ta juyo tace “naji wani rumor yana yawo a cikin class dinmu, wai zaki yi aure?" na dan jijjiga mata kai ina murmushi, tace “amma gaskiya ban ji dadi da baki fada min ba" nace “sorry, auren ne kawai za a daura kin gane? Shi yasa ma ban wani yi shela ba saboda ina makaranta ma za a daura" ta matso da bakinta saitin kunnena cikin rada, “amma naji ana cewa wai wani lecturer ne anan zaki aura, da gaske ne??" na zaro ido cike da mamakin yadda aka yi zancen ya isa garesu, koda yake dama an ce zancen duniya baya buya. Nace mata “rumors ne kawai amma ba haka bane" tace “idan ma hakan ne meye na wa ko na mutane a ciki? Allah ya baku zaman lafiya mai daurewa" na mata murmushi ina kokarin boye dariyar data ciwo ni don nasan magana ce ta fada min, nace Ameen. Ta juya ta tafi abinta. Na duba agogon hannuna naga karfe sha daya ne da rabi lokacin, da sauri na dauki hanyar da zata kaini ofishin Abbu don nasan yana can yana jira na, ranar juma'ah ce ga masallaci ga kuma cinkoson ababen hawa. Na tura kofar office din na shiga fuskana dauke da murmushi, duk lokacin da zan ga Abbu sai in dinga jin wani irin doki da farin ciki a cikin raina kamar wadda ta shekara bata ganshi ba, alhalin duka duka jiya alhamis har karfe tara na dare muna tare dashi, ranar ta Jumma'ah da safe wayar shi ta tashe ni daga barci, muka gaisa ya maimaita min how eager he was to have me as his, farin cikin da yake ciki saboda samuna da yayi a cikin rayuwar shi. A gare shi wadannan kalmomin kamar wasu routine words ne da ya saba fada min a duk sanda muke tare, a gare ni kam they were far more than golden and diamond words, suna saka ni cikin tsananin farin ciki da jin dadi, suna hana duk wata damuwa da bacin rai samun matsuguni a cikin raina, they were my remedies. Ya juyo daga gaban book shelves din dake kusa da desk din computer dinshi, wani tattausan murmushi ya sakar min da suka sa naji alamun butterflies na yawo a cikina, sanye yake da wandon jeans blue da knit shirt mai kama da sweater, irin shigar da naga samarin zamanin nan nayi kenan a wannan lokacin, shima sai ta maida shi kamar wani saurayin bayan kyawun data mishi, Abbu yasan kan fashion kamar wani fashionista shi yasa ko wane irin kaya ya sanya suke haska shi. Ya maida littafin dake hannunshi cikin jerin littafan dake cikin shelves din, ya juyo gareni gaba daya yana murmushin nan nashi dai, kallona yake kamar wanda zai tsuke ni ta cikin idanuwanshi, it was so intense and disconcerting sai dana ajiye idanuwa kasa ina jin kamar kasa zata tsage in shige, yace “tun dazu nake jiran ki yanzu nake shirin biyawa ta library din in duba ki" nace “ban kula da cewa lokaci yaja bane, sorry!" ya dauki wata jaka mai kama da box dinnan akan tebur ya miko min, nasa hannu na amsa ina kallon shi cikin alamun tambaya, ya dan jingina jikinshi da teburin yace “akwai reception da aka hada mana ranar Sunday, kayan da zaki saka ne" na bude jakar na kalli kayan ciki, shadda ce bugaggiya ruwan kasa mai haske sai jaka, takalmi, da gyale su kuma dark brown kalar zaren da aka yi amfani dashi wajen yin surfani, na kara kallon shi nace “ranar Monday fa zamu fara exams dinmu" yace “ba zai taba karatunki ko jarabawar ki ba I promise, ni kaina ban san da zancen ba sai da suka riga suka shirya komi sannan suka sanar dani. I don't want to disappoint them, please help Nafeesah kinji?" yadda ya wani rausayar da kai yana kallona pleadingly, who m I to say no to him a yadda yayi dinnan taking my breath away?? Sai kawai na girgiza kai ina murmushi, nace “Allah ya kaimu ranar" yayi murmushi “Ameen Amour.... Mine" na sunke kai a cikin hijabina, ya wani kuta, “just wait till tomorrow, war haka kin zama tawa, mallakina ta har abada, wannan kunyar taki sai nasa kin neme ta kin rasa" ya saki murmushi mai sauti, “Allah ya kaimu goben nan dai, I really can't wait baby" na kara kanannade fuskata a hijabin, jin abin nake yi kamar a mafarki, mafarkin ma wanda ba zai zama da gaskiya ba, wai goben ne daurin Auren mu? Oh, zan zama matar Abbu, Abbu na wanda so da qaunar sa suka mamaye jini da jijiyoyin jikina, na kauda tunanin daga cikin raina bana so in fara fayyace matsayin da gobe take a gare ni don nasan ba zan gama da wuri ba. Ya dauki key din motar shi muka fita, na jira ya rufe office din kafin muka fara tafiya a hankali zuwa inda ya ajiye motar shi. Ya bude motar ya shiga ciki ya juyo ya kalleni, “sorry, bazan iya maidaki hostel ba saboda sai na biya na dauki su Abdullahi sannan mu wuce masallaci" nace “babu komi, a gaida su" ya gyada kai, “zan kira ki anjima" na maida mishi murfin motar na rufe, ya mata key ya tafi ina daga mishi hannu, sai dana ga fitar shi sannan na daga kafa da niyar tafiya. Kamar daga sama naga tsayuwar mutum a gabana, naja baya a dan tsorace har ina dafe kirji ina jan salati, Matar nan da muka hadu da ita a ofishin Abbu ranar nan ta bayyana a gabana, da alamu shigar rashin mutunci da na ganta da ita ranar a jininta take don kuwa lokacin ma irinta ce a jikinta, zan iya cewa ta ranar tafi ta waccan lokacin bayyana surar jiki ma. Hararata take yi tun karfinta da gwala-gwalan idanuwanta da suka sha uban eye shadow da girar kanti in ka ganta kamar wata doll. Nima na mayar mata da kwatankwacin hararar da take jifana dashi, “Malama lafiya zaki tare min hanya?" ta kama kugu tana wani jijjiga jiki, “ina so ne in fada miki ki rabu da Ibrahim" nayi fuskar alamun tambaya “me yasa?" ta dan daga murya, “saboda nawa ne! Na sha alwashin babu wadda ta isa ta aure shi muddin ina raye" nace “da alamu baki samu labarin cewa gobe ne daurin auren mu dashi ba, na tabbata da kin sani kam da ba zaki tare ni a hanya kina barking kamar tsohuwar karya ba" a girmame matar ta girme ni nesa ba kadan ba, sai dai ni a rayuwa na sau daya zaka zubda daraja da kimarka a idona, abin na matar yayi yawa, ko a lokacin da nayi shirmen son Muneer ban taba tunanin zan yi kwatankwacin abinda take yi yanzu ba, bin kan namiji yana wulakanta ni kamar karya amma in ki in hakura har ta Kai ni ga bibiyar wadda zai aura ina threatening dinta. Fuskar ta tayi looking so pale saboda maganar da nayi, “ni kika kira da karya? just wait, in har ina raye sai na mayar dake abin kwatance, sai na muzanta ki fiye da kare, I'm warning u, ki fita daga rayuwar Ibrahim kafin in mayar dake abin kwatance!!" na daga kafada, “I'm not stopping you from doing whatever you will do, kawai abinda nake so yanzu shine ki matsa ki bani hanya in wuce" ta hasala iya hasala, hannu ta daga kamar zata mare ni, kallonta nake yi kamar wata kayan kashi a yatsine, ita da kanta ta janye hannunta ta maida shi kasa, nayi murmushin mugunta nace “kece kike ta shirme kina bin namijin da yake kin ki, tunda yace baya yi let him be, ana so dole ne malama?" ta wani zare ido tare da buga tsawa “ke...!!" nayi saurin katseta kafin ma ta gama fadin abinda tayi niyar cewa ta hanyar zare ido nima, nace “malama kin ganni nan ban yi kama da matan da threats dinki zasu yi tasiri a kan su ba, kiyi duk abinda zaki yi wanda kike ikirarin mallaka ba zaki taba mallakar shi ba saboda ba don ke aka yi shi ba, a shawarce zan gaya miki ki fita daga rayuwar shi, Idan kuma kin ki ji sai dai kiyi mutuwar da kike ikirarin yi! Abbu ne kamar na aure shi na gama" naja tsaki tare da zagayawa ta gefenta ta wuce abuna ina muttering kalmomin dani kaina bansan me nake fada ba duk don in yi provoking dinta, na kuwa yi nasara. Ina bada baya naji sautin karan data saki cike da takaici, na kuwa saki murmushi kamar zan sheke da dariya.

Washegari da misalin karfe daya aka daura auren a babban masallacin juma'ah dake garin Malumfashi. Muna zaune a dakinmu Ni'imah ta kawo wata yarinya tana min kunshi wanda hakan umarnin Abbu ne, text dinshi ya shigo wayata. Na mika hannu na da nake jin shi kamar ba a jikina yake ba na dauki wayar, kai gabadaya ma sauran sassan jikina haka suke tunda garin ranar ya waye, ina ji Niimah da Firdausi suna ta hira amma na kasa saka musu baki duk da cewa rabin hirar a wajen tsokanata ne. Text din cewa yayi, “Alhamdulillah. Yanzun nan aka shafa fatiha, kin zamo tawa ta har abada. Ina taya junanmu murna da farin cikin mallakar junanmu, Allah ya bani ikon rike ki cikin amana da kulawa Nafeesah" sai kuma wani da yace, “Wannan ranar rana ce da ban taba tunanin zata Riske ni ba, ranar dana mallaki abinda ban taba kawowa raina zan mallake shi ba. Jina nake kamar wani sabon halitta saboda tsananin farin cikin da nake ciki wanda na kasa misalta shi, Nafeesah kina da gurbi mai matukar girma da fadi a cikin zuciyata, na roki Allah mai Girma akan ya bamu zaman lafiya mai dorewa. You've Completed My Puzzled and Shattered Life, I really Cherish You Nafeesah" naji hawaye sun cika min idanu, nayi saurin runtse idanun ina kokarin maida hawayen, Allah abin godiya da Girmamawa, wai ni ce yau na zama matar Abbu?? Naji ina narkewa kamar wata jelly akan kujerar da nake zaune, na tabbata da ace ina tsaye ne da sai na fadi. Rangadediyar gudar da Ni'imah ta rangada ce ta dawo dani cikin tunani na, guda take tun karfinta da waya a hannunta ta hau kiran waya tana bada albishir din an daura aure. Wayana ya shiga kara na daga, Daddy ne. Cikin rawar hannu na daga, “Uwata! Amarya!!" abinda na fara dokar kunnena kenan, na kasa magana sai kai dana jijjiga, yace “Nagode Allah da yasa naga wannan rana, ranar dana damka amanar ki a hannun wanda na tabbatar zai rike ki dari bisa dari, dama babu burin duk wani uba na kwarai daya wuce wannan. Yau dai kin zama matar Ibrahim, kin fita daga karkashin kulawar mu kin koma karkashin shi, yanzu shi zai yi sanadiyar ki zuwa gidan Aljannah wadda nasan babu haufi zaki sameta da yardar Allah uwata, Allah ya miki Albarka, Ya Albarkaci Rayuwar Auren ki, Allah ya baku zuriya Dayyiba!" muryar shi tayi kasa can kamar wanda yake so yayi kuka, ni kam kasa daurewa nayi kawai na fashe da kuka, gabadaya wani iri nake jina a tunanina idan nayi kukan zan samu sanyin zuciya. Ya shiga lallashina har na samu nayi shiru kafin ya min sallama. Yana kashe wayar kiran Mommy ya shigo, itama dai Addu'ah ta min kamar yadda Daddy yayi, zuciyar Mace mai rauni, sai tasa kuka, nima kukan nake yanzu sosai su Ni'imah na aikin bani hakuri, ina ji daga wayar Anty Uwani da muryar wasu mata suna ba Mommy hakuri, Anty Uwani cikin fada tace “sai kisa hankalinta ya tashi ai, gashi nan itama kin sata kuka, ina amfanin haka?" tace “kukan farin ciki ne" tace “ai godiyar Allah ya kamata kiyi ba wai kuka ba, shima Abban nata yanzu na baro shi a waje yana share kwallah Allah yasa ba ita ya kira yana kukan ba.... Wannan ai sai ku sanyayar mata da gwiwa...." daga haka dai suka kashe wayar. A hankali nima nawa kukan ya fara yin kasa har ya dawo shessheka kafin nayi shiru ina ajiyar rai. A ranar dai har ba zan iya lissafa iyaka mutanen da suka kira ni suna taya ni murnar yin aure ba, tun daga kan abokaina da yan uwa har wasu daga cikin abokan Mom. Da yamma sai ga Ramlah ta dira a Kanon kamar daga sama, muka yi tsalle muka rungume juna ni da ita muna ihun murna, watanni biyar ciff tunda muka rabu da ita bamu sake haduwa face to face ba sai dai a Video call. Muka zube akan gado muna maida numfashi daya bayan daya, kallona take tun daga sama har kasa ta kyalkyale da dariya, “kaga Amarya a gidan Ibrahim Galadanchi, kin ga wani kyau da kika yi kuwa??" na kai mata duka ina dariya, “meye haka zuwa babu sanarwa?" tace “surprise, dazu na dawo har mun yi hutu abinmu" nace “kun huta ku kam" nan muka shiga hirar yaushe gamo, tana nan tare dani har aka kira sallar magriba, ganinta ne yasa na warware har na samu naci abinci. Nan dai ta min sallama ta tafi akan cewa zata dawo Washegari, bayan na rakata zuwa bakin kofar hostel din na koma daki nayi sallar isha'i, bayan na gama na zauna nayi ta jero addu'o'i game da neman albarkar Allah da zaman lafiya a cikin sabuwar rayuwar da nake tunkara a cikin rayuwata. Abbu ya kira ni yace yana jirana a parking lot inda muka saba tsayawa, na tsinci kaina cikin faduwar gaba da sanyin jiki, cikin sanyin jikin na tashi na gyara zaman hijabin jikina na sauka kasa. Jingine yake da motar shi yana danna wayar shi, sanye yake cikin shadda ruwan Makuba yau kam har da hula a kanshi, akwai wadataccen haske a wajen hakan ne ya bani damar ganin fuskar shi sosai kamar cikin rana. Tunda na hango shi naji kafafuna sun fara hardewa, ban taba tsintar kaina cikin fargaba da tsoron fuskantar Abbu ba tunda nake a rayuwata sai ranar, da kyar na iya karasawa gaban shi ina maida numfashi kamar wadda ta sha gudu, babu abinda yayi motsi a jikinshi sai idanun shi da suke kare min kallo tun daga sama har kasa, kafafuna ba zasu taba iya daukana a haka ba sai nima na jingina da jikin motar ina kallon zara-zaran yatsun kafar shi da suka fito ta cikin kyakkyawan bakin budadden takalmin kafar shi yana ta sheki.....
~Yau dai Allah yayi Dare Gari ya waye An Daura Auren Nafeesah da Abbu, Woah!
~Me zaku ce game da Shafin yau??
~Lots Of Love and Hearts
#TeamAbbu
#OneLove
#AnaTare...





*♡Jeedderh♡*
[1/1, 18:03] Hauwa-Jedderh💕: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*

*®•°Fikrah Writers Association°•*🖋
_In Dedication to Aunty Zee_
_Tukuici zuwa ga Marubuciya SADNAF_
_Godiya Mara Adadi Masoya, Makaranta Littafin Ni Da Abokin Babana, yawan ku ya kai adadin da ba zan ma fara jero sunayenku ba, just know that where ever you are Jedderh really appreciate your love and kindness, #OneLove_


*47*


A hankali ya sauke ajiyar zuciya wadda take nuna tsananin farin cikin da yake ciki, “Hii there My Queen, My Happiness, My Amour, My Bride! Sunayen naki suna da yawa fa, amma kullum zan dinga kiran ki da guda daya wanda nasan sai mun dauki shekara basu kare ba, how are you?" kunya ta kama ni na sadda kaina kasa, yau ko sallama ban iya nayi ba balle in gaida shi, haka kawai naji wani nauyi da matsananciyar kunyar shi sun dabibaye ni.
A hankali kuma kamar wadda aka tursasa na bude baki nace “Ina yini Abbu?!" ni kaina sai da nayi mamakin muryata, it was very low kamar wadda take rada, ban yi tunanin yaji abinda nace ba sai da naji yaja wani sharp breath har yana hadawa da lumshe ido, “Masha Allah!" ya furta a hankali yana kallona da lumsassun idanuwan shi, ya Allah!! Da ace yasan yadda kallon yayi affecting dina da yayi gaggawar dauke idanunshi daga kaina saboda nasan ba zai so amaryar shi ta zube kasa kila hakan yayi sanadiyar karyewar kafarta ba, sai ya ci gaba da kallona kawai. Na samu nace “Ya hanya?" duk don in katse kallon da yake jifa na dashi da kuma hirar da zukatanmu suke yi, yace “Alhamdulillah, akwai gajiya kam amma tunda mun iso lafiya ai shikenan, besides ni tunda na ganki ma naji ni kamar an dauke min duk gajiyar dake tattare dani" nayi kasa da kaina, yace “Dad dinki ya bada sakon gaisuwa a kawo miki, ya damka min amanar ki har sai da sashen karbar sakonni a kwalwata ya cika, he even threatens me, heol!!" ya wani yi rolling idanu tare da dan chuckling, na kalle shi ya haske ni da murmushin nan nashi da yake sa ni yin abin da ban shirya ba, ba shiri na sakar mishi murmushin. Yayi cocking kanshi gefe guda, “ko ke fa! Keep smiling like that baby, yau fa rana ce ta musamman a gare mu bai kamata ace murmushi ya kau daga kan fuskar ki ba.... Hmm, how I wish gidana za a kaiki yau din nan, da sai na nuna miki kaunar da babu namijin daya taba nunawa wata ‘ya Mace a duniyar nan, na saka ki a cikin farin cikin da baki taba tsintar kanki a
Showing 81001 words to 84000 words out of 122880 words