wani saurin ku aurar dani kuke yi kamar wadda kuka gaji dani? Wane irin aure ne kuke shirin yi mun haka daura aure kafin tarewa?" tace "to ai gani nayi hakan zai fi mana sauki da mutanen da zasu zo daurin auren, ace anyi aure da wata daya wasu ko gama kafe gajiya basu yi ba a sake juyowa yin wani auren kin ga ai akwai takura, ba gwara ayi a wuce wajen ba?" nace "Mommy ni bani da zabi, kuyi duk abinda kuke ganin daidai ne" tace "to Allah ya miki albarka, Yasa hakan shi yafi alkhairi.... Oh su Ummiey za a zama matar aure!" da sauri na kife wayar a kan gado na fara juyi akan gadon idanuna akan fuskata kamar Ina gaban ta. Abbu ya kira ni a daren ranar cikin tsananin farin ciki da murna, yace "kin gama yi mun komi Nafeesah, kin saka zuciyata cikin farincikin da bata taba shiga ba, Allah ya miki albarka Nafeesah! I'll definitely compensate you Amour, yau zan ma iya barci kuwa saboda murna?" da wadannan kalamai nashi na kwanta suna min amsa kuwwa a cikin kaina, tabbas I'll be the luckiest bastard on earth matukar na auri Abbu, Abbu!! Allah ya nuna min ranar da zan zama matar shi lalle zan kere sa'ah.

Bayan kwanaki biyu Abbu ya dawo daga Ilorin, da yake dawowar safe yayi gida ya wuce ya dan huta ya shirya kafin ya shigo cikin makaranta, lokacin muna cikin lab muna practical don haka yace in same shi a office dinshi idan mun gama. Sai karfe biyar muka fito, ban tsaya yin komi ba na tunkari ofishin Abbu cikin wani irin doki, ji nake kamar in yi fuffuke ko in bude idanuna in ganni a gaban shi, in dora idanuna akan kamilalliyar fuskar shi mai saka ni cikin nishadi, nayi kewar shi, ban taba kewar abu a rayuwata har nake ji numfashina yana daukewa saboda rashin wani abu kamar yadda nayi kewar shi ba, how I can survive without Abbu a rayuwata yanzu, only Allah knows. Jikina har rawa yake lokacin dana hau corridor da jerin offices yake ba, naja nayi burki a kofar ofishin shi Ina kokarin saita kaina kila idan na shiga kai tsaye a yadda nake zai iya zaton ko gudu nayi naxo gare shi. Na daga hannu da niyar yin knocking na jiyo wata murya tana magana, cikin Jan hankali, cikin kissa da kisisina, cikin wata murya dake baiyana tsananin bukatuwa da roko..... Zuciyata ce ta bada wani irin sauti da naji shi tamkar saukar aradu......
~Me kuke tunani game da chapter din Yau?
~Mommy fa? Ya kuka gani? Ta burge ku??
~Keep voting, sharing and commenting word by word dearies,
#TeamAbbu
#OneLove





*♡Jeedderh♡*
[12/25/2017, 00:47] Hauwa-Jedderh💕: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*



*42*


"Dr. Ibrahim baka tunanin lokaci yayi da xaka yi recognising din soyayya ta zuwa gare ka? Kana sane da halin da ruhina yake ciki saboda kai, soyayyar ka na azabtar da zuciyata a kowace rana amma kayi kunnen uwar shegu dani kana nuna kamar baka san komi ba, haba Ibrahim, ka tausaya min mana please!!" kafafuna suka shiga rawa na kasa yin knocking din da nayi niyar yi, a hankali na matsa ta jikin tagar office din da yake a bude take. Abbu yana tsaye ya juyawa tagar baya, ya rungume hannayen shi a kirji yana fuskantar ta yayin da ita kuma take fuskantar tagar duk da cewa dai bana iya hango fuskar ta amma yanayin shigar da tayi m not satisfied with it. Ko dai tayi kwalliya ne don tayi seducing din Abbu na ko kuma ta saba yin tambadaddiyar shiga ta marasa mutunci kamar yadda tayi yanzu. Abbu yace "Dr. Luba Ina ga wannan abu ai yana gare ki ne, ba tun yau ba na riga da na fada miki cewa Ina da aure har da 'ya'ya...." ta katse shi, "nima ai nace maka zan iya aurenka a hakan, meye hadina da matar ka ni? Kai zan aura ba ita ba!" yace "am getting married, in the next two months in shaa Allah!" ta laulayo wani ashar ta maka, "says who? Karya ne Dr Ibrahim, wallahi Karya ne! Babu 'ya macen data isa ta aureka Ina tsaye Ina kallo, idan ma wasa kake yi tunda wuri ka fadi kafin in aikata abinda ran mu ba zai mana dadi ba" yace "me yasa zan miki wasa? Ba tsoron ki nake ji ba kuma ba shakkar ki nake yi ba, ban san ko sau dubu nawa kike so in fada miki cewa bana son auren ki ba, you are not my type Ramlah" tace "but you are my type, and there's no way da zan zauna ina kallo a gaban idona wata ta dauke abinda nake so ba, Karya ne wallahi...." ta kara taku zuwa gaban shi ta kai bakin ta daidai kunnen shi, ban san me ta rada mishi ba, naga dai taja da baya yayin da Abbu yayi shiru kawai, can kuma naji yace a hankali, "get out please Dr Luba" tace "ba kai kace in zo ofishinka ba ra'ayin kaina ne, don haka idan zan fita ma yanzu sai nayi ra'ayi, gashi kuma ban gaji da ganin fuskar ka ba, ya za ayi kenan?" na hangame baki cike da tsananin mamaki, lallai duniyar Allah mai fadi, xaka ga mutane daban-daban masu hali iri-iri, ita kuma wannan wacece? Zuciyata ta hau wani suya kamar zata fito daga kirjina, ji nayi kamar in banka kofar ofishin in shiga in jawo ta by her hair in fada mata Abbu nawa ne, in ma ta kai ga tofa mata yawu a fuska duk zan yi matukar zata fita daga cikin rayuwar Abin sona. Na koma ga kofar na fara knocking da karfina kamar zan balla ta, Abbu ne ya min izinin shiga. Na tura kofar na shiga with full of attitude and Charisma, so that wadda take ikirarin mallakar Abbu na ta karfi da yaji taga cewa am not the type of people da ake musu kwacen abinda suke so, abinda suke Jin cewa ba zasu rayu ba tare dashi ba right in front of their eyes ba tare da sun yi abu ba. Abbu ya juyo yana kallona, murmushin daya saki kadai yasa naji wani irin kwarin gwiwa ya mamaye ni, naji duk wata fargabar kada fa matar dake gabanshi ta kwace min shi ta tafi ta barni a take, tabbas Abbu shine mahadin rayuwata. Nima na mayar mishi da martanin murmushin wanda yake kunshe da zallar so da nuna tsananin kewar shi da nayi kafin idanuna suka sauka akan matar dake ikirarin claiming din abinda yake nawa. Ta sha uwar kwalliya a fuska saboda tsabar kwalliya ba zaka tantance ainihin kala ko kamanninta ba, tasha adon izgar doki wanda ya sauko a kafada da gadon bayanta, wani material ne a jikinta an mishi wani irin watsattsen dinki na Allah wadai wanda ya fito da shafaffen kirjinta kamar shafaffen silifas, dinkin ya matse ta tun daga kirjinta har cinyoyinta, ta wani kalleni tun daga sama har kasa yayin da nake kallonta disgustingly cikin nuna kyama kamar wadda taga abin kyankyami wanda na tabbatar da cewa sai ya kada mata 'ya'yan hanji. Abbu ya katse mana kallo-kallon da muke wa juna ta hanyar cewa "Dr Luba meet my dearing wife, Nafeesah. Nafeesah she's my co worker" nace "sannu, ya kike?" ta tabe baki tana wani yamutse fuska, "wannan abar ce dama kake wani tada jijiyoyin wuya kana cewa wai zaka aura? Me ta fini dashi?" Abbu yace "ko zaki iya bamu waje, Ina son sirri" ta buda kofofin hanci har suna naso, "ko baka ce ba yanzu zan bar maka ofishin ka kafin ka wulakantani a gaban wannan er yarinyar, sai dai kada kayi tunanin na hakura ne, ko ta halin yaya sai na mallake ka Ibrahim saboda kai nawa ne!" ta warci jakar hannunta ta fita tana murguda kugu kamar wani shafaffen plate saboda rashin cikowar shi, na bita da kallo Ina murmushin mugunta, matar nan ta rainawa kanta hankali da yawa, ni ta kira da yarinya koh? Allah ya kara hada ni da ita wani lokacin, ni kuma nayi alkawarin nuna mata aikin yarinta. Na maida kallona ga Abbu lokacin data fita daga office din ta maida kofar tayi banging kamar tashin duniya. Murmushi na sakar mishi softly, duk da cewa har zuwa lokacin zuciyana tana itching game da Luba ce ko Bana yace sunanta? Bana so in sani. Yaja kujera ya zauna a kusa dani tare da nuna min wata kujerar nima na zauna, yace "kiyi hakuri da abinda ya faru, kada kuma ki sa maganar ta a cikin ranki, ta saba irin wadannan maganganun duk burga ce da tauna tsakuwa don aya taji tsoro" nace "wai wace? Ni ban ma fahimci abinda take fada ba balle in saka shi a cikin raina...," ya kura min idanu yana murmushi, "kin san abinda yasa nake kara jin ki a cikin raina kenan? Nafeesah my other being" na sadda kaina kasa Ina dan murmushi, Abbu with his flirtations, a hankali nace "sannu da dawowa, ya hanya?" yace "it was tiresome, amma yanzu na dawo normal dana gan ki, my wife!" wayyo kunya! Na rufe fuska ta da hannuwana ina er dariya, shi kuwa dariya ya saki sosai, a tausashe. Nayi shiru Ina jin dariyar da yake yi, he sound so relieved and happy, and I feel proud knowing that ni ce sanadin farincikin da yake ciki.

Cikin barci na kai hannu kasan filona na lalubo wayata dake vibrating, duka-duka karfe goma ne da rabi na safiyar ranar Assabar, da yake ranar hutu ce kuma ban samu nayi barci da wuri a daren jiya ba shi yasa na ke jina kamar wadda ta kwanta a lokacin saboda tsabar barci. Ban ko tsaya duba caller ID ba na dauka, muryar Sadiya ce ta doki kunnena, "Asslm, Nafeesah hope ban katse miki barci ba?" cikin muryar barci nace "kin katse min mana" tace "sorry, dama muna nan AKTH ne shine zan fada miki" na tashi zaune a sukwane nace "Teaching Hospital kuma? Waye babu lafiya?" tace "Ni'imah ce wallahi, ta samu miscarriage yau da safen nan" jikina yayi sanyi sosai, Allah sarki Ni'imah. Nace "ki turo min da number din dakin da kuke, gani nan zuwa" na ajiye wayar tare da dirowa daga kan gado. Wanka nayi na fito na Karya, ban wani tsaya yin kwalliya ba na saka kayana kawai na fita, sai a cikin mota ne na kira Ramlah Ina fada mata, tayi jimamin abin sosai tace zata kira ta mata jaje. Ban samu Sadiya ba a dakin da aka ajiye su lokacin da naje, Anty Ameenah da Anty Rayyah suna nan a dakin tare da wata dattijuwa sai kannen Bashir mata su biyu, Ni'imahr na kwance tana barci an sa mata drip, ta wani dashe tayi fari tas kamar wadda babu jini a tattare da ita. Muka gaisa dasu Anty Ameenah cikin mutunci har tana bani hakuri akan wai an taso ni daga makaranta, nace a kunyace haba Anty, Ni'imah tafi karfin haka a wajena ai.... Allah ya mayar mata da mafi alkhairi, suka amsa da ameen. Sadiya ta shigo dakin hannunta rike da na Jameel dan Anty Jameelah wanda yake tafiyar ta-ta-ta, muka gaisa da ita itama na musu jaje, naja Jameel a jikina ina tambayar shi inda yaje yana ta min gwaranci ina murmushi. Ni'imahr bata farka ba sai bayan azuhur, su Anty Ameenah suna waje suna sallah da yake ni fashin ta nake yi, na matsa gefen gadonta Ina mata sannu tare da tambayar ta abinda take bukata? Kuka kawai ta saka tana shafa cikinta, na rungumo ta a jikina ina dan jijjigata kamar nima in rushe da kukan nake ji, it's not easy ka dauki cikin abu ka raine shi, bayan ka gama kwallafa ranka a kanshi kuma sai Allah ya jarabce ka da rashin sa, hakika Allah kadai yasan irin sakayyar daya tanadarwa irin wadannan matan. Nace "kiyi hakuri Ni'imah, haka Allah yaso. In shaa Allahu zai kawo miki mafi alkhairin sa, stop crying please kinji?" ta jijjiga kanta. Naje na xubo mata ruwa a cikin cup ta kurba, lekawa nayi na gaya musu ta farka sai gasu sun duro cikin dakin, kowa sannu yake jera mata tare da nasihar fawwalawa Allah lamuranta, nan aka zuba mata abinci muma muka zuba namu muka ci. Da yamma sai ga Bashir din yazo ashe ma baya gari saukar shi kenan daga Abuja, bawan Allahn nan har da hawayen shi abin gwanin ban tausayi wallahi. Bayan Magriba su Anty suka yi haramar tafiya gida, Anty Rahina tace in zo ta sauke ni a makaranta mana nace mata ai ni anan zan kwana, tace inah! ga Sadiya nan da Gwoggo Hinde sun isa in zo ta maida ni makaranta kawai, nace mata ni fa anan nayi niyar kwana. Tayi shiru tana kallona ganin na kafe kafin tace "kin fadawa iyayen ki?" nace "zan fada musu anjima dai" tace ai shikenan, Gwoggo Hinde zo mu wuce gida dake kawai. Da haka suka mana sai da safe suka tafi bayan sun ajiye mana duk abinda zamu bukata. Na shiga bandaki na gyara jikina, ban taho da panties bama sai dana fita waje na sayo wasu pad ce ma ban nema ba da yake ni ma'abociyar ajiyar su ce a cikin jakata saboda emergency. Na fito daga bandakin ina gyara zaman rigar jikina, daidai lokacin Abbu yayi sallama ya shigo cikin husky voice din nan nashi Hafsy na biye dashi a baya, zuciyata tayi wani irin fari da ganin shi kamar zata haske duniya da abinda ke cikinta, gabadaya ranar ban ji muryar shi ba mun dai yi exchange din messages a tsakaninmu da rana, fuskar shi ta nuna zallan mamaki da ganina kafin baiyanannen farin ciki daya kasa boyuwa ya nuna akan fuskar tashi, na ja kujerar kusa da gadon Ni'imah din na zauna. Na Kalli Hafsy dake tsaye a bakin gadon Ni'imah na mika mata hannu alamun tazo ina murmushi, ta makale kafada tare da kara lafewa a jikin Abbu alamun ba zata zo ba, na janyo ta jikina tana kokarin kwacewa amma na hana ta, nace "haba Hafsy na ni dake bata baci, Waye ya tabo min ke?" ta turo baki tana nuna ni da yatsan ta, nace "ni da kaina? Me na miki?" tace bake bace ba kike kin zuwa ki gaida ni, kullum sai nace kizo ki ganni amma baki taba zuwa ba! Na dan saci kallon Abbu dake gaisawa da kannen shi amma idanuwan shi suna kanmu yana mana dan murmushi, na janye tare da kallonta nace "kiyi hakuri kinji? In shaa Allahu zan dinga zuwa Ina ganinki, so stop frowning and smile kinji?" tace "promise?" na gyada mata kai. Aka kwala kiran sallahr Isha'i a daidai lokacin, Abbu ya zube min wayoyin hannunshi a gabana ya fita da niyar yin sallah.....
~Nasan zaku ce chapter din yau ma yayi kadan, amma ya zanyi? Wallah bani da lokacin yin typing da yawa Ne shi yasa
~Lots of love and Hearts Ni Da Abokin Baba Na Fans
#TeamAbbu
#OneLove❤❤
#AnaTare🤝🤝🤝





*♡Jeedderh♡*
[1/1, 18:03] Hauwa-Jedderh💕: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*

*_Wannan shafi dungurungum na marubuciya RUFAIDA UMAR IBRAHIM ne. I was touched and impressed lokacin dana ji cewa cikin masoya kuma makaranta littafin Ni Da Abokin Baba Na kina ciki. Sauran Marubuta dake bibiyar littafin ina gaishe ku, wadanda suke kan posting nasu littafan ina musu fatan alkhairi. Masoyan Ni Da Abokin Baba Na ina gaishe ku a duk inda kuke. #OneLove_* ❤❤❤



*43*



Suka kalli juna kafin suka kalleni, Sadiya ta dage gira daya "me kenan?" "me fa??" na tambayeta ina wani fuskewa ni ala dole ban fahimceta ba. Tace “ki wani daina fuskewa malama, mun san abinda ke faruwa tsakanin ku biyun nan" na kada mata idanu innocently, “ni da wa??" ta kai min duka a kafada, “zaki sani ne maras M, ace kamar mu kuna cikin relationship da Yayan mu mu kasa sani?" na kallesu su duka biyun ina so in karanta yadda suka amshi zancen, ban karanci komi ba sai dai murmushin dana gani kwance akan fuskar su na farin ciki ne bana embarrassment kona takaici bane, naji sanyi ya lullube min zuciya, at least abotar mu dasu tana nan. Ni'imah tana murmushi tace “Sady ke kike wani tsayawa ma kina neman karin bayani, ni fa dama tun ba yau ba na harbo jirgin su ita dashi, they were making it obvious shi yasa ni ban tsaya jira a fada min ba nayi jumping into conclusion" na dan harareta cikin wasa nace “ni kar ki mun sharri wallahi" tace “ba wani sharri sai gaskiya. Irin kallon da kuke wa juna dama tun ba yau ba be it kuna cikin mutane ko ku kadai ne wallahi na soyayya ne, ai Anty Rahina tace an kusa yin auren" na dafe kirji ina zaro idanu, nace “su Anty har sun sani??" dariya suka saki suna kallona kamar wata kuntacciya dinnan, “Allah kina kwafsi matar Babban Yaya, tunda har muka sani ai dole su Anty su sani kuwa" na rufe fuskana ina diddira kafafuwa a kasa, “Ya Allah! Da wani idanu zan kallesu ni kam?" suka sake kwashewa da dariya har da tafawa, na hade fuska ina kallonsu, “this is not funny fa!" na fada in
Showing 72001 words to 75000 words out of 122880 words