-manyan mutane masu fad'a aji ak'asarnan, wad'anda al'umma suka d'auki ragamar Kansu da d'aukarsu iyayen k'asa, amma sukaci amanarmu da k'asarsu wajen aikata wanann ta'addaci, wannan k'ungiya tanada k'arfin gaske, danba'a Nigeria kawai takeba, akwaisu ak'ashe daban-daban Na duniya, babbar illar dasuke mana itace d'aukar yaranmu mata suna kaiwa karuwanci, dashigo mana da miyagun kwayoyi".

*_'yan jarida:-_* "to amma yalla6ai, wane mataki kuka d'auka domin ruguza wannan k'ungiya mai k'arfin iko? Sannan zaku iya dawo da yaran dasuka salwanta tasanadin wannan k'ungiya?".

" insha ALLAH munakan yin hakan kam, Dan zuwa yanzun sauran ma'aikatanmu dake k'asashe daban-daban sun duk'ufa akan aikin zak'ulo dukwani mai alak'a dawannan k'ungiya. Sannan zamu dawo da sauran yaranmu gida da'aka kai wasu k'asashe".


*_'yan jarida:-_* "yalla6ai ance akwai jami'an tsaro dayawa ta fannonin kowanne aiki dake cikin wannan k'ungiya, kuma manya-manya masu fad'a aji, shin gaskiyane kuwa?".

" hakane, akwaisu, kuma insha ALLAH nangaba kad'an duk za'aji sunayensu, bayan mun kammala aikin cikin gida".

*_'yan jarida:-_* "yalla6ai dagaskene rad'e rad'in daketa fad'a cewar ankashe babban jami'in tsaronnan mai jarumtar aiki dakan tsorata 'yan ta'adda saboda rashin tsoronsa awannan gumurzu, Ibraheem Abdallah Jigawa, Wanda kowa yafi saninsa dasuna j!".

" hummm", youseef yafad'a yana murmushi.
"Gaskiya bahaka baneba, yalla6ai j! Yananan daransa, ko harbin bullet d'aya baishiga jikinsaba, Dan haka mutane su kwantar da hankalinsu, Ibraheem Abdallah bai mutuba".

*_'yan jarida:-_* ''to amma miyasa yak'i yarda kowa yagansa har zuwa yanzun? Ko hakan yana cikin sirrin aikine?".

Dariya.
" kokad'an Bahaka baneba, bai 6oye Kansa dan bayason agansaba, saidai wasu 'yan dalilai, amma insha ALLAH nanda kwanaki kad'an za'a iya jin bayanaima kaitsaye daga bakinsa".


*_'yan jarida:-_* "to ALLAH yasa hakan takasance, nasan kowa zaiyi murna da hakan, Dan zuciyar 'yan k'asarnan tana cikin jimamai dafargaba kam sosai, basuda burin daya wuce suka j! Darai ayanzu.
Duka duka anan muka kawo k'arshen rahoton namu, jama'a kuma yakamata su kwantar da hankalinsu, kundaiji yalla6ai j yananan daransa, saidai wani daliline ya6oyesa.
Munyi-munyi Nason jin dalilin 6uyar tasa hakan bai faruba, hakama munso jin tabakin shugaban wannan hukuma amma hakan yaci tura, munkira wayarsa har kusan sou hud'u bai d'agaba k'arfin had'a wannan rahoton.
ALLAH ka zaunar dak'asarmu lafiya, kamana maganin 'yan ta'adda.

Kowa ajiyar zuciya yasauke ad'akin, ya khaleel kam saiya lumshe idanunsama gaba d'aya...........✍🏻



*_Happy juma'at Mubarak my sweet fans_*πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ™‹πŸ»β€β™€πŸ™‹πŸ»β€β™€πŸ™‹πŸ»β€β™€.



Duk wanda yaga yamin magana ta PC ban amsashiba yamin afuwa, mura nakeyi, typing d'in kawai nake dauriyar yi, amma zan duba. ngd sosai.πŸ’‹πŸ’‹








πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜.



πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜πŸ˜˜.?.*_TypingπŸ“²_*


🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_


*_Bilyn Abdul ceπŸ€™πŸ»_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of expert & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyuπŸ“˜)_

πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€
*_yau ranarkuce masoya, kumarmatso kusa, ngd da k'auna da k'ok'arin bibiyata, inasonku irin trillions d'innan, kunanan manne azuciyar bilyn Abdul, bazan ta6a mantawa dakuba kona dak'ik'a d'ayaπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»β€β€β€β€β€β€β€β€β€β€πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹, kud'in nadabanne wlhyπŸ’ͺ🏻._*

Zainan umar, Mmn khadija, Hawwa, Aysha admin, Mmn siyama, Ummu hanan, Kbbello87, Amina isah n, Mycm, Zeeharuna, Mss calm, Maryam, mamu, Amina aliyu, Hanan yusuf, Haleema s adam, Ummu'assisdiq, Umar ruqaiyah, Precious, Hajara, Mmn fatima, Mmn beauty, Falmi k aliyu, Mariam a umar, Billy A A, Ummu barakat, Hajara isma'il, Fatima (zarah), Ummu Ahmad, Mommyn iman, Juwairi, Maryam Haruna, Mom muhaseen, Zubby Abdullahi, Maryam sulaiman, Mmn ihsan, Ummin sayeed, Nafisa salis, Amina musa, Aunty baraka, Mmn sanah,
Mmn fkyht, Marnona, Aneesah Abubakar Rimi😎(πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»my Dota), Ummy fingers, Rashida tabacco, Maman ihsan, Zainab, Maman Ruky, Sa'adatu Aliyu, maman AbdallahπŸ˜‚.

_ina mik'o gaisuwar ban girma da fatan alkairi_
πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ˜‰


4⃣2⃣

Alhmdllh jikinsu yayi sauk'i sosai, maganar 'yan dubiya kam ba'a cewa komai, manyan ogannin ya khaleel Sai zuwa sukeyi dubashi, hakama wad'anda suke k'asansa, abokan baffah ma da matansu, koda yaushe asibitin FAM da mutane, saidafa idon securitys nakan kowa, gudun kar a cutar da ogansu.
Ammah ma tanata samun lfy, Dan bakinnan yana nan rad'am🀣bai mutuba.

Nagafa gayyar fans dadama awajen sunzo gaisuwa, su o'e akaita washemin hakwara😁, naganoki toπŸ˜‚, kunjifa su madam son gulma anbaza kunne aji wacece, to nak'i fad'a d'in😏.

Da safe aka sallami su ya khaleel, amma banda Ammah, aikam tasaka rigima akan bazata zaunaba, aii k'afarta k'afar ironta, itafa baza'a barta a wannan asibitiba babu iro wani yabiyo dare yasakata abuhu.
Anta lallashinta, aka nuna mata akwai securitys za'a bari suna tsaronta.

"Yo duk tsaron mutum yakai ALLAH ne?, nidaifa bazan zaunaba, duk wad'annan dakake gani iro yafisu jarumta, ganinsa yasakasu wannan zazzare idanun, dasunga yatafi gida gyangyad'i zasu farama mutane, har aje asaceni basu saniba."😏
Babu Wanda bai daraba awajennan.
Ya khaleel yataka ahankali gaban Ammah, hannunta yakama tasakko daga gadon batareda yayi maganaba, shiya taimaka mata takama sandunan dazatayi tafiya.
Saida tarik'e da k'yau sannan suka fara tafiya ahankali, tana d'an d'ingisawa, suka fice.
Kowa da kallo yabisu, baffah yay murmishi tareda kallonasu, " to tsayuwar mi mukeyine? Saimu tafi aii, Dan mu'azzam sunyi gaba da Ammah, muskilancin nakusa har yanzu, shiyyasa baza'a mana maganaba".
Duk d'an darawa sukayi, sannan suka tattara komai suka tafi.
Amotar Sultan suka iske Ammah da khaleel.
Kowa saiya shiga mota, Anty zuwairah tabud'e kusada khaleel tazaunar da Aysha, sannan takoma gaba ta zauna kusada Ya Sultan dazaiyi tuk'i.
Juyowa ya khaleel yayi yakalli Aysha data raku6e jikin murfin motar, talumshe idanunta.
Tausayintane yakashi, ahankali yasak'alo hannunsa tabayan k'ugunta ya kwantota jikinsa.
d'ago idanunta tayi ta kallesa, shima idonsa nakanta, ya d'age gira d'aya tareda k'anne idonsa d'aya.
'Dan murmushi Aysha tayi, tamaida kanta gefen hannunsa ta kwantar.
Yad'anyi murmushi, tareda sumbatar kanta ahankaki.
Duk abinda sukeyi Anty zuwairah da ya Sultan Na kallonsu, murmushi kawai sukayi, amma babu Wanda yace komai.
Ammah dai batasan wainar da'ake toyawaba, hankalinta nakan danna wayarta, Wai tana neman number uncle ma'aruff.😹
Bawata tafiya mai nisace takaisu gidaba.
Suna zuwa mama tace Aysha da khaleel suwuce 6angarensu kawai.
Babu Wanda yace komai, khaleel yakama hannunta suka tafi.
Tsaf suka tadda ko ina, da'alama kullum sai'an gyara ko ina.
Aysha tazube saman gadon tana sauke numfashi, Dan har yanzu jikinta babu wani k'arfi.
Kallo khaleel yabita dashi kawai, baice komaiba yafara k'ok'arin cire kayan jikinsa.
Aysha nadaga kwance take kallonsa, harya gama, yad'auki towel ya d'aurama k'ugunsa, sosai Aysha taga ramar da ya khaleel yayi akwana ukunnan.
Ruwan wanka maid'an zafi yahad'a, sannan yafito.
Idon Aysha alumshe taji and'uketa cak.
Da sauri taware idonta akansa, yad'age girarsa duka yana kallonta, bazata juri kallonba, sai kawai ta lumshe idanunta.

Atare sukayi wankan, konace yamusu, Dan duk khaleel ne k'arfin komai, Aysha duk batada wani kuzari ajikinta.
Dakansa yadawo da'ita cikin d'akin, yad'an Mirza mai, yasaka jallabiyya milk color mai gajeren hannu. Ayshama tad'an dage ta shafa man, amma duk awahalce, burinta kawai ta kwanta.
Tana gamawa khaleel ya taimaka mata ta sanya doguwar rigar daya ajiye mata mara nauyi sosai, fara mai adon bak'ak'en furanni, batada hannu, sannan anmata d'inkinne kamar Na yara, rigar tamata k'yau, iyakarta kwaurinta, batakai k'asabaπŸ‘—.
Ita kanta saikuma kallon kanta takeyi amadubin, tasan rigar tagama amsar jikinta, kaikace saida aka gwadata aka d'inka, danma tad'an rame, tana mamakin a ina ya khaleel keta zak'ulo kayanan d'ai-d'ai hakane?.
Bata samu amsarba, saima ajiyar zuciya data sauke, sakamakon jin hannun ya khaleel acikin sumar kanta yana warwareta, dukta cirkud'e saboda rashin samun gyara Na kwana biyu.
Sai matse baki da rik'e hannunsa Aysha keyi, zafi takeji sosai, amma baice komaiba yad'auki cumb yana taje mata, bayan yasaka mai sosai, dukda haka zafi Aysha keji, sai shiii take fabaki tana rirrik'e hannunsa, amma muguntar khaleel saida yaga gashin ya warware sannan yamaida ribbon d'in ya d'aure mata a tsakkiya.
Sai tunzura baki Aysha take gaba, wai ita zafi.
Yatsansa yasaka ya d'alli bakin.
Da sauri tadafe da hannayenta sabida zafi, tuni idonta sun cika da kwalla kuwa, murmushi yayi, yaduk'o ahankali yasumbaci bakin bayan ya janye hannunta akai.
Harya cire bakin amma saiya maida.

Hummmm lallai masoyanann sunyi missing juna kam, Dan Ayshama a wannan karon tabada gudunmawa🀫.
Saida sukaji ana knock d'in k'ofa sannan khaleel yazare bakinsa awahalce .
Showing 132001 words to 135000 words out of 181849 words