I'll finish it anjima" ta gyada kai, na mata sallama na fita daga cikin class din. Sanye nake da da riga da zani na atamfa, dinkin zanin single ne kamar yadda rigar take fitted, ban tsaya wani daurin dankwali ba na dora hijabi akan kayan wadda ta kusan sauka har gwiwa na. Yanayin garin na yau aka rana kuma da zafie, kowa dai yasan yadda Kano take idan damina ta fara shigowa. A hankali nake takawa ba wai don yanga ko wani abu ba, saboda tsabar gajiyar dake tattare dani, yau tun karfe bakwai muka shiga lacca, gashi yanzu har to five amma ban saka abun kirki a bakina ba tun karin safe. Sai dana fito daga farfajiyar da classes dinmu suke na bi wani dan karamin corridor da zai sada ni da gate din fita daga cikin department dinmu, a bakin gate din can inda aka tanada saboda ajiye motoci, wata farar Picanto ce anyi parking dinta ta yadda duk wani wanda zai fito daga wajen da nake fitowa zai yi ido biyu da motar. Yeah motar ta hadu karshe haduwa ta kuma cancanci kallon da jefi-jefi din mutanen dake wucewa suke jifanta dashi. Sai dai a gareni ba motar bace ta dauki hankali na ba, mamallakin motar ne da yake tsaye a gefen motar ya juya min baya yana amsa waya. Sanye yake da baggy pants da shara-sharan farar T-shirt don har ana iya hango farar singiletin dake jikin shi, na ja na tsaya a hankali idanu na kafe akan mutumin. Well I didn't want to jump into conclusion din ko waye duk da nasan cewa halitta ce da ko mutuwa nayi na dawo zan shaida ta. Sai dai wannan ta banbanta da wanda na sani, yadda fatar jikin mutumin da bakar sumar kanshi suke sheki a cikin hasken ranar ya saka ni doubting Anya shine? Kamar Wanda yaji wasi-wasi da tantamar da Zuciyata take ciki, a hankali ya juyo ya sauke idanunsa a kaina, and there He is, Abbu Galadanchi standing right in front of Me......





*♡Jeedderg♡*
[12/23/2017, 13:52] Beluvd Zee: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*38*



Ban san me ya kamata inyi ba a daidai lokacin nan ba, juyawa zan yi in koma ta hanyar dana fito, tunkarar shi zan yi ko kuwa zan zagaye shi ne in wuce abina?? A hankali na daga kafafuna na fara tafiya har naje gabanshi na tsaya, kamshin turaren Hugo boss dana Secret Men suka ziyarci hancina har sai data kaini ga lumshe idanuna. Kaina sadde yake a kasa amma nasan cewa kyawawan idanunsa suna kaina saboda ina jin su all over my body. Na daga baki a hankali nace "Abbu ina yini, an dawo lafiya?" ya kura min idanu ba tare dana yi magana ba, a hankali na dan saci kallonshi, Kyawawan idanunsa suna kaina yana kallona intensely, muna hada ido ya wani daga gira sama, "is that all?" na bude idanu na kalleshi sosai cikin alamun tambaya, "na'am?" ya kai yatsa ya dan dangwali hancin sa tare da dan sosawa, "well, you didn't seem that happy to see me girl...." ya saddo kanshi daidai fuskata very close wanda na tabbata idan ya kara taku biyu sai hancinsa ya gogi nawa, na dan ja taku biyu baya ina jin bugun Zuciyata yana karuwa saboda kusancin da Abbu ya kirkira a tsakaninmu. Ya kalli kafafuna da suka matsa, ya dauko kallona tun daga kafafuna har zuwa kan fuskata bakinshi yayi coiling forming wani irin mischievous smile sending shivers down my spine. Ya rike idanuna da nashi yayin dana kasa janye nawa idanun daga gare shi, wasu irin abubuwa ne suke fita daga nashi idanun suna shiga nawa idanun suna haddasa min wani irin rawar jiki da bugun zuciya yayin dana fara jin zufa tana tsattsafo min a tafin hannu dana kafata, murmushi ya saki mai sauti tare da janye jikinshi ya jingina da mota, na saki ajiyar zuciya a hankali. Mota kawai ya bude ya shiga tare da bude daya bangaren ya kalleni, "get in" na kalleshi na dan lokaci kafin na zagaya ta daya gefen na shiga, kamshin freshener na water lily ya gauraye cikin motar, motar was unbelievably nice da alamun sabuwa ce, ya tashi motar muka fara tafiya yayin dana lumtsume a cikin seats din motar masu tsananin laushi, gajiyar dana yi ta fara sirarewa daga jikina, na kara relaxing gami da lumshe idanuna, ban san ina muke nufa ba, Ya Allah! Ban ko yi tunanin ina zai kaini ba na fada cikin motar shi, way to go Nafeesah!! Naji zuciyata tana tuhumata akan rashin tunanina. Na bude idanuna a hankali da niyar tambayar shi inda muka nufa, daidai lokacin yayi parking a bakin wani restaurant. Ya bude murfin motar ya fita nima na take mishi baya. Cikin restaurant din babu mutane sosai, muka samu table muka zauna. Da sauri waiter yazo da list din dishes dinsu, Abbu ya karba yayi order muka zauna jiran a kawo abincin. Abbu jingina yayi da kujera kawai ya kura min idanu yana kallo kamar wanda ya samu TV, yayin dana sadda kaina kasa ina wasa da hannun jakata. Kunya gabadaya ta rufe ni, baisan yadda kallon da yake jifana dashi yake affecting dina bane, bai san yadda nake ji kamar in nutse a cikin kasa bane saboda yadda yake kallona kamar wani wanda ya shekara dari bai ga wani abu so dear to him ba, na rasa da wanne zan ji, da kunyar shi ta tun asali dana ke ji ko ta maganar 'aure' daya kirkiro mana ko kuwa ta rejecting dinshi da nayi? Ya danyi leaning hannuwanshi akan table din yana kallona, nima kallonshi nake yi amma fa kamar wadda take tsoron shi ko tsoron jin wani abu daga gare shi, kodayake a zahirin gaskiya ina jin tsoron abinda yazo dashi ne, yaje in jira yi dawowar shi, gashi ya dawo din, me zai faru kenan? Ya bude baki yayi magana a karo na farko tun da muka shiga restaurant din, "to ya kike Nafeesah? Hope you are good?" na gyada mishi kaina, ya koma ya jingina da kujerar da yake kai a zaune tare da rabbe hannuwanshi a kirji, "well actually you kinda amazes me" na saci kallonshi ina so in san dalilin shi na cewa haka, yace "I mean ban yi zaton zan samu tarba irin haka daga gare ki ba, ace common sannu da zuwa wannan daga gare ki ta zama golden word, why Nafeesah?" nayi shiru ina sauraren shi, why? Nasan na tsinci kaina a cikin mixed emotions, na farin cikin ganin shi da kuma confusion na ganin shi da wata fargaba wadda ban san dalilin jin ta ba. Aka kawo mana abincin da yayi oda fried rice with liver sauce da plaintains sai lemun 5 alive, ya turo min nawa plate din gabana, "ci koh?" na ja plate din gabana na fara cin abincin a hankali, duk na takura saboda presence din shi a gabana. Gabadaya jina nake yi so strange, tunda maganar auren nan ta shiga tsakaninmu nake jin kaina a gaban Abbu kamar wata bakuwa na rasa ko me yasa haka?? Ya dago daga kai abinci bakinshi ya kalleni, "me yasa kika zabi zaman hostel ne?" na daga kafada, "kawai. Na ga kamar hakan zai fi sauki ne" yace "are you sure ba guduna kike yi ba?" na girgiza kai da sauri, "haba dai, gudu kuma? Beside why would I?" ya tabe baki, "wai ma idan abinda kike tunani kenan in fada miki it's of no use Nafeesah, because you will never, ever escape from me!" na hangame baki cike da mamakin wannan Al'amari na Abbu, wasu abubuwa da yake yi kwanan nan suna daure min kai, sometimes zai yi magana ne kan shi tsaye ina tunanin baya tuna cewa Nafeesah yake yiwa magana ba matar auren shi ba, yana nuna yana da control over me kamar an riga an daura mana aure. Na rufe bakina tare da kai spoon din abinci bakina, shima murmushi yayi kawai ya cigaba da cin abincin shi. Babu wanda ya sake yin magana a cikinmu har muka gama cin abincin, Abbu ya biya kudin muka fito. Sai da muka fara tafiya na kula ashe a cikin makaranta wajen yake, ko a cikin mota bamu yi magana ba sai kallona ta madubi da Abbu yake, shi kanshi yasan cewa ya takura min da kallo, ya danyi murmushi yace "na takura ki koh? Sorry, bani da zabi ne Nafeesah when you look this attractive..... Me kike shafawa fatar kine kullum wani fresh kike kara yi" naji alamun blushing a kan fuskata, Anya Abbun dana sani ne kuwa? Yau gabadaya ya zame min wani sabon mutum, maganganu yake jefa min carelessly ba tare daya kula da yadda suke affecting din zuciyana da gangar jikina ba. Yayi parking a cikin parking lot muka bude motar muka fita, na zagaya ta gefenshi nace "Abbu nagode, Allah ya saka da alkhairi sai da safe" kallona yayi ba tare da yayi magana ba, sai na rasa abinda zan yi, in jira umarnin shi ne ko kuma in tafi abina? "me yasa kika ce ba zaki aure ni ba?"

Kamar daga sama naji saukar maganar tashi, na zaro ido sosai. Ban taba zaton zai kawo maganar yanzu ba shi yasa na rasa irin excuse din da zan bashi ma don haka nayi shiru ina jin kafafuna suna rawa a hankali, dama ta yaya nake tunanin tsayawa da kafafuna under Abbu's gaze?? Yace "ina jin ki Nafeesah, last time dana tambaye ki baki bani amsar data gamshe ni ba, yanzu na sake tambayar ki ina bukatar jin gamsasshiyar amsa wadda zata yi convincing dina, so gaya min, me yasa baki son aurena, na miki tsufa ne?" da sauri na girgiza kaina, "baki so na?" na zaro ido ina muzurai, me ya kamata in ce? Yace "kince kina da wanda kike so kuma ni na tambaya a gidanku ance babu kowa, Nafeesah! Dana ce ina son auren ki ba wasa da hankalin mu naso muyi ba, kada kiyi tunanin nima ban hango ko tunana abubuwan da kike hangowa ba, amma meye a ciki? Babban abin bukata Anan shine ace muna son junanmu kuma muna da muradin kasancewa tare, then babu abinda zai faru, there's no body that can criticise us saboda akan gaskiyar mu muke. Enough of all this Nafeesah, na gaji, na gama baki iya uzirin da zan baki, yanzu amsar ki nake so kawai, aure yes ko a'ah?" fuskata ta taru da kwalla, me yake so inyi a irin wannan lokacin idan yazo min da magana kai tsaye yana bukatar amsata? Ya kalle ni da mamaki, "kuka? Na bata miki rai ne?" nayi saurin girgiza kai, "to menene?" nace "I just need time to think over it" ya shafa sumar kanshi, "Lord! Wani lokaci kike so kuma bayan duk lokacin dana baki? Dana ce miki na gaji Nafeesah I mean it, and I don't have the heart to wait any longer" na dan rausayar da kaina gefe, wannan abun fa nice zanyi shi, idan ma da wani abu I'll be the one to take the responsibility, me yasa ba zai barni in yanke hukunci da kaina ba? Yace "ok.... ok... Naji. But believe me Nafeesah, wannan shine lokaci na karshe da zan baki, idan baki yanke shawara ba I'll just do it on my own way, Allah yasan cewa na baki hakkinki" na dan jijjiga kai, ya bude bayan motar ya ciro dan karamin kwali ya miko min, ba musu nasa hannu na amsa tare da mishi godiya, ya bude motar ya shiga tare da mata key, na dan ja baya har yayi ribas, ya kalle ni yana murmushi, "any sako for pretty??" nima nayi murmushin, "a gaida min ita sosai, ace mata nayi kewar ta" ya gyada kai, "well, kiyi duk iya kewar ta din da zaki yi kafin kizo kema kiyi naki babyn na kanki" na zaro idanu yayin daya saki murmushi gami da min wink yaja motar ya wuce ya barni da bin shi da kallo kafin na girgiza kai ina murmushi na wuce cikin hostel. Firdausi bata dakin, na ajiye kayan hannuna akan gado naje na watsa ruwa tare da dauro alwalar sallah na fito, lotion kawai na murza a jikina na saka kayan barci tare da daura zani a saman kayan nayi sallah, dana gama na dauko Al-Qur'ani Mai Girma ina karantawa har aka kira sallar isha'i nayi tare da Shafa'i da Wutiri, ina cikin nade abun sallar Firdausi ta dawo, na mata sannu da zuwa ta amsa. Waya na dauka na kira Mom muka gaisa tana tambayana karatu na amsa mata da lafiya lau, naso in tambayeta dalilin da yasa bata son Aurena da Abbu sai kawai nayi shiru, na mata sai da safe tare da kashe wayar. Anty Shafa na kira muka gaisa, mun jima muna hira da ita tana kara bani shawarwari akan rayuwata, tace idan har ina son Abbu I should just go for it, na mata godiya muka yi sallama. Na janyo assignment dina na karasa, lokacin dana gama karfe goma tayi already, kwanciya nayi ina tunanika a cikin raina. I think I should just give it a try kamar yadda Anty Shafa tace, after all ba wani sabo ne muke shirin aikatawa ba da nake kokarin kashe kaina saboda son faranta ran mutane wanda nake tantamar ko zasu ga farin abinda nayi at the end of the day?? Nayi murmushi tare da lumshe idanuna, ba jimawa barci mai dadi ya daukeni.

*****

Washegari da safe sai ga kiran Anty Ameenah a cikin wayata, da mamaki na daga muka gaisa da ita, tambayana tayi ko ina free yau? Nace mata ina da class dai amma karfe biyu zan gama, tace how about we have a cup of tea a Flower Garden by four?? Nace mata ba damuwa. Muka yi sallama tare da kashe wayar. Na ajiye wayar a hankali daga kasan raina ina tambayar ko lafiya take son ganina? Curiously.

~Well, m sorry kwana biyu ba kwa ganin posting akai-akai, commitments sun yi mun yawa ne har yanzu ina kokarin sorting out dinsu ne shi yasa amma komi ya kusa zuwa karshe in shaa Allah
~So me kuke tunani game da chapter din yau?
#TeamAbbu 💞💞💞





*♡Jeedderh♡*
[12/23/2017, 13:52] Beluvd Zee: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*



*Wannan shafi na Sadaukar dashi ga Marubuciya SADNAF da MAKAWA, I really appreciate you guys with your cheerful and concern, thanks. Sauran Marubuta ina gaishe ku sosai tare da duk wani Makamancin littafin Ni Da Abokin Babana!*

*39*



Muna fitowa daga lectures masallaci na shiga nayi sallar La'asar daga nan na wuce flower Garden. Anty Ameenah tana zaune a daya daga cikin kujerun da aka tanada, tana hangoni ta fara waving dina tana murmushi, nima murmushin nayi na karasa gareta, kujera naja na zauna ina fuskantar ta, na gaisheta ta amsa tana tambayata abinda nake so a kawo min nace a bani egg roll da lemu don tun safe da zan fita dana sha shayi ban kara komi a cikin cikina ba, aka kawo mana egg roll, meat pie burger da lemun peach. Anty ta kalleni tace "Allah yasa ban takura miki ba da nace ina son ganin ki?" nayi saurin girgiza mata kai, "haba ko kadan wallahi" tayi murmushi tare da gyara zamanta akan kujera, "da farko ban yi niyar sa baki ba akan maganar wannan sai dai ina ga lokaci yayi daya kamata in saka baki, ba shisshigi nake miki ba amma ina so inji inda maganar ku ta kwana?" na dubeta cikin mamaki, "Anty wace magana kenan?" tace "maganar ku da Ibrahim mana!" sai dana kusa zubdo da abinda nasa a bakina saboda maganar da naji cikin bazata. Ta miko min tissue na goge bakina tare da korawa da ruwa, Anty Ameenah tace "m sorry idan baki so hakan ba" kai kawai na girgiza mata, amma a kasan raina ina mitar me yasa don kawai Abbu yana son aurena sai kowa a cikin dangin sa ya sani? Kamar wadda take karanta mind dina, tace "kada fa kiyi zaton Ibrahim ne ya gaya min ko ya turo ni, bashi bane. Kwanakin baya dai ya taba neman shawarata akan cewa yana so ya aure ki, me nake gani? Naji dadin hakan sosai, wallahi abu ne wanda ya jima yana min amsa kuwwa a cikin kaina, tun ranar farko dana fara ganin ki Nafeesah na yiwa Ibrahim sha'awar kasancewar ki matar shi, sai dai sanin halin Ibrahim yasa na kame bakina nayi shiru. Ba tun yau ba nake mishi maganar kara aure amma sai ya wawantar da maganar, ba ni Kadai ba Hajiyar mu ma tayi nata kokarin ganin irin zaman da yake yi da matar shi but to no avail. Amma jin da kanshi yazo yana ce min yana sha'awar kara aure nasan cewa da gaske yake, Ibrahim baya nuna bukata akan abinda yasan baya so, musamman akan zancen nan Nafeesah, I've seen something different in him. To kuma tun daga lokacin har yanzu ban sake jin yayi magana game da hakan
Showing 63001 words to 66000 words out of 122880 words