Me kike nufi?" nayi kasa da kaina "na ga kamar yayi kusa ne" ya girgiza kanshi "bai yi kusa ba Nafeesah, na gaya miki na kagauta ki zama mallakin, ni da so samu ne ma sai ince satin sama a daura mana aure in killace ki a gidana, Ya Allah! Na tabbata burina ya gama cika, I wouldn't ask for anything sai dawwama dake a gidan Aljannar Firdaus" sai kawai na daga kafa na fara tafiya, Anya Abbu ne? Ban san me ya shiga kan shi da kwalwar shi ba a Kwanakin nan sai ya dinga min wasu maganganu da suke saka ni cikin ramin matsananciyar kunyar shi. Ya mike tsaye, "tunda baki son yin hira dani bari in maida ki hostel to" na fita na tsaya a bakin kofar Ofishin ina jiran shi, ya fito daga ciki ya rufe office din yayi gaba na bishi a baya har inda yayi parking din motar shi. Muka shiga yaja motar, a hankali muke tafiya yana ja na da er hira. Duk yadda nake kauce-kauce da kare-karen fuska sai dana dawo ina dariya, kafin mu karasa hostel na sake daga awkwardness din daya dabaibaye ni, a cikin motar ma mun jima muna hira a gaban hostel dinmu har sai da aka fara kiran sallar azuhur sannan muka yi sallama. Na bude murfin motar ina ce mishi ya gaida su Hafsy, yace "me zaki ce musu bayan tunda kika zo baki ziyarce su ba? Fushi ma take yi dake don ki sani... Koda yake ai na kusa ciccibar ki in kai mata ke cikin gidan gabadaya, ki fara haifo mata kanne nasan zata yi farin ciki sosai, zan gaya mata ta daina fushi dake haka nan" ni dai na ida sa kafata waje na fita ina dan murmushi, da gaske Abbu ya canza daga cool and calm Abbun dana sani zuwa Romantic, wanda yake fadar duk maganganun da suka zo bakin shi ba tare da yayi la'akari da cewa sun girmi kunnuwana ba. Ya dan leko da kanshi ta cikin motar, "baki ce komi ba fa" na dan juyo na kalleshi tare da haske shi da murmushi na juya na shige cikin hostel, ina jin hot gaze dinshi a kaina har na yi nisa a cikin hostel din, na tura kofar dakin na shiga. Firdausi na zaune akan kujera da littafi a hannunta tana karatu, ta dago tana min sannu da zuwa na amsa, kallona ta cigaba dayi kamar wadda taga wani bakon abu a jikina, na rataye jakar hannuna a jikin hanga na kalleta, "wannan kallon naki lafiya dai koh?" tayi murmushi tace "you are blushing! Did someone propose to you??" na kalli kaina a cikin madubi, I couldn't help the chuckling daya fito min, na kalleta ina murmushi "Ina ga dan zafi zafin da ake yi ne kawai" ta kalleni tana murmushi tare da gyada kai ta maida Idanunta ga littafin hannunta. Nima nayi murmushin na fita naje nayi alwala na dawo nayi sallah, kafin in gama Firdausi ta dafa mana indomie ina gamawa muka ci na sake fita wajen lecture.

A daren ranar sai ga wayar Daddy ta shigo, na daga wayar cikin sanyin jiki da faduwar gaba. Ina gaida shi ya amsa ya dora da fadin, "Ibrahim ya kira ni yanzu yana fada min wani labari" na sadda kaina kasa kamar ina gaban shi, "kayi hakuri Daddy" ya danyi murmushi, "meye kike bani hakuri dear? I just call to know that you are okay with it. Are you sure zaki iya?" na gyada kaina amma ban yi magana ba, yace "naji dadin zabin da kika yanke sosai Uwata, naji dadin cewa mutumin da kika zaba ya zama abokin rayuwar ki Ibrahim ne, naji dadin cewa zan barki a hannu na gari kuma na kwarai, nasan ba zan taba yin fargaba game da yadda kike ba saboda na yarda da Ibrahim. Allah ya miki albarka Nafeesah" naji hawaye suna kokarin cika min ido, da ace ina kusa dashi da sai na rungume shi, nace "I love you Daddy, nagode" yace "You are all we have Uwata, dole mu so farincikin ki, ina Alfahari dake" nace "nima haka Daddy.... Amma Mommy fa?" yayi kasa da murya nasan sirri yake nufi, "Mommy dinnan taki fa sai a hankali, tun dazu take hawa tana kumbura kamar fulawa daga mata maganar wae ai ita bata yarda ba cin amana zata yi, shine nace mata idan haka ne itama za a turo mata yarinya kamar ki idan tayi watanni sai in aureta, don Allah ba anyi 1-1 ba?? Sai kawai ta hau kumbure-kumbure, yau ko magana bata min ba dana dawo daga aiki" duk da banji dadin abun ba sai dana yi er dariya nace kai Daddy! Yace "it will be better idan baki kira ta ba for two days, zan yi kokari in ga cewa na ganar da ita abinda take fahimta" nace toh Daddy. Yace good girl, kije kiyi alwala ki kwanta, nasan kina da darasi da safe nace "exactly Dad, goodnight" muka yi sallama na ajiye wayata jikina a sanyaye. Na jima a zaune ina tunanin yadda zan yi idan Mommy taki bamu albarkarta game da auren nan, ni dai nasan cewa ba zan iya auren Abbu ba tare da yardar Iyayena ba gaskiya. Na tashi naje na dauro alwala nayi shirin kwanciya barci. Dana daga wayata naga message din da Abbu ya turo min mintuna biyar da suka wuce, cewa yayi; "A lokacin da kowa yake neman makwanci da niyar warware gajiyar data addabe shi, a daidai lokacin bawan Allah Ibrahim yake karawa kan shi wani tarin gajiyar, why? Saboda bashi da makwanci kwanciya balle filon tada kai. Ina fata wadda take karanta sakon nan zata yi gaggawar kasancewa tashi ko zai samu sanyin rai dana zuciya a tare dashi. Sai da safe, lots of love and kisses" n zan iya rantsewa naji saukar lebba a kumatuna, na kai hannu na dafe wajen ina duba gefe na, dariya na saki tare da dan dukan goshi na, silly me! I am even expecting him to kiss me, woah!! 'Goodnight' kawai na tura mishi as a reply na kwanta tare da lumshe idanuna. Barci mai dadi cike da kyawawan mafarkai ya daukeni ni.
~So how are you doing outta there Abbu and Nafee's fan??
#TeamAbbu
#OneLove





*♡Jeedderh♡*

[12/25/2017, 00:47] Hauwa-Jedderh💕: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*



*♡41♡*


Kwana biyu kuwa ban yarda na latsa sunan Mom a wayana da sunan kira ba sanin halinta na sauka daga fushi da kanta idan ta hau don sau tari idan tana fushi bata cika son ana bin kanta ana bata hakuri ba ma, she prefers a kyaleta har sai ta sauka don kanta, don haka ban tarki kiranta ba sai dai na tura mata text message which of course bata yi replying ba.
Ina fitowa daga class na koma daki, su Ni'ima suka kira ni suka ce suna dakina. Ina shiga suka tare ni da shewa ni har suka sa gabana ya fadi ina tunanin ko zancen mu da Abbu ya kai kunnensu ne, sai da muka gaisa har muka fara hira naga basu yi maganar ba sannan na dan saki jikina. Na kunna stove ina kallonsu, "me zan dora muku?" Ni'ima tace Indomie noodles, Sadiya kuma tace Spaghetti, na kallesu "guys, idan zaku daidaita akan abu daya ku daidaita don kun san bani da lokacin yin girki biyu" suka kwashe da dariya, Sadiya tace "dora mana noodles, wannan maman Babyn ba zata barmu mu shaki iska mai dadi ba idan ba a dafa noodles dinnan ba" nace "kema ai Maman Babyn ce" ta wani zare ido, wa?? Muka kwashe mata da dariya ni da Ni'ima. Nan da nan na dora Indomie na ta dahu na juye mana a tray muka fara ci. Muna cikin ci kiran Abbu ya shigo wayata, na kalli wayar tare da kallon su Ni'ima dake kallona suma, na ci mur tare da janye wayar na kife ta akan gado, suka yi sharing glancing a tsakaninsu. Sadiya ce tace "wai ni me ke tsakanin mutanen nan biyu ne? I've started putting a big question mark a tsakanin su" Ni'imah tace "kamar kin shiga zuciyata wallahi... Ni kaina na kasa fahimta" na kara hade fuska ina cusa indomie bakina ba tare da nayi magana ba, sam bana so maganar mu da Abbu ta fita ta shiga cikin dangin sa don tsakanina da Allah ban san da wani ido zan kallesu ba, ban shirya ba. Ni'imah tace "idan tayi wari dai mun ji" ni dai na kyale su ban tankasu ba. Muka gama na wanke kwanuka na kai mana soft drinks muka sha, daga nan na koma class bayan nayi sallah na bar su a dakin, dana dawo ban same su ba sun bar mun sako dai kan cewa sun tafi. Da dare Abbu ya sake kirana, na daga wayar da sallamata ya amsa ya dora da cewa "me bawan Allah yayi aka ki daga kiran shi dazu" nace "bana kusa da wayar ne Abbu.... Ina yini?" ya amsa, anan yake fada min wae washegari zai tafi Ilorin zai yi sati daya a can. Yace "me zai hana idan na dawo kawai a daura mana aure Nafeesah?" nace "Abbu baka tunanin it's too sudden?" yayi sighing, "Nafeesah, y do u always keep saying yayi sudden? Kina tunanin haka zan ci gaba da kallonki Ina kauda kai har zuwa yaushe? Har ki gama makaranta ko me?" nayi kasa da murya nace "at least in dan yi nisa a karatu na mana!" yace "really? Kin san? Ko session dinnan ba zan bari ya kare ba ba tare dana aure ki ba Nafeesah, idan kuma ba so kike yi in..... God! Nafeesah wae me kike nufi da rayuwata ne??" muryar shi ta dan fara yin sama alamun ranshi ya fara baci, nayi shiru ban bashi amsa ba. Lokacin dana gama yanke shawarar yarda da Abba, kamuwa da son shi da amincewa akan cewa zan aure shi, ban yi tunanin zancen aure ba, ban yi tunanin cewa zai taso zancen aure nan kusa ba, ban yi tunanin zai so ya aure ni ina cikin karatu na ba, nayi tunanin zai bar ni in karasa karatuna ko kuma at the very least ya bari sai na kusa kammala karatuna sai kuma gashi yana zancen aure in the next two weeks when I'm not even ready for it, hell ban ma san meye ma'anar auren ba, me zan yi kenan?? Ga zancen mu da Mommy ga.... Ya katse ni ta hanyar cewa "just forget about it Nafeesah, bana son tursasaki yin abinda baki yi niyar yi ba. Na hakura da zancen auren, idan muka ci gaba da zama a haka ma ya ishe ni, I want your happiness" naji kwallah ta tsattsafo min a idanu, nace "Abbu kayi hakuri" yace "don't mind Amour, na fahimce ki" nayi murmushi mai sauti wanda na tabbata ya jiyo sautin shi, ya maido min da martanin wani wanda yasa naji gwiwoyin kafana sun yi wani sanyi, yace "Pretty na tana ta cigiyar ki, yaushe zaki zo ki ganta?" na zaro ido kamar yana gabana, har sai da naji gabana ya fadi nace "ni?? A'ah gaskiya" ya danyi er dariya, "tsoron me kike ji ne? Na manta ma dazu in fada musu you are now my wife to be" nayi saurin cewa "pls Abbu no! Don Allah ba yanzu ba!" yace y? Na dan turo baki, "ni dai don Allah a'ah" yace "naki, sai na fada musu" na kula tsokana ta kawai yake yi don haka na kyale shi yayi ya gaji sannan muka danyi hira kafin muka yi sallama na mishi Allah ya kiyaye hanya muka ajiye wayar. Abin mamaki sai ga kiran Mommy ya shigo wayana, nayi tsuru Ina kallon wayar kamar ba zan daga ba, Ina tsoron abinda zai faru idan na daga kiran. Sai daya kusa tsinkewa sannan na daga, a hankali kamar mai tsoronta nayi sallama tare da gaida ta, cikin usual tone dinta ta amsa yadda take min, ta tambayeni karatu da sauran abubuwa duk na amsa mata da lafiya lau, tace "naji abinda kika yi Nafeesah, kina ganin daidai ne hakan?" nace "Mommy kiyi hakuri don Allah" tayi shiru kafin tayi ajiyar numfashi, "to tell you the truth naji haushin Abin daga farko, daga baya sai naga cewa abinda kike so kenan and I don't have the right da zan hana ki yin auren da kike so ba Ummiey. I really hope decision din da kika yanke shine daidai kuma zai kawo miki farinciki mai dorewa a cikin rayuwar auren ki" naji zuciyata tayi wani irin sanyi, na saki sansanyar ajiyar zuciya Ina jan hamdala a cikin raina, nace "Mommy nagode sosai" tace "Ni me ma zaki ce mun ne? Kwana biyu baki kira ni ba saboda kina gudun kar in hana ki yin soyayya ko?" nace "mommy ba haka bane" tace "idan haka ne ma ya zanyi? Tunda daddyn ki ya kitsa miki kin hau kai kin zauna, ina jinshi ai yana baki shawarar kar ki kira ni shine ke kuma kika ki kirana" na sake cewa "kiyi hakuri" ina danne dariyar data taso min, ta kuta, "he was even threatening me wai zai iya karo aure, bai san cewa abinda matar shi Ibrahim din zata yi da halin da zata shiga idan taji zancen auren bane nake gujewa ba, yayi zaton son raina ne nake shirin shiga tsakaninki da abinda kike so ba. Ummiey mata da kike gani baki san irin tashin hankali da fargaba da suke shiga idan suka ji zancen kishiya ba balle ita data zauna dake a gida daya ta rike ki cikin amana, dare daya ace zaki aure mata miji kin san ba zata ji dadi ba dai koh?" jikina yayi sanyi na sadda kaina kasa, wannan yana daya daga cikin abinda ya saka ni hesitating at first amma ya zamu yi? Ba zamu danne farinciki cikinmu don faranta ran wadda bata san namu farin cikin ba. Mommy tace "kada ki damu fa, kuma kada ki saka maganar a cikin zuciyar ki babu abinda zai faru da yardar Allah. Amma ya miki zancen aure? Yaushe yace za ayi?" nayi wuri-wuri da ido, tace "baki sani bane? Zan yiwa Daddyn ki magana, ya kamata ace anyi auren nan kawai" nayi saurin cewa, "Mom, ba zaku bari in gama karatu bane?" shiru ya biyo baya kafin tayi magana, "kina da hankali kuwa Ummiey? Shekaru nawa suka rage miki kafin ki gama karatunki, kina tunanin zamu zuba miki ido ko kuma shi Ibrahim din ne yace sai kin gama karatu?" nace A'ah, tace "to ai ko shine Ummiey ba zamu zuba miki ido ba, zan yiwa Daddynki magana a zauna ayi maganar auren ku don gaskiya hankalina ba zai kwanta ba kina karatu a Kano shima wanda ke son naki yana Kano mu muna nan Kaduna bamu san abinda ke faruwa ba a yadda duniyar nan ta baci" nace "Mommy baki yarda dani bane?" tace na yarda dake Ummiey, nasan irin tarbiyar dana baki, but still, hankalina ba zai kwanta ba gaskiya" nayi rolling eyes, "ai shikenan Mom" tace "zan dai tuntubi Daddynki inji, goodnight baby" na mata sai da safe tare da kashe wayar.

Babu ranar da bamu yi waya da Abbu ba tunda ya tafi, idan ma bamu yi wayar ba muna tare ta hanyar text message yana kashe ni da dadadan kalamai da suke kara narka zuciyata zuwa gare shi. Sai a dan tsakanin na fahimci ainihin ma'anar Soyayya, ashe da shirme nayi, ashe ba son Muneer nake yi ba tunda ko a lokacin dana yi tashen son shi ban taba kawowa raina bazan iya rayuwa idan babu Muneer ba, amma a yanzu, na tabbata cewa muddin babu Abbu a cikin rayuwata to tabbas rayuwa ba zata yiwu a gare ni ba, ko zan yi ta to mara gardi da dandano ce. A yanzu bana taba iya tunanin runtsa idanu matukar ban ji muryar Abbu a yini ba saboda nasan cewa ba zan iya barci ba, nayi wani irin sabo da muryar Abbu wanda sau tari hakan yake bani mamaki. A kowace rana kuma a kowane lokaci wata kofa a cikin zuciyata sai ta bude da sunan Abbu rubuce a jikinta Ina da tabbacin nan da dan lokaci kankani kila numfashina ma idan aka kula sunan Abbu ne zai dinga fita daga cikin shi. Duk da dai ance wai sanin gaibu sai Allah amma zan iya cewa ta bangaren Abbun ma hakan take koma fiye da haka. A yadda na fahimce shi cikin dan lokacin, yana daga cikin mutanen da baiyana halin da zuciyoyin su ke ciki abu ne mai matukar wahala da wuya a gare su, sai dai su baiyana shi through their actions kawai. Baya zama yana wani tsara min kalamai na soyayya kamar yadda yace bai iya irin wannan Abun ba but I am comfortable da yanayin yadda yake tafiyar dani, yadda yake tattalina da yadda yake nuna kamar duk duniyar nan babu wata 'ya mace mai gashi a cikin idanun shi sai ni, wannan kadai ya ishe ni numfashi mai dadi a rayuwa sanin cewa abinda nake matukar so da qauna shima yana sona da kaunata equally. Shi yasa ko a lokacin da Mommy ta sake tuntuba na da zancen aure a karo na biyu, tace "bikin Hansa'u yana matsowa, me zai hana a hada auren ku gabadaya kawai a daura a can Malumfashi? Bai fi watanni biyu ba za a daura in yaso ko bayan kun karar da session dinnan ko semester din sai ayi biki da tarewa ko?" nace "Mommy sai
Showing 69001 words to 72000 words out of 122880 words