yayi ya shiga ciki, ɗakin nan kamar yanda yake, bayi ya nufa ya dunga cuɗa kansa kamar zai yage fatar dake jikinsa saboda tuna ya haɗa jiki da Aina'u. Ya jima kamun ya fito daga wanka, wajen mirror ya nufa yana ƙarewa kansa kallo ganin yanda ya koma kamar mahaukaci, gashin kansa yayi buzu-buzu babu gyara. Hawaye zafafa yaji suna biyo ƙirjinsa sakamakon tuno duk abubuwan da yayiwa Sarah, "Hajiya ki taimakeni kar ki raba ni da uwar ƴaƴata!" Ya faɗi yana mai zama a kan kujerar dake gaban mirror ɗin tare da ɗaura kai a kan drawer. Ya jima a haka kamun ya tashi ya saka don ko shafa mai bai yi ba. Fitowa yayi daga ɗakin, kiciɓis suka yi da Laure a ƙofar ɗakinsa, kanta a ƙasa don kuka take yi tace, "Ya kalif kaje inji Hajiya!" Ba tare da yace komai ba ya gittata ya wuce. Ɗakin hajiyan ya nufa, sai da ya Kwankwasa sannan ya shiga ciki, zaune ya same tana waya kamar zata taune harshe don masifa, "To shikenan sai kazo goben, don wasu abubuwan ma baza su faɗu ba har sai ka iso, ku taho kai da Ayshan." Faɗin Hajiya. Tun da tace ku taho kai da Ayshan, Khalil ya fahimci da Ya Abdullahi take magana. Ajiye wayar tayi tare da kallonsa tace, "Khalilullah, ka dai ji abunda na faɗa maka ko? Tom! Yanzu abunda nake so da kai, kayi maza ka tashi ka tafi gidansu yarinyar nan ka taho min da jikokina, sannan ka tabbatar kamun ka dawo cikin gidan nan ka tsinke igiyar dake tsakaninka da ita, sannan gobe in Sha Allah idan Marmari daga nesa ya iso yaga wannan la'ananniyar yarinyar data tarwatsamin gida, zaka nemo akori kura a kwasheta a kai ta gidan iyayenta can susan yanda za suyi da ita, mu baza mu yafe mata ba, amma kuma baza muyi mata komai ba domin Allah ya riga ya soma nuna mata iyakarta tun a nan gidan duniya! Sauran kuma sai mun je can. Don haka ka tashi maza ka bar gidan nan kayi abunda na umarce ka da kayi." Ta ƙarisa maganar tana mai nuna masa hanya. Ya kwashi kusan mintuna biyu jikinsa na rawa kamun ya miƙe ya fita daga ɗakin. Kai tsaye parking lot ya nufa ya buɗe mota ya shiga yayi reverse ya bar gidan, a hanya babu abunda yake yi sai goge zufa kuma a lokaci guda gabansa na wani irin bugawa da ƙarfin tsiya, kuma hakan ƙara faruwa ne idan ya ƙara kusa da unguwarsu Sarah. A ƙofar gidan yayi parking sannan ya fito daga cikin motar, glasses ɗinsa ya fiddo ya saka saboda yanda idanunsa suka yi jazur. Kallon layin ya riƙa yi, domin tunda ya saya masu gidan zai iya irga zuwansa unguwar. Gaban gate ɗin gidan ya tsaya tare da kai hannu ya Kwankwasa gidan sau uku, jin alamar ana cire jamlock sai ya ɗan matsa baya kaɗan yana jiran a buɗe Ƙofar. Murmushi ta sakar masa tare da faɗin, "Ah Khalil kai ne a gidan namu yau? Wallahi yanzu muka gama magana da mama (Lami, kasancewar malamar mu ta hana su kiran sunanta kai tsaye. Tace masu hakan rashin tarbiyya ne da nuna rashin ɗa'a ga mahaifiya )" Faɗin Na'ima wacce gaba ɗaya ta rame kamar ba Na'ima ƴar gayu ba. Murmushin kawai ya iya mata, "Shigo mana ka tsaya a tsaye." Ta faɗi tare da matsa masa, shigowa yayi yana mai ƙara gyara zaman glasses ɗin fuskansa, a tsakar gidan ya taras da Lami da sauraran ƴaƴanta, sai dai yaji gidan tsit ba kamar yanda ya saba jin hayaniyar yaransu ba aduk sanda ya leƙo, kasancewar yana zuwa masu da abun motsa baki, suna jin muryansa ko da basu tsakar gidan suke fitowa da gudu suna masa oyoyo. Har ƙasa Khalil ya tsuguna tare da faɗin, "Mama ina wuni, na same ku lafiya?" Sai da Lami ta ƙura masa idanu na kusan tsayin mintuna biyu kamun tace, "Lafiya Khalil? Shin kayi dogon jinya ne? Amma Saratu bata kyauta ba da bata zo ta faɗa ba, ashe shiyasa kenan babu ganta wajen zaman makoki ba!" Faɗin Lami cikin jimami. Gaban Khalil ne ya buga da wani irin ƙarfi jin abunda Lami tace, amma kuma sai yayi saurin kawar da hakan cikin ransa tare da furta, "Mama wanene ya mutu har akai zaman makoki bamu sani ba?" Nuna su Na'ima tayi tare da faɗin, "Gaba ƴaƴansu ne suka mutu sakamakon saran maciji!" Na'ima har idanunta sun cicciko da hawaye sakamakon tado mata da mikin da Lami tayi. Khalil kuma sai yanzu ya tuna abunda Aina'u tace lokacin da take confessing, cewar ta tura maciji ya sari duka ƴaƴan gidan ta bawa bokanta jininsu. "Wannan yarinyar tsinanniya ce ta ƙarshe!" Faɗin Khalil cikin zuciya. Shuru yayi na wasu lokaci kamun yace, "Mama idan babu damuwa ina son magana da dukkan ku dan Allah, amma kamun nan bari na duba Baba tukun." Jinjina kai Lami tayi, yayin da shikuma ya miƙe ya nufi ɗakin baba wanda har yau yana nan kwance kamar gawa. Sallama yayi tare da saka hannu ya cire takalmin ƙafarsa sau ciki sannan ya shiga, baba na nan kwance a kan gadon, Sai dai cikin tsafta yake don ba ƙaramin ƙoƙari su Na'ima suke yi ba wajen kula da tsaftar baban kasancewar anan yake bowali da bahaya! Har gaban gadon Khalil ya jawo kujera tare da zama sannan ya kamo hannun baba dake bacci tare da soma faɗin, "Baba kayi haƙuri duk da nasan cewar kalmar ciwo zata ƙara saka maka cikin zuciya! Tabbas ko da ban san ainahin ciwon da kake ji ba matsayin ka na uba, amma zan iya ɗan kwatanta ko da kaɗan ne. Kayi haƙuri, shine kawai abunda zan iya ce maka. Sannan in Sha Allah baba bazan taɓa bari rayuwar Sarah dana sauran ƴaƴanka ya taɓarɓare ba kamar na Aina'u, nayi maka wannan alƙawarin, zan tsaya tsayin daka a kansu, Ni ba sirikinka bane kawai, Ni ɗane a wajenka kuma yayyinsu Na'ima. Kai kuma Baba in Sha Allah zaka warke kuma ka cigaba da harkokinka kamar da. Kayi haƙuri baba!" Abunda ya matuƙar bawa Khalil mamaki jin Baba ya ɗamki hannunsa ya riƙe gam-gam kuma a lokaci guda hawaye na zirarowa daga kwarmin idanunsa har suna shiga kunnensa. Khalil ɗaura ɗayen hannunsa yayi a kan na Baba tare da riƙe hannun da ƙarfi yana kallon fuskan baban dake a rufe kuma yana zubar da hawaye. "Kayi haƙuri baba, in Sha Allah zaka samu cikakken lafiya." Baba magana yake so yayi, amma babu damar haka, a zuciyarsa kuwa cewa yake, "Dan girman Allah Ibrahim kar ka nema min lafiya, ka barni a haka, ni fatana ɗaya in koma ga Allah cikin gaggawa kuma tare da imani, don baƙin cikin dake cin zuciyata ni kaɗai na san shi. Dan Allah Khalil ka barni a haka." Da kyar Khalil ya iya zame hannun Baba a cikin nashi sannan ya fita daga ɗakin, dama kuma Na'ima na jiransa domin tayi masa jagora zuwa parlourn Lami, yana fitowa tayi gaba, shi kuma ya bita a baya har cikin ɗakin Lamin. Be zauna a kan kujera ba, a ƙasa ya zauna tare da zare glasses ɗin dake maƙale a idanunsa ya ajiye a gefe yana kallon mutanan dake ɗakin cikin dabara, amma har ya gama kallosu bai hango fuskan annurin zuciyar tasa ba a cikinsu. Kai a sunkuye ya kuma gaida Lami a karo na biyu tare da yi mata ta'aziyar jikokinta ƴan gaba da fatiha sannan ya ɗaura da faɗin, "Haƙiƙa na taho maku da labari mai girgizarwa da tashin hankali gami da baƙin ciki!" Yana kaiwa nan ya ɗan dakata na wasu daƙiƙu, yayin da Na'ima ta shiga nanata "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Kasancewar malamar su ta faɗa masu duk ɗayansu da ya faɗa cikin wata masifa to ya karantata. Lami kuwa da ƙarfi ta faɗi, "Yesu Almasihu mai ceto, ka kawo ɗauki da sassauci, ka sanyaya zuciyarmu da ruwa mai tsarki." Khalil kuwa bayan dogon ajiyar zuciya sai ya soma basu labari tiryan-tiryan, bai rage komai a cikin abubuwan da Aina'u ta aikata ba, har kwanciyar aure da yayi da ita sai da ya faɗa masu, kashe-kashen da tayi har zuwa koran da ta saka yayi wa Sarah da kuma halin da Aina'un take ciki yanzu na girban abubuwan data shuka. Kif! Lami ta faɗo daga kan kujera ta sume, yayin da su Na'ima suka fashe da kuka jikinsu na rawa jin abubuwan da Aina'u ta aikata daga ciki har da kwanciyar aure da tayi da mahaifinsu. Hassana ce tayi kan Lami tare da yayyafa mata ruwa ta farfaɗo, wani irin kuka Lami ta fashe dashi tare da faɗin, "Ubanmu wanda ke cikin Sama, na tsarkake sunanka, mulkinka shi zo akan abin da ka ke so ayi shi cikin duniyar nan kammar yada ake yinsa cikin sama. Ka gafarta mana laifinmu, kamar yarda muna gafarta ma waɗanda su ke yi mamu laifi. Kada ka kai mu wurin jaraba, amma ka cece mu daga Shaiɗan. Duka mulki, da iko da girma naka ne, har abada. Kada ka kama ni da laifin haihuwar Aina'u ya Yesu Almasihu! Na san ita mai saɓo ce mummana a gareka, saɓo mafi muni shine kwanciya da mahaifin daya haife ka, ya Yesu amintace, bani da laifi akan abinda ƴata ta aikata, kayi mata hukunci amma ka cire mu Ni da sauran ƴaƴana. Mai girma Yesu Almasihu, na duƙa da duka guiwowina a ƙasa ina neman yafiya da yafiyarka, ka amsa min, Amin." Khalil duƙar da kai kawai yayi yana jiran ace masa ga inda matarsa take. Na'ima da su Hassana kuwa kamar zuciyarsu zai fito saboda irin kukan da suke yi, "Mama dan girman Allah Aina'u ƴarki ce? Anya kuwa ba canje aka yi maki a asibiti ba? Ina ina ganin babanmu bashi ya haifi Aina'u ba, ɗan halak ba zai taɓa yin tarayya da mahaifinsa ba." Faɗin Na'iman. Sai da Lami ta fyace majina sannan tace, "Na rantse da girman Yesu Almasihu mai ceto, Ni da mahaifinku Nuhu muka haifi Aina'u, Aina'u ƴata ce, kuma ƴar Nuhu ce, Ni ina ganin baƙin da Mahaifiyata pasto Emanuella tayi min ne yake bina, don ta taɓa tsine min lokacin da zan auri mahaifinku Nuhu. To ni babban tashin hankalina shine, kai Khalil kace ka kori Sarah, to tun yaushe? Don Sarah dai bata zo gidan nan ba." Da sauri Khalil ya ɗago tare da faɗin, "What! Bata zo nan gidan ba? To ina zata je daya wuce nan ɗin." Duk a gigice yayi maganar kuma ya miƙe tsaye. "Gaskiya Saratu bata zo gidan nan ba!" Lami ta kuma faɗi tare da kallon su Na'iman dake kuka tace, "Ko ku kun ganta?" Girgiza kai suka yi dukansu, Khalil yace, "Wallahi yau kimanin kwanaki goma sha bakwai kenan da barin ta gidana, to idan bata zo nan ba, ina zata kenan? Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!! Allah ka tsare min matata da ƴaƴana a duk inda suke." Lami hannu ta ɗauka akai tare da soma kwarara ihu har da kwance zani tana faɗuwa a ƙasa tare da faɗin, "ƴata kina ina, ina kika je kika ɓuya? Yesu Almasihu ka nuna min hanya cikin sauƙi!" Khalilullah fita yayi da sauri tare da barin gidan hankalinsa a bugun tashe, buɗe mota yayi tare da shiga ya ɗaura kansa akan steri yana tunanin hanyar da zai fara neman Sarah. Kwankwasa masa glass yaji ana yi, a hankali ya ɗago tare da sauke glass ɗin motar Kasancewarta tinted, "Muneeba!" Ya kira sunanta da mamaki don rabon da ya sakata a idanunsa tun lokacin data kawo masu ziyara lokacin Sarah na fama da cutar tsutsotsin nan, don shi bai ma san tafiyarta ba, kuma tun daga ranar bai Kum samun labarinta ba. Buɗe mata murfin motar yayi tare da faɗin, "Naji daɗin ganinki, shigo ciki Please." Girgiza kai tayi tare da faɗin, "Kayi haƙuri ba zan iya shigowa ba, domin a yanzu haka maganar da nake faɗa maka idan har Babana ya samu labarin to tabbas zan fuskanci mummunar hukunci mai tsanani don ya haramta min nufa inda kuke ko yin magana da ɗayanku. Kaga wancen makarantar, acan nake koyarwa, fitowata kenan na ganka ka fito daga gidan nan shine nace bari na ƙariso mu gaisa." Shuru yayi na wasu ƴan daƙiƙu sannan yace, "Mai ke faruwa ne Muneeba?" Dafa glass ɗin motar tayi tare da faɗin, "Abunda ya wuce ya wuce, amma dai bari na tsungulo maka kaɗan daga halin da na shiga sanadin zuwa gidan ka wancen ranar. Bayan naga halin da ƙawata take ciki, sai na tashi da sauri domin zuwa wajen iyayena su taimaka mata da magungunan karya sammu da kuma addu'o'in da zata riƙe ya zama makaminta don its obvious matarka sammu ne a jikinta. To ina fitowa kawai naji an taɓa ni ta baya, juyowar da zanyi sai muka yi idanu huɗu da ƙanwar matarka, sai ta daki goshina tare da cewa in kalli gabas inyi tafiya kar in kuma dawowa gidan! To tun daga wannan lokacin ban kuma sanin inda kai na yake ba sai tafiya kawai nake ta yi, amma kasancewar iyayena ma'abota ambaton Allah ne haka nima kuma na tashi da wannan ɗabi'a shiyasa Allah ya sauƙaƙa min wahala ban jima ina garari ba aka gano inda nake aka dawo dani gida, sai dai na sha jinya mai tsayi kamun na samu kaina, bayan na dawo cikin hayyacina ne na shaidawa iyayena abunda ya faru, to daga nan ne sukai min iyaka daku, sannan suka ce in dai addu'a ce aduk inda aka yi to da cikin ƙarƙashin ƙasa ne zata karɓu indai anyi ta cikin yaƙini, saboda haka zasu riƙa bin ku da addu'a daga nan inda suke ba sai na kuma takawa inda kuke ba, sannan Babana ya saka min doka mai tsauri akan kar in kuskura ko hanyar gidanku na ƙara bi ta wajen." Shuru Khalil yayi yana mamakin irin mugun hali da rashin imanin Aina'u. "Allah ya saka maki Muneeba, muma Aina'u tayi mana muguwar cutarwa da tafi wanda tayi mai, sai dai kawai Allah yayi mana sakayya!" Rausayar da kai Muneeba tayi tare da faɗin, "Ameen, a gaida Saran, sai anjima." Tana gama faɗin haka ta ɗaga masa hannu sannan ta wuce. Ɗaga glass ɗin sama yayi tare da kunna motar ya bar wajen, a kan hanya sai saƙe-saƙe yake yi ta inda zai fara neman Sarah, ɗilin! Yaji saƙo ya shigo cikin wayarsa, kamar ba zai duba ba, sai kuma ya mika hannu ya ɗauko wayar dake kan seat ɗin gefensa, ganin debit alert daga GTbank sai yayi tsaki ya ajiye wayar, can kuma ya taka wani mahaukacin burki a tsakiyar titi, Allah yaso babu wanda ke binsa a baya, hannunsa na rawa ya ɗauko wayar ya shiga cire key da sauri, 'wrong pin' ya nuna masa kasancewar da sauri yake danna code ɗin. Khalil bai taɓa dana sanin saka pin a rayuwarsa ba sai yau don ƙosawa yayi ya buɗe wayar, ƙara sakawa yayi stil cikin sauri, wannan karan ya bude, shiga message ɗin yayi ya shiga karantawa da sauri, wani irin sanyin Ni'ima ce ta shiga bin saƙo da lungu jikinsa, "Allah Ubangijin mai kowa mai kowai, mai sauƙaƙawa bawa a cikin matsala, Allah Nagode da a wancen lokacin ka bani courage ɗin bata ATMcard ɗina." Faɗin Khalil sakamakon ganin debit alert daga Nasarawa, Lafiya state. "Wamba, unguwar abakwa!" Ya kuma faɗi a bayyane tuno lokacin da yake tambaye Sarah a kan wani yare su har ta faɗa masa sunan garinsu har da unguwar. "Alhamdulillah!" Ya kuma faɗi daidai da lokacin da wayarsa tayi ƙara, ganin Hajiya ke kiran wayar sai da gabansa ya faɗi. Jiki a sanyaye ya ɗaga wayar, "Ka dawo gida tunda ba'a can aka haife ka ba, kuma Marmari ya biyo jirgin sojoji yazo, isowarsa kenan shi da Ayshan. Abu na gaba kuma, kar ka kuskura ka shigo cikin gidan nan idan har ka san akwai igiyar aurenka aka ƴar dangin matsafan nan!"
_Wai me Hajiya take nufi damu ne_😞
_Kuyi haƙuri dan Allah da rashin ganin update jiya, wani ɗan matsala aka samu_
*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID
Showing 117001 words to 120000 words out of 129453 words
_Wai me Hajiya take nufi damu ne_😞
_Kuyi haƙuri dan Allah da rashin ganin update jiya, wani ɗan matsala aka samu_
*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40 Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44