tashi kixo ki ci kafin ya huce" na sauka daga kan gadon ina cewa "yanxu kuwa" toilet na shiga nayi brush, na fito na bude wardrobe na janyo bakar BF jacket ta cotton na dora akan vest din dake jikina, na nannade kitson da aka min na daure da ribbon na saka hular beanie muka fita falon, dama nasan yara suna makaranta don haka ban yi mamaki da naga falon babu kowa ba, sai da muka shiga second falo ne na ga Any Mubeenah zaune akan kujera, muka gaida ta ni da su Ni'ima da alamun suma sai lokacin suka gaisa, ta amsa kamar ko da yaushe, babu yabo babu fallasa. Lamarin Anty Mubeenah sam ya daina bani mamaki, shi yasa bana ganin laifin dangin mijinta akan duk abinda zasu ce a kanta, tunda koma meye ai ita ta jawowa kanta. Ace kannen mijin auren ki wai kina amsa musu gaisuwa kamar wasu baki ko irin dangin nan na nesa? Kai ko dangin nesa ne ai ya cancanci ace ka dan nuna sanayya. Na saci kallon su Ni'ima da alamun su abun bai dada su da kasa bama. Muka nufi kan dinning muka zauna, har su na zuba mana funkasun muka fara ci muna er hira. Abbu ya shigo sanye da wata farar riga da farin wando, ya gyara sumar kan shi sai wani irin sheki take yi, da sauri su Ni'ima suka taryo shi suna babban bros! Da fara'ar shi ya tare su ya jingina kowaccen su da jikinshi yana kallonsu, "wato ku dai idan ba aiko ku aka yi ba ba a ganin ku sai a gida ko?" Sa'adiya tace "bros ai kasan halin Baba, baya bari muna yawo fa" yace "ba wani nan dadin baki, ai naji ance har weekend kuke zuwa gidan su Ameenah, wannan ba yawo bane ba kenan?" Ni'ima tace "kar ka damu bros, yau yini ma zamu yi anan" yace ban yarda ba, kwana zaku yi. Ni kam idanuna yana kansu, fadar irin burge ni din da suka yi bata baki da lokaci ne, ban san sun zauna ba sai dana ji muryar Ni'ima a saitin kunnena, "me kike kallo?" nayi firgigit na kalleta, "umh?? Babu komi" ta jefa min wani irin kallo alamun bata yarda dinnan ba, nayi saurin maida hankalina ga Abbu na gaida shi, fuska a cune ya amsa duk sai naji ba dadi, ba haka yake amsa min gaisuwa ta ba. Ji nayi abincin ma ya fita daga raina, na fara tsakura ina turawa a bakina ba don ina jin dadin abincin ba. Su Ni'ima kam hirar su suke yi da Abbu suna dariya. Sa'adiya ta dan tabo ni, na kalleta a sanyaye, cike da kulawa tace "you okay?" na gyada mata kai kawai, Abbu ya kalleni na dan lokaci kafin ya maida kallon shi ga Ni'ima. Anty Mubeenah tazo tayi joining dinmu itama, lokaci zuwa lokaci Abbu yana saka ta cikin hirar da suke yi da kannen shi amma bata cika maida hankali ba duk da nima suna sako ni amma sai dai kawai in danyi murmushi ko inyi nodding a haka dai muka gama cin abincin. Hirar su suka cigaba da yi, na tashi na hada kan kayan da muka 6ata na kai kicin. Kasa komawa inda suke nayi kawai sai na shige daki, Su Mommy na kira na hada mana video call, daddy ma yana gida don haka hirar mu muka sha sosai, na basu labarin bikin da muka je har hotuna da videos din da muka yi na tura musu. Ban yi kuskuren fada musu har dare nayi a wajen bikin ba wanda dalilin haka yasa Abbu ya mun fada kuma har yanxu yake fushi dani saboda nasan kuskurene hakan, kamar nayi kirari ne na dabawa kaina wuta. Su Ni'ima suka shigo dakin na wa su Daddy sallama, nan muka bude sabon shafin hira dasu.

Kamar yadda suka ce, yini sur suka mana a gidan. Da rana Abbu yace kar mu yi abinci, oda aka mana daga Chicken Delicacy peppered chicken da spaghetti lasagna sai yoghurt mai sanyi, muka ci muka yi nak tare dasu Hafsy. Bayan mun gama cin abincin na ja su kicin muka yi baking din cupcakes, babu kayan icing don haka bamu yi icing din shi ba. Da yamma likis Abbu yace su fito ya maida su gida, na rataya gyale a kafada ta muka fita tare dasu zan musu rakiya, cikin motar Abbu picnic su Qaseem ne a ciki sun hakimce Hafsy tana gaba su kuma suna baya Abbun yana jingine da motar yana amsa waya cikin hadadden turancin shi hannunshi daya saye cikin aljihun wandon shi, su Sa'adiya suka shige mota ni kuma na tsaya daga waje muna er hira har ya gama wayar ya shiga motar ya tayar, na ja baya kadan ina daga musu hannu, ya zuro kanshi ta cikin motar yace "yah? Baki zuwa ne ke?" na kalli su Ni'ima kafin na kara kallon shi, "can I?" ya tabe baki, "that is idan kina son zuwa fa" na bude motar nima na shiga ya ja motar. Hira muke dasu Ni'ima amma jifa-jifa idanuna su kan sauka akan Abbu dake tuki hankali kwance, wata dagawa da nayi idanuna suka sauka cikin kyawawan sparkling eyes din shi masu cike da kwarjini ta cikin madubin gaban motar, kamar wadda aka zarewa kuzari haka naji jikina yayi sanyi, gashi na kasa janye idanuna daga nashi sai shine ya janye nashin. Nayi ajiyar zuciya a hankali tare da sauke kaina kasa, ina kallon su Ni'ima suna kus-kus suna en da-re-re-ku a raina nayi fatan Allah yasa ba jirgina suka harbo ba. A gidan muka yi sallar magriba da ishai'i muka ci dambun couscous sannan muka musu sallama muka tafi. Dawowar tamu shiru, su Hafsy kadai su ke shan hirar su ni kam ina kan wayata ina buga game din piano tiles saboda bana son satar kallon Abbu da idanuna suke yi har ga Allah. Muna shiga falo ban tsaya a falo ba nayi hanyar dakina, Abbu ya tsaida ni ta hanyar kiran sunana, na juya a hankali. Cewa yayi "Plss dafa mun shayi mana" nace toh. Kayan hannuna kawai na ajiye a dakin na shiga kicin na dafa shayin da kayan kamshi a ciki, na matsa dan lemun tsami na zuba a cikin butar shayi na dora akan tray tare da kofi na kinkima na kai mishi. Yana zaune ya sa system dinshi a gaba da tulin takardu a gefen shi da alamu aiki zai yi, na ajiye akan coffee table dake gefenshi na durkusa a gaban shi, ya dago a hankali ya kalleni, "lafiya Nafeesah?" na sadda kaina kasa nace "Abbu don Allah kayi hakuri da abunda ya faru jiya, in shaa Allahu ba zan kara ba. Don Allah ka daina fushi dani!" shiru yayi yana kallona kafin ya nisa, "ba fushi nayi ba Nafeesah. Kawai ban ji dadi bane yadda kika biyo namijin da baki sani ba cikin dare, what if God Forbid, something bad happens to you Nafeesah? Bayan wannan kin duba shigar dake jikin ki kuwa? Haba Nafeesah!! Ke da nake ganinki da hankalinki da komi, how could you walk in front of many people with that dressing? And you were smiling and laughing in front of that guy, me yasa??" na sake yin kasa da kaina, ina mamakin ta yadda aka yi har Abbu ya ga irin shigar da nayi da kuma hirar da muka yi da Bilyamin, sai dai yanxu is not the right time to think about that, fata na daya kawai shine Abbu ya daina fushi dani. Last 20 to 23 hours has been like a hell to me, sukuni da walwala sun kaurace min saboda fushin mutumin nan daya; Abbu. Ji nake idan na kai gobe ba tare da na ga murmushin shi a gare ni ba zuciyata zata iya bugawa. Kaina na kara yin kasa dashi nace "kayi hakuri Abbu, ba zan kara ba" yace "dadi na dake Nafeesah kina da saurin admitting mistakes naki ki kuma yi repenting immediately, Allah yasa ki dore a haka" nayi kasa da kaina zuciyata ta fara washewa, da alamun ya huce. Yace "tashi ki je ki kwanta, ki daina damun kanki kuma ba fushi nake yi dake ba kin ji?" na dago a hankali na kalle shi kamar mai son karanta gaskiyar abinda yake fada, ya sakar min murmushin shi reassuringly. Naji wani irin sanyi ya mamaye min zuciyata, nima murmushin na sakar mishi sosai cike da farin ciki nace "Abbu nagode sosai, Goodnight!" na mike cike da kuzari da kwarin jiki na tafi, ya bini da kallo yana murmushi sai dana shiga daki sannan yayi ajiyar numfashi ya dauki shayin dana hada mishi ya fara kurba a hankali yana gyada kai cike da nuna gamsuwa. Ni kam ina shiga daki har sai dana yi dan tsalle cike da murna, na shiga bayi nayi brush na fito ina en wake wakena cike da farin ciki nayi shirin kwanciya barci, tsalle nayi na fada kan gadona, na mirgina daya gefen inda wayata take na bude, sai dana yi chatting na shiga accounts dina na twitter ne, instagram, facebook duk nayi posting ina cikin muudu mai dadi kafin na kashe wayar, na kashe wuta, na balle ma6allan gaban rigata na gaba guda uku naja bargo har wuyana, nayi addu'ar kwanciya barci na shafa na rufe idanuna, ba dadewa barci mai dadi ya yi awon gaba dani.





*♡Jeedderh♡*
[11/25, 20:56] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*20*


*Sakon taya murna zuwa ga marubuciya MAIMUNA SANI BELI na lashe gasar HIKAYATA da BBC ta hada na gajerun labarai. Allah ya kara miki kaifin basira*



"I heard that You are leaving the lab at the end of this week koh?" cewar Mrs Smith Head of Lab dinmu. Na gyada kaina nace "yes ma'am" tace "bayan kin gama Program din me zaki yi? Zaki wuce da HND ne?" nace "I'm not very sure ma, I'm thinking of filling D E form" tace "ina fata a nan BUK ne?" na girgiza kaina da sauri, "no ma'am, ABU Zaria ne" ta kalleni tana murmushi, "why?" na sadda kaina kasa kawai, me zan ce? Nace "maa nafi son Zaria ne sabida mun fi kusa dasu, bana son yin nesa da gida" ....ina so nayi nesa da Abbu da Iyalan sa Saboda ina jin tsoron abinda zan janyowa kaina, naso in kara da gaya mata haka sai dai nayi shiru. Ta gyada kai, tayi signing din takardar dana bata ta miko min nasa hannu biyu na amsa, tace "am wishing you all the best Nafeesah" nace "thanks ma'am" na fita.
Mun gama ayyukan mu na ranar muna zaune a cikin lab din muna hira ni da Ramlah, su Khaleesat tuni suka gama nasu IT din sati biyu da suka wuce. Nayi scrolling down ta cikin facebook account dina, anan na ci karo da status din da Muneer yayi mintuna biyar da suka wuce, "Soon.....!" na dan rausayar da kaina cike da alamun tambaya, me yake nufi? Na danna button din like. Ramlah ta kalle ni tana tabe baki, "ni har na rasa abinda zan fada miki game da Muneer wallahi. Ki kyale gayen nan haka nan kin ki kiji, yanxu har ta account din shi kike bi kina stalking din shi?" na yamutsa fuska, "stalking kuma Ramlah sai kace wata mara aikin yi? Kawai ina chatting ne na ci karo da status dinshi nayi liking, shine nayi stalking saboda Allah?" tace "ni dake da marar aikin yi duk daya nake ganin ku wallahi, wani mara aikin yi din ma ya fiki Nafeesah. Kin makalewa namiji daya kamar wata wadda bata da masoya, da girman ki da class din ki da komi. Allah ban taba ganin mutum marar fahimta ba irin ki ban sani ba ko duk sangarta ce ko kuwa? Amma......" "For Heaven's sake Ramlah!!" na katse ta a fusace har ina hadawa da buga hannuna akan bench, "this is my life kin gane? You have no right da zaki zauna kina lecturing dina akan abinda yake feeling dina ne kina ji? Baki son Muneer fine!! Ni da nake son shi sai ki bar ni inyi ta son nashi please!!" cike da mamaki ta kalleni, ta daga baki zata yi magana nayi saurin tashi na bar mata wajen. Yinin ranar haka nan muka karasa shi cikin kuncin rai su kan su en lab dinmu sun fahimci akwai abinda ke faruwa damu don basu saba ganin mu a haka ba, we are always cheerful koda yaushe muna tare muna hirar mu mai burgewa muna tsokanar juna amma ranar kowa tashi yake yi a cikin lab din, ina kallon Ramlah sosai ranta ya baci don har sai data share hawaye, jikina yayi sanyi sosai, ni kaina nasan Ramlah bata cancanci abinda na fada mata dazu ba, Raina ne ya 6aci sosai, so many annoying thoughts were running through my mind a lokacin, zan iya cewa Ramlah Sara ne tayi akan ga6a na sauke fushi da takaicin wasu a kanta. Karfe biyu tana cika na suri jakar hannuna na musu sallama na fita, a bakin kofar na tsaya, bayan kamar minti goma Ramlah ta fito. Da sauri na tari gabanta, "am sorry babe, I shouldn't have said what I said earlier.... M sorry, really" ta kauce daga gabana, "me zan ce miki Nafeesah? Ban cancanci in miki magana bama balle inyi intruding din personal life dinki ba, m sorry!" nasan cewa magana ce ta gaya min, naji kunya ta kama ni a lokacin, A taron mu da Ramlah I must have hurt her feelings da maganganun dana fada mata, bata cancance su ba ko kadan. Da sauri na kara tarar gabanta tare da riko hannunta, "look Ramlah! Wallahi I really didn't meant what I said da gaske nake, ni kaina abun yana damuna Ramlah. I'm trying, ina kokarin ganin cewa nayi yaki da son Muneer a cikin raina amma na kasa. No matter how hard I try, na kasa shi yasa nake jin haushin kaina nima, ina jin takaicin abun nima Ramlah har na fiki sai dai ya zan yi? Zuciya ta taki aminta da hakan ban san ya zanyi ba Ramlah...." zuciyata ta karye na kasa cigaba da maganar, idanuna suka yi jawur, lebena na ciza ina kokarin tsayar da hawayen dake kokarin xubo min. Ramlah ta dafa hannuna fuskarta cike da damuwa, "m sorry too Nafee. Bana jin dadin abinda yake yi miki ne ko kadan, it's hurting me. I love you babe, duk abinda zai bata ranki ina kin shi har cikin raina, na ga alamun baki son kyale shi bayan nasan cewa yana bata miki rai, I didn't know, ki yafe min" rungumeta nayi ina tapping bayanta, "I love you too Ramlah, m sorry too. I shouted at you" ta rungume ni itama, mun dan jima kafin muka saki juna, ta kalleni fuskarta da wani expression dana kasa ganewa, ta sake cewa "m sorry Nafeesah" nace "what for again? Idan maganar Muneer ce ta wuce don Allah mu daina yin ta haka nan" ta gyada kai. Muka samu waje muka zauna muna er hirar mu har Malam Bala yazo na mata sallama na tafi tana daga min hannu, taren mu da Ramlah kenan!.

Shirye-shiryen komawa gida nake babu kama hannun yaro, ganin abun nake yi kamar a mafarki. Kamar yau ne fa nake shirin tahowa Kano gashi har watanni shida sun wuce, na fada a cikin raina ina karewa akwatuna na kallo wadanda na gama shirya kayana a ciki. Hafsy ta leko dakin, gani na a tsaye ina karewa dakin kallo ta shigo ciki tare da maida kofar ta rufe, gefen gado ta samu ta zauna ta kalleni a marairaice, "yanxu Yaya Nafee gobe zaki tafi ba zaki kara mana ko kwana daya bane?" na zaro ido ina kallonta, "Lallai ma Pretty ashe baki tausayi na, ko don ke kina gaban Mom and Dad dinki ne shi yasa? Nima ina so in je in gansu saboda nayi kewar su sosai" ta turo baki, "to ba kina zuwa kina ganin su ba duk weekend?" nace "dat's a different magana ai, so nake in koma kusa dasu gabadaya kin gane?" tayi rau-rau da idanu sai ga hawaye shar-shar, da sauri na zauna a gefenta na fara lallashinta har tayi shiru, nace "haba mana da girman ki kike kuka? Kar ki damu zan dinga zuwa kuma ina muku weekend kinji?" da sauri ta dago kanta ta kalleni, "da gaske?" na gyada mata kai ina murmushi, sai dai daga can kasan zuciyata nasan cewa yaudarar ta kawai nake yi don ta warware, ina fata idan na saka kafa na bar gidan Abbu ya zama fita ce ta har abada, ko a mafarki bana fatan in sake komawa. Da biyu nake gaggawar in koma gaban su Daddy na, ina so inyi nisa da Abbu da gaggawa, he has started putting some effects on me wanda duk iya kokarina nason ganin na hana su affecting dina abun ya ci tura, shi yasa nake so in bar gidan as soon as possible kafin abubuwan su fi karfina. Hira na fara jan ta dashi ina tsokanar ta, nan da nan ta ware ta fara dariya, tare da ita muka cigaba da shirye shirye, na fidda kaya masu dama da wasu daga cikin kayan kwalliyata na ba Harira tayi ta godiya kuwa. Ana kiran magriba muka bar shirin muka yi sallah,
Showing 30001 words to 33000 words out of 122880 words