su shirya sukoma d'akunansu hakanan, tunda komai yalafa, sukuma cigaba dayima mahaifiyarsu addu'a.
Ammah ma tasakama kowa albarka sannan tarufe taron da addu'a kowa yakama gabansa...................✍🏻




Jiya kunjini shiru, anguwa naje tareda Oga wlhy, nadawo kuma a late, babu damar typing a time d'in, ga gajiya kuma.






*_ALLAH ka gafarma mahaifanmu baki d'aya, dadukkan 'yan uwa musulmaiπŸ˜­πŸ˜­πŸ˜­πŸ€šπŸ»βœ‹πŸ»._*?πŸ˜­πŸ€šπŸ»βœ‹πŸ»._*.*_TypingπŸ“²_*


🀰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{πŸ”ͺwuk'a bata hudashiπŸ—‘}_


*_Bilyn Abdul ceπŸ€™πŸ»_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyuπŸ“˜)_

*_k'yak'yk'yawar addu'a da fatan alkairi su iso agareku, inasonku da k'aunarku wlhy._*

Ashcute the group admin, Fauziya, Mrs abdul'azeez, Maman salma, Maman Adam, Binta Suleiman, Yusuf amina, Amina ali adam, MUMMIETIE, Maimuna kulloma, Auta khan, Fmujeedat9, Aisha yakubu, Maryam khamis, Aisha,
Ummu basma, Aisha Mustapha maina, Momyn twins, maman haneef, Zahra maigari, Mmn Ahmad, Hauwa saleh, Hajara Iliasu musa, Jamila D Iliasu, mom ashraft, ummin assiddiq, safiya tanimu, Sauda, Aisha gambo, Hauwa chindo, Ummu mufeeda, Zainab (Nafzee), Rahmat, MMN musty, Yar mamanta, Sanzee, bbyn dady, Ummi Ahmad Iliasu, Hawwa zakari, mmn khady, Eman, ummu aysha, fadila, fauxiyya Hussain. maryam hassan, Maman salma, Zainab Yusuf Abdullahi aji, Adama Abubakar sumaye, Aysher wali, Maman muniba, Mrs Useef, Deeja mashi, Maman mus,ab, Meeral mash, Princess Ayeeesha, Maryam lawal, Hadiza Abbas, Yar AmmiπŸ’•.

_alkairin ALLAH yakai garekuπŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹β€πŸ’ƒπŸ»πŸ‘πŸ»._


4⃣7⃣

Yau bayan Anty Zuwairah tagama shirinta tsaf tashiga dukkan d'akunan matan gidan, tamusu sallam dasake neman gafararsu, musammam akan abinda taitamusu abaya narashin girmamawa, hakama tanemi gafarar gwaggo bintu akan k'untata rayuwarta dasukayi sanda ta zauna a Lagos, gwaggo bintu tace babu komai yawuce aii, kuma tayafe mata.
Hakama d'akunan matansu Ramadan Duk saida tashiga tamusu sallama, sannan tashiga mota hafeez da Muhseen sukatafi kaita airport.
Anty shukurah ma tanufi gidanta, dansuma sundawo nan Nigeria baki d'aya.


_____________________
Dayake yau takasance asabar kowa yana gida babu aiki.
Aysha dataji d'an k'arfi-k'arfin jikinta tatashi tunda safe tahau gyaran gidan, khaleel kam Na d'akinsa kwance yana shak'ar barcinsa.
Bayan tagama tsaftace ko'ina dukda tagaji sosai haka tadaure tashiga kichin, duk tanayine domin faranta ran ya khaleel, aganinta itama yakamata yanzu ta maida hankalinta sosai wajen kulawa da mijinta kamar kowacce mace, burinta yacika akan mafi yawan tanadinta, to shima yakama ta fuskanceshi, Abu mai sauk'i ta shirya amma masu dad'i, bakuma tayi masu yawaba yanda zai zama almabazzaranci da abinci, dai-dai cikinsu tayi, sai kad'an data k'ara koda wani yashigo, dukda haryanzu takanyi amai idan abinci baimataba.
Bayan tagama wanke kayan data 6ata tafara sharan kicin d'in, jiri takeji kad'an-kad'an amma haka taita dafe bango tana morphing, wani yuuuu dataji acikin kanta yasaka saurin zama akaujerar plastic dake kichind'in, tadafe kanta tana sauke numfashi.
Ya khaleel datun d'azun ke tsaye yana kallonta ya jinjina kansa yana guntun murmushi, aransa yace agaida jaruma.
Takowa yayi ahankali har inda take, ya durk'usa agabanta tareda d'ora hannayensa bisa guywoyinta, d'ago ido tayi ahankali tasauk'esu akansa. Ya d'age gira d'aya yana kallonta shima, da hannu yamata alamar mike faruwa?.
Kanta ta girgiza masa tana murmushi.
Yace.
"banason k'aryafa".
Murmushi tayi, tace, " jirine kawai, kuma nadainaji".
''Yanzu nan waya sakaki duk wannan aikin? ana lalla6a d'an cikin kekuma kina gingimo masa wahala".
"Sadauki kenan, idanfa zan biye tawani lalla6awa babu abinda zanma kaina, insha ALLAH ma sonake wannan week d'in dazamu shiga nakoma aikina".
" yayi k'yau babie". 'Ya khaleel yafad'a yana mik'ewa, morper d'in data ajiye yad'auka yak'arasa morphing d'in kicind'in, itakam sai binsa da kallo takeyi da mamakinsa.
Bayan ya kammala yace, " oya tashi muje muyi wanka, yau zuminci zamuje".
"Zumunci kuma sadauki? Ina da ina zamuje?".
juyowa yayi yana kallonta, ya kashe mata ido d'aya, "to ganin babe zamuje, matar Joseph ta haihu baby boy".
" woow! Sadauki da gaske Dan ALLAH".
"I'm telling you my Angel".
Cikin farin ciki Aysha ta rungumesa, kaikace itace ta haihun, sai gero addu'ar fatan alakairi takeyi akan jaririn.
Cikin amsawa da ameen ya d'auketa cak, bai direta ako inaba sai toilet.

Nidai najawo tsumman k'afata nadawo falo.
πŸšΆπŸ»β€β™€


Ganin sunk'i fitowa nad'an kwanta jiransu, 'Yar wayata nad'auka nabud'e data, banzame ko ina sai group d'in ciki da gaskiya fans daketa suburbud'a firarsu ya khaleel, can nahango 'yan BBC hausama, suma nad'an lek'a muka gaisa, pherty novels ma hirar suke, dansuma akwai k'ok'arin comments, nashagala sosai a charts najiyo dariya khaleel cikeda nutsuwa.
Tashi nayi zaune nad'auk'i d'an takardana da alk'alami nacigaba daga Inda Na tsayaπŸ˜‰πŸ‘πŸ»πŸ˜‚.


Cikin shagwa6a Aysha kefad'in "nidai kakema dariya ko? Babu komai zan ramane aii, kuma saina had'aka da Ammah jar wuya".
Dariya yakuma tuntsirewa dashi, yamatso kusada Aysha, ''kinga sorry my Angel d'ina, aii had'ani da Ammah tamkar taro March ne."
''Kadai gaya musu saina fad'a d'in".
"OK OK naji, fad'i mikikeso amatsayin cin hanci?".
" la ila sadauki! Kaima kana karya doka?".
Cikin d'age gira yace, ''aii kezan bama cin hancin bawaniba, yanzu dai zan saya miki ice-cream, saikuma mi bayanshi".
"Dan ALLAH da gaske?".
" eh mana, amma saimun dawo daga ganin baby".
"Shikenan muje to muyi break fast".
Break fast suka zaunayi, adaddafe dai aka gama, Dan anyi nisa dacin abincin zuciyar Aysha tafara tashi.
Cikeda kulawa khaleel yake kallonta, yace, "lafiya kuwa?".
'Dan yatsine fuska tayi, da hannu tamasa nun amai.
Tausayi tabashi, yasan tanason abincin wani lokacin, amma data faraci sai labarin ya canja. jikinsa ya zawota, ahankali yayta shafa bayanta, lokaci-lokaci yakan mata sannu.
Kanta kawai take d'aga masa, talafe ajikinsa tana shak'ar k'amshin turarensa.
Zuwa wani lokaci yad'agota. Idonsa akan fuskarta yace, " ya daina?".
"Ya daina, amma nahak'ura da abincinnan kawai, k'arasa mutafi".
Jinjina mata kansa yayi, k'asan ransa kuwa yana jinjina k'ok'ari da jarumta irinta iyaye mata, amma ahaka har ake samun azzalumai irinsu hajia babba dake iya raba d'a da mahaifiya, wani bak'inciki ya tokare mak'oshinsa, daurewa yayi ya danne, Dan bayason hankalin Aysha yatashi.
Amma dukda haka taga fuskarshi ta canja, badai tace dashi komaiba.
Shima tashi yayi, Dan duk abincin yafitarmasa arai.

Ajere suke tafiya gwanin sha'awa, dolene kagansu su burgeka, domin sunyi bala'in dacewa da juna, lamarinfa zaaaaam fansπŸ˜‰πŸ‘πŸ».

Cikin gida suka shiga, afalo suka iske mama da ummi amarya, zaune suna hira, saisu Adeel daketa wasa agefe, rissinawa sukai suka gaidasu, cikin tsokana ummi amarya tace, " amarya da ango sai ina kuma da gayu haka?."
Aysha tasaka hannu tarufe fuskarta tana 'Yar dariya, khaleel kam k'asa yay da kansa yana murmushi, akunyace yace.
"Zamuje ganin babyn matar Joseph ne".
" tofa, yanzunan matar Joseph d'in ta haihu amma baka fad'aba babanmu?".
"Amin afuwa ummi, dama nazo sanar mukune yanzun, babu dad'ewa muma yakira yafad'a".
" ayya to ALLAH ya raya, mi'aka samu?".
"Baby boy".
" masha ALLAH kuma kunfara zama iyaye, ALLAH ya raya", 'cewar mama dabatace komaiba tun d'azun'.
Khaleel ya amsa da ameen.
Saiga Anty Mamie tafito daga 6angarensu samarin gidan itama, hannunta rik'eda Khaleefa.
Cikin ladabi duk suka gaisheta, ta amsa idonta akan Aysha.
"d'iyata ya jikin? Incedai yau babu aman?".
Akunyace Aysha ta jinjina kanta alamar eh.
" to Alhmdllh, ALLAH ya d'orar da lafiya".
Ummi amarya ta amsa da ameen, khaleel ma a kan la66ansa ya amsa, sannan suka mik'e, sallama suka musu suka fice.
Anty Mamie tabi khaleel da kallo, danta hango damuwa atare dashi, batace komaiba dai.


_________________
Haka suka tafi amotarma shiru, tuk'insa kawai yakeyi ahankali, Aysha ma tayi shiru, harsukaje gidan Joseph babu mai cewa uffan.
Horn yayi maigadi yabud'e gat, khaleel yatura hancin motarsa ciki.
Suduka duk suka fito domin tararsu, Ashe matansu youseef ma duk sunanan, rungume Aysha sukayi cikin farinciki, matar youseef ma ciki yatsufa, da k'yarma take takawa.
Afalon Joseph suka Shiga, Dan Na joy akwai 'yan uwanta.
Khaleel yakar6i jariri k'ato dashi masha ALLAH, kallon Aysha yayi yana murmushi, jiyake inama nashine, itama murmushin tayi, dantaji aranta abinda yake rayawa kenan, tasan ya khaleel akwai son yara, shiyyasa kullum cikin yima 'yan uku da yaran su ya sultan hidima yake.
Addu'o'i yamasa ya tofama yaron, tareda fatan shiriya agareshi tareda iyayen nasa, Dan kullum khaleel saiyayi addu'a akan ALLAH yaganar da Joseph gaskiya akan muslinci idan yanada rabo, yanamasa kwad'ayin son kasancewa acikin wannan addini mai yawan ni'imomi.
Yini guda yau anan sukayishi, ansha hirakam sosai.


*******
Sai dare suka baro gidan, harsun gota shop rite Aysha tace, "sadauki ice-cream d'ina".
Rage gudun motar yay yajuyo yana kallonta, "yanzu nan saboda ice-cream roba d'ayane zamushiga har shop rite?".
Baki tad'an tunzuro gaba, ashagwa6e tace, " nidai koma rabine muje, aidai nayi kallo ko".
"Uyim, salon muje agamu da 'yan fashi kice zaki nunamusu jarumtar kwace gun ko?".
Dariya Aysha tayi, saboda tuno waccan ranar datayi, cikin dariya tace, " aii wancanma dominkane nayi".
Murmushi yayi yana juyawa d'ayan hannunsa danya samu damar shiga shop rite d'in.
Yace
"Kin San yanaji aranar kuwa?".
''A'a''.
'Aysha tafad'a tana maido kallonta kansa'.
"Hummm, dukda nasan kindawo k'asar, hakan baihananin jin wani nishad'iba dana ganki, tun awajen shopping damuka had'u, jinayi tamkar kawai na...... Uhm bara nayi shiru, ashe bamu kad'ai bane".
" bamu kad'aiba kuma?, to mudawaye?."
Saida yay parking motarsa sannan yajuyo yana kallonta, da d'anyatsa yanuna cikinta.
Kallon cikin itama tayi, samnan tad'ago ta kallesa.
''Aikin gane". 'Yay maganar yana bud'e k'ofar motar, tareda zura k'afarsa d'aya waje'.
Girgiza kai kawai Aysha tayi, itama tabud'e k'ofar suka fice, k'asan ranta tana mamakin halayyar khaleel, shid'in wani irin murd'ad'd'en mutumne, awani lokacin kisameshi mutum mai sauk'in kai, wani lokaci kuma saidai ahankali kawai, maganama wannan wuyar fad'a take abakinsa, tabbas yadace da aikinsa, amma ita koma Yaya yake tanason kayanta ahaka...........
Kama hannunta dayayi yasakata dawowa hayyacinta, baice mata komaiba suka nufi cikin shop d'in.
Saida securitys d'in wajan sukai searching nasu kamar kowa sannan suka shiga ciki.
Amaimakon ice-cream dasukazo suye, saisuka 6ige da shopping mai zaman kansa, Aysha taita jidar kayan zak'i, ganin abun nata bana k'are bane khaleel yamata magana cikin had'e fuska.
"K! Wai lafiyanki kuwa? bakisan yanzu shan zak'i had'arineba agareki?, toki ragesu kokuma kinemi mai biya miki, Dan badai kud'inaba".
Shiru Aysha tayi tana kallonsa, saida taji zuciyarta ta sosu, kamar tafasa kuka haka taji, sauk'inma babu kowa akusadasu, ahankali kuma yayi maganar.
Batace komaiba tafara rage chocolate d'in data jida, shikuma yajuya yacigaba da latsa wayarsa.
Koda tagama batace dashi komaiba tayi tafiyarta wajen biyan kud'i, ta gefen ido yake kallonta, guntun murmushi yayi, aransa yace Aysha kenan, Zuma saida wuta, idan bahaka namikiba aisai ki cutar da kanki dawannan zak'in.
Bayanta yabi, daidai angama duba abinda suka siya d'in, ana fad'a mata kud'in, gani kawai tayi ya khaleel yamik'o ATM d'insa.
Tajuyo tad'an kallesa, fuskarsa a d'aure, danhaka ta kauda kanta, shikam baima kalletaba, bayan angama cirewa aka mik'o masa ATM d'in, yana kar6a yakama hannun Aysha yazare ledan yay gaba abinsa.
Cikeda jin haushin abinda yake mata tabi bayansa tana k'unk'unai.
Yana jiyota, saidai bayajin abinda take fad'a, aransa yace yarinyarnan dantaga ina wasa da ita takeson fara rainanifa, bara zan saitata kuwa.
Baya yabud'e ya ajiye ledojin, sannan yadawo mazaunin driver yabud'e yashiga, kusan tare suka Shiga da Aysha, koda tarufe k'ofar saita juya masa k'eya, takoma kallon waje ta glass.
Yi yay tamkar baisan da itaba amotar, yatada motar suka tafi.
Har sukaje gida babu Wanda yakula wani, kuma ta 6angarensu yabi, baibi tacikin gidaba, haushi yakama Aysha, Dan tasiyoma su Anty Mamie Abu, tanason kaimusu.
Koda yagama dai-daita parking sai Aysha tayi zamanta amotar tak'i fitowa, yakashe motar yafita abinsa tareda bud'e baya yad'auki ledojin.
Ganin da gaske tafifa zaiyi yabarta amotar yasakata fitowa da Sauri, ashagwa6e tace, ''nika rakani nakaima au Anty Mamie abunsu".
Kamar bazai tanka mataba saikuma yajuyo yana kallonta, ledojin yamik'o mata duka.
K'in amsa tayi, tace, "to zaka rakani?".
Kansa ya girgiza mata alamun a'a.
" kai ya khaleel please mana".
Gaba yayi yana fad'in "idan zaki kar6a kije ki kar6a, babu Inda zanje tundani ba yaronki baneba".
Idon Aysha yacika da kwallah, tana hangensa harya bud'e k'ofar falonsu yashige, da sauri tak'arasa itama saboda tsoron kar wani Abu ya cafketa.


🀣🀣nikam dariya takamani, nace, " ho shollyn khalilullah.πŸ˜‚πŸ‘πŸ»


Afalo ta iskeshi zaune akan 1 seater yana cire takalmi da sock's d'in k'afarsa.
Tazauna itama tana wani fiki-fiki da idanu tana tura baki gaba.
Dariya takama khaleel, amma saiya danne yayi azuciyarsa kawai, yakula wannan 'Yar odar tasa sai a slowly.
Mik'ewa yayi yad'auki takalman zaibar wajen, saida yay taku kusan uku sannan Aysha ta daddage ta kwallah k'ara, tareda dafe ciki tana fad'in wayyo cikinta, zata mutu, cikinta zafi.

🀣🀣
A 100 khaleel yazubda takalman hannunsa yadawo gabanta, hak'waransa har karo suke wajan tambayarta lfy?, ''mike damunki A'eesha? Kodai muje asibiti?".
Ganin yarud'e dayawa yasaka Aysha kwashewa da dariya.
Shiru khaleel yayi yana kallonta, wato tama maidashi wani soko, rankwashi mai zafi yazuba mata akai.
Babu shiri tadafe kanta tana fad'in "wayyo mama zai kashe mikini".
" kad'anma kenan yarinya, aii yau sakinsan wakika raina, zaki fad'amin yanda akayi muka zama abokan wasa"..... 'yak'are maganar da d'aukarta'.
Wuysil-wutsil Aysha taitayi da k'afafu, tana bashi hak'uri, amma ina bai sauraretaba, saida yadireta agado.
Da sauri tajuya zata gudu, ya cafkota tareda danneta.
Rok'onsa tafara tana fidda numfashi dak'yar, please ya khaleel zan mutu wlhy, Dan girman ALLAH kayi hak'uri ka d'agani natuba wlhy".
Ganin da gaske tana shirin shid'e masa saiya d'agata yana dariya, "matsoraciyan banza kawai, gobema ki sake".
" murgud'a masa baki tayi tana share hawaye".
"OK baki horuba kenan? Bara nak'ara".
Kafin tayi magana ya had'e bakinsu waje d'aya, da zafi-zafi yake sarrafata, dama andad'e ba'a gamubaπŸ˜‰, tun randa momy tabasu meatpia.😱

Sum sum nafito dad'an takardana. Dan lamarin Nasu yafi k'arfin alk'alamin bilyn Abdul.
πŸš΄β€β™€

__________________________
*_Monday morning._*

Tunda khaleel yadawo daga sallah bai koma barciba, Dan yau yakeson komawa bakin daga.
Aysha daketa kurin aiki itama antashi anyi shiri.
Yana tsaka da shiryawa cikin uniform d'in aiki saiga Aysha tashigo d'aukeda tire.
Ta madubi yake kallonta yana saka ma6allan rigarsa.
Mamaki ya kamasa harya d'an juyo ya kalleta itada tiren, sannan ya juya yacigaba da saka ma6allan.
"Wai daga ina haka da tire?".
''Daga kichin mana, kad'anyi breakfast kafin kafita".
Showing 156001 words to 159000 words out of 181849 words