Na raya masa akwaidai abinda basu saniba, Dan haka kawai Aysha bazatace Momy tabasu guba suciba, ya salam, wannan wane irin lamarine haka? idan zancen Aysha gaskiyane miye ribar hajia laura Na kashesu?, Mu'azzamfa d'antane nacikinta, Wanda tafiso duk cikin 'ya'yanta, dan tasha fad'a masa hakan, ya ALLAH ka warwaremana wannan lamari cikin sauk'i".

Nace amin baffah.

Ya khaleel office d'in babban likitan yaje gaba d'aya, yafad'a masa aikin dayakeso amasa yanzun cikin gaggawa, Dan gudun kar gubar tafara aiki ajikin wad'anda sukaci, inhar gaskiya Ayshan takeyi.
Babu kuwa 6ata lokaci aka kira duk Wanda yaci meatpia d'in, likitoci dayawane suka maida hankali Kansu, harda meat pia d'in da ya khaleel yad'akko a Leda.
Yini guda zubur a asibitin sukayishi, Dan har zuwa bayan isha'i anata bincike, Aysha kuma ta farka, amma sun mata allurar barci.
Ganin dare yayi aka sallamesu akan sukoma gida, zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu komai zai kammala, amma dukkan wanda yaci meatpia d'in anmasa allurar rigakafi, dukda dai doctors d'in sunga alamun babu guba ajikinsu.
Ya khaleel da baffah sai anty mamie gwaggo bintu kawai aka bari a asibitin, sauran duk baffa yace su koma gida, tuni ya khaleel yabaza ma'aikata a asibitin.
Dukda hakan bai hanasu hajia babba k'ule-k'ullensuba akan Aysha, saidai har yanzun basu sami nasarar aiwatarwa bane.



*****"*****
Daren ranar gaba d'aya hajia babba bata rintsaba, tasan wanene khaleel akan bin k'wak'wk'wafi, dukda babu wata hanyar daza'a gane tabasu meatpia mai guba, tunda sauran 'yan gidan Wanda babu gubane tabasu, kuma dije tayi saurin canja Wanda tabama Ayshar.
Haka taita safa da marwa a d'akinta, takasa zaune takasa tsaye.


******

Kusan dukkan ahalin gidan atsorace suka kwana jiya, musamman ma yara😉.


*WASHE GARI*

Washe gari takama lahadi, salla ce kawai ta fidda ya khaleel daga jikin d'akin da aka kwantar da Aysha, garama baffah bayan sallar asuba yaje gida ya kimtsa yadawo.
Aysha har sannan barci takeyi sosai, tafiyar baffah babu dad'ewa saiga Momy.
Ya khaleel ya gaidata, ta tambayi jikin Aysha yace da sauk'i badai ta farkaba har yanzun.
Dad'i sosai Momy taji.
Tace, "to aii dakunje gida kaidasu Bilkeesu, nisaina tsaya wajenta kafin kudawo".
" A'a Momy, saidai su Anty Mamie suje su, amma ni barin asibitinnan bai kama niba yanzun".
Shiru Momy tamasa bata tankaba, Dan yazama dole tayi yanda zatayi subar asibitin, dansu sami damar aiwatar da shirinsu, zuwacan wani tunani yafad'o mata, tabbas baikamata ta matsa akan saisun tafinba, Dan zai iya zargar wani abun.
Suna nan zaune awaje su duka Dan ba'a buk'atar yima Aysha hayaniya, wata nurse ce tazo tashiga d'akin da Aysha take kwance, kusan mintuna 30 tafice, fitarta dakamar minti 10 saiga watama, kamar ya khaleel zaiyi magana amma saiyayi shiru, yakoma yasake jingina da bango.
Kusan mintuna 20 nurse d'in ta d'auka ad'akin Aysha, sannan tafito ad'an hanzarce, harta gotasu ya khaleel ya tsaidata dafad'in jimana".
Idanu tarintse, gabanta Na fad'uwa tadawo baya.
Ya khaleel yace, "mike faruwane sai shigi da fici kukeyi?, kunk'i kuce mana komai, tafarkane naga kin fito jikinki Na rawa?".
Gabantane yakuma fad'uwa, muryarta Na rawa tace, " sorry Alhaji, zankira doctor, naga kamar tana motsawa".
Ajiyar zuciya ya khaleel ya sauke, da hannu yamata alamar taje to.
Da saurinta kuwa tayi gaba.
Saida ta6acema ganinsa kuma saiyaji zuciyarsa takasa nutsuwa, da sauri yatura k'ofar d'akin da Aysha ke kwance yashiga, idanu yazaro waje😳, Dan ganin halin da Aysha take ciki, sai juye-juye takeyi kumfa Na fita ta bakinta.
Aguje yafito, su baffah Na tambayarsa lfy, INA bai sauraresuba yashige sashin offices d'in doctors d'in asibitin.
Ganin haka suma suka afaka d'akin da gusu.
Sallallami kowa yakamayi, Anty Mamie da Momy suka fashe da kuka, gwaggo bintu ce tayi k'arfin halin rik'e Aysha daketa fisge-fisge, harta fincike k'arin ruwan da aka saka mata.
Da doctors uku ya khaleel yashigo, cikin hanzari suka kori su baffah waje, sukuma suka duk'ufa kan aikinsu, duk yanda sukaso ya khaleel yafita yak'i fita, yanzukan hankalinsa atashe yake, yadafe kai yana jujjuyawa, waimike faruwane haka a gudundune? Wlhy kwalwar kansafa Na neman tarwatsewa daga jiya zuwa yau.
Ganin halin dayake ciki doctor Faisal ya lalla6ashi da k'yar yakaishi waje.

Yana zama kiran youseef yashigo wayarsa, tamkar zai fasa kuka yad'aga wayar.
Daga can youseef ya sanar masa cewar sunfa sauka Nigeria dasu glory, babu wani Neman bayani yace, sukaisu su ajiye.
Cikin mamaki youseef yace, "j! Kana lfy kuwa?".
Huci ya khaleel ya furzo kawai, amma yakasa cema youseef komai.
" j! Kayi shiru, kana inane wai?".
"Asibiti".
Abinda ya iya fad'a kenan ya yanke wayar.
Youseef ya sanarma su Samuel da Taheer, gaba d'ayansu suka furta asibiti kuma? Atare.
''Haka kawai yace ya yanke wayar".
Taheer yace, " tabbas babu lafiya, nidama tun a jiya dana kirashi yak'i d'aga waya kusan 18 call nacemuku badai lfy ba, tunda yasan irin aikin damukaje yi mai had'arine".
Gaskiyane, yanzu dai kawai munemi asibitin dayake, wani yakira mana Emanuel.
OK.
Bayan sun kira Emanuel yamusu bayanin abinda yasani shima, yace suna babban asibiti.
Cikin mintuna 40 saigasu kuwa.
Bak'aramin tashin hankali suka shigaba daganin abokin nasu, kuma ogansu ta fannin aiki, gaba d'aya yafita hayyacinsa, gawata uwar rama ta kwana biyu dayayi.
Basu nemi ba'asi awajensaba, sai baffah ne yamusi bayanin komai, babu abinda sukace sai ALLAH ya k'yauta.
Babu Wanda yay tunanin tafiya gida yahuta acikinsu, Dan isowarsu kenan daga islands uk, sunsami nasarar kamo glory da yaranta su Lola, amma john basu sameshiba.

Kusan awanni biyu likitocin suka d'auka aciki, sannan ne suka fito kowanne yana yarce gumi, ya khaleel ya taresu da tambayoyi.
"Cool down mana j! Zomuje office zanmaka bayani". 'Cewar Dr Faisal'.
Yajuya yakalli sauran doctors d'in, inason a ajiye security a k'ofar d'akinnan yanzunnan Doctor Ahmad".
"OK sir".

Ya khaleel yajuya yana kallonsu Taheer, wannan aikinmu ne bana doctors ba.
Atare suka jinjina masa kai.
Tsurewa Momy tayi, dandanan tafara k'yak'yk'yafta idanu.
Saurin bin bayan khaleel tayi office d'in doctor Faisal.
Amma tana shiga doctor Faisal yanemi alfarmar tafita, da khaleel kawai yakeson ganawa, sai baffah.
Kamar hajia babba tashak'e doctor Faisal haka taji, tafice tana dalla masa harara, aranta tana fad'in zanyi maganinka ne aii.
Tana fita doctor Faisal yakira baffah awaya.
Baffah yashigo yazauna akujerar dake kusada ta ya khaleel.

Kusan mintuna 3 doctor Faisal Na 'yan rubuce-rubucensa, saida yagama yad'ago yana kallonsu baffah, ''maganar gaskiya Alhaji akwai wani 6oyayyen Al'amari dake faruwa, ajiya duk na duba mutanen gidanka babu wanda yaci guba, munkuma bincika meatpia d'in da Ibraheem yabamu, shima babu komai acikinsa, to amma ita matar khaleel tabbas inhar taci wani Abu ko yayane to shine aka sakama gubar, shinema yafara aiki ajikinta jiya, Dan tabbas ta had'iya, kodai abisa kuskurene kokuma bayan zubar da meatpia d'in bakinta bata wanke bakinba ta had'iya yawu, dan gubar tanada k'arfi sosai, cikin mintuna 20 kacal take fara aiki ajikin mutum, Alhmdllh kunyi azamar kawota asibiti jiya, muka samu nasarar ceto rayuwarta, saboda gubar batada tasirin dazata hallakata, dama cikin jikintane abin damuwa, amma Alhmdllh yanacikin k'oshin lafiya".
"Abinda kuma yafaru yau, tabbas akwai Wanda yashiga d'akin datake kwance yabata wata gubar.......".
Zabura ya khaleel yayi daga zaune, jikinsa har rawa yakeyi yace, "nurse d'inku biyu sunshiga d'akin, kuma ina zargin ta k'arshe, dan alamun rashin gaskiya sun bayyana tartare da ita, harna tsaidata amma tacemin zataje kirankane A'eesha ta farka".
"Ni!, no nurse d'aya natura d'akin da take kwance, kuma bana zarginta, sister Ruk'ayya ce, kuma tasanarmin taje tadubata tana barci har lokacin, bayan ita ban tura kowaba, babu kuma wata nurse datazo wajena saikai Daka kiramu,
Amma ina zuwa, waya ya d'auka yakira wani doctor, yana d'auka yace, "doctor Hambali inason a tattara dukkan nurses d'in asibitinnan".
" no dukansu, harda masu aikin safe dasukazo yanzun".
Yana ajiye wayar ya khaleel yace wannan ba aikinku baneba, namune.
Waya ya d'akko shima yakira Joseph, "hello Joseph, kunemi Dr Hambali inason a atattara min dukkan doctors da nurses dake cikin Hospital d'inan, harda ma'aikata cleaners".
"OK sir".

Baffah dai yayi shiru Danshi gaba d'aya ma tunaninsa ya kulle.
Ya khaleel Na ajiye wayar yace, "yanzu ya jikin matata doctor?".
"Alhmdlh, mun sami nasara, yanzu hakama barci takeyi, amma cikin jikintane dai kamar.........
" kamarme? Doctor karkacemin dai ya salwanta please...... "
Yanda yay maganar sai tausayinsa yakamasu, doctor ya girgiza masa kai, ''bahaka nake nufiba j, ka kwantar da hankalinka, cikin yana nan lfy, saidai muyita addu'a ALLAH yasa gubar karta shafi wani sashe Na lafiyar yaron/ko yarinyar kawai".
Huci mai azabar zafi ya khaleel yafuzar daga bakinsa, yarintse idanu da k'arfi yana dukan tebir d'in gaban doctor.
.
Please j ka kwantar da hankalinka, bawai inada tabbacin za'a haifi babien da dawata nakasabane, kawai hasashene".
"Haba doctor yazakace haka? Karkayi k'ok'arin yimini yawo da hanakali akan abinda kakeda tabbas akansa, wlhy ko wanene wannan mai aika-aikar saiyayi nadamar shiga gonata........
Ganin yanda ya birkice sai baffah yajawoshi jikinsa, rungumesa yayi, jinsa ajikin mahaifinsa sai kawai yasaki kuka mai tsanani.
Bubbuga bayansa baffah yashigayi, shikansa jiyake tamkar yay kukan saboda tausayin d'an nasa, amma saiya dake, yashiga k'arfafashi.
" haba Mu'azzam kaifa namijine, kuma ma'aikaci mai kare rayukan al'umma, mizaisa ka karaya hakane?, karka bari abinda yafaru da matarka ya raunanaka, kamata yayi yak'ara maka karfin guywa, kowaye ya aikata wannan abun tabbas sanadin tonuwar asirinsane, kuma hakan yana nuna yadad'e yana cutar damu, yanzune ALLAH ya nuna mana hakan, banaso ka zargi mahaifiyarka, dan batada dalilin kasheku, sannan mutane dayawa sunci meatpia d'in, amma baimusu komaiba, wandama mamanka tabaku an bincikashi babu komai acikinsa, amma miyasa aka samu gubar ajikin Aysha?, kuma shine last Abu dataci ajiya?........"
Zumbur ya khaleel yatashi daga jikin baffah, danya tuna masa abinda yamanta, kuma yakamata kowa yayi nazarin hakan awannan ga6ar, shikansa shaidane Aysha bataci komaiba jiya, daga rake sai wannan meatpia d'in, amma miyasa babu gubar acikinsa?, wannan lamari da d'aure kai gaskiya.
Wayarsa yazaro, kiran wasu doctors yayi cikin ma'aikatansu, yasanar musu yana buk'ar ganinsu a General hospital yanzunan.
Cikin girmamawa duk suka amsa, bai kuma sauraren bayanin doctor faisalba yatashi yafice.
Daga doctor har baffah da kallo kawai suka bishi.....
Harya kama handle d'in k'ofar zai fita doctor yace, "j!".
Cak ya khaleel yatsaya amma bai juyoba, Dan allurar 'yan mazan tamotso.
Doctor Faisal bai damuba yace, " please bamuson kowa yasan matarka nacikin k'oshin lfy, anunama kowa tana cikin halin k'ila wakala, inaga hakanne zai dakatar da masu harinta, kuma zai bamu damar aikinmu atsanake".
Jinjina kansa kawai yayi batareda yace uffanba yafice.
Baffah ya sauke ajiyar zuciya yana kallon doctor, "doctor ngd sosai, amma Dan ALLAH ak'ara bama yarinyar nan kulawa sosai".
"Insha ALLAH alhaji, Na yanzunma kuskurene, bakuma zamu bari yasake faruwaba, kuma babu Wanda zai sake shiga d'akin datake kwance, dagani sai kai da Ibraheem".
" masha ALLAH, hakan yayi".
Baffah yabashi hannu sukayi musabaha yafito...........✍




*_wasu sun zata yau asiri zai Tonu kai tsaye ko?, ai idan hakan tafaru labari yasamu rauni kenan, kuma kanku saikunji babu dad'i, amma Ku k'ara hak'uri kam, Dan dolenen komai yafito fili awannan ga6ar, tunda Aysha tabasu bakin zaren, yanzunkam fad'an Na manyane🤣🤣._*




*_masu had'a fitina tsakanin writers kuji tsoron ALLAH wlhy, karku d'auka hakan kamar k'aramin abune, kuji tsoron addu'ar Wanda aka zalinta, shin miye ribarku wajen cewa wasu na amfani da fasahar wasu?, wlhy idan kin had'a kinci riba yau, aranar gobe kiyama zakiyi Dana Sani, Dan ALLAH baya barin hak'in wani akan wani, kudaiji tsoron ALLAH, akwai mutuwa, akwai hisabi, duk Wanda yake k'irk'irar irin wad'annan fituntunun ya ALLAH kayi gaggawar tarwatsa al'amarinsa, kahanashi barci mai dad'i, kasaka bak'inciki da k'unci a zuciyarsa, ALLAH kamana maganin munafukain fili dana 6oye dake la6ewa abayan writers suna kunna musu wuta ameen._*😭🙏🏻






*_ALLAH ka gafarma mahaifina, da dukkan sauran musulmai baki d'aya.😭🙏🏻_**_Typing📲_*


🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_


*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_

*_Na gaisheki k'yauta Anty Ruk'ayya maikan doya🤭😉, saura kicigaba da gulmata nahanaki page🤫🤣😜_*


3⃣8⃣

Yana fita a can baya wani d'aki da doctors kanyi meeting yanufa bisa jagorancin Taheer, dukkan nurse's d'in da doctors anhad'asu awajen, shigarsu babu dad'ewa doctor Faisal ma yashigo.
"Amma zaka ganeta j!?".
"Zan iya ganeta insha ALLAH, saidai inbata nan".
" d'aya bayan d'aya nurse ke tasowa mazansu da matansu, ya khaleel Na kallonsu, amma harsuka k'are babu komai kama da ita, sai wadda tashiga Na farko kawai, danhaka aka tsaidata ita.
Bayan kammala dubawa babu ita aciki ya khaleel yamaida hankalinsa kan d'ayar nurse d'in, yayi masifar had'e fuska.
yace, "k wace nurse ce tashiga bayanke? Nasan kin santa?".
" wlhy yalla6ai ban Santaba, danni inagama dubata nafita kuma duk kuna tsaye, saida nasanarma doctor cewa barci takeyi, amma wlhy bansan wacece takoma d'akinba bayan fitata".
Ran ya khaleel bak'aramin 6ace yakeba, ya maida hankalinsa akan doctor Faisal. "Doctor tabbas kowacce wadda ta aikata tana cikin ma'aikatan asibitinnan, dan haka nikoma wacece nabada awa 50 kacal anemomin ita".
Yajuya yafice daga d'akin.
Kowa da kallo yabishi, tabbas kowa yasan yau ma'aikatan asibitinnan sunshiga tarkon khaleel saidai ALLAH.
Dayake su Anty Mamie ma duksun ganta, dole saidaisu aka cigaba da duba har masu shara da goge-goge, tunda abune Na laifi, cikinsuma za'a iya samu.
Khaleel kam yama bar asibitin shida doctors d'insu nawajen aiki, su doctor Abraham, amma saida yakuma saka tsaro mai tsauri azagayen d'akin da Aysha ke kwance sannan suka tafi.
Gidansu sukaje, su Ammah duk suna harabar gidan, shirin tafiya asibitin sukeyi saiga motarsu khaleel, dakatawa sukayi harya fito.
Suduka babu wanda bai tsorata da yanayin khaleel ba, har Ammah, Dan sunsan idan yana cikin irin wannan Fushin komaima zai iya faruwa, sannan komin kusancinka dashi bazai d'aga maka k'afaba, kuskure k'ad'an wani zaimasa yaci dukan banza.
Babu Wanda ya isheshi kallo acikinsu yaja zugarsa suka wuce 6angarensa.
Afili Ammah tace, " lallai gidannan gab yake da kamawa da wuta, tabbas inaji ajikina akwai gagarumin Abu dazai faru".
Kowa kallonsa ya maida kanta, amma batasake furta komaiba, kujera tanema ta zauna.
Suma duk sai suka nemi wajen zaman.

Su khaleel suna shiga yace, bincike mai k'yau nakeso, Dan tabbas akwai abinda bamu saniba, ajiya A'eesha bataci wani abuba agidannan, kowa ya shaida haka, amma dai ina zuwa.
Waya yaciro yakira Ammah, babu dad'ewa saigata tazo.
Suna zazzaune, itama saita nemi waje ta zauna. khaleel yace, "Ammah kamar yanda bincike ya nuna a 6angarenki Aysha take kwana, kuma kinfi
Showing 114001 words to 117000 words out of 181849 words