irin kwallon tashin hankali ya riƙa yi da Aina'u tana buguwa da edge ɗin bangon ɗakin yana faɗin, "Mahaifiyata kika ɗaga hannu kika mara? Mahaifiyar tawa!!" Baki, kai da hancin Aina'u sai tsiyayar da jini yake yi tsabar naushi da Khalil ke aza mata, da sauri Hajiya ta nufi Khalil tare da faɗin, "Mu'azzam ka sake kyaketa haka, ka kyaleta nace!" Faɗin Hajiya da ƙarfi, shi kuwa Khalil bai saurareta ba ya cigaba da naushin Aina'u a duk inda ya samu a jikinta, fuska, baki, ciki da ƙirjinta duk sun nausu, sai da Hajiya ta shiga tsakiya tukunna Khalil ya dakata da dukanta, ita kuwa Aina'u sai tsiyayar da jini take yi, tafin hannunta kuwa ta murza yafi sau shurin masaƙi. Ganin Hajiya a tsakiyarsu, da sauri ta rarrafa ta fice daga ɗakin ta nufi ɓangaren Sarah riƙe da cikinta. Tana shiga sama ta haura zuwa ɗakin Khalil ɗin tare da duƙawa ta janyo tukunyar tsafinta, sai dai tana gama fuddoshi ya bada sautin fuuus ya watse a ɗakin, nan da nan ɗakin ya ɗauki wani irin ɗoyi, kuma hayan yayi daidai da wani irin murɗawa da cikin Aina'un yayi, ƙafafuwanta su hau wani irin rawa, idanunta na wani irin far-far-far kamar wacce kwayar idanunta zasu faɗo ƙasa, nan da nan wani irin guguwa ya tashi a tsakiyar ɗakin na kusan tsayin mintuna biyar kamun _Hell Ofulafu_ ya bayyana a tsakiyar ɗakin rabin fuskansa a ƙone, shi kuwa mummunar halittar nan gaba ɗaya jikinsa a ƙone yake. Wata shimfiɗeɗiyar bulalace a hannun Hell Wanda gefe-gefe bulalan wasu irin manya-manyan ƙayoyi ne masu matukar tsini da kaifi, jikin Aina'u wani irin rawa ya ɗauka ganin Hell da wannan bulala. Ɗaga bulalan yayi tare da shimfiɗa mata sai da ya zagaye jikinta har zuwa kan fuskanta, wani irin ihuu ta saki wanda ya ɗauki gidan gaba ɗaya, nan da nan jikinta ya hau tsirtuwar jini har zuwa fuskan, don bulalan yana sauka a kan fatan jikinta ya taho da fatarta, haka ya dunga zubaba mata bulalan tana ihu tana birgima, bayan ya gama farfashe jikinta sannan ya zaro wata doguwar ƙarfe wanda kallo ɗaya zaka yiwa Ƙarfen zaka tabbatar ya ɗauki awanni a cikin wuta saboda irin jan da yayi. Ba tare da tausayi ba ya dunga ɗaura wannan ƙarfen a ko'ina na fatar jikinta, Aina'u tsabar azaba ko kuka ta kasa yi sai wani jan numfashi da ta riƙa yi. Hello bai haƙura ba sai da ya banƙare Aina'u sannan ya fiddo da wani abu kamar kwaɗo mai matukar muni da azababben wari ya tura cikin gabanta sai har sai da tsintsiyar hannunsa ya shige ciki. Aina'u wani mahaukacin gurnani ta saki wanda ya taho da wani mulmulallan jini da bakinta, Hell na ciro hannunsa a gabanta jini ya biyo baya baƙiƙƙirin mai masifaffan wari. Wani irin dariya ya shiga ɓaɓɓakawa kamun ya dafa mummunar halittar nan suka ɓace, Aina'u kuwa sai wani irin birgima da buga kanta a ƙasa take yi saboda mummunar azabar da take yi mai wuyar fasaltuwa, bayan jinin dake biyu jikinta da gabanta, wani manya-manyan tsutsotsi da ƙananan baƙaƙen kunamu suka shiga fitowa ta gabanta kuma masu cizo da tsungulin, Aina'u sai zaro harce take yi tana wani irin surutan gigin azabar da take ji a cikin jikinta. Wani irin ɗaukar zafi jikinta ya soma yi kamar ana dafa mata jikin, da kyar ta iya cire komai na jikinta tana wani irin gurnanin azaba, kuka ta fashe dashi gani yanda tsokar naman jikinta ke yankowa yana faɗowa kuma duk tsokar data faɗo, wasu fararan tsutsotsi ne ke mamaye wajen suna tsungulin jikinta. Hatta naman dake wuyanta zazzagowa yayi ya faɗo kana ganin tafiyar maƙogwaronta, idanunta sunyi wani irin ɓulu-ɓulu sun zama abun tsoro, cikin ƴan wasu mintuna gaba ɗaya kamannin Aina'u ya sauya ta koma wata abun tsoro, fuskansa ya mokaɗe, bakinta ya turo yayi tsini kamar na kare, haƙoranta sun turo sunyi cirko-cirko a baki. Ɓangaren Hajiya kuwa, Khalil na tsaye ya yanke jiki ya faɗi yana wani irin jijjiga kamar mai farfaɗiya, ruɗewa Hajiya tayi tana faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Laure! Laure!! Laure na shiga uku ki taimaka min ya zanyi." Daidai nan aka murɗo ƙofar aka shigo, ya Abdul-Hakeem ne da Aunty Maryam ce wacce tayi wani irin mahaukacin rama kamar wacce ta tashi daga ciwo, "Alhamdulillah, Abdul-Hakeem taimaka min mu kaita asibiti dan Allah!" A raunane Aunty Maryam tace, "Hajiya ba asibiti za'a kai shi ba, daddyn moon ɗauke shi ka mayar dashi kan kujera ka bashi wannan maganin mu gani." Ta ƙarisa maganar tana mai fiddo wani goran magani a cikin jakarta. Cicciɓarsa ya Abdul-Hakeem yayi tare da mayar dashi kan kujera sannan ya karɓi goran hannun Aunty Maryam ya bude tare da buɗe bakin Khalil yayi bismillah ya zuba masa har sau uku. Cikin minti ɗaya ya miƙe da sauri yana faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Ya faɗi hakane tare da ɗaura hannunsa biyu a kai yana girgiza kai. "Hajiya meke damuwa? 'Hajiya mafarki nayi ko? Ba gaskiya bane duk abunda na gani ko? _Ƙanwar matata_ bata zo cikin gidan nan ta raba ni da matata ba ko? Hajiya Sarah tana ɗakinta ko?" Dafa shi Hajiya tayi tare da faɗin, "Kwantar da hankalinka Khalil, dawo cikin na tsuwarka." Da sauri Khalil yace, "Hajiya natsuwata baza ta taɓa dawowa ba har sai kun faɗa min duk abunda nake tunanin ya faru bai faru ba. Hajiya kinsan abunda ke min gizo a idanuna kuwa? Hajiya kin san bala'in da nake gani kuwa!" Da wani irin ihu yake maganar domin kwanciyar da yayi da Aina'u agaban twins da Sarah kawai yake dawo masa cikin idanunsa. "Khalil ba mafarki kake yi ba!" Faɗin ya Abdul-Hakeem. Wani irin duum Khalil ɗin yaji a cikin kansa, "Dagaske ne na koreta, dagaske ne da kaina na kori matata, dagaske na kwanta da _ƙanwar matata_ agaban matata da ƴaƴana. Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Wai meke faruwa dani ne, ku faɗa min!" Ihun da yayi sai da ya razana kowa a cikin ɗakin. Ya Abdul-Hakeem ya kalli Aunty Maryam tare da faɗin, "Mommyn moon yi masu bayanin da kika min!" Hawaye na kwaranyo a idanun Aunty Maryam ta soma faɗin, "Hajiya tun da uwata ta haife ni, ban taɓa ganin azzaluma kuma mushrika irin Aina'u ba, duk wani bala'in dake faruwa a cikin gidan nan sanadinta ne, Aina'u itace sanadin kurmancewar Laure, rashin lafiyar da kika yi har ya zazzago da idanunki, rashin kiranki da ya LTG da ya barrister, domin ita ta karkatar da hankalinsu da barin nemanki, mutuwar jinjirar Nafeesa da kuma korata da daddyn moon yayi har da dakatar dashi da akai a wajen aiki. Aina'u matsafiyace ta gaske, domin bokanta a tare da ita yake koda yaushe, tana matsa tafin hannunta yake bayyana a ciki, sannan kuma tana kallon komai da kowa dake cikin gidan nan ta cikin tafin hannun, har kisa tana iya aikatawa ta hakan. A ranar da na kamata tana magana da bokan, a ranar ta saka ya Abdul-Hakeem ya sake ni, sannan tayi min kashedi akan idan har na faɗawa wani abunda naga tana yi, sai tayi min irin abunda tayiwa Laure. Tun da na bar gidan nan, kullum a firgice nake kwana har na tsawon shekara ɗaya da rabi duk da cewar wata na biyu a gida baban moon ya turo min da text akan ya mayar dani sai dai kuma inyi haƙuri ba zai iya dawo dani cikin nan gidan ba, a hakan nayi ta hakuri ina kai wa Allah kukana babu dare babu rana, ban taɓa tunkarar kowa da Maganar ba, sai ranar da naje taron wani wa'azi a makarantar da nayi sauka, sai nayi katari malamin yana ta wa'azi akan harkan bin boka har da kuma addu'o'in da mutum zai lazimci yi domin kariya, tun da na fara wannan addu'o'in babu dare babu rana ina roƙon Allah ya karya alkadarin Aina'u da tsinannun matsafanta, cikin ƙanƙanin lokaci tsoran Aina'u ya fita daga cikin zuciyata har na nemi mijina na bashi addu'o'in shima da kuma magungunar da zai riƙa sha da kuma turare gidan, to sai kuma kwanakin baya yazo ya faɗa min kin kawo almajirai sunata sauke alƙur'ani, sosai hakan yayi min daɗi ganin zamu haɗa hannu mu yaƙi azzaluma Aina'u. Khalil kayi haƙuri, Allah zai saka mana kai da matarka, domin ta cutar da kowa na cikin gidan. Kuma Allah ba azzalumin bawansa bane, baya taɓa kama mutum da laifin da ya aikata ba da gangan ba, kayi komai ne bisa tsafi da makirci irin na shaiɗaniya kuma annoba Aina'u." Da wani irin speed Khalil ya bar ɗakin ya nufi nashi side ɗin, Hajiya da ya Abdul-Hakeem har da Aunty Maryam da Laure suka bi bayansa. Khalil bai tsaya murɗa handle ɗin ƙofar ba, kafaɗa ya saka ya bugi ƙofar da wani irin mahaukacin ƙarfi sai ga ƙofar a ɓalle, faɗawa ɗakin yayi idanunsa a rufe tsabar zafin zuciya da fusata, dai-dai nan ya Abdul-Hakeem ya faɗo ɗakin shima, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Faɗin ya Abdul-Hakeem da ƙarfi saboda ganin wani mummunar halitta mai ban tsoro a nannane kuma fatar jiki na zagwanyewa sannan tsutsotsi na fita, ga kuma ƙananan kunamu baƙaƙe masu cizo dake fitowa daga gaban Aina'u, gaba ɗaya tayi watsi da kayan dake jikinta. Rintse idanu yayi tare da faɗin, "Allahumma arji'ini fi musibati wa aklifni khairan minha, wannan wacece haka? Hajiya kar ki shigo don Allah!" Ya fadi don baya son Hajiyar ta razana. Amma tuni Hajiyar ta sako kai ta shigo ɗakin, zuuu ta tafi zata faɗi saboda razanar da tayi ganin Aina'un. "Nice Aina'u, ku taimaka min ku kaini asibiti, wallahi mutuwa zan yi, ku taimaka min!" Faɗin Aina'u, wanda bai san abinda ta aikata ba, dole yaji tausayin halin da take ciki. Maƙogwaro a waje, tsokar fata sai yankowa take tana faduwa tsutsa na cin ramin wajen da tsokar ta faɗo, ga tsutsotsi da baƙaƙen ƙananan kunamun dake fitowa daga gabanta masu azabar harbi da ciwo, idanu sun zazzago, baki ya turo uwa na kare, ga kuma zafi da mummunar wari da jikinta yake yi, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Faɗin Hajiya tare da fashewa da kuka tana faɗin, "Aina'u, kece kika dawo haka? La haula wala quwata illah Billah! Aina'u kin ga ƙarshen aikata sharri ko!" Hajiya na ida zancenta Aina'u ta ɗuka kamar kare ta hau kukan jaki kamar zata fasa ɗakin, can kuma kamar an tambayeta ta soma confessing abubuwan data aikata, "Abia naje nayi mummunar tsafi domin in samu zuciyar Khalil, ban san sau nawa wani inyamuri mai suna Ugo yayi amfani dani ba, nayi kwanaki cikin tukunyar tsafi, sannan na kashe mutane babu adadi, daga cikin akwai jikanki ƴar wajen Nafeesa, ni na sadaukar da jininta wa Hell, sannan nice na kashe Nafeesa da mijinta ta hanyar tura aljani ya tsotse jininta sannan ya bude tukunyar gas wanda hakan yayi sanadin rayuka da dama. Nice na kashe ƴaƴan ƴan uwana duka ta hanyar tura aljani ta suffar maciji ya sare shi, nice na kashe ɗan adaidaita sahu saboda rashin tafiya da sauri da yayi har na rasa damar kashe ƴan biyun Sarah tun suna jarirai, Ni ce na tura Muneeba cikin duniya wanda har yanzu tana ta tafiya bata san inda kanta yake ba, nice nayi wa Khalil mummunar tsafi yayi ta amfani dani ba cikin hayyacinsa ba, sannan nice na tura na saka Hell ya tura aljami mantau cikin kwakwalwar Ya Abdullah da ya barrister domin su manta dake Hajiya har abada, nice nayi asiri Abdul-Hakeem ya saki matarsa domin ta gano sirina, sannan na saka aka dakatar dashi daga wajen aiki, kuma duk na samu ƙarfin tsafin nan ne ta silar kwanciyar aure da nayi da mahaifin da yayi sanadin zuwana duniya domin hakan shine cikar tsafina, na samu nasarar kwanciya dashi ne ta sanadin tsafin da nayi masa sannan na juye masa sak Lami, sai bayan ya gama amfani dani sannan hankalinsa ya dawo jikinsa, baƙin cikin haka ya saka ya yanke jiki ya faɗi, dalilin faɗuwar da yayi shine silar ciwon da yake fama dashi yanzu na shanyewar ɓarin jiki." Tsabar zuciyar Hajiya ta kasa ɗaukar abunda taji daga bakin Aina'u, faɗuwa ƙasa tayi a sume. Khalil kuma yayi kan Aina'u da dukan fitar rai. Sai Abdul-Hakeem ya rasa wa zai riƙe a cikinsu, daka ƙarshe dai ya bawa Hajiya taimakon gaggawa ta hanyar fitar da ita daga ɗakin ya yayyafa mata ruwa, sai da ta farfaɗo tukun ya koma ɗakin ya riƙe Khalil dake neman kashe Aina'u, "Baka da hankali ne Khalil? Mai yasa zaka kashe gawar da ba taka ba? Ai wannan yarinyar bata buƙatar komai na hukunci daga gare mu, hukuncin da Allah ma yayi mata tun a nan duniyar ya isheta wallahi." "Ka barni na kasheta dan girman Allah Ya Abdul-Hakeem!" Fadin Khalil yana kuka sosai. "Wallahi ba zan bari ka rage mata nauyi ba. Ɗan yatsarka ɗaya ma ba zan bari ya kuma taɓata ba." Ya faɗi tare da kama hannunsa ya fito da shi daga ɗakin sannan ya jawo karyayyan ƙofar ya rufe. Ƙasa suka sauka inda Hajiya take tana kuka sosai, idanunta sun kaɗa sunyi jajur tuno autarta Nafeesa. Kallon Khalil Hajiya tayi tare da faɗin, "Kaga sakamakon rashin ji ko Khalil? Da ace baka ɗurawa ƴar mutane ciki ba, yaushe har wannan bala'in zai shigo cikin gidan mu. Ka kwaso mana dangin matsafa, dangin masifa da bala'i cikin gidanmu muna zaune lafiya! Me za ayi da irin wannan tsinannen zuri'a, wallahi haɗa zuri'a da irin yarinyar nan mafisa ce babba rayuwa, ina jin dama ace ban haifeka ba Khalil, da duk haka bai faru damu ba. Sanadinka rayuka da dama sun salwanta, ƴata, autata Nafeesa ta kashe min ita, ta ashe ƴarta wacce idan ina ganinta zanji sanyi, ta kashe mijin, ta kashe kowa! Allah ya isa tsakani na da wannan ƴar iskan yarinyar. Ibrahim, aurenka da Saratu bai amfane mu da komai ba sai bala'i da masifa, kuma ka rubuta ka ajiye, idan har nice nayi naƙuda sannan na tsuguna na haifeka, ba amince maka ka dawo da Saratu cikin gidan nan ba, ƴaƴa kuma a dawo dasu zan riƙe!"
_Wacece take ganin Hajiya bata kyauta ba? Ni dai na fahimci ciwon da take ji_ 😬🤐
*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*
_MATAR SAYYADEE_
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*37*
Hajiya na gama faɗin haka ta miƙe ta fita fuuu tana sharar hawaye. Khalil kuwa mutuwar tsaye yayi a wajen yana jin wani irin matsanaicin bugun zuciya kamar zata faso ƙirjinsa ta fito, Abdul-Hakeem kallonsa yayi tare da ɗaga hannunsa yana shafa ƙirjinsa alamar he should calm down sannan ya fita ya bi bayan Hajiya. Aunty Maryam ƙarisowa tayi kusa da Khalil tare da faɗin, "Khalil ka kwantar da hankalinka, in Sha Allah Hajiya zata sauko. Maganar laifi kuma, ba laifin Sarah bane, Sarah bata da laifi akan abinda Aina'u ta aikata, ita kanta Sarah ai Aina'un ta cutar da ita, don wannan tsutsotsin da ta riƙa fitarwa warin nan ai babbar cutarwa ce! In Sha Allah hajiya zata sauko, don tabbas babu laifin Sarah a cikin abinda Aina'u ta aikata, kuma wallahi ko da ba Sarah ka aura ba, Aina'u sai ta shigo cikin gidan nan ta wata hanya daban ta cutar damu don hakan rubutacce ne a cikin ƙaddarar mu, kuma muma duk muna da namu laifin na sake da muka yi da Allah muka kama jin daɗin duniya, mun manta da azkar da karatun Alƙur'ani wanda Alai ya gina a cikin gidan nan, mun ɗauka kawai salloli biyar da azumin watan Ramadan ɗin da muka riƙe kawai sune dolen mu. Wannan izinace a gare mu dukanmu. Amma tabbas Sarah bata da laifin komai, kuma ina ji a jikina zata sauko nan kusa, yanzu dai shawarar da zan baka itace, tunda har Hajiya tayi fushi haka har ta furta waɗannan kalamai, ka kyaleta na wasu lokaci, kar ka kuskura ka tunkareta da maganar, ka bari har ta huce tukun." Gyaɗa kai Khalil yayi tare da faɗin, "Shikenan, Nagode Aunty Maryam!" Yana faɗin haka ya fita ya bar ɗakin, side ɗin Hajiya ya koma ya nufi ainahin ɗakinsa dake sashen, buɗe Ƙofar
Showing 114001 words to 117000 words out of 129453 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39 Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44