Anty Shafa ce ta shirya ni, sai a lokacin nasan tazo ashe kwananta biyu a Naija. Ta shirya ni cikin wasu riga da zani da wani farin yadi mai holes a jikin shi, sai aka min nadi da blue din tie, blue din takalmi high heel, blue purse, blue mayafi karami data dora shi akan kafadata. Fadar irin kyawun da nayi ma bata bakine. Haka dai aka gabatar da bikin cikin salama komi ya tafi yadda aka tsara, anyi ciye-ciyen abinci, snacks da lemu kamar ba gobe, bayan nan su Ramlah suka fita suka kwashi rawa har da su Anty Shafa, koda aka nemi da in fita filin rawa ki nayi, na kara hakimcewa akan tuntu inda aka yi shirin kayan gargajiya kamar irin bikin nan na gidajen sarautun da, sai da Hajiya Amina kawar Mommy na tazo ta fiddo ni sannan na tashi naje filin nayi tsaye, dama can ni ba gwanar rawa bace balle kuma a gaban manyan mutane irin wannan kuma ace bikina ne? Taya ma zan iya rawa?? Nan mutane suka fara sauke ruwan naira a kaina sababbi kamar wasu takardu, ba shiri DJ ya maida sautin wakar dake tashi zuwa Ruwan Kudi, taro dai yayi lafiya lau Alhamdulillah, da yammaci likis aka watse taron.
Anty Shafa ta dauke mu a motar ta zuwa gidanmu, ai sai a lokacin take fada min cewa wai washegari za a kaini Kano. Na zuba mata idanu na a sanyaye cikin sanyin jiki kamar wadda aka zare mata laka, har muka isa gidanmu ban iya cewa komi ba. An sake fente gidan ya dawo kamar sabon gini, a farfajiyar gidan canopies ne an shirya su kashi-kashi ga kuma kujeru irin wadanda ake yi na tyres a shirye, hasken bulbs jajaye ya kawata wajen sosai da sosai, ina ji Ramlah tana tambayar Anty Shafa abinda za ayi tace wai shi kuma Dinner ce kawai su Mom da Dad suka hada min, a raina na girgiza kai ina jinjina bidi'a irin ta su Mom. Yan uwa suka wa motar da muke caa kamar kiyashi da kyar muka fito daga cikin motar, kai tsaye dakin Mom dina aka wuce dani, mutanen dake ciki basu wuce biyar ba duk abokanta ne sai Nene matar kawu Hassan da kuma Anty Asma'u matar Kawu Ali.
Mommy ta taso ta rungume ni, ina ji na a jikinta kawai naji na saki kuka, ta fara tapping bayana alamun lallashi ba tare da tayi magana ba nasan tana tsoron tayi magana ne kuka ya kufce mata. Anty Asma'u ce ta janye ni daga jikin Mom din ta kaini bandaki, nan ta cire min kwalliyar da aka min ta hada min ruwan wanka ta fita daga dakin, jiki a sanyaye na shiga cikin bath tub din nayi wankan tare da daura alwala na fita. Lokacin dakin daga Anty Shafa sai Mom da Anty Asma'u, suka umarce ni da inyi sallah, nayi. Ina gamawa suka fara caccaba min kwalliya, ana cikin yi aka kira Isha suka saki muka yi, Anty Shafa ta bar Anty Asma'u tana min kwalliyar ta koma wajen Mommy itama ta fara mata. Doguwar rigar shadda suka dauko mana maroon ta sha aiki tun daga sama har kasa, Mommy ma irin kayana ta saka sun mata kyau sosai ta fito kamar wata karamar yarinya. Muka jera muka fita falo da ita muna ta sheki, babu kowa a cikin falon sai Daddyna, ya sha babbar riga ta shadda irin ta jikinmu har ma da surfanin jikinmu, yana ganin fitowar mu ya tashi tsaye, hada mu yayi mu duka da Mommy ya rungume mu, na rirrike shi zan fara sana'ar hawaye yayi saurin daga fuskana yana girgiza min kai cikin murmushi, “umh umh Uwata, banda kuka ko so kike ki bata min kwalliyar ki?" na girgiza mishi kai, yace “good girl, muje koh?" suka saka ni a tsakiya shi da Mommy kowa ya rike hannuna muka fita. Wajen ya kara kawatuwa saboda dare da yayi, mutane duk suka mike tsaye suna tafi lokacin da muke wucewa ta gefen tables din da suke zaune har muka karasa wajen da aka tanadar mana muka zauna sannan suma suka zauna.
Anty Uwani ce ta bude taron da addu'ah, bayan ta gama ne kuma Daddy da Mommy suka fita suka wa baki barka da zuwa, daga nan suka fara bayanin farin cikin da suke ciki na aurar da kwallin kwal din diyarsu, Daddy yace yanzu duk wasu burikan shi sun cika sai fatan gamawa da Duniya lafiya Mommy kuma tace buri daya ya rage mata shine taga Diya na jikoki a wajenta, aka yi dariya ni kuma na sadda kaina kasa. Bayan sun gama bayanan su suka dawo suka zauna, aka ci farfesun kifi sardines, chips, da lemuka, aka sake rufe taro da addu'ah sannan aka watse. Bamu tsaya yin komi ba kowa ya nemi makwanci.
Washegari Daddy ya ja mu sallahr Asubah a dakin shi, bayan mun gama sallar munyi karatu kamar yadda aka saba, Daddy ya fara min nasiha Mommy ma ta dora da nata, Daddy ya rungume ni yana lallashina daga kukan da nake yi babu kakkautawa, ya shiga lallashina har nayi shiru, yace “Allah ya miki Albarka Uwata, hakika ke ‘ya ce ta gari wadda ta zama sanyin idaniyar iyayenta, in Allah ya yarda sai kin samu wadanda zasu miki fiye da abinda kika mana, Allah ya albarkace ki da rayuwar aurenki gabadaya. Na hore ki da Biyayya ga mijin auren ki, ki bishi sau da kafa, ki mishi biyayya tsakanin ki da Allah, idan kika yi haka in shaa Allah ba zaki tabe ba Uwata!" kuka muke ni da Mommy, shi kan shi daddy sai daya share kwalla, bayan mun yi shiru muka koma dakin Mommy muka kwanta barci bamu tashi ba sai bayan karfe goma, break fast ya kammala amma na kasa cin abincinnan saboda tsabar fargabar rabuwa da iyayena, dama haka kowace ‘ya mace take ji ne?? Kwance nake shame-shame akan gado tunda na tashi daga kan dinning, yatsun hannuna ma da kyar nake iya daga su, Ramlah ce tazo ta dame ni da hira har na dan warware. Karfe daya motocin daukar amarya daga Kano sun dira, gabana ya shiga dukan uku-uku, kafin kace me! Na fara hawaye. Anty Shafa ta harare ni tace “wai ke tsabar iskanci ne ya miki yawa zaki saka mutane a gaba kina musu kuka, wa ya zage ki?" sai na kara kware mata baki, ta kama baki tace “to?! Ikon Allah, ni kam ba zan iya dake ba..." ta fita jim kadan ta dawo da Anty Uwani, da wuta-wuta Anty Uwani ta tura ni bandaki nayi wanka da wasu sabulai masu kyau da kamshi, ina fitowa nayi sallah. Anty Shafa ta min sharp kwalliya na fita muka gaisa da bakin da suka zo daukar amarya ciki har da Anty Ameenah, muna gaisawa na koma daki. Dama already duk wasu kayana an riga an kaisu Kano kwanaki biyu da suka wuce, bayan su Anty Ameenah sun huta sun ci abinci, nan aka fara min kwalliya data daukemu kyakkyawar awa guda, ana gamawa muka yi sallar La'asar aka bani riga da zani na atamfa super ruwan ganye nasa, Anty Shafa ta dora min gyale akaina suka kama ni har dakin Daddy muka yi sallama ta karshe, ya jaddada min yin biyayya, juriya da hakuri a cikin rayuwar aurena, ana tashi dani na yi rau-rau da idanu, Anty Uwani tace “wallahi kika kuskura hawaye ya zuba a fuskar ki sai na mazge ki!" Daddy yace “a'ah Uwani, bi ta a hankali mana" ta kamo hannuwana ina turjewa ta jani tana mitar Daddy ya bata ni da yawa gashi za a kaini gidan aure, mutane suka biyo mu duu har gaban farar rantsamemiyar Land Cruiser ta daukar amarya, Daddy da kanshi ya bude motar ya kamo hannuna ya saka ni a ciki, zuwa lokacin kam kuka nake yi sosai har da ihu, da kyar suka tura ni aka rufe motar, Anty Shafa da Ramlah suka shigo aka rufe motar, sauran masu rakiya da su Anty Ameenah suka shiga sauran motocin. Ina kallon su Mommy a tsaye, Mommy ta kwantar da kanta a kafadar Daddy tana kuka, motar tana fita daga gidanmu na yadda kaina a kafadar Anty Shafa na kara sakin wani kukan. Lalle gaskiyar bahaushe da yace ‘Aure yakin mata!' in ba aure ba meye zai raba ni da masoyan Ruhina bayan mutuwa??
~Hii dearies, sorry for the short Chappy da kuma rashin posting jiya, I was engaged in soooooo many commitments shi yasa amma in Allah ya yarda ku tara gobe, I promise a very long chapter for u my Dears.
#TeamAbnaf
#OneLove
#AnaTare





*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*


*©°•Jeedderh Lawals•°*

*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋

This page goes to you, Jedderhs World Group Members, Lobi you dearies sosai da sosai.....
Shafin yau Tukuici ne a gare ki Mayrowh, thank you and lobi you too.....



*50*


Munyi nisa sosai kafin kukan da nake yi ya dauke, Anty Shafa ta miko min handkerchief na share fuska ta dashi, ta bude Jakarta ta ciro kayan kwalliya ta juyo da fuskata ta gyara min kwalliyar dana bata, na juya kaina ga window din motar na fuskanci waje zuciyata cike fal da tunanika iri-iri. Karfe shida muna cikin Kano, kai tsaye unguwar Galadanchi aka wuce damu gidan su Abbu. Can muka tarda mutane na jiran isowar mu, dakin Hajiya Siyama Mahaifiyar su Abbu surika a wajena muka sauka, aka damka musu Amana ita da Dattijan da muka samu a dakin nata, daga nan kuma aka kaini dakin Hajiya Fati nan ma dai gaisuwa da bada amanar ne, bayan an gama aka dauke ni zuwa wajen mahaifin su, ya mun nasiha sosai mai shiga jiki tare da addu'o'i, ya bada abin Sallah, Carbi da Turare aka bani a matsayin tsarabar gidan aure daga nan muka koma cikin mota sai gidan Aurena a Sharada phase 2.
Gida ne flat mai kyau, dakuna uku manya duk an yi jere, akwai toilets a cikin kowane daki, kicin, sai toilet daya a cikin falo kila na baki ne.
Su Ni'imah sune en jagora har zuwa dakina, sai da muka shiga daki Anty Ameenah ta yaye min gyalen kaina duk da haka kin daga kaina in kallesu nayi, Su Anty Shafa daya dakin aka kaisu ni kuma su Ramlah suka zauna a tare dani, nan dai muka dauro alwala muka yi sallah, kasancewar lokacin Sallar Isha'i yayi yasa muka yi har Isha'i din. Muna gamawa aka dire mana plates din abinci, Macaroni jollop da lemuka, tsakanina da Allah cikina a cike yake shi yasa na dinga tsakurar abincin, Sadiya data fara nauyi haihuwa ko yau ko gobe duk da ita aka yi jigilar gaisuwa da ita ko nauyin cikinta bata ji, tace “Amaryar Babban Yaya ya dai baki cin abinci ko dai kazar amarcin kike jira?" na harareta kasa-kasa ganin gasu Anty Ameenah a gefenmu suna zaune, Ni'imah tace “ta fa riga da taci kazar amarcinta tun ranar da aka daura aure, muma ba har muka ci saura ba?" na kuwa kai mata mintsini a cinya tayi tsalle gefe guda tana sosa wajen, Ramlah tace “ku kyale yarinyar nan, tun dazu take nuku-nuku kamar ba ita bace tace tana son auren, lokacin da yunwa zata taso mutum ya nemi abinci kuna ihu?" duk suka sa ihun, “Gida!!" tace “kun gani?!" ni kam sai na tashi na bar musu wajen kawai, na koma kan bencin dake gefen gado na zauna ina satar kallon kayan dakin, komi na ciki silver ne da black, gadon irin kananun Italian beds dinnan ne medium king size sai wardrobe data kusa cinye bangon dakin na gefen dama, dressing mirror, end of bed table, rug carpet, labulaye silver, sai sauran kananun tarkace da ba za a rasa ba amma kayan sunyi kyawu sosai, babu wata hayaniya irin ta kayan dakin zamanin nan.
Su Anty Ameenah suka mana sai da safe suka tafi suka barmu da su Anty Shafa da Ramlah, er hirarraki muka yi kafin Anty Shafa tace yakamata mu kwanta haka, ni na fara shiga toilet nan ma kayan ciki har ba a magana, katoton Jacuzzi tub, sinks, akan canters kuma mayuka ne tun daga na gyaran fata har na gashi ne da turaruka abin ba a cewa komi, na tari ruwan dumi na dan yi relaxing saboda warware gajiya kafin na dauro babban towel na fito na danyi en shafe-shafe na fita, Ramlah ta shiga.
Wardrobe na bude da niyar duba kayan barci, baki na bude a tsorace ina kallon cikin wardrobe din. Layi daya atamfofi ne wasu ma ko dinga su ba ayi ba, sai daya na laces, daya nasu jallabiya ne da dai dogayen riguna, daya nasu materials, saitin kayan barci kuwa sai da suka kwashe biyu, na zaro riga daya na daga ta sama, it looks more like a lingerie yawancin kayan barcin duk ire-iren su ne.
Na juya da rigar a hannuna ina nunawa Anty Shafa, “meye haka Anty?" tace “kayan barci mana" na kara kallon kayan, “you didn't mean... Ni zan saka su koh?" ta harareni, cikin gatse tace “a'ah ni zan sa..., ko kuma shi mijin naki!" na gumtse dariyata nace “amma Allah Anty kayan suna nuna jiki da yawa fa" tace “yi mun shiru malama, don suna nuna jiki sai me? Ina ce dai hakan ba Zunubi bane? Idan kin san ta yadda aka yi kayan nan suka zo nan ba zaki zauna kina ce mun wai suna nuna jiki ba, I specially went to Kamfanin da suke sarrafasu na bada oda, don haka tun kafin raina ya baci ki saka kayan nan, besides kayan nan na arziki ne idan kika yi comparing dinsu da wasu kayan, koda yake ke da kanki zaki san amfanin su kizo kina nema na" sai na gumtse baki na juya na maida rigar na fara laluben kayan sa wa, da kyar na lalubo riga da wando suma dai sai a hankali, wandon 3q, rigar mai hannun vest gasu silk, lokacin Ramlah ta fito nan muka bi lafiyar gado. Anty Shafa kuma ta ajiye katifa a tsakar dakin muka yi light off muka kwanta, kamar jira yake, sakon Abbu ya shigo.

*“Sleep??"* nayi gaggawar tura mishi da, *“about to.... How was your day?"* ya turo *“dama nasan ba zaki iya barci ba baby na, tun yau fa baki ji murya ta ba balle kiga text dina, nima ina kewar ki baby na nasan da kyar barci ya dauke ni yau, amma kar ki damu, na yau ne kawai..., daga gobe babu wanda zai sake shiga tsakaninmu da yardar Allah"* lokacin dana karanta sai da er dariya ta kufce min, kai Abbu is full of self confidence. Na tura mishi *“says wanda yake da mata., plus ni fa barcin ne kawai bai zo ba amma babu wanda nake kewa sai Mommy da Daddy na!"* na tura ina dariyar tsokana, nasan kila har gari ya waye yau muna musayar sakonni ne, sai kuma har barci ya dauke ni bai dawo da reply ba.
Sai da muka tashi sallar Asabar naga amsar daya maido mintuna kadan da fara barci na, *“zaki ce haka ai tunda har yanzu baki zo hannu ba, gobe war haka ki maimaita abinda kika fada yanzu please...." nayi murmushi kawai na maida wayar kasan filo na fada toilet. Muna gama Sallah muka koma wani barcin, sai karfe tara na safe muka tashi. Muka yi wanka muka kimtsa, an kawo mana abinci daga gidan su Abbu muka fita parlour muka karya. Falon madaidaici ne wanda ya dauki wasu rantsattsun beige couches guda biyu an jera su daya ta kalli gabas daya kuma ta kalli arewa, sai wasu Everette chairs navy blue guda biyu suna fuskantar couch daya, a tsakiya kuma an saka babban teburin gilashi kasan shi wasu woods ne suka tokare shi, a sama kuma an dora flower base mai kyau, sai lamp mai kama da bishiya, kasan parlor hardwood flooring aka yi, kai komi dai na falon ya fita very unique, muka hau kan dinning mai cin kujeru takwas muka karya.
Dakina muka koma Anty Shafa sai cafta take sauke min tana karawa duk da wasu abubuwan duk tuni ne take yi mun. Karfe daya munyi sallar Azzuhur sai ga Abbu shi da abokan shi biyu, nayi sauri na dauko hijabi na dora akan kayana, falo muka fita muka gaisa dasu, ban yi gigin daga ido na kalli kowa ba. Ramlah ce tayi jigilar entertaining dinsu, ni kam suna fara cin abubuwan data kai musu nayi wuf na fada daki. Gefen gado na samu na zauna, ban jima ba sai ga Abbu shima ya shigo. Kai tsaye
Showing 90001 words to 93000 words out of 122880 words