Jingina yad'anyi da madubin, yagama sauke numfashi Na Seconds sannan yanufi k'ofar fita.
Itadai Aysha kunyarsace takamata, kanta Na k'asa takasa kallonsama.
Yana fita tamik'e ta haye gado ta kwanta.
Hasnah ya iske a bakin k'ofar falon bayan ya bud'e, sannu tamasa cikin ladabi, ya jinjina mata Kansa.
Itakuma tamik'a masa basket k'arami dake d'aukeda kuloli, tace inji Ummu amarya, kar6a yay yakoma ciki, itakuma tajuya tatafi.
Bin Aysha yayi dake kwance akan gado da kallo, aransa yace yarinyarnan dukta zama ragguwa wlhy.
Saman sofa yazauna, yad'ora basket d'in abincin saman k'aramin table Na glass dake gaban kujerar.
Ahankali ya furta "A'eesha".
Tunda abinnan yafaru sai yanzu taji muryarsa, ko'a asibiti akazo dubasa bayama kowa magana, saidai d'aga kai ko girgizawa yayinda aka masa magana ko tambaya.
Aysha tad'an d'ago idanunta dasuka fara shanyewa saboda barci, ta amsa da " na'am".
Yace, "sakko kici abinci, saiki kwanta".
Kanta ta girgiza masa alamar ta k'oshi, tana yatsine fuskarta.
Baice komaiba yashiga bud'e abincin, jallof d'in macaroni ce dataji kayan vegetables da busashshen kifi, sai k'amshi takeyi kuwa.
d'ago ido yayi yasake kallon Aysha, yace.
" kingafa macaroni ce".
Kallon abincin Aysha tayi, haka kawai taji tana sha'awar taci.
Saita sakko tanufoshi.
Zama tayi kusadashi, ta jingina ajikinsa, dukta koyi son jikin tsiya.
Baice komaiba yad'auki fleet d'aya yazuba abincin, cokali d'aya yasaka yagyara zamnsa sosai, saida yafaraci sannan yad'iba yakai bakin Aysha.
Bakin tabud'e bayan tayi bismillah.
Haka sukaci abincin a tsanake, yanaci yana bata, har suka kusa cinyewa, amai Aysha tafaraji.
Tsayawa yayi dabata abincin, yay saurin zuba ruwan lemon cittan a cup yabata.
Kad'an tasha, ALLAH ya taimaka aman yatsaya batayiba, saikawai yadaina bata abincin, ya jinginata da kujera, tareda tartare kayan yafita dasu.
Mintuna kad'an yadawo, akwance ya isketa saman sofa, tashinta yayi yana fad'in, "kibari mana abincin yad'an narke, babie yasamu cikin salama shima".
Itadai batace masa komaiba, sai kallonsa datad'anyi, tamaida kanta gefen kafad'arsa ta kwantar tareda lumshe idanu.
Shima ajiyar zuciya ya sauke, yajingina kansa da kujera ya Lula suniyar tunani daya zame masa aboki ahalin yanzu.☹
Bayajin dad'in komai sama da tunani, shikad'ai yakeyi yaji d'an sanyi aransa.
Sun d'auki tsawon lokaci ahaka, hardai Aysha tafara isarsa da mutsu-mutsu saboda tagaji da zaman, gashi barci takeyi k'ak'as abinta.
Bud'e idanunsa yayi akanta, ganin barcinta taketasha ya girgiza kansa, d'aukarta yayi suka koma saman gadon, bayan yakai dubansa ga agogon dake d'akin, ganin da sauran lokacin sallah shima saiya kwanta, yagyarama Aysha kwanciya ajikinsa.
Hannunsa d'aya Na saman cikinta yana shafawa, tareda tunanin wai mutumne anan ciki?, yagadai randa cikin Aysha zaiyi girma😊.
Itakam bama tasan yanayiba, tuni barci yakuma yin gaba da'ita.
Shikam yakasa barcin kwata-kwata, abubuwane dayawa akan Momy suketa dawo masa, har yanzun zuciyarsa takasa fassara wasu abubuwan....
Shigewa jikinsa da Aysha takumayine yasakashi maida idonsa kanta, tausayinta yakamashi, k'aramar yarinya da ita amma tasha gwagwarmayar da wani namijinma bazai iyaba, yakai hannunsa d'aya saman kanta yana shafawa ahankali, wata k'aunarta da soyayyarta tana kuma ha6aka a zuciyarsa, murmushi yad'an su6uce masa daya tuna ranar daya fara ganinta, ahankali yakai bakinsa saman goshinta yasumbata, har yanzu fuskarsa d'aukeda sauran murmushin, shikad'ai yasan miyakeji a zuciyarsa, kuma k'ank'ameta yayi tamkar za'a kwace masa ita, har saida tad'an motsa sannan ya sassauta mata.
Haka yacinye lokacin barcin NASA da tunani iri-iri, wad'anda suka shafi al'amuran rayuwarsa daban-daban.
Kiran sallah ne yasakashi tashi, ahankali yazare Aysha daga jikinsa, danya lura tanajin dad'in barcin nata, filos yad'an sakamata sannan yashiga toilet ya d'auro alwala.
Bai tashi Ayshaba yafice masallaci bayan ya kulleta tabaya, dukda akwai securitys zagaye dagidan, hakan baisashi jin yarda da kowaba, inhar matum irin Momy zata iya aikata abinda ta aikata, tokuwa baikamata zuciyarsa aminta daduk wani makusancinsaba ahalin yanzu, har yanzu baigama farkawa daga magagin barcinsaba, Dan maganar gaskiya har yaud'inna tunaninsa a birkice yake, yakasa samun nutsuwar warware komai dake dank'are a zuciyarsa ballantana ya fahimci komai dalla-dallah, saidai yana kamanta rashin fahimtar tasa da neman son dalilin momy Na aikata wad'annan abubuwan masukama da labarai kokuma tatsuniyoyi.

Har yadawo daga massallaci Aysha nata barcinta, zama yayi gefen gadon saitin face d'inta, yakai hannusa saman sumar kanta yana kwantar daduk wadda tad'an tashi, d'ayan hannun kuma yanajan hancinta dashi.
Bud'e idanunta tayi akansa, tad'an lumshe sannan takuma bud'ewa.
"Sorry, nakatse miki barci ko? Daure kitashi kiyi sallah time Na tafiya kingani".
Marairaice fuska tayi kamar zatayi kuka, "please sadauki, ALLAH barcin bai ishenibafa".
Yad'an zaro manyan idanunsa tareda d'ora hannunsa saman bakinsa, "kai, bakiji minaceba kenan? anfayi sallar zuhur, duba 1:35pm".
Batace komaiba kuma, ta yunk'ura dak'yar tatashi zaune, shine ya taimaka mata ta sakko k'asa, zai rakata toilet tace zata iya.
K'yaleta yayi, yajingina da fuskar gadon yana kallonta yanda takebin bango ahankali, aransa yace ALLAH yarabaki lfy matana, yakaimu randa zanga kin haifamin baby girl ko boy d'ina, nasan dai zansha raki a d'akin haihuwa😊.


_____________________________

Bak'aramar azabar wahala hajia babba tashaba akan cizon da kud'in cizo yayata mata adaren jiyaba, haka tatashi jiki dukyayi burd'ai-burd'ai, Dan kokad'an fatarta batason kwari dama, koyaya wani Abu yata6ata saikaga ya lalata mata fata.
Duktayi wani iri da'ita, ga azabar sanyi da ciwon kai dake damunta.
Kwana d'aya kacal amma dukta fita hayyacinta, sai soshe-soshen jiki takeyi, jitayi wata wutar k'iyayyar mama nak'ara zafafa zuciyarta, wlhy da ace zata samu damar fita awajennan saita tarwatsa kan mama da d'iyarta Aysha da bullet, hakama khaleel, tatsani shegen yaronnan, sannan tayi bak'inciki da takaicin rainon abinda yazama mata masifa arayuwa, inda har tasan haka Ibrahim zai zamema rayuwarta masifa datun yana jinjiri tagama murd'e kansa anwuce wajen, ta zabga kwafa tana zirar da hawayen bak'incikin barin Ibrahim aduniya.



Nikam nace, "to Momy, zakaranfa da ALLAH yanufa da cara, ko'ana mazuru ana shaho saiya kai, khaleel yazama kainuwa dashen ALLAH, shifa mai arzik'i ko a kwara ya saida ruwa, sannan mairabon ganin bad'i........😜👌🏼.

🤪garama ki rungumi k'addara, danta k'are miki keda muk'arrabank.
Saima Anfara muku sassafar gero a turmi🤣, sannan ne zakiji tsanar tasa mai dalili😜😹😹🤷🏽‍♀.


____________________________

Wuni guda haka yau suka kasance manne da juna, dukda babu wata fira dake shiga tsakaninsu, Dan gaba d'aya ya khaleel yamaida hankalinsa kacokan a duniyar tunani, saima Aysha tad'an gaji da shirunne take zungurarsa.
Yakan juyo ya kalleta, wani lokacin yakan mata alamar tambayar miyafaru?, kokuma yamata murmushi.
Bayanda Aysha ta iya dashi, haka tahak'ura suka taru sukai jugum-jugum, saidaifa Aysha nacikin tsananin farincikin kawo k'arshen Momy, tana kannewane kawai saboda kunyar khaleel, dantasan koyayane akwai shak'uwa tsakaninsa da Momy mai k'arfi, baidace takuma assasa damuwa aransaba, danta kula kokad'an bayason jin dukwani Abu daya shafi Momy, wannan yasaka Aysha kame kanta, tacigaba da ririta jikintama.
Bayan yayo sallar isha'i suna zaune afalo, kan Aysha saman cinyarsa tana kwance a doguwar kujera, hannunsa Na cikin gashinta yana wasa dashi, idonsa kam akan TV yana kallon labaran ait.
Kallonsa Aysha tayi, murya ashak'e tace, "ya Sadauki!".
" uhhm".
Yafad'a yana maido idonsa kanta.
Shiru tayi itama tana kallonsa.
Yace, ''ina jinki, akwai matsalane?".
Kanta ta girgiza masa tana shagwa6e fuska.
Ya tattaro dukkan hankalimsa akanta, fuskardai babu walwala, wannan yasaka Aysha jin Shankar masa tambayar dake ranta, dantasan halin kayanta sarai.
Ganin tayi shiru saiya d'alli la66anta da d'anyatsa, baki taturo masa, ashagwa6e kuma ido cikeda kwallah tace, "kai ya khaleel, ALLAH mugunta babu k'yaudai".
"uyimmm hakanefa, bara Na daina miki karfa nima ama d'iyata wataran".
Kunya takama Aysha data tuna lokacin data fad'a masa maganar, hannu tasaka ta rufe fuskarta.
Bakinsa yad'an ta6e yana guntun murmushi.
Har yanzu idonta arufe yake, tace, " inban takurakaba, kafad'amin miyasa kayita bibiyata har k'asar Islands?".

'Dan murmusawa yayi, Dan dama tun d'azun yalura da abinda takeson tambayarsa kenan, danyaga kallon tuhuma datake jifansa dashi tun suna asibiti, ya lumshe idanunsa yanamai tariyo komai tamkar yanzun yake faruwa.
Itakuma ta tsuramasa idanu tana sauraren amsarsa.
Kusan mintuna 5 sannan yabud'e idon akanta, cikin murya k'asa-k'asa kamar mai gudun kar wani yajisu yace, "miyyasa kikeson ji? Miyasa kikeson tunomin abinda yawuce?, tuna abinda kike buk'ata tamkar tuno wasu muhimman abubuwan da zuciyarsa ke buk'atar mancewane, baki labarinnan tamkar ruguza tubalin hak'uri da juriya dana fara tanadama rayuwatane, fad'a miki tamkar sake dawo da abubuwa masu cimin zuciya da cizonsune, please & please my Noorulhayat d'ina, karkice saikinji, karkice saina fad'a, karki tono komai, barni Na manta, kid'auka Na manta komai, kid'auka nid'in sabon mutumne, Wanda yafara rayuwa daga shekaranjiya waccan zuwa yau, kimanta komai A'eesha, kimanta please, kimanta kamar yanda Na d'auka Na manta Nima............
Da sauri Aysha ta rungumeshi tareda sakin kuka, ''kayi hak'uri ya khaleel, ka gafarceni, bannemi kafad'a d'inba danna tada maka da ahankali, inason jine akwai, kaikanka Idan kafad'a zuciyarka zata rage nauyi, zakaji sassaucin abubuwan da suka maka dabaibayi azuciya, barin abubuwan arai sukan assasa bak'inciki da damuwa mai tsanani, sukan gusar da dukkan farinciki ko walwalawar mutum, sukan ruguza dukkan wani security mai kare lafiyar garkuwar d'an Adam, kafad'a koyayane ya khaleel, kafad'a please, karkacemin a'a, kafad'amin koda sau d'ayane domin fiddani daga rud'ani, kafad'amin kodan nayi farinciki, kafad'a kodan naji araina banyi nadamar aurenkaba, Dan ALLAH ya Ibraheem.
Tsam suka rungume juna, zukatansu suna k'una, sunkai tsawon lokacin ahaka, saman khaleel yad'ago Aysha daga jikinsa.
Amamkinta saitaga yana murmushi.
Kallonsa takeyi cikin mamaki.
Yad'age mata gira sama, muryarsa a sanyaye yace, "kinsan mizaisa Na iya fad'a miki?".
Kanta ta girgiza masa.
Ya kauda kansa yana furzar da huci abakinsa, dawo da kallonsa yayi kanta, yad'auki hannun damarta yahad'a da nasa yad'ora saman cikinta, " zanfad'ane kodan yarinyata ko yarona, zanfad'a domin idan sunzo duniya kibasu labarin wahalar da mahaifinsu yasha akan soyayyar mamansu, zanfad'a kodan suji cewa mamansu taciri tuta, kuma itad'in lucky ce wajen janye zuciyar mahaifinsu a KALLON FARKO, wlhy ked'in kinzamemin maganad'isu, zanfad'a koda kowa bazai yardaba, harke kanki matata. Domin kin tankwara zuciyar Ibrahim alokacin danakejin babu wata mace datakai isar hakan, kin ruguza dukkan kurina da cika baki alokacin dani kaina nakejina on top, kece kika canja komai A'eesha, kece kika sauya Ibrahim khaleel alokacinda nakejin babu wata mace datakai isa ko k'arfin ikon hakan, alokacin danake d'aukar soyyaya shirme, wasan yara, rashin aikinyi, da k'arancin k'arfin zuciya."
Dolene yau d'inan kiji tushen soyayyar Ibrahim Abdallah *(J!)* akanki 'yammatana😉👍🏻...................✍🏻




*_Ayya jiya kunjini shiru, murace tamin kamun kazar kuku👩🏻‍🍳, da k'yar aka tsamoni a tukunya😂_*.


Kumuje zuwa my guys😉🤪👍🏻👍🏻👍🏻👍🏻.



Bilyn Abdul ce🤙🏻👯‍♀.










*_ALLAH ka gafartama mahaifanmu baki d'aya._*😭😭😭😭🤲🏻🤲🏻.*_Typing📲_*


🤰🏻
*_CIKI DA GASKIYA!!......._*
_{🔪wuk'a bata hudashi🗡}_


*_Bilyn Abdul ce🤙🏻_*


*_HASKE WRITERS ASSO......_*
_(Home of experts & perfect writer's)_


*_part 2_*
_(littafi na biyu📘)_

*_kuna cikin zuciyar bilyn Abdul kuma, kuna dabbane wlhy my fans_*

@⁨Maryam Muhammad⁩, @⁨Safiyya Danmusa⁩, @⁨Khadyinde.⁩ @⁨Fulani, Shamcydurling🥛🥛🥛,⁩ @⁨きαmiια チiκα💖⁩,@⁨Jamila zozo🧕🏼,⁩ @⁨Fadeelah Goje⁩, @⁨LAILA⁩ @, @⁨Mom Abdulmalik⁩ @⁨MOM MEENAL💃🏼⁩ @⁨Maimuna Ado⁩, @⁨Momyn Afnaan 😊⁩ @⁨Dallua⁩ @⁨Fadila DM⁩ @⁨Zainab Mshinkafi⁩ @⁨🎀ummu~ maryam🎀⁩, @⁨+234 703 972 6966⁩ @maijidda abbas. @SADDIQA BAFFA. Fatima saleh, khairat, karima, princes rasmah, habiba dakare,asiya saidu, marcy, 1, Sukhailah Hassan Umar or Ummu Sadeeq 2, Maryam Adam Abdullahi 3,Souraya,Nana yakaku, Mum shureym, 76uwaniy, Ummu iman, Mrs usman, Mahdauwalu, Anty saa, Ummu suhylerh, Munauwara bature, Zainab Gadaka, Mom Amar, Marry beauty, Maman khalil,, Mummyn ihsan, Itz sury d one, Safiyya Aminu, Maryam G wada Garba, Baby mommy, Rabiyat, Teemah, MamanHumaira, Hadizan baba, Babybluv, Saadatu Ibrahim, Rukayya bala kamilu, Beeky, Buy your chebe powder, Bilkisu isah, Maryam sulaiman, Ayshatu UST, Maman waleeda, Aisha, Khadijat umar said, Fauziyya sidi, Wisdom is a gift , Inna sokoto, Hafsat Ahmad Muhammad, Akori kishiya aci Daula, Mrs fawwaz, Mmn xee, Maryam yahya umar, Maryam Hassan, Hasana Ibrahim, Maimuna baba, Fatima ZANGINA, Mum rukky, SARATU SABO, Innan noor, Sadiya TELA, Maman faty, Dija dankakalo, Aisha yero, Sarauniya Fatima, Maman humaira, Ummu ameera, Umcycool , Umhana kabeer, Maryam Abdul aziz, Fazla ardo, Ummu salsabil, Jiddatul khairr, Rabi at nasir83, Ruquyya saleh, Ami, Nice one, Maman fati, Maman muhammad.

_Alkairin ALLAH ya iso gareku cikin salama ababen alfaharina._
❤❤❤💋💋💋👍🏻👍🏻👍🏻


4⃣3⃣

Idon Aysha k'yam akan ya khaleel, yayinda shikuma ya lumshe nasa, bayansa ya maida ya jingina da kujerar, tamkar mai karanta labarin novel ko maibada labarin wani film dayake shauk'i.
Hannunsa d'aya nakan cikin Aysha, d'ayan kuma yana shafa sumar kanta ahankali.😉👍🏻

"Hummm karon farko da Ibraheem khaleel yaji fad'uwar gaba yayin kallon mace, wadda bama takai macenba. aranar dana dawo daga k'asar Tanzania bayan aikin kwanaki 70 danayi a can, kaitsaye nabama su Adams damar wucewa dani gida, saboda matuk'ar gajiya da kasalar jiki dake tartare dani. Ina cikin shauk'in son ganin mo... Momy aranar, saboda sayo mata wata sark'a data dad'e tana so, amma bata samu sayaba, nikuma cikin ikon ALLAH saina samu wannan sark'ar zinari acan, wannan ne dalilina Na d'okin ganinta."
"Sabon labari a shafukan tarihina, koda Na sakko amota sainaci karo da tauraruwa mai wutsiyar alkairi........
Da sauri Aysha tabud'e idonta, shima yabud'e, suka kalli juna, cikin turo baki Aysha tace, " nice tauraruwa mai wutsiyar?."
Guntun dariya yayi, yaduk'o ahankali ya sumbaci goshinta, "a'a fa, bakiji minaceba? Tauraruwa mai wutsiyar alkairi".
Baki Aysha tamurgud'a tana kauda idonta daga kansa, shima kauda kan yayi yana murmushi.
Yacigaba da fad'in, ''akanki idona ya sauka kaff yawan jama'ar dake harabar gidan, bak'aramin fad'uwa gabana yayiba lokacin dakika d'ago manyan idanunnan naki kema kina kallona kuna magana keda d'iyar iya hama, bansan yazan misalta miki halin dana shigaba alokacin saboda rud'ani, (small girl like you kina Neman sakani Na rasa tunanina) bak'aramar jarumta nayiba wajen tattare dukkan hankalina namaida kansu Ammah, gaisawa nakeyi dasu ammafa dukkan hankalina nakanki, burina kawai nasake kallonki, amma hakan batafaruba.
Bamma sake ganinkiba saida Mamie takawoku domin yimin gyaran d'akina.
Hummm bazaki ganeba A'eesha, wlhy lokacin dana bud'e k'ofa wa Anty mamaie naganki zuciyata bugawa tayi tamkar zata fito, saida Na had'a da addu'a gudun kar Anty Mamie ta fahimceni.
Inakan Sani nasakaki wankin toilet alokacin, sannan kina shiga natura bishirah kar6omin tea badan inason shaba, saidan kawai nagankine atsanake.
Zaman jiranki nazaunayi har kika gama kika fito, lokacin dakika fito kintadda ina latsa waya ko? Bakomai nakeyiba face video d'inki, duk abinda kikeyi inata kallonki ta wayane, harnabaki umarnin cigaba da aikin, da lokacin da kika d'auki bedsheet zaki shimfid'a Na hanaki........
......."kadai dakamin tsawa".
Aysha tayi maganar tana cije la66anta.
Murmushi yayi, kawai yana cigaba da zagaya hannunsa akan cikinta.

Daban Daka miki tsawarnanba da tabbas babu makawa saikin harbor jirgina alokacin. natsuwarki itace Abu nabiyu daya kuma zuzuta wutar sonki araina, inason mace mai yawan nutsuwa, gakidai k'arama alokacin amma komai naki mai ajine.
Bank'i nakasance dakeba tun alokacin, saidai k'ank'antarki tamin katanga dahakan, kuma kodama kinkai girman dazan iya aurenki alokacin to tabbas, tarbarki nace inasonki shine babbar matsalata, Dan maganar gaskiya bazan iyabama.

Aysha tace, "sabodami?".

" saboda banason raini". 'Yay maganar yana jan hancinta".

K'aramar dariya Aysha tayi tareda salute nashi, cikin salon kissa tace, "agaida boss".
Dungure kanta yayi yana mata hararar wasa, shima yace, " agaida 6arauniyar zuciya".
Atare suka
Showing 135001 words to 138000 words out of 181849 words