da nayi mistaking taba hannunshi. Na zabura nayi tsalle gefe guda tare da sakin matsamin dake hannuna ya fadi a tsakiyar kicin din, Abbu ya dube ni cike da mamakina, "hey! Are you ok??" cikin zaro idanu da rawar murya nace "ehh?" yace mai ya fallatsan miki a hannu, are you ok? Baki kone ba?" sai lokacin na tuno, sai kuma a lokacin naji zafi a wajen. Na dago hannun na kalli Inda man ya taba, thankfully bai yi komi ba sai dan ja da wajen yayi, nace "lafiya lau babu abinda ya same ni.... Ina kwana Abbu?" na fada ina dan dukawa, ya amsa, tare da dorawa da, "ya aka yi kike girki tun da safe?" na duka na dauki matsamin dana yar a kasa ina cewa., "Harirar ce bata jin dadi, shine tace in kama mata" ya gyada kai. Nace Akwai abinda kake bukata ne? Ya zuba min ido kamar mai tunani, "abinda yake bukata?" me yake bukata exactly? Shi dai yasan yana cikin yin exercise dinshi yaji kamshin girki mai dadi yana bi ta cikin hancinshi, kamar maganadisu haka yaji ana jan shi har cikin kicin din..., ganin bai amsa ba yasa na juya na fara kwashe doyar dake cikin kaskon na fara tsoma mata. Yayi gyaran murya tare da fitar da dan sautin tari, "ehhhem, ruwa nake so" na bude fridge na dauko mishi mara sanyi na mika mishi da hannuna biyu ya amsa idanunshi na kaina. Na sadda kaina kasa saboda wasu particles da naga suna fita daga cikin idanunshi nashi suna shiga ta nawa kamar mashi, dan murmushi yayi ban san me yake nufi da hakan ba. Sai daya shanye ruwan tas ya miko min goran, na amsa na jefa ta cikin dustbin. "What can I help you with?" na jiyo muryar kamar daga sama, da sauri na dago ina kallonshi cike da mamaki, ta wani bangaren kuma ina tantamar Anya shine ya furta maganar? To amma waye zai furta idan bashi ba? Mu biyu ne kadai a kicin din. Kai na girgiza mishi a kunyace, ya daga kafada, "k! Let me go and take a shower then" ya juya ya bar kicin din, ni kuwa me zanyi ba kallonshi ba? Har ya fita daga kitchen din. Na maida bayana na jinginar da canter, idanuna a lumshe ina kokarin tantance abinda ke faruwa da jijiyoyina, kwalwa da zuciyata.
Bakwai saura na gama shirya komi akan dinning table, a gurguje na watsa ruwa na fito. Yau kam ban tsaya yin kwalliya ba balle bata lokaci wajen ciro kaya, simple kwalliya nayi daga hoda sai janbaki, na janyo wata atamfa English maroon color, dinkin rigar fitted ne sai zani 6-pieces, na kashe saurin dankwali kaman inji ne yayi ba hannu ba, na fesa turare tare da daukar jakata na zura flat din takalmi baki naja gyale na fita falon. Gabadaya kowa ya hallara akan dinning, nima sahun su nabi. Naja kujera kusa da Hafsy kamar yanda nake yi na zauna, Anty Mubeenah na gaida wadda yau er kwalliyar safen ma da take yi ba tayi ba da alamun ba zata leka wajen aikinta ba yau kenan. Shima Abbu sai dana sake gaida shi, shi kam a shiryen shi yake cikin Kaftan riga da wando ruwan madara bai san hula ba amma fa yayi kyau kamar ka sace shi, su Qaseem suka gaida ni kafin muka fara cin abinci a nutse. Abbu ya kaimu makaranta yau, sai da muka ajiye su Hafsy kafin muka wuce. Ina zaune a gaban motar kaina a kasa, a darare nake kamar ace kyat! In zura da gudu, kira'ar Sheik Sudeis ce take tashi a cikin motar cikin suratul-Anfal, munyi nisa sosai babu mai yin magana a cikin mu. Ya kalle ni yayi dan murmushi, "me yasa ba kya sakewa ne idan ina kusa dake Nafeesah?" ya tambaya idanunshi akan titi kamar ma bashi ne yayi maganar ba, na kara sadda kaina kasa, Ya Allah! M I making it too obvious?? "umh?!" ya kara tambaya jin nayi shiru ban amsa ba, "ko kina jin tsoro na ne Nafeesah?" da sauri na girgiza kaina, yace to meye? Da kyar na iya cewa "babu komi Abbu?" ya kalleni sosai da idanuwanshi masu kama da wanda yake jin barci, da sauri na janye idanuna daga cikin nashi, yace "anya kuwa Nafeesah?" na gyada kaina da sauri, "da gaske nake Abbu, ba tsoronka nake ji ba" ya tabe baki yace "koma dai menene Nafeesah kiyi kokari ki rage shi, bana son hakan ko kadan kin gane?" na gyada kaina, yace good! Daga haka muka yi shiru har cikin makaranta, na bude murfin motar zan fita ya miko min kudi yan dubu dubu sabbi kar da ban san adadin su ba, kallonshi nayi cike da alamun tambaya, yace karbi mana! Na dan girgiza kaina, "amma Abbu me zanyi dasu?" yace ki badda mana. Na girgiza kaina da sauri, "no Abbu. Akwai kudi a hannuna wallahi, nagode sosai" ya dan hade fuskar shi, "to dama nace dake babu kudi a hannunki ne? Karbi nan tun kafin raina ya baci mana!!" a kunyace nasa hannu na karba, nace nagode Allah ya saka da alkhairi Abbu. Yayi murmushi kawai, sai dana ga bacewar motar shi daga idona sannan na shiga cikin lab. Ranar kam muka shiga shopping complex a cikin makarantar, sai da muka ga karshen 10k din daya bani tas ni da Ramlah, tarkacen kayan kwalam dana shafawa kamar zamu bude tireda.
*********
Na maida littafin na rufe bayan nayi striking din date din ranar, calender ta ce wadda nake lissafin iyaka ranakun daya rage min in koma ga daddy na, in bar gidan Abbu. Gabana yayi wani mummunan bugawa dana tuno ranar da xan bar gidan? Me zai faru?? Nasan zan yi kewar su Hafsy sosai, I will miss them very VERY much! Zan yi kewar girkin da nake musu, yana saka ni jin cewa yes! M the controller, sai abinda na girka zasu ci.... Oops! Tunanin abinci da nayi yasa na kalli agogo da sauri, karfe hudu da mintuna ashirin, Abbu yaje Lagos, naji Ramlah tana cewa wai kamar wani event ne, Dr. Zai dinga zuwa makarantar da ba anan yake ba yana lecturing dalibai, yau dai kwanan shi hudu da tafiya tun ranar assabar, nasan dai duk yadda aka yi sun taso don tun dazu naji yana gaya mata bayan La'asar zasu taho. Na mike na fara kokarin cire riga da wando na kamfala din dake jikina, girki nake so inyi mai dadi wanda zai sanyaya mishi rai ya warware mishi duk gajiyar daya kwaso. Na saka wani blouse baki da riga turtle neck purple, na sakaye kaina cikin hula na fita daga dakin. Karan shigowar text a waya na yasa na dakata daga bude kofar da zan yi, na dawo da baya na daga wayar. Wow! Abbu ne!! Wani irin tsallen murna zuciyata ta dinga yi tun kafin inga abinda ke ciki., "on my way to the airport, me kike so in sayo miki a hanya?" nayi murmushi a hankali kamar wata wawuya, kwana biyun nan dai sai da Abbu yayi kokari yaga na saki jiki dashi, haka kawai zai saka ni a gaba da hira, wancan satin daya wuce ban samu naje gida ba, ranar Saturday ya dauke mu muka je Gidan Zoo muka yini a can, Washegari ya kaimu gidan Makama daga can muka shiga jifatu, siyayya iri-iri ya mana har sai da muka rasa abinda zamu dauka, daga nan muka wuce Golden Stars restaurant muka ci abincin lunch kafin muka koma gida, wannan satin naje gida ya kira daddy suka gaisa daddy ya bani wayar nima muka gaisa mun kwashe kyawawan mintuna talatin muna hira, ni kaina nasan cewa yanzu na sake dashi sosai, yana yawan yi mun text kwanan nan, idan ya min juma'a text ya kan hada da tambayar "hope kina lafiya? Babu matsalan komi koh?" idan kuwa yana gida watarana zai min text yace yana son abu kaza, zan dafa in dora mishi akan dinning, ko kuma in an yi girki bai mishi ba zai ce in dafa mishi wani abu, tun ina dar-dar har na daina tunda naga daga matar tashi har mai aikin da take girka abincin abun bai dame su ba.
Sai dana yi cracking din kwalwa na kafin na lalubo abin fada, "Chocolate cookies, sweets and chocolate" cikin kamar kiftawar idanu ya maido reply, "noted and done! A tanadar mun delicious dinner pa!" nayi murmushi kamar yana kusa dani, "yes In shaa Allah. A dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya". Shiru shiru bai dawo da reply ba, na ajiye wayar na fita zuwa kicin. Harira nata kokarin hada wuta, na shiga kicin din. Da murmushinta ta juyo tana kallona, wani lokaci dama idan bana komi nakan kama mata da wasu ayyukan. Nace me za a girka mana ne yau kam? Tayi murmushi, tuwon semo ne zanyi da miyar egusi. Shit! Ba abinda nayi niyar girkawa ba kenan, I had to change her mind. Nace "amma tuwo? Baki ganin dare yayi, zamu iya gamawa da wuri kuwa? Don dai ni I need something simple to cook saboda yunwa nake ji" ta dakata da ciro nama da take yi daga fridge "kuma fa haka ne, me zamu dafa to?" nayi er dariya, "just watch me!" na fada store. Na fito da duk kayan da nake bukata na ajiye, ta kalle ni tare da dan dafe kai, "Ohh! Nafee ina zuwa don Allah! Na manta zan goge kayan su Qaseem na makarantar gobe" ta fita da sauri ko amsa mata ban samu nayi ba, Kai kawai na girgiza ina murmushi. Ba yau ta saba ba, duk ranar da nake taya ta girki ni nake karasa shi, bata taba rasa excuse din tafiya ta bar ni da aiki kaji pa dan Adam! Na kara gyada kai kawai na fara yanka green beans, albasa, carrots, cabbage, na watsa su cikin frying pan nayi frying sama sama. Na bude freezer da suke ajiyar dangin nama da kifi na ciro kayan ciki, na wanke su tass na dora a wuta tare da er citta, tafarnuwa da albasa. Kafin kace me gida ya kaure da kamshin daddadan girki mai dadi.
Dambun cous-cous nayi wanda na yanka hanta kanana a ciki, na zuba veggies dinnan dana soya, na soya cous-cous din sama-sama under low heat, kafin na kara ruwa kadan na barshi akan wuta ya turara. Nayi farfesun kayan ciki na hada lemun cocktail, ana kiran sallar Magriba na gama hada komi a kan dinning table, na ajiye numfashi cike da jin dadi. Daki na koma nayi sallah, ina gamawa na fito falo ina jiran dawowar Abbu. Nayi shiru na tsunduma cikin duniyar tunani, meye haka nake yi? Girki? Zaman jira? For what?? I sound like a married woman waiting for her husband, meye haka nake yi saboda Allah? Anya bana yaudarar kaina kuwa?? A hankali na mike jiki a sanyaye zan wuce daki na, karar bude kofa naji, da sauri na juya. Tuni nayi gefe guda da tunanikan da suke neman tarwatsa min kwalwa, na bude baki ina murmushi sosai "Abbu welcome!!"..... A hankali murmushin ya fara dusashewa ganin yana dingisa kafar shi.....
*♡Jeedderh♡*
[11/16, 01:44] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
Da gudu na karasa wajen shi na riko hannunshi dake rike da brief case, tambayoyi nake watsa mishi ba kakkautawa, "Abbu lafiya? Abbu mai ya samu kafar ka? Abbu accident kayi a kan hanya?!....." ya zauna akan kujera yana maida numfashi, "it's just a minor targade, an gyara min. Kar ki damu" jin hanyaniya su Hafsy duk suka fito daga dakunan su, ganin halin da yake ciki tuni Hafsy ta fara kuka, sai da Abbu ya jata jikinshi ya rarrashe ta sannan tayi shiru. Ya kallemu duk munyi carko-carko a gabanshi muna muzurai, bai san sanda ya saki dan murmushi ba. "nace muku lafiya ta lau guys, oya Nafeesah dauko min abinci anan zan ci" jiki ba kuzari na koma na zubo mishi iya wanda zai iya ci na dora akan karamin coffee table na kai mishi, na koma kicin na dauko ruwa shima na ajiye mishi. Mu kuma muka koma kan dinning table muna cin abincin amma fa hankulan mu suna kanshi, muna cikin ci Anty Mubeenah ta fito daga dakinta, hankalina yana kanta har ta tsaya kusa da Abbu kamar suna yin magana ne, ta kalli kafar shi da yake nuna mata ta yi magana kafin ta nufo kan dinning din. Duk muka gaishe ta kafin muka koma wa cin abincin mu. Muna gamawa na tattara komi na kai kicin na wanke kayan tas na dawo falo, Abbu baya falon, na zauna ni dasu Abdullahi muka danyi kallo kafin na musu sallama na tafi dakina. Shirin kwanciya barci nayi na janyo wayana na shiga chats da friends dina ta whatsapp, dp din Muneer naga ya dora hoton wata kyakkyawar yarinya matashiya da alamun ta dan girme ni, naji wani abu ya soke ni a makogaro, kasa daurewa nayi na tura mishi tambayar "who is she?" mintuna biyu kyawawa kafin reply ya shigo, "a sister" nayi ajiyar numfashi lokacin dana ji wani sukuni yana ratsa ni, "Ohh! Ashe sistern ka ce.... Ya kake?" muka danyi chatting sama sama kafin ya min sai da safe wai barci yake ji, ni kuwa har da tura mishi hearts da clouds. Yana sauka nima na kashe wayana don dama saboda shi na tsaya.
Washegari ta kama daya ga watan mayu, public holiday ne don haka muna gida. Sai wajen karfe goma na fito daga dakina, nayi break fast na koma daki nayi wanka na sake fitowa falon. Su Qaseem suna zaune yanzu suna game, na zauna a tsakiyar su muka fara bugawa. Muna nan zaune muka ci karan intercom, Abdullahi yaje ya bude, sai gasu sun shigo shi da Aunty Ameenah. Da sauri na mike tsaye ina mata sannu da zuwa har ta zauna akan kujera, na shiga kicin na dauko mata lemu da ruwa na kawo mata, gaishe ta nayi ta amsa da fara'ar ta na koma gefe ina kallonta, wannan shine karo na farko da naga wani dan uwan Abbu a gidan tunda nazo. Qaseem ta tura yaje ya gayawa Abbu tazo, tare suke fito dashi, har yanzu yana dingisa kafar shi. Na bishi da kallo cike da tausayi har ya zauna, na gaida shi tare da mishi ya jiki ya amsa. Aunty Ameenah tace "tare muka zo da Abban Ikhlas, zai shigo ya duba maka kafar" na kai dubana ga kafar tashi, sai da cikina ya kada ganin yadda kafar ta kumbura suntum! Ya yamutsa fuska "kema na fada miki ba wani abu bane ba, targade ne an gyara min shi kuma, kumburin saboda targaden ya dade a jikina ne shi yasa" ta Harare shi, "ai ba cewa nayi kayi lecturing dina ba koh?" ta daga wayarta ta kira wata lamba, ba a jima ba wani kamilallen mutum da zai yi sa'an daddy na ya shigo falon, ya ba Abbu hannu suka gaisa. Kafar tashi ya kalla yana girgiza kai, "Anya haka zamu yi da kai kuwa Farfesa?" Abbu ya rausayar da kai kamar wani karamin yaro, "Abban Ikhlas kawai neman rigima ne irin na matar nan taka, sai dana fada mata targade ne amma taki yarda" ya kara kallon wajen, "anya targade anan wajen kuwa? Bari dai mu duba mu gani" ya fiddo kayan aiki, wata er karamar naura ya fiddo ya jona da wani abu, ya kara abun a kafar Abbu sai ga komi na kafar dake kasan fatar shi ya fito a jikin na'urar, amma babu abinda muka fahimta tunda ba profession dinmu bane, ya gama dube-dubenshi ya daga ido ya kalli matar shi, "tsagewar kashi ce!!" ta zaro idanu yayin dana dafe kirji, yace yanzu bari in kira mai gyara yazo tukun. Muna nan zaune jugum-jugum har mai gyaran yazo, har kuma zuwa lokacin bamu ga ko giccin Anty Mubeenah a cikin falon ba. Wani dan tsamurmurin farin dattijo ya shigo falon, maigadi wanda ya rako shi ya duba jikin uban gidan shi kafin ya juya ya fita. Mai gyaran ya fiddo kayan aiki ya fara, yana taba kafar Abbu na saki kara saidsai da duk suka juyo suka kalleni, jikina rawa yake, tsigar jikina tana tashi, Ji nake kamar nice naji ciwon. Abbu yace mu tashi mu koma daki amma fir naki, ganin mun ki tashi yasa ya kyale mu. Tunda aka fara gyaran kuka nake har da jan shessheka, ganin ina kuka sai Hafsy itama ta fara, nan da nan falon ya karade da kukan mu ni da ita, Anty Ameenah dariya ma ta hana ta lallashe mu. Mai gyaran ya gama gyaran da zai yi yawanci fara maida tarkacen kayan gyaran cikin jaka yana dan murmushi, "da alamun amaryar ce koh?" ya tambaya yana kallon Abbu, kusan a lokaci guda shi da Aunty Ameenah suka ce "ehhh?? Aah!!" ya bisu da kallon mamaki kafin ya murmusa yace to Allah ya kara sauki. Ya dauki jakarshi ya saba a kafada ya mike, mijin Anty Ameenah ta rufa mishi baya. Abbu ya kalleni a sanyaye, "bani ruwa Nafeesah!" da sauri na mike har ina hardewa, na dauko ruwan na kawo mishi na koma kusa da Hafsy na zauna.
Mijin Anty Ameenah yana dawowa falon ya mana sallama ya tafi,
Showing 18001 words to 21000 words out of 122880 words

*©°•Jeedderh Lawals•°*
*14*

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7 Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41