"to Daddy nagode, Allah ya bar min kai!" yayi dariya tare da cewa "uwata kenan". A ranar muka shiga kasuwa muka sayo ashoben bikin, muka biya ta wajen telan Ramlah muka ajiye dinkin. Ranar juma'ah muka je saloon aka mana wankin kai da kitso, ni har kunshin hannu aka min, dama gani da son lalle kamar me. Ya kuwa yi min kyau sosai, sai da Ramlah taga na hannuna wai take cewa data sani da an mata itama, na kuwa dinga mata dariya. Daga nan muka yi shatar taxi muka wuce gida, sai da muka ajiye ta kafin muka wuce. Ina shiga falon naci karo da buhunan Irish, plantain ne, kayan marmari dasu doya, tunda na gani nasan cewa Abbu ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa Ibadan taron Doctors na fadin Nigeria, Allah ya taimaki rayuwata na mishi text na gaya mishi zamu biya ta saloon daga lab, yau da na shiga uku na ai. Na taimakawa Harira muka kai kayan kicin muka ajiye su a inda ya dace kafin na wuce dakina nayi sallah. Ina xaune Hafsy ta leko dakin tace in fita mu ci abinci, bana ma jin yunwa amma haka nan dai na fita don nasan bani da wani excuse din badawa. Na dauki gyale mai fadi na dora akan doguwar rigar jikina. Bana yarda in fita daga dakina ba tare da mayafi ba matukar nasan Abbu yana gari sai dai by mistake. Suna kan dinning table a zaune, Abbu na fara hangowa. Sanye yake da shirt din KC brown da bakin Jeans, ya kara wani irin kyau na musamman a kwanaki shida din da nayi ban gan shi ba. Na tafi da dokina na durkusa na gaida shi, shima cike da fara'ah ya amsa min, na gaida Anty Mubeenah kafin naja kujera na zauna muka fara cin abinci. Da muka gama Abbu ya fita, Anty ta wuce daki mu kuwa muka zauna a falo muna kallo har wajen karfe goma da rabi, har lokacin Abbu bai dawo ba. Na kashe kayan kallon kowannen mu ya nufi dakin shi ya kwanta.

Wajen karfe uku na dare na farka, kishi ya dame ni sosai ji nake kamar numfashina zai dauke dole na farka daga daddadan barcin da nake yi, gidan dama duniyar gabadaya tayi shiru kamar babu mai numfashi babu ko karar fan saboda an dauke wuta. Fitilar wayana na kunna na lalubi goran ruwa dana saba shiga daki da ita a kullum Saboda na sanni da bukatar shan ruwa sometimes sai dai babu, da alamun na manta ban shiga da ita ba ranar. A hankali na bude kofar dakina na fito, na fara tip toeing zuwa kicin kamar wadda zata je yin sata. Daidai kafar dakin Anty Mubeenah na jiyo kamar alamun sautin tashin maganganu, ban san dalilin daya saka ni kara kasa kunne ba, muryar Abbu ce take tashi kamar cikin fushi, "For goodness sake Mubeenah! How long has it been?? Kin san yaushe rabona dake? Kina ma kirga yawan kwanakin kuwa? Me yasa ne?! Me yasa ne ba zaki yi treating dina kamar yadda kowanne namiji yake samun kulawa daga matar auren shi ba? Na tambaye ki time without numbered Mubeenah, idan ma wani laifi na miki don't you think it's high time da zamu manta da komi mu rungumi rayuwar yayanmu hakanan ba?" tsaki naji taja, "kace duk abinda zaka ce Ibrahim! Ba damuwata bace, yaya da kake magana a kansu inaga ai bai kamata ka sako su ba, kai kace I just need to have birth to them, you will take care of them, meye hadina dasu then??" shiru na tsawon mintuna biyu ya wuce yayin dana kara kasa kunne, a sanyaye naji muryar Abbu wannan lokacin, "hakkina fa kuma Mubeenah?" "ni fa kaga ka dame ni ka hana ni barci na haba! Saboda tsabar fitina da jaraba a kyale mutum yayi barci ma cikin kwanciyar hankali ma ba za ayi ba?" amsar Anty kenan. Cikin daga murya yace "am fed up with ur cruel habits Mubeenah, dole ki gyara halinki idan kuma ba haka ba....!" katse shi tayi ta hanyar sakin dariya, ".... Idan ba haka ba zaka kara aure? Go ahead then, ko a da can ma hakan bai dame ni ba Ibrahim balle yanzun ka gane? Allah yasa matan duniyar nan zaka auro, I wouldn't give a damn! Now can u get out please? Ina so inyi barci!!" ina jiyo hucin daya dinga fitarwa a fusace kamar zuciyar shi zata fito waje, cikin wani irin threatening murya yace "zan shayar dake ruwan mamaki kuwa Mubeenah" cikin muryar ko-in-kula, I bet she was shrugging her shoulder up ma lokacin kila tace "m looking forward to it" daga nan naji ana kokarin fitowa daga dakin nata, a sukwane na fada bayan labule tare da saka yatsa na danne saitin wajen dake samar da hasken flashlight a wayata. Yana fitowa ya maida kafar dakin da karfi ya rufe ji kake 6ammmmm!!! Ina jin lokacin daya bude kofar dakinshi ya shiga, sai dana bashi kyawawan mintuna goma kafin na fito daga maboyata na fada daki ruwan da ban sha ba kenan na koma kan gado na kwanta xuciyata fal cike da tausayin ma'auratan. Me ke damun Rayuwar Auren su ne haka??





*♡Jeedderh♡*
[11/24, 15:13] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*18*


_'Turn to Allaaah he's never far away......_
_'Put your trust in him, raise your hands and pray..... Ohhh Ya Allah! Guide my steps don't let me go astray..... You're the only One Who can show me the way..... Show me the way........ Show me the way...........'_
*In Shaa Allah by Maheer Zayn*



Da kyar na samu na sauka daga kan gadona ganin na gaji da juye-juye barci yaki zuwa misalin karfe tara kenan na washegarin ranar Assabar. Na fito daga dakina sanye da wandon Sports da rigar shi cotton ruwan madara, na dora hular beanie akaina wadda na nannade gashin kaina na saka a ciki. Wandering na fara yi a cikin falon hannuwana saye cikin aljihun wandon. Na tsaya a kasan staircase din dake falon, tunda nake a gidan ban taba Hawa saman ba, jifa-jifa dai na kan ga ko dai Abbu ya hau ko kuma yara sun sauko kuma ban taba tambayar me suke yi a wajen ba. Out of curiosity na fara takawa ina hawa saman, Tun kafin in karasa na saki baki galala ina kallo. Gym zan kira shi ko kuwa amusement park?? Kayan wasan yara kala-kala da different types of exercising machines ne birjik a wajen, wasu na san su saboda nima ina zuwa gym duk weekends lokacin da ina gida. Na fara zagaye wajen cike da mamaki, as in Abbu will never cease to amaze beings. Kan Dip station na hau na fara kokarin dagawa amma ko motsi, da alamun yafi karfina ne don haka na sauka. Daga bayana naji ance "hey! What are you doing here??" da sauri na juya, yana tsaye a jikin wata kofa sanye da sportys ya rataya dan karamin tawul a wuyanshi, na sadda kaina kasa cikin rashin abin cewa. Ya fara takowa a nutse har yazo gab dani, ya jingina da station machine din, jin yayi shiru nasan sauraren amsar da zan bashi ne yake yi, nace "umh! Dama kawai ina zagaye ne sai kuma naga na shigo nan" yace "this is your first time here I believe?" na gyada kaina. Yace I see. Are you interested in exercising?? Da sauri na dago ina kallon shi, "sosai ma Abbu! A gida ma ina zuwa gym duk sat...." wani irin kallo yake wata min babu shiri na kama bakina na bame, na sadda kaina kasa ina jin kafafuna suna dan shaking. Kokarin fita ya fara yi yana cewa "sai ki dan motsa jikinki ko? Ni zan sauka kasa..... By the way, I like your lalle!" nayi murmushi ina kara kallon hannuna, ni kaina nasan lallen yayi kyau sosai. Yana fita na fara wasa da karafa, sai wajen karfe goma da rabi na sauko falo, break nayi na koma dakina, sai lokacin naji gajiya da barci sun tarar min na kwanta. Kiran wayar Ramlah ne ya tashe ni daga barcin da nake yi, tace gata nan ta shigo layin mu daga amsar dinki in fito waje, na tashi da sauri na dora hijabi akan kayana na fita. Abbu da maigadi da wani makocin Abbu din suna kofar gida akan dan benci suna hira, na gaidasu. Ina tsayawa sai gata cikin napep, ta fito ta biya mai napep din, ta gaida su Abbu kafin muka shige cikin gida. Muna shiga ta fara jefo mun tambaya a rikice, "ke waccan giant gaye din waye? Anan gidan yake zaune?" cikin alamun tambaya nace wa kenan? Tace "wani farin gaye haka da jallabiya baka a jikin shi??" dariya na kwashe da ita nace "wai dama baki san Abbu ba duk abinnan da ake yi?" tayi turus! Da gaske wancan ne Abbu? Na gyada mata kai, "Ya Allah! He's cool babe, dan dai yana da mata wallahi....!" duka na kai mata ina dariya, "da bashi da mata fa sai kiyi me maras M? Kina da mijin aure a hannu dai shegiya" ta turo baki. A dakina muka zube, ta fiddo kayan sun yi kyau sosai, "sai dai rigar tayi show me da yawa" na fada cikin korafi ina kara juya rigar, ta harare ni, "to sheikha. Ina cewa gyale zaki saka?" na turo baki kafin na daga kafada sama.


Wajen karfe hudu muka isa wajen shagalin bikin. Tuni an fara shagalin, yawancin en makarantar mu sun je abin an jima ba a hadu ba nan muka hadu aka yi ta hirar yaushe gamo ana hotuna. Ana gama sallar ishai'i aka fara daukar mu zuwa wajen dinner. Mun sake wata kwalliyar cikin doguwar rigar gown ta ankon zuwa dinner, purple ce sai rose head maroon color da heel shima maroon sai er karamar jaka maroon. Mun sha kyau abinmu kamar ka sace. Mun fito muna kokarin shiga mota zuwa wajen dinner nace karo da Bilyamin abokin Muneer, da mamaki ya min magana na juyo ina kallon shi, nima mamakin ne ya kama ni kafin muka gaisa dashi yake gaya min angon abokin shine. Ya Kalle ni tun daga sama har kasa yace "amma kinyi kyau sosai Nafee" nayi murmushi sosai har da fari, I'm a sucker for compliments. Yace "naga kina yawo ke kadai, Zan iya rokon alfarmar ki zama date dina for today?" nace "y not?" na kira Ramlah tazo muka shige mota abin mu muka wuce. Muna tafe muna ta hira har wajen dinner, wajen ya tsaru sai sautin kida ke tashi muka samu waje muka zauna, amarya da ango ana kan high table. An fara shagali kawayen couple din suka fita fili muka dan taka rawa da liki muka koma wajenmu muka zauna, ana ta shagali har ban san lokaci ya tafi ba sai dana ji karan shigowar message a wayana ta hanyar vibrating, na daga karfe goma da rabi gabana yayi mummunan bugawa, na duba message din daga Abbu ne, *"Where are you now?"* na mike da sauri jikina yana rawa, su duka suka juyo suka kalleni, Ramlah tace meye? Cikin rikicewa nace "Abbu..... Gida. Gida zan tafi yanxu" tace haba! Ki jira a tashi mana dan Allah kinda fa sauran mutane suna nan" nace "noo Ramlah. Abbu just texted me, nasan ma sai na sha fada yau wallahi" ta kalle ni sosai, "to sai me? Ina ce ba Daddy bane? Nasan ko daddy ne ba zai miki fadan kinyi dare a wajen dinar biki ba" na girgiza kai, "baki san Abbu bane Ramlah..... Bilyamin don Allah ko zaka taimaka ka mika ni gida? Babu nisa daga nan" na maida maganar ga Bilyamin don nasan idan nace zan tsaya fahimtar da Ramlah zamu iya kwana a wajen bata fahimta ba, ya mike yana lalubar makulli a cikin aljihun wandon shi, ya ciro key din ya Kalle ni, "muje koh?" na wa Ramlah da wasu daga cikin mates dinmu dake kusa da inda muke muka tafi. A cikin mota Bilyamin yana ta ja na da hira amma sam hankalina baya wajen ko kadan, da kwatance yayi parking a kofar gate. Na bude murfin motor na fita shima ya fita, na zagaya ta gefen shi nace "to Bilyamin ka gaida gida, thanks for the ride" yace "Kar ki damu.... Me za a cewa mutumin ne?" na danyi murmushi nace "kyale mutumin nan naka, kwana biyu shiru amma bai neme ni ba" yayi dariya yace to sai da safe. Sai dana shiga cikin gidan kafin ya tashi motar shi ya tafi. Bakina dauke da addu'ah da komi na shiga falon, babu kowa a ciki, da sauri na shige dakina na rufe, na tuge dankwalin kaina na zauna a gefen gado ina ajiyar xuciya cikin samun relief. Wayata ta dauki kara, ganin Sunan Abbu a jiki sai dana yi kamar Kar in dauka, na dai daure na daga na kara a kunnena tun kafin inyi magana muryar shi ta doki dodon kunnena, a fusace yake maganar, "wato Nafeesah kin raina ni koh? Karfe nawa na kafa miki dokar dawowa gida idan kin fita?" jikina yayi sanyi, naji dama ban je wajen dina din ba da ran Abbu bai baci Saboda ni ba, nace "Abbu don Allah kayi hakuri, wallahi dinner din ne ba a fara da wuri ba" yace "sai kuma aka ce dole ne sai kin je wajen dinner din koda zaki kai karfe sha biyu ne a waje koh?" na girgiza kai kamar yana gabana, yayi shiru. Har ina murna ya gama fadan shi sai kuma naji yace "waye ya kawo ki yanzun?" nace "Bilyaminu ne, dan makarantar mu ne" yace "dan makarantar ku? Kawai Saboda yana dan makarantar ku zaki kwashi kafa ki shiga motar shi babu tsoron komi a matsayin ki na diya mace?" nayi saurin cewa "ai abokin....." sai kuma nayi shiru, harshe na yayi min nauyi sosai na kasa fadar kalmar. Shiru ya biyo baya, bai yi magana ba ni kuma na kasa karasa abinda nayi niyar fada, "it's okay!" naji yace daga can a hankali kamar ba shine wanda yake daga murya yanxu ba, "goodnight!" ya kashe wayar. Na bi wayar da kallo cikin sanyin jiki, da kyar na iya sauka daga kan gadon na cire kayan jikina nasa na bacci na kwanta.





*♡Jeedderh♡*
[11/24, 20:52] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*19*


Juyi kawai nake yi na kasa barcin, na rasa abinda yake min dadi a cikin raina. In normal sense nasan cewa da ace wani ne ya min ihu da daga muryan da Abbu ya min yau sai naji bacin rai saboda ni fa na tsani kawai mutum ya dinga nuna he has control over me alhalin baya da, abunda nasan cewa koh a gida nake Daddy ba zai min kwatankwacin fada da tuhumar da Abbu ya min ba, yes! Daddy zai min fada amma ta cikin lumana da nasiha ba irin na Abbu ba. Amma me yasa? Me yasa ko kadan ban ji cewa Abbu bai kyauta ba a cikin raina?? Na juya daya gefen ina kallon wani frame, hoton mu ne ni da Hafsy, ni na dauke mu ya min kyau sosai shi yasa na kai aka wanke min shi. I was extremely confused a lokacin, kwata-kwata na ma rasa a wani matsayi na ajiye Abbu balle in yanke hukunci. I never, even in my dreams wai inyi mafarkin ajiye shi a cikin jerin abokan Baba na, to amma idan ba Abokin Baba na bane shi ba to waye?? Da wadannan tunanukan barci ya dauke ni cike da wadansu irin mafarkai marasa kan gado. Ranar har so nayi in makara sallar Asubahi, sai wajen karfe shida da rabi nayi sallah, ina gamawa na koma na sake kwanciya. Yatsun kafata naji ana ja, cikin barci na janye kafafuna na maida su cikin blanket tare da kara kankame pillow. Tafiyar tsutsa naji ana min a wuyana, da sauri na bude idanuna tare da hantsilawa kasan gado har ina dan buge kaina, na dago da sauri, yanayin fuskana ya canza daga harara zuwa na mamaki. Da mamaki nake kallon su, Ni'ima ne da Sa'adiya. Zaune suke a gefen gadon suna kallona, nayi tsalle a kansu muna shewa, sai da muka gama na zauna a gefen su nace "me kuke yi ne anan yammata?" ni'ima tace ziyara muka kawo, ko it's not allowed? Nace "ni na isa in ce? Amma da safe haka?" idanuna ya sauka akan agogo, karfe goma da rabi. Sa'adiya tayi murmushi tace "Abinci fa muka kawo wa babban Yaya." na Kalle su "Abbu?" Ni'ima tace "to da wa?? Funkasu ne da mijin taushe mai dadi wallahi,
Showing 27001 words to 30000 words out of 122880 words