GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*
_MATAR SAYYADEE_
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*40*
Taɓe baki Hajiya tayi, don gaba ɗaya Sarah ta gama ficewa daga zuciyarta. "Allah ya kiyaye hanya! Yaushe zaka wuce?" Ɗan shuru yayi, sai kuma can yace, "Hajiya, idan so samu ne in tafi tun yau!" Ya ƙarisa maganar a raunane. Wannan karon ma taɓe bakin tayi tare da faɗin, "Allah ya jiyaye hanya, ka dai tabbatar kana tafiya kana sauraran karatun Alkur'ani, sannan kana isa ka kuma tabbatarwa da Li'ilafi a bakinka, atoh! Na dai faɗa maka." Murmushi ya Abdallah da ya Abdul-Hakeem suka yi a lokaci guda, yayin da Khalil yace, "In Sha Allah Hajiya." Yana gama faɗin haka ya miƙe jikinsa har rawa yake yi ya fice, ya ƙosa yaje yaga halin da matarsa take ciki. "Uhm, dubi yanda jikinsa ke rawa akan mace kamar wawa, Allah dai ya kyauta!" Faɗin Hajiya tana wani rausayar da kai. Wannan karon ya Barrister ne yayi dariyar yana mai sunkuyar da kai don yanda Hajiyar ta rausayar da kai ba ƙaramin dariya ta bashi ba. Khalil kuwa wuta-wuta ya tafi ya ɗauko ɗayan ATMcard ɗinsa da kuma 200k da yake dashi cash a ƙasa sannan ya canza kaya sharp-sharp ya fito ya ɗago ɗakin Hajiya, kallo ɗaya Hajiya tayi masa tace, "Uhm" tare da kawar da kai. Har gabanta ya isa tare da faɗin, "Hajiya kiyi addu'a zan tafi." "Allah ya tsare ya kiyaye hanya." Shine abunda tace kanta a juye. Miƙewa yayi tare da kallon yayyin nasa tare da faɗin, "Zan wuce, a saka ni cikin addu'a yaya." Gaba ɗaya suka haɗa baki wajen faɗin, "Allah ya kiyaye hanya Ibrahim." Ya Abdallah ya ƙara da faɗin, "A gaida iyayen matar naka, kar kuma ka manta ka tafi hannu rabbana, kayi masu tsaraba a hanya." Da "In Sha Allah." Khalil ya amsa. "Allah ya kiyaye hanya yaya Khalif, a gaida Aunty Sarah da ƴan biyu, a faɗa masu nayi kewarsu." Faɗin Laure. "Ameen Laure, in Sha Allah zasu ji." "Ƙarshen kewa, je kwaso kayanki ki bishi ku tafi." Faɗin Hajiya tana mai zabgawa Laure harara. Shi kansa Khalil ɗin sai da ya murmusa kamun ya fice daga ɗakin. Kai tsaye wajen mota ya nufa tare da shiga ya tada ya bar gidan ya ɗau hanya. A can Nassarawa kuwa, Nnanne ce a ɗaki daga ita sai Sarah wacce ke zaune a wajen ƙafafunta. "Takwarata, zan baki labarin wanene mahaifinki da kuma mahaifiyarki. Kin ganni nan, bani ce na haifi ubanki ba, amma yanda nake sonsa da ƙaunarsa, ko mahaifiyarsa sai da ta nuna min ta jikinta ya hudo yazo duniya. Ni da mahaifiyar Nuhu, uwarmu ɗaya, uban kowa da dashi. Don bayan mutuwar mahaifin ya Rahmatu, shine Mahaifiyarmu ta auri babana. Ita tasha mama ta sakarmun, gaba da bayan mahaifiyarmu, Nindire ne, kuma anan cikin wamba aka haifi mamanmu, gadon gidanmu shine ilimi, don sunan gidanmu, gidan malamai. Ubansu Nuhu, da Mahaifiyarmu ni da mahaifiyar Nuhu, uwa ɗaya uba ɗaya suka haifesu, kin ga kenan auren zumunci akai wa mahaifiyar Nuhu da mahaifinsa. Mahaifiyarsu Nuhu, kakarki kenan, macece mai haƙurin gaske, da wuya mutun yaga ɓacin ranta, ko shi mahaifinsu Nuhun, yace har ta koma ga Allah bai taɓa ganin ɓacin ranta ba, ga biyayyar aure! Bayan rasuwarsa ne mahaifinmu ya bashi ni, don ya Rahmatu tana haihuwarsu Nuhu da Nura jini ya ɓalle ta amsa kiran Ubangiji. Bata taɓa haihuwar ɗa ɗaya ba, baban ku Lukman da Kamal sune ƴaƴanta na fari, bayan ta yaye su ne ta haifi su mahaifinki, ina tunanin ita kika gado. A wannan lokacin ni kuma mijina zaman mu ya ƙare, haihuwar mu ɗaya dashi, Ruƙayyatu, gaba ɗaya dai zaman namu dashi na shekara ɗaya ne auren ya mutu, kuma ban kuma wani auren ba, ashe rabon Alyasa'a ne. Bayan arba'in ɗin yayata Rahmatu, aka ɗaura aure na da Alyasa'a, ni na cigaba da shayar dasu ƴan biyu tare da rainon su Lukman da Kamal. Yarane masu matuƙar tarbiyya, tun sun Lukman nada shekaru goma sha ɗaya suka haddace Alkur'ani, don yaro ma ba'a saka shi boko sai ya haɗa izu goma. Na haifi ƴaƴa hudu a nan gidan, Raliya, Zainabu, Khadijah da Usman. Duk a cikin ƴaƴana nafi ƙaunar Nuhu, don yarone mai sanyin hali da biyayya, duk da sauran ma suna da biyayya, amma Nuhu daban ne, abunda yasa ake saurin bambamce su kenan da tagwaininsa, don Nura sak nine, yana da zafin rai da kuma riƙo. Lokacin da suka kammala secondary School, basu cigaba da makarantar gaba ba, sai kowanne ya cigaba da sana'ar da yake yi, Lukman harkar noma yake yi, Kamal kuma sana'ar fata, Nura kuma harkan kayan mata yake yi, wanda kuke kira konsimetis (Cosmetics), shi kuma Nuhu sai ya zaɓi harkar tafiye-tafiye a mota yana tuƙa irin manyan motocin nan. Duk abunda nace wa Nuhu ina so, sai dai idan bai da shi, sannan idan nace masa bani son abu kaza, har abada ya bar abun nan duk son da yake masa. A can ƙasan layin nan, idan kika yi kwana daga hannu dama, layine na wasu mutane wanda basa addinin musulunci, ɓangare ɗaya, addinin kakanni suke yi, bautar gumaka (Traditional religion), ɗayan ɓangaren kuma, kiristoci ne, (Christianity religion), sam waɗannan addinai biyu, basa shiri da juna, kuma basa ga maciji. Pasto Emmanuelle, wasu kuma suna kiranta Debora, itace mahaifiyar mahaifiyarki, ita ta kasance cikakkiyar kirista ta Catholic, irin masu zafin nan ne su, kamun zamanta pasto, ko kuma ince maki kamun ta girma izuwa pasto, sun ƙulla soyayya da mahaifin Debora (Mahaifiyarki), kuma shi mahaifin Debora yana bin addinin kakanni ne wanda kiristoci basu yarda dashi ba, kuma suna ganin addinin da suke yi bana gaskiya bane, sannan dangin Samuel (Akanchewa Uchendo), sun ƙasance ƙasurgumamun matsafa ne na bugawa a jarida. An kai ruwa rana sosai kamun dangin biyun nan suka amince da aurensu wanda sai da Samuel yayi mata ƙaryar ya koma addininta na kiristanci sannan akai auren wanda kuma a zahirin gaskiya bai koma addininta ba, yana nan yana tsafinsa. Bayan haifuwar Elizabeth, mahaifiyarki Kenan, sai a lokacin Debora ta gano cewar Samuel bai bar addininsa ba, yana nan kuma yana tsafinsa, dalilin haka ta kaisa kotu suka rabu tare da goyon bayan iyayenta sannan kuma ta kwace Elizabeth ta mayar da ita hannunta. Su kuma iyayen Samuel sun ji haushin haka sosai, sai suka yi wani mummunar tsafin da yayi sanadin rayuwar iyayen Debora ta hanyar dogon jinya da kuma aman jini. Bayan mutuwarsu, hakan ya ƙara tsananta wutar gaban dake tsakanin two families ɗin sosai har ta kai ga sai da hukuma ta shiga tsakanin su. Samuel baya zuwa ganin Elizabeth, haka itama Elizabeth bata zuwa ganin Samuel kamar ba mahaifinta ba, don mahaifiyarta ta nuna mata cewar ai dangin Samuel gaba ɗaya ƴan wuta ne. Duk lokacin da Nuhu yazo Nassarawa, yana yawan zuwa can unguwarsu Elizabeth kasancewar yana da abokin da suke aikin mota tare, duk da Chidebere ba musulmi bane, amma yarone yaron kirki don na jima ina masa fatan hasken musulunci. To a wannan unguwar Nuhu yaga ƙawar Elizabeth (Lami) kuma yaji yana sonta. A yanda labari yazo min, ita Elizabeth ɗin ya samu da zancen kasancewarta babbar ƙawarta domin ta shawo masa kan ita Merry ɗin. Amma bayan wasu kwanaki Kwatsam, sai Nuhu yazo ya same ni da zancen yana son wata yarinyar ƴar unguwar wai ita Elizabeth, koda yazo min da wannan zancen, koren kare nayi masa tare da faɗa masa in har nice mahaifiyarsa, to ban yarda ya ƙara kallon unguwar ba balle ma ya ƙara zuwa wajen yarinyar. Tun daga wannan rana kuwa, ban kuma jin makamancin labarin ba, sai na ɗauka ya watsar da zancen. Amme me, bayan wasu watanni, sai ga motocin ƴan sanda har biyu a ƙofar gidan nan, lokacin mahaifinsu Nuhu na fama da cutar ciwon ciki na ajali, sai ga sallama wai ana neman mu a police station, duk da Alyasa'a bai jin daɗi haka ya kwashi jiki shi dasu Lukman da shi kansa Nuhun suka tafi caji ofis, acan caji ofis sai da akai masu tijara sannan aka rubuta yarjejeniya akan babu Nuhu babu kula Elizabeth, Wai a cewarsu zai ɓata mata tarbiya kuma ya hure mata kunne. Sosai wulaƙancin da akai masu a caji ofis ya tsayawa Alyasa'a a zuciya har yayiwa Nuhu furucin idan har ya sake ya ƙara kula masu ƴa to bai yafe masa ba. Ni kai na kamar zan ari baki wajen faɗa. Ashe a can gidansu Elizabeth kuma, tana can tana ta ihu da kuma akan ita tana son Nuhu a haka, kuma idan aka rabata dashi zata kashe kanta. Ance har coci-coci aka kaita ana mata addu'a akan ta dawo cikin hayyacinta, amma tana nan kan bakanta. Wata rana da daddare ta haɗa kayanta ta gudu gidan babanta, a wannan ranar sai da Samuel yayi shagali ana ta yanke-yanken dabbobi, saboda ya ƙuntatawa Pasto Emanuella Debora rai, sai yayi alƙawarin sai ya cika mata burinta na auren Nuhu. Ranar da farin ciki Elizabeth ta kwana. A can gidan pasto Deborah kuwa, ba ƙaramin tashin hankali ta samu ba, don ta san idan har haka ta kasance, sosai zata samu koma baya daga mabiyanta. Don da yawan mutane zasu daina zuwa cocinta balle su saurareta. Har gida taje ta samu Samuel akan ya bata ƴarta, amma ya nuna mata sam bai san wannan maganar ba, ƴarshi ita ta zaɓi dawowa ƙarƙashinsa, amma kuma ga Elizabeth nan, idan ta yarda zata bita, to ta kama hannunta su wuce. Amma ƙememe Elizabeth ta nuna baza tabi Pasto Debora ba. Debora a zuciye ta fice daga gidan, in taƙaice maki dai magana har kotu, kuma Samuel ne da nasara, don Elizabeth ta nunawa alƙali cewar bada ƙarfi mahaifinta ya mayar da ita gidansa ba, itace taji tana son komawa da zama wajen mahaifinta. Ana fitowa daga kotu pasto Emanuella ta kira taron ƴan jarida ta shaidawa duniya ta tsinewa Elizabeth, yanzu ba ƴarta bace ba har sai lokacin da ta dawo wajenta gaba ɗaya ta kuma bata haƙuri tare da fita harkan Musulmin saurayin da take so gaba ɗaya. Duk wannan bala'in da ake yi, ashe kullum idan har Nuhu na gari yana gidan matsafan nan wajen ɗiyar Debora, a can yake cin abinci. Lokacin da mahaifinsa ya samu wannan labarin a cikin gari, kusan faɗuwa ya kusa yi kuma dama gashi ba isasshen lafiya ba, nan muka tara Nuhu muna masa faɗa sosai. Wani ihu daya kwatsatsamin bani ba, hatta mahaifinsa sai da ya firgita, Nuhu babu kunya ya shiga cemin, 'Ke ba Mahaifiyata bace, baki isa ki yankewa gobena hukunci ba, don haka babu wani banzan da ya isa ya hanani auren Elizabeth Lami'. Dafe ƙirji Alyasa'a yayi tare da faɗin, har dani kake faɗawa haka Nuhu?' Nuhu sai ya riƙe ƙugu ya ɗage kai yana hura hanci. Zamewa ƙasa Alyasa'a yayi tare da kallona na buɗe baki zanji magana kenan yace, 'Bar shi Saratu, bar shi! Yaje duniya zata koya masa hankali. Ban amincewa ɗan da na haifa ya ƙara yi masa magana ba, sannan ban yarda ya ƙara zama min a cikin gida ba, sannan duk wani abu da yasan nawane, ya ajiye ya tafi!" Yana gama faɗin haka ya juya ya shige ɗaki. Ina kallon lokacin da yake share hawaye. Shi kuwa Nuhu kaɗa kai yayi ya fice yan faɗin 'To se me don an kore ni, duniya ai faɗi ce da ita.' wannan rana ita ce ranar da na saka Nuhu a idanuna na ƙarshe. Daga ƙarshe muka samu labarin wai ya musuluntar da Elizabeth har sunyi aure sun bar garin. Basu fi wata biyar da barin garin ba, Alyasa'a ya amsa kiran Ubangiji, amma kin san wani abu, tsakanin ɗa da mahaifa, kamun Alyasa'a ya cika sai da ya furta kalmar yafiya ga mahaifinki. Wannan shine labarin sanadin barin gida da mahaifinki yayi." Sosai Sarah ke kuka kamar ranta zai bar jiinta. "Nnanne ina ji a jikina Babana ba'a cikin hayyacinsa yayi maku duk abinda yayi maku ba, ke da kanki kin ce baban mamana matsafine, kuma yayi alƙawarin cikawa mamana burinta domin ya baƙantawa mahaifiyar mamana, to wallahi zai iya komai daga ciki har da juya kwakwalwar mamana. Kuma jikina ya bani, shi ya mayar da soyayyar da Babana kewa Aunty Rose Merry izuwa kan mamana domin ya samu cikar burinsa, tunda tun farko ai Aunty Rose Merry ɗin Baba ke so ba Mamana ba. Nnanne akwai alamar tambaya akan wannan batu!" Shuru Nnanne tayi na wasu daƙiƙu tare da faɗin, "To, Allah masanin gaibu Saratu. Mahaifin mamanki ne kawai zai iya warware wannan ƙullin, idan shi sanadi ko bashi bane." Da sauri Sarah ta kalleta tare da faɗin, "Yana nan a raye ne?" Jinjina kai Nnanne tayi tare da faɗin, "daga Samuel har pasto Emanuella Debora suna nan a raye!" Dafa Nnanne tayi tare da faɗin, "Nnanne idan kinyi min lamuni, zan je gidan domin na gana dashi mahaifin maman nawa." Murmushi Nnanne tayi tare da faɗin, "Bashi kaɗai ba, har ita pasto ɗin zan so ki kai mata ziyara. Idan kin nutsu zuwa gobe, zan saka a kai ki. Idan zaki tafi, zan baki kuɗi sai ƴar wajen Lukman ta raka yi." Da sauri Sarah tace, "Nnanne Ina da isassun kuɗi, Khalil ya bani ATMCARD ɗinsa domin nayi amfani da kuɗin ciki idan buƙatar haka ta taso." "To ma sha Allah!" Faɗin Nnanne. Sarah kuma tashi tayi tare da faɗin, "Nnanne zan fita na ciro kuɗin yanzu nayi sayayyar, kin ga goben sai dai kawai mu wuce." Gyaɗa mata kai Nnanne tayi. A nan gaban ƙofar gidansu ta ciri dubu hamsin. Kuma a wannan lokacin ne Khalil yaga alert ɗin kuɗi ya shigo wayarsa wanda hakan ya nuna masa inda Sarah take. Washa gari tun ƙarfe goma Sarah ta saka Suhana a gaba akan ta tashi su tafi gidan Samuel. "Wai ke baki da kunya ko? Kakanki ne kike kiran sunansa gatsau haka? Kaka Samuel zaki ce!" Harara Sarah ta maka mata tare da faɗin, "Anƙi ace kakan, kako ba kaka. Kaji wani suna wai Samuel!" Ta ƙarisa maganar tare da bushewa da dariya. "Baki da kirki maman twins!" Faɗin Suhana tana ƙarisa sakawa Sam'an takalmi. "Wai auntyn Sam'an, dasu za muje?" Faɗin Sarah. Hannun Sam'an ɗin ta kama tare da faɗin, "Kwarai kuwa! Sauban muje kaji." Ta faɗi tana riƙe hannayensu. Komai Sarah bata ce ba har suka fito parlourn, matar ba Lukman suka samu a parlour, "Aunty zamu wuce!" Faɗin Sarah. "To Sarah, Kar dai a manta ayi addu'a, sannan idan sun baku nama, kar kuci." Da "To" suka amsa sannan suka fita daga ɗakin, sai da suka ƙara zuwa wajen Nnanne suka yi mata sallama sannan suka fito. Kasancewar babu nisa, a ƙafa suka yi ta takawa har suka gangara, sun zo wajen ƙofar gidan wani makeken gida wanda gaba ɗaya wanda shi ya haska unguwar, sai Suhana ta taɓo Sarah tare da faɗin, "Sis ga gidan kakarki, pasto Emanuella Debora." Ɗaga kai Sarah tayi, babu abunda idanunta suka fara ganin sai tafkeken sunanta a jikin saman gidan, _Pasto Emanuella Debora Gabriel House_. "Lallai matarnan taji kuɗi, duk wannan uban gidan nata ne?" Gyaɗa mata kai Suhana tayi tare da faɗin, "Kuma ƴata rak kawai gareta, Mahaifiyarki!" Taɓe baki Sarah tayi suka cigaba da tafiya har zuwa wani ƙaton ginin ƙasa, rabin katangar ta zube kana iya hango mutanan dake ciki, ga manya-manyan tukwane nan a kan murhun duwatsu har huɗu, gefe kuma ƴan matane su kusan bakwai da ɗaurin ƙirji, wasu kuma ɗan siketi ni iya ƙauri sai riga da bata gama rufe cibiya ba da uban kitson attachment har baya, farcen hannu zaƙo-zaƙo da ƙumba. Wasu tsoffi kuma zagaye a akan wani banci suna wani abun da su Sarah basu sani ba don basu iya hangowa. Can gefe kuma samarine da manyansu suna shan wani abu a kofi, wasu kuma suna buɗe wannan tukunyar suna ɗeban abun ciki suna sha. "Kin ga wancen abun da suke sha a kofi, sunansa burkutu." Faɗin Suhana. "Burkutu dai!" Sarah ta faɗi tana kallon Suhana, jinjina mata kai tayi daidai lokacin da suka iso ƙofar gidan. "Gafaranku dai!" Faɗin Suhana. Gaba ɗaya mutanan gidan suka zuba masu idanu, "Lafiya?" Wata budurwa mai ɗaurin ƙirji ta faɗi. "Mun zo wajen baba Samuel ne." Faɗin Suhana. Da hannu suka yi masu nuni da ɗakin, domin idan da sabo sun saba ganin musulmai suna zuwa gidan wajen baba Samuel domin yayi masu aikin asiri kasancewarsa shahararren matsafi. Daga asabarin dake ƙofar suka yi sannan suka shiga. Ɗagowa wani tsamurarren tsoho yayi tare da kallonsu, wani murmushi ya saki sannan ya nuna masu wajen zama tare da kallon Sarah yace mata, "Jikata, ƴa ga Elizabeth! Kin zo nan ne domin son sanin mahaifinki Nuhu yana cikin hayyacinsa ya ƙi bin umarnin Mahaifansa ya auri Elizabeth ko?" Da mugun mamaki Sarah ta kalli Suhan sannan ta mayar da kallonta izuwa ga Baba Samuel. Murmushi yayi tare da nuna mata tukunyar tsafin dake gabansa, sannan yace, "Duk wanda ya iso ƙofar gidana tukunyar tsafina take faɗa min zuwansa da kuma abunda ya kawosa gare ni. Ina ƴata Elizabeth?" Shuri Sarah tayi tana kallonsa, babu ta inda ta hango kamannin mamanta a jikin wannan yamutsatstsan tsohon, sai dai tabbas taga wani baƙin halitta dake cikin kwayan idanunsa wanda akwai shi sak a idanun Lami. Dariya Baba Samuel yayi mai sauti wanda ya saka Sarah saurin kallonsa ita da Suhana. "Tabbas hasashenki gaskiya ne! Ni na juya tunanin mahaifinki, sannan ni na sanya soyayyar ƙawar mahaifiyarki ya juye na mahaifiyarki a zuciyar babanki, Elizabeth bata taɓa son Nuhu ba, haka Nuhu bai taɓa son Elizabeth ba, nayi amfani da dutse ɗaya ne na jefi tsuntsu biyu, na haɗa wannan soyayyar ne domin in wulaƙanta tsohuwar matata pasto Emanuella Debora Gabriel, na biyu kuma domin in rama abunda mahaifin Rose Merry yayi min, kuma naji daɗi sosai saboda na rama komai cikin sauƙi." Ya ƙarisa maganar yana dariyar jin daɗi. Miƙewa Sarah tayi tare da kama hannun Suhan tace, "Tashi mu tafi Suhan, tsoro
Showing 126001 words to 129000 words out of 129453 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43 Chapter 44