idan ba mistake ba, da ace dan iska ne kamar yadda nayi zato anya zai iya kyale ni kuwa bayan da ace yaso ya lalata ni da tuni yayi hakan? Mutumin da ko bayan aurenmu sai daya jira da ixini na da komi kafin ya kusance ni?? Dana kara tuno wasu abubuwan sai na samu kaina da sake kallon hotunan idanuna na hango katon question akan kowannen su zuciyata na tamvaya na anya kuwa babu lauje a cikin nadi??.

Da sauri na koma na hau tattare hotunan na janyo drawer ta gefen gado na watsa su ciki tare da fadawa toilet da sauri na, dole in zauna in sake tunani kafin in yanke hukuncin abinda ya dace inyi, ina rufe kofar bayin naji shigowar Abbu dakin....

Ganin bana dakin yasa ya fita daga dakin tare da maida min kofar dakin ya rufe. Na kurawa kaina idanu a jikin mirror ina kallon reflection dina, kwalliyar da nayi ta hade da ruwa da hawaye ta maida ni kamar zombie. Ruwa da sabulu nasa na wanke fuskana na kara yin wata kwalliyar kafin na fita, akan kujera na gan shi a zaune. Yana ganina ya saki murmushi mai taushi, yayin da naji gabana ya fadi sosai, anya zan iya daurewa kuwa? Don a daidai lokacin zuciyata tana kitsa min in ci kwalar shi ne kawai. Na daure na kakalo murmushi wanda nasan ko fatar bakina bai gama hadewa bama, a sanyaye na karasa kusa dashi na dan duka tare da cewa “Abbu sannu da zuwa" ya amsa yana murmushi, “kin ga na dade koh?" na gyada mishi kai kawai, yace “wai gidan Rahina na biya, shine ta hado ni da kaya ma tace in kawo miki" ya miko min ledar daya shigo da ita na amsa tare da dubawa, turaren wuta ne sai wani kamar na tsuguno idan ban manta ba naga irin shi cikin kayayyakin da aka hado min daga gida. Na maida ledar na rufe tare da kallon shi nace “abinci?" ya lumshe idanu tare da gyada kai, “please, m hungry... Very" da ace zuciyana cikin kwanciyar hankali take da babu abinda zai hana ni kamo fuskar shi in bashi sumba a baki, a yanzu kam koda tunanin ya fado cikin raina I found it disgusting sosai. Sai kawai nayi wajen dinning table ban ko yi magana ba yayin da naji lokacin daya tashi ya biyo bayana.

Abincin na hau zuba mishi, gabadaya cikina a cushe yake nasan sam babu abinda zai shiga cikina a lokacin don haka na zuba mishi iya wanda zai iya ci kawai, ina gamawa na tura mishi su gaban shi na juya da niyar tafiya yayi saurin sa hannu ya riko hannuna, ji nayi kamar garwashi ya taba ni, kallona yayi sosai, “ina zaki je haka? Ba zaki ci abincin bane?" na girgiza kai tare da kallon shi, “naci tun dazu da naga baka dawo ba" ya kara kallona kamar wanda bai yarda da abinda nace ba kafin naga yayi murmushi tare da jan kujerar gefen shi tayi baya ya zaunar dani, “ok, zauna ki taya ni hira toh, kin san cewa dai bana jin dadin cin abinci idan ba kya gefena koh?".

Haka na zauna tare da kurawa kasan carpet din idanu ina ta saka da warwara, ban san lokacin daya gama cin abincin ba, ya juyo dani na fuskance shi, “baby, me ke damun ki ne?" ya fada cikin nuna damuwa da halin da rashin walwalata a gare shi, nima nasan cewa yaudarar kaina kawai nake yi idan har nace wai zan iya pretending inyi behaving kamar yadda na saba.

Na girgiza kaina kawai, “babu komi Abbu, bana jin dadin jikina ne kawai" da sauri ya dora hannun shi akan goshina yaji babu zafi, ya dawo dashi wuya nan ma komi normal, yace “amma jikin ki lafiya lau... Are you sure ba sai mun je asibiti ba??" nayi saurin gyada kai, “m ok" yace “idan kin ji da wani abu don't hesitate fa, ki sanar dani" na gyada mishi kai, yayi murmushi tare da cewa “good girl" fuskana ya matso daidai tashi tare da kawo bakin shi saitin nawa, ina fahimtar abinda yake shirin yi nayi saurin kauda kaina gefe ta yadda leben shi ya kare da sauka akan kumatuna ba lebe na ba, ya dago ya kalleni cike da alamun tambaya, da sauri na tashi na tattara kayan da yayi amfani dasu na kai kicin. Wanke su nayi tare da dora abincin dare, ya leko kicin din ganin ina girki yazo ya kashe gas din, a hankali na dago na kalleshi amma ban yi magana ba, kafada ya daga cikin alamun tsokana “hey chill! Ba sai kinyi girki ba yau, zan fita in sayo mana abinci" sai kawai na juya na sauke tukunyar dana dora na zubar da ruwan tare da rabawa ta gefen shi na fita.

Ina gaban wardrobe dina ina shirya kayan ciki wadanda na ciro su daga ciki musamman saboda in dauke hankalina daga tunanika, Abbu ya sake shigowa dakin. Gefen gado ya samu ya zauna yayi tagumi tare da zuba min idanu wadanda seriously na dinga jin su a cikin jikina kamar me?? Kokari nake kawai naci gaba da aikina. Can kasan zuciyata ina so in mishi maganar, sai dai ina matukar tsoron abinda xai fito daga bakinshi, ina tsoron ya amsa min da ehh shine don a hakikanin gaskiya ban san ina zan jefa rayuwata idan hakan ta kasance ba.

Haka muka wanzu har aka kira sallar Magrib, Abbu ya tashi ya shiga toilet dina ya fito daure da alwala ya wuce masallaci, sai dana ga fitar shi sannan ne nima na dauro alwalar naxo na tada kabbarar sallah, anan kan sallayar na zauna bayan na gama ina laxumi har aka yi Isha'i nayi sallah. Tashi nayi na nade abin sallar, ina ta en kimtse-kimtse na wanda a zahirin gaskiya basu da amfani ina yi kawai don kada su dauke mun tunani, Abbu ya dawo daga masallaci. Dakin kawai ya leko yace in fita mu ci abinci. Na fita falon na same shi har ya fiddo plates waje, naje gefen shi na zauna kawai.

Gashin nama ya xuba mana cikin plate din da yoghurt a cikin cups, na sa cokali muka fara ci daga cikin kwano daya. Ba wai don wani abu ko yunwa nake cin abincin ba, kawai saboda bana so Abbu ya dame ni da korafi ne don a lokacin ko kadan bana so inyi magana, gabadaya raina a jagule yake. Abu na karshe da nake bukatar yi shine in kadaice a waje guda in nemi mafita a cikin rayuwata data aurena gabadaya.

Duk da halin da nake ciki hakan bai hana ni jin dadin naman ba har ma ban san lokacin dana bude ciki naci naman sosai ba, sai dana ji cikina ya cika kafin na kora da yogurt din, lokacin Abbu ya ture kwanon gefe alamun ya koshi don haka na tattara kayan na kai kicin, sauran kayan duk na saka su a cikin freezer na fita falo. Abbu yana zaune akan kujera yana kallon labaran kasa, na shige shi zuwa dakinshi da yake yanzu yawancin kayana ma suna dakin don ragewa kaina wahalar je ka dawo daga wannan dakin zuwa wancan. Toilet na shiga nayi brush na fito na shirya cikin kayan barci tare da fesa en turaruka na kwanta. Not that barci nake ji ko kuma gajiya, kawai ina gujewa Abbu ne.

Misalin karfe tara Abbu ya shigo dakin, ina jin alamun shigowar shi na kara lafewa akan gado kamar mai barci. Ina ji ya gama duk abubuwan da zai yi kamar su brush, shafa turare, sa kayan barci da sauran su. Ina jin lokacin daya kashe wutar dakin kafin inji alamun hawan shi kan gadon, na kara sakankance jikina sosai. Ina jin lokacin daya janyo ni jikinsa, duk da ihun da naji ana min a kunne akan in kwace jikina sharewa nayi, bana so inyi abinda zai sa Abbu yayi zaton idanu na biyu. Ina jin shi yana lalubata wanda da da ne tashi zanyi koda barcin nake yi in shige cikin kirjin Abbuna mai fadi, yau kam ban yi hakan ba.

Bayan lokaci mai tsayi naji alamun yayi barci, a hankali na zare jikina daga nashi tare da juya mishi baya, wasu siraran hawaye suna gangaro min a kumatu, ban san yaushe barci ya kwashe ni ba. Da asubahi Abbu ya tashe ni daga barci ya wuce masallaci. Ina kan sallaya ina karatu lokacin daya dawo daga masallacin, kan gado ya hau ya kwanta rigingine, ban motsa daga inda nake ba har sai da gari yayi sha, na rufe al-qur'anin na mayar dashi inda ake ajiye shi na fita daga dakin. Kicin na shiga na fara shirya break fast.

Abbu ya shigo kicin din, ina tsaye ina wanke hanta a jikin sink, ya tsaya a daidai gefena na dama. Kwana daya kacal daga ni har shi mun yi wani zuru-zuru damu, hannu yasa ya kamo habata a kokarin shi nason mu hada ido, sai nayi kasa da nawa idanun na hana shi ganin kwayar idanu na. Muryar shi tayi kasa sosai cike da damuwa yace “hey, me ke faruwa da ke ne Nafeesah?" na kara yin kasa da kaina na kasa magana, ya kara matsowa kusa dani sosai har ina jin saukar numfashin shi a kaina, fuskana ya sake dagawa sama, “talk to me Nafeesah please..... Look at me" yadda yayi maganar kamar wanda yake rokona yasa na daga idanuna na kalli nashi idanun, tsananin damuwa da kulawa dana hanga a cikin idanunshi suka sa ban san lokacin da hawaye suka zubo min ba, sai dana ji dumin su akan kumatuna sannan na ankara...
Abbu ya ida hade er tazarar dake tsakaninmu tare da rungume ni kam a jikinsa, a hamkali ya kai hannu bayana yana shafawa a hankali alamun rarrashi, hakan ya kara karya min xuciya sosai... Na zagaye hannuwana a bayan shi tare da fashewa da kuka ba tare dana shiryawa hakan ba.....
#TeamAbnaf
#OneLove





*♡Jeeedderh♡*
​NI DA ABOKIN BABA NA....!!!​



​©•°jeedderh Lawals°•​


​®°•Fikrah Writers Association•°​🖊🖊


*57*


Bayana yake tapping a hankali ba tare da yayi magana ba, ina jin yadda zuciyar shi take bugawa da sauri ban sani ba bacin rai ne ko tausayi na? Shi dai ya bar wa kan shi sani. Hannu yasa ya kashe gas din dana kunna, yaja hannuna ba musu na bi bayan shi muka fita daga cikin kicin din. Daki ya kaini ya zaunar dani a gefen gado yayin da shi kuma ya zauna a kasa a gabana ina fuskantar shi.

Sai dana gama shesshekar kukan da nake yi da komi, ya tashi yaje kan mirror ya dauko tissue ya miko min, hannu nasa na amsa na goge fuskata dashi. Wajen daya tashi ya koma ya zauna ya kalleni..., “ok, ina sauraronki. Fada min, me ya faru??".

Idanu na kura mishi cikin tunani, shin in gaya mishi ko kuwa in yi shiru? Shin in nuna mishi hotunan ko kuwa zan ci gaba da boyewa ne ina kwarar mu?? Ganin nayi shiru ba tare da nayi magana ba yasa ya kara matsowa gab dani, ya kamo hannuwana ya damke cikin nashi tare da dora su akan cinyata, murya can kasa wadda ta dakushe cike da damuwa yace “Kalle ni Nafeesah!" na dan yi hesitating na en dakikai kafin na daga kai a hankali na kalli kwayar idanun shi, take jikina yayi sanyi sosai, na kasa daurewa kallon tsananin kulawa, so da kauna da suke cikin idanun shi sai na kara yin kasa da kaina.

Yace “Nafeesah, idan ban manta ba na fada miki cewa babu boye sirri a tsakaninmu, ba zamu boyewa junan mu Abu ba komi tsananin munin shi kuwa, amma meye yanzu kike yi? You are hiding something from me Nafeesah, kin saka ni cikin damuwa gashi na rasa gane matsalar balle in magance miki ita, please tell me Nafeesah, tell me me ke damun ki??" rikon da yayi min a hannuna ya kara karfi, ajiyar zuciya na sauke a hankali. That's it! I couldn't do this anymore, kawai bari inji ta bakin shi in yaso komi ta fanjama shi kenan.

Naja numfashi a hankali tare da tashi cikin sanyin jiki bayan na zare hannuna daga cikin nashi, ya juya ya bini da kallo. Drawer din na bude na ciro hotunan cikin faduwar gaba na koma inda yake, sai dana lalubi gefen gado na zauna kafin na mika mishi hotunan, ya kalleni sosai kafin yasa hannu ya karba, na kura mishi idanu sosai ina so in ga yadda zai karbi ganin hotunan..

Idanun shi suka fito waje sosai kamar wadanda zasu fado kasa, nuna su yake yi da hannunshi kamar wani tababbe, da kyar ya iya kakaro sautin “Naffee..sah.... Daga ina??..." cikin rawar murya yana nuna min hotunan, na kura mishi ido ina kokarin karanta kalar tsoro dana gani a cikin idanuwan shi, na tsoron asirin shi ya tonu ne ko kuma na wani abu daban?? Nace “ba kai bane ba koh Abbu??" na kura mishi idanu cikin tsananin tsoron jin amsar da zata fito daga cikin bakin shi. Kai ya girgiza min da sauri, “bani bane ba Nafeesah., I promise you bani bane ba!".

Wani irin sanyi ya xiyarci zuciyana da gangan jikina gabadaya, na silale daga kan gadon na fada cikin jikin shi na rungume shi kankam kamar zan tsaga shi, nadama ta shige ni sosai. Da ace tun a jiyar na mishi magana da hakika bamu yi kwanan rashin sukuni da bacin rai ba, da ace tun a jiya din na mishi magana da ban ji bugun zuciya da ya dinga yin kamar zai kashe ni ba, da ban kwana cikin dacin rai da fargaba ba..... Nasa kaina a cikin wuyan shi ina kuka a hankali wanda sautin shi baya fita sai jikina da yake rawa saboda danne kukan da nake yi.

Abbu ya zaunar dani a kasan carpet din yasa hannu yana share min hawayen, sai da kukan yayi kasa kafin naji ya fara magana a nutse. “waye ya baki hotunan nan? Yaushe kuma?" naja shessheka kafin nace “ban san ko wanene ba, kawai dai wani yayi mun sallama sai ya bani yace wai sako ne tun shekaranjiya, sai jiya ne na bude" ya kura min idanu kamar wanda yake mamakin abinda nace mishi.. Can yayi magana a hankali, “kuma shine kika boye min, why??"

Na girgiza kaina kawai, yace “look Nafeesah!” na daga kai na kalleshi, yace “na fahimci tsoron abinda zai biyo baya ne ya hana ki fada min. Naji dadin hakan kamar yadda naji haushin boye min din da kika yi. Daga yanzu kada ki sake yi mun irin haka don Allah kinji? Kome ya faru kada kiji tsoron fada min, ta haka ne kadai zamu gina rayuwar aure mai inganci irin wadda nake so kin gane??” na gyada mishi kaina a nutse.

Hotunan ya sake dagawa yana kara kallonsu daya bayan daya yana girgiza kai idanunshi jawur, “Wallahil-Azeem bani bane Nafeesah. Ban taba bin mata ba, ban taba kusanta kaina da zina ba, bane bani!” hannunshi na rike cikin nawa ina gyada kai, “wallahi na yarda da kai Abbu. Ban san me yasa na kasa fada maka ba tun farko, amma ba zan sake maimaita hakan ba” hancina ya dan ja a hankali yana dan murmushi, nima nayi. Hoto daya ya dago yana nuna min, “kalli nan ki gani” na kurawa hoton ido ina kallo, hoton Abbun ne a tsaye babu riga a jikin shi yayin da macen da aka nuno su tare har lokacin ba a ganin fuskarta a kwance akan gado, nace “me zan gani?” kirjin mutumin jikin hoton ya nuna min, “nan, kin ga babu alamun tabo dina” na kama baki cike da tsananin mamaki, ya aka yi ban kula da haka ba? Ba mamaki saboda idanuna sun rufe ne shi yasa. Wani tabo ne a kirjin Abbu kusa da kafadar shi, tabo ne babba wanda yace lokacin da yaji ciwon it took him almost 3 months kafin ciwon ya warke amma tabon yana nan, yanzu dana kalli mutumin jikin hoton sai naga babu alamun tabon, kai karewa ma dana kare mishi kallo sam sai naga Abbuna yafi na jikin hoton kiba, to idan ba Abbu bane waye?.

Abbu ya kuta, “da alama wani ne yake so ya shiga tsakanin rayuwar auren mu Nafeesah, shine yasa aka yi photo editing din wani da fuskana aka kawo miki don ki tada balli, koma waye yayi haka ya gina ramin kuskure mai zurfi wallahi, I wouldn't spare him!”.

Wani tunani ya darsu a cikin raina, da sauri na kauda tunanin. Abbu ya kalleni “menene?” na girgiza kai, “m not sure don zargi bashi da dadi. Amma ranar da saurayin ya bani envelope din lokacin ina kokarin karya kwana, naga the same saurayin a tsaye shi da Dr Lubah... Ganin su kawai nayi, ban sani ba ko tana da hannu akan hakan?” Abbu ya dunkuke hoton hannunshi, “Dr Lubah!!! Zata aika, ta sha fada min zata yi duk abinda zata yi duk abinda zata yi wajen ganin cewa ta raba ni da farin cikina. Ban yi zaton da gaske take ba, I thought kawai tana fada ne don cika baki ashe da gaske take? So she can stoop this low kawai don ta raba ni dake?” nace “ni fa kawai ganin su nayi tare, bani da tabbacin ko ita ce” yace “ki ma daina wani tantama, she's the one” nace “zato dai bashi da kyawu, kamata yayi ka bincika kafin ka yanke hukunci” yayi shiru kafin ya gyada kai, “haka ne kuma, zan bincika in shaa Allah.... Now.., food!” dan murmushi nayi tare da mikewa na
Showing 111001 words to 114000 words out of 122880 words