labari daga gare ki" na karasa cira daya kafar na fita daga motar. Mai gadi ya maida mishi murfin motar ya rufe, ya sungumo trolley dina ya biyo ni dashi. Da kyar nake daga kafa ta. Taimakon Allah ne kadai ya kaini cikin gida, Mommy ta fito da saurinta tana min oyoyo, gani na a haka sai data yi turus. Ta matso tana tambaya na lafiya na lau kuwa? Da kyar na iya daga baki nace mata "gajiya" tace "shine kuma kika yi zuru-xuru haka? Wuce kije kiyi sallah kici abinci sai ki kwanta" babu musu na shige dakina. Na dauro alwala nayi sallah, yadda nake jin cikina a cike nasan babu abinda zan iya ci a lokacin. Ko kayan jikina ban cire ba na haye gado tare da lashes wutar dakin. Ina jin lokacin da Mom ta leko dakin ta maida min kofar dakin ta rufe. A gajiye nake, barci nake ji, sai dai awa daya kenan da kwanciyata babu alamun barci a tattare dani. Maganganun Abbu suke replaying a cikin kwalwa ta over and over, for once in my life da naji farin ciki yana so ya saka ni kuka, sai dai shima kukan yaki zuwa. Ya Allah!! What in the world am I suppose to do??! Ranar nasan dama babu barci, ina zan iya barci dama idan har na cigaba da hango ni zaune akan gado a cikin gidan Abbu lullube da gyale???





*♡Jeedderh♡*
[12/15, 02:34] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*34*


Da murmushi na tashi akan fuskata, rabon da inyi barci mai dadin na yau har na manta. Naje nayi brush na fito falo, babu kowa a falon dama nasan ba lallai in ga kowa ba saboda karfe goma sha daya na safe ne lokacin. Break fast na fara yi kafin na shiga dakin Mommy na gaida ta. Tace inje in shirya zata aikeni gidan Aunty Uwani, da saurina naje na watsa ruwa na shirya na fito. Turaren wuta ne da kayan labule da bed sheets ban san dai kona waye ba sai da naje can take ce min na diyar kanwar mijinta ne. Can kuryar dakinta na shige na nade akan gado ina kara tunanin makomar zancen Abbu a cikin raina, wani bangare yana shawarta ta da in kira shi a yanzu in fada mishi na amince, wani kuma yana gaya min hakan bai dace ba, wani kuma yana ce min in dan bashi lokaci dai gabadaya na rasa wanda zan dauka, a haka barci ya dauke ni saboda rashin barcin da ban samu a daren jiya ba, sai wajen karfe uku Anty Uwani ta tashe ni nayi sallah, bayan la'asar na musu sallama na wuce gida. Ina zuwa na ba mommy sakon data bani in kawo mata na wuce daki, ba a jima ba na fito muka shiga kicin da ita muka fara girki.

Kamar yadda yake Al'adar gidan mu, bayan an gama muna haduwa a dakin Daddy a yawancin darare, wani lokaci muyi kallo wani lokacin hira, sometimes ma musamman idan daddy yana ayyuka zaku ga kowa abinda ke gaban shi kawai yake yi. Ina zaune a kasan kujera ina browsing Mummy kuma tana kan kujera a xaune, Daddy ya fito daga bedroom din shi ya zauna a kusa da Mommy. Daddy ya kira sunana in a serious tone, "Uwata" na amsa a nutse tare da kallon shi, yace "last two weeks da suka wuce Ibrahim ya same ni da wata magana mai Muhimmanci" yayi shiru yana kallona yayin da zuciyata ta hau duka kamar zata fado kasa, ya cigaba da magana "Yace wai Yana So Ya Aure Ki! Ni kuma nace mishi sai naji daga bakin ki don bana son tursasa ki akan abinda baki da niyar yi, me kika ce? Zaki Auri Ibrahim?" Na sadda kaina kasa ina wasa da yatsun hannuna, ban san abinda yakamata in ce ba, ina son Abbu kuma Ina son Auren shi? Ina son Abbu amma ina tunanin auren shi is not a good idea? Ko kuwa me zan ce?? Mommy tayi saurin riga ni magana, "Haba Abban Ummiey, kaima kasan cewa wannan ba abu bane mai yiwuwa. Shi bai yi tunanin abinda zai zo ya dawo bane ya kirkiro wannan magana? Wannan abu ba zai yiwu ba sam!" duka ni da Daddy muka kalleta, fuska a hade sosai take yin maganar, daga ganin yanayin idanunta nasan cewa she is strongly against it, sai jikina ya kara yin sanyi akan na da. Daddy yace "me kike cewa ne haka Habibty?" tace "Abinda ya kamata mana, Idan shi idanun shi sun makance da cin Amana bai kamata naka su rufe ba Abban Ummiey. Haba! Ace daga tura yarinya yin IT na wata shida kawai sai aji wai ta buge da aure mai gida? Kaima kasan cewa wannan ba abu bane da zai yiwu ba, sai dai idan so kake ka saka mu a bakin duniya kuma" Daddy ya danyi murmushi, "sai dai idan basa son junan su Habibty, amma idan suna so then who cares about what people will say? Su mutane ai aikin su kenan ina tabbatar miki idan kika ce zaki biye ta mutane to numfashi ma sai sun miki izinin kiyi kenan?" Mommy ta hade fuska "na kula ga gaskiya nan kana gani kuru-kuru amma kana takewa, son Kai ne ko me? Aure dai Nafeesah da Ibrahim babu shi!! Ba zan taba bada hadin kaina ga cin amanar wannan da kuke shirin yi ba" Daddy yace "ke kuma kin ki fahimtar abinda soyayya zata yi da wannan ba zata iya ba, baki tsaya kinji ta bakin yarinya ba kin zauna kina ta tada jijiyoyin wuya, be it zaman aure ko cin amana kamar yadda kika ce don ni dai ban ga komi ba a ciki, ina ga ai ya rage ga yarinyar koh?" Mommy tace "ni nasan Ummiey ba zata taba aminta da hakan ba, ga samari nan bila adadin suna karakaina a kanta sai ta buge da wani can, ga mata ga 'ya'ya, abokinka kuma for that matter, anya Abban Ummiey ka duba maganar nan sosai?" Daddy ya kalleni yace "Uwata!" na daga kai na kalleshi, yace "kada ki damu da abinda take fada kin ji? Just tell me idan kina son Ibrahim kuma zaki iya auren shi" na kalli Daddy na kalli Mommy, toh fa! Ga sanyin Idaniyata guda biyu a gabana, ko wanne ya zuba min ido yana jiran amsa ta wanda nasan cewa amsar da zan ba daya daidai take da bacin ran daya, abinda na tsani gani da ji kenan a duniyata ace daya daga cikin Iyayena yana cikin bacin rai sabida ni. Abinda Mommy take fada gaskiya ne, shima Daddy akan gaskiyar shi yake, to me zan yi kenan? M I going to disappoint one of them? Ya Allah!! M extremely confused! Na samu kaina da girgiza kai wanda ni a karan kaina ban san dalilin yin hakan ba, Daddy yace "me kike nufi da girgiza kai, eh ko aah??" na sake girgiza kaina, "ban sani ba Daddy!" Daddy ya kura min ido na tsawon lokaci, yace "tashi ki tafi kawai Uwata, Allah ya zaba mana mafi alkhairi" ba musu kuma ba tare dana kara uffan ba na musu sai da safe na wuce dakina. Hannu dafe da kai na fada kan gadona na kwanta, na gaji! Na gaji haka nan. Haba! Kwana biyun nan kaina har ciwo yake yi tsabar tunanika da suka hana ni sukuni, abin ya ishe ni haka nan. Tashi nayi na fada toilet na dauro alwala na fito na haye kan Abin sallah, sallah na fara jerowa, dana gama na roki Allah akan yayi mun zabin abu da yafi alkhairi a cikin rayuwata, na gama nayi shirin kwanciya barci na kwanta zuciyata cike da sake-sake.


*****
Tsawon sati guda Daddy bai sake min zancen Abbu ba Mommy ma haka, haka a tsayin lokacin nan ban sake ji daga Abbu ba. Mun koma makaranta don dama ba wani hutu aka bamu mai tsayi ba. Ranar Asabar ina kwance a dakina da hantsi, mun gama waya da Harith kenan yana gaya min yadda suke shan fada shi da Ikram akan wai ni budurwar shi ce ni kuma ina ta shan dariya, na ajiye wayar tare da kurawa ceiling ido ina kallo. Wani kiran wayar ne ya dawo dani cikin hankalina, na mika hannu a sanyaye na dauki wayar. Ban san lokacin dana zabura na tashi zaune dangargar ba, Abbu. Kallon wayar kawai na dinga yi har kiran ya kusa karewa, in daga in ce mishi me? Koda yake na riga na gama yanke shawarar abinda nake ganin daidai ne a rayuwata so let's just finish this once and for all kawai, na karfafawa kaina gwiwa. Nayi gyaran murya tare da daga kiran na kara wayar a kunnena......





(Sorry for the short Chapter, m kinda busy this days wallah..)
So Kafin in tafi let me ask you this:
~Me kuke tunani game da Littafin Ni Da Abokin Baba Na so far?
~Me kuke gani ya kamata Nafeesah tayi a wannan lokacin, Accept or Reject?
~Who's siding with Mom, Dad? Raise your 👐 so I can count you guys lol
~Stay blessed and cool, see yah
Lots of Hearts and Flowers #teamAbbu 💞💞💐💐




*♡Jeedderh♡*
[12/16, 12:04] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*35*



"Assalamu Alaikum" sansanyar muryar shi ta doki kunnena, duk wani karfin gwiwa dana tanada da kaudin da nake na cewa Abbu ya daina firgita ni ashe aikin banza nake yi, a take muryar shi tayi raga-raga da naman jikina, yayi gyaran murya tare da ambatar sunana, na amsa a nutse kuma a hankali cikin muryar rada, shiru ya biyo bayan hakan na lokaci mai tsayi, baka jin komi sai karan iska dake wucewa ta cikin wayar. Yace "Nafeesah! Ya muka kare da maganar mu ne?" nayi shiru ina zare idanu, da me na shirya zan ce ne? Gabadaya komi ya fita daga cikin kwakwalwata, yace "umh?! Ina sauraron ki" na bude baki zan yi magana sai dai sautin dake fita kawai shine "ermm.... ermmm" na kasa yin takamaimiyar magana. Abbu ya tausasa murya, "look Nafeesah. I don't have much time yanzu, mintuna kadan suka rage min in tashi zuwa Vancouver zan yi wani four months course acan so please do tell me, me kike tunani? Ina son ayi ayi auren mu dana dawo Nafeesah, da so samu ne a gare ni da tafiyar nan dake zan yi ta a matsayin mata ta Nafeesah don ba wani tsayawa zan yi bata lokaci wajen soyayya kamar yaro ba, kin san na tsufa da hakan koh?" wata hudu a Vancouver? A perfect timing!! Yace ina jin ki Nafeesah, an fara kiran fasinjoji, me kike tunani? Zaki iya aure na??" na lumshe ido a hankali zuciyata na suya a kirjina kamar an tsoma ta a ruwan zafi, "I Am Sorry Abbu...... I can't!" shiru ba magana daga bangaren shi yayin da kowace wucewar dakika zuciyata take nunka gudunta har na fara tunanin idan na kara minti daya a wannan lokacin zata iya bugawa gabadaya. Bayan kaman wucewar lokutan dana kasa lissafawa, yayi gyaran murya, muryar shi lullube da wani irin embarrassment da daci yace "zan kira ki idan muka sauka Nafeesah" a hankali hannuna da wayar suka sauka akan gadona kamar wadda aka zare mata numfashi. Nayi imanin da ace Duniya da lokaci suna tsayawa da sai ince nawa sun tsaya, komi nawa ya tsaya cak. Bana fahimtar komi sai daci da sanyin jiki dana ji suna fita daga bakin Abbu, ban yiwa kaina adalci ba, sai dai ina bukatar sanyin rai dana zuciya. Ina bukatar farin cikin iyayena, nasan cewa definitely Mommy zata yi farin ciki da hakan Daddy ne dai ban sani ba, ni kuma I only need those four months, In shaa Allah kafin lokacin ya cika, "I'll over come it!" na fada a fili cikin karfafawa kaina gwiwa. Karan bude kofa yasa nayi firgigit na kalli kofar, Mommy ta shigo tana kare min kallo, tace "kin yi bakuwa Ummiey" na kalleta da sauri, "bakuwa, wacece?" ta dan maida kanta wajen kofa tare da furta "shigo" Ikram ta shigo dakin bakinta dauke da sallama, da sauri na tashi tsaye ina amsawa, iso na mata zuwa gefen gadona ta zauna, Mommy ta juya ta fita ta barmu muna gaisawa, ruwa da lemu na dauko mata a fridge na dawo, muka zauna shiru a dakin saboda ba wani sabo muka yi da ita ba dama, can na katse awkward silence din nace "so???" ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta ta kasa magana, na dan yi murmushi nace "Kina son tambayar Abinda ke tsakani na da Harith koh?" ta kalleni cikin mamaki kafin ta gyada kai, nace "magana ta gaskiya Ikram babu abinda yake tsakani na dashi, duk abinda kika ga mun yi was just a plan, yana so ne yayi provoking dinki" ta nuna kanta da yatsa, "ni kuma? Why??" na zayyane mata labarin duk abinda kenan, Ikram tayi shiru kanta a kasa har na gama. Tace "yaki ya fahimce ni ne kawai, shekaru biyu kadai suka rage min a karatuna, menene a ciki idan ya hakura zuwa shekarun biyu?" nace "Ikram kina son Harith shima yana son ki saboda haka ni ban ga abin tada jijiyar wuya a wannan maganar ba. Shawarar da zan baki shine to just go for it, karatu baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu idan har kika maida hankalinki akan hakan" tayi shiru kamar mai tunani kafin ta kamo hannuwana ta rike, "nagode sosai Nafeesah. In shaa Allahu zan zauna in duba hakan, nagode" na danyi rubbing hannunta dake kan nawa ina murmushi. Mun dan kara hira da ita kafin ta min sallama ta tashi, na raka ta har bakin titi ta samu abun hawa ta tafi ni kuma na koma gida. Da dare Daddy yake gaya min an sai min DE form a BUK, na turo baki nace "Daddy ni fa ABU nace maka ina so" yace "sun riga sun rufe saida basically ne shi yasa nasa aka nema miki BUK din" nayi shiru ina tunani, wannan shine kaka-kara-kaka din fa, ina gudun Abbu shi kuma yana kara bibiyata, nace "ni dai kawai na hakura sai next year" daga Mommy har Daddyn kallona suka yi, Mommy tace "sai mu saka ki a gaba muna kallo har shekara koh?" Daddy yace "Duk maganar zama bata ma taso ba, tunda an samu admission din ki daure ki tafi can din kawai" nace "amma a cikin hostel zan zauna koh?" Mommy tace "to in ba can ba ina? Dole can zaki zauna" Daddy ya daga baki kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru kawai. Daga haka aka fara processing din nemar min admission a BUK. A gefe daya kuma naci gaba da karatu na.

Sati daya, biyu, uku suka shude babu alamun kiran Abbu a cikin wayata, ban kuma sake jin magana game dashi ba. Tunanika iri-iri game da hakan babu kalar Wanda ban yi ba da wasi-wasi, kila ya hakura ne, kila maganar da nayi ta bata mishi rai, kila dama ba sona yake yi ba.





*♡Jeedderh♡*


[12/23/2017, 13:52] Beluvd Zee: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*36*



"So sai kawai kika yi rejecting din golden opportunity like that?" cewar Ramlah. Zaune muke a lecture hall dinmu bayan mun gama lectures. Kwana biyu bana cikin natsuwata, walwala ta min kaura kamar yadda fara'a tayi kaura daga fuskata., a duk lokacin dana samu na kebance babu abinda nake yi sai tunani, Ramlah ta kula da yanayin da nake ciki yau dai ta rike ni sai dana fada mata abinda ke faruwa, ko babu komi naji dadin fada mata din da nayi. Tunda abin ya faru babu wanda yaji maganar, ni kadai nake juya abun a cikin raina. Fadar irin mamakin da Ramlah tayi ma bata baki ne, data hangame baki sai dana cika mata shi da popcorn sannan ta rufe. Na kai popcorn bakina tare da gyada kai, "babu wani zabi daya rage wannan Ramlah, kema kin sani" ta kura min ido, "akwai so many and n much more choices Babe, ke ce dai baki so zaba ba". Muka yi shiru na dan lokaci, ta sake cewa "wai ba kince kina son shi ba?" na gyada mata kai, "then why did you do it? Bayan kin san zaki kasance cikin damuwa?" na kalleta sosai, "Ramlah, ina cikin rudani wallahi" ta girgiza kai, "no! Ki kike confusing din kanki dai, wannan abu ne mai sauki da cikin kiftawar ido zaki magance shi. Kina son mutum, then marry him mana, meye matsalar ki wai? You once fall for the wrong
Showing 57001 words to 60000 words out of 122880 words