ɗaga sama tare da faɗin, "Ubangiji mahaliccin sammai da ƙassai, mai kowa mai kome, ga bawanka nan Ibrahim, ka kiyaye shi daga sharri da tsafin Aina'u, ga kwato shi daga hannun azzaluma mara imani Aina'u, ya Hayyu ya Ƙayyumu, alfarman soyayyar dake tsakaninka da mafificin halitta, Muhammadur Rasulullah (SAW) ka ceto mijina daga halakar Aina'u ya rabbis samawati al'ardi." Ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka. Juyawa tayi ta kai hannu kan handbag ɗinta dake kan gado tare da buɗe zip domin ta ɗauko wayarta, a firgice ta soma zazzage jakarta tana neman wayarta mai tsada da Khalil ya canza mata ranar da suka yi celebrating first anniversary ɗinsu bayan haihuwar twins. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Wallahi to duk yanda aka yi a tasha aka sace wayar nan, shikenan I missed everything including our history pictures!!" Faɗin Sarah tana mai fashewa da kuka, don sam ba satar wayar bane yafi tsaya mata a rai, hotuna da videos ɗin dake cikin wayar ne wanda dawowarsu zai yi matuƙar wuya ke mugun bata takaici. Jin alamar ana nufo ɗakin sai tayi saurin goge hawayenta tana mai ƙirƙirar smiling face tana ɗaurawa a nata fuskan. "Assalamu alaikum, Maman twins kin idar?" Faɗin Suhana, ganin Sarah a zaune sai ta juya ta koma parlourn, can sai gata da abincin a rufe a plate, murmushi Sarah tayi mata tare da faɗin, "Nagode Suhan." Murmushin itama Suhan ɗin tayi mata tare da faɗin, "Bari naje parlour wajen su twins, don har yanzu basu gane bake bace ba." Ta faɗi hakane tare da miƙewa ta fita. Bayan fitan ta, Sarah sai ta buɗe plate ɗin, alalen gwangwani ne yaji miyan source da hanta. Guda ɗaya kawai Sarah ta iya ci ta rufe, don da kyar take haɗiyewa saboda damuwar dake cinta a rai, data rufe idanunta, Khalil kawai take gani yana yi mata gizo, idan ta tuna lokacin da suke farin ciki kamun zuwan Aina'u, sai taji daɗi har sai hakan ya bayyana a fuskanta, idan kuma ta tuna baƙin cikin da Aina'u ta ƙunsa mata, sai taji hawaye na wanke fuskanta. Wani ƙaramin ƙur'ani ta gani irin mai zip ɗin nan a side drawer, hannu ta kai ta ɗauko tare da zuge zip ɗin ƙasa, ajiyar zuciya ta saki tana mai ƙoƙarin tuna when last ta riƙe ƙur'ani a hannunta ta karanta, kuka ta fashe dashi ganin ta kasa tuna wani lokaci ne na ƙarshe data ɗauki Qur'ani domin karatu, ko a can gida sai dai idan zata goge ta saka masa turare take ɗauka, amma bayan haka kam, bata ɗauka domin niyyar karatu, har akai azumi guda biyun da tayi a gidan Khalil, bata taɓa karatun ƙur'ani ba, sai dai ana yin asham wani lokacin har da tahajjut kasancewar masallacin a cikin gidansu Khalil ɗin yake, "Dole ko mai aka yi mana ya kama mu tunda mun saki Allah mun kama Duniya!" Faɗin Sarah cikin zuciya. Suratul Yusuf ta buɗe ta soma karantawa don surar na ɗaya daga cikin surorin da take matuƙar so a cikin Alqur'ani don sai da ta haddace tsaf amma rashin muraji'a yasa duk ya zube, suratul Ma'ida, Maryam, Buruj da Nisa'i, don Nisa'i ma gaba ɗaya surar ta haddace ita da Kahfi, don lokacin da suke tashin ƙawance da Muneeba, duk juma'a sai sun sauketa don musaffa suke yi. Sarah bata iya baccin kirki ba, Allah yaso ma Suhan tazo tayi mata sallama a kan tare zasu kwana a ɗayan ɗakin ita da ƴan biyu, ita kuma Sarah anan ta kwana ita kaɗai, sai dai rabi da kwata na cikin daren, raya shi tayi da tsayuwan dare saboda ta kasa baccin. A idanunta akai sallar asubah, abunda yayi matuƙar burgeta a gidan shine, tun bayan saukowar masallaci take jin sautukan ƙira'a mabanbanta na Alkur'ani cikin muryoyin maza da mata ya ɗume gidan, sai kawai itama ta hau karatu da wannan ƙur'anin data gani a ɗakin. Sai ƙarfe takwas daidai taji gidan ya ɗauki tsit, sai itama ta saka aya sannan ta rufe ƙur'anin tana mai yin sujada ɗon ta tsaya ne a kan ayar da ake sujada. Suhan ce ta shigo ita da twins har anyi masu wanka amma sun ƙi yarda ko wando ta saka masu, akwatin kayansu Sarah ta buɗe tare da fiddo kayansu ta mikawa Suhan ɗin tare da rufe akwatin ta miƙe tsaye tana nannaɗe dardumar, "Maman twins ki fito za muje muyi breakfast, you will be shock idan muka shiga side ɗin Nnanne." Ba tare da ta cire hijjab tabi bayan Suhan data rigata fita, Sarah tayi mamaki ganin duk da twins sun ganeta amma basu ƙoƙarin gudu daga wajen Suhan ba duk ƙiwarsu. Bata taras da kowa ba a parlourn, duk sun hallara ɗakin Nnanne, "Ina su Ba Lukman?" Faɗin Sarah, "Suna can ɗakin Nnanne." Suhan ta bata amsa tare da fita both hannunta na ɗauke da twins. "Da kin ajiyesu su taka da ƙafursu, sai baki wahala suke yi." Faɗin Sarah, su kuwa twins najin haka suka ƙare lafewa a jikin Suhan, Suhan Kuma cewa tayi, "Ai wallahi ban sauke su." Dariya kawai Sarah tayi don ta lura Suhan ɗin na matuƙar ƙaunar twins, itama sai taji tana ƙaunar Suhan ɗin. Sun ɗan yi tafiya kamun suka iso sashen Nnanne da yake da girman ban mamaki, ga uban uban takalma birjik a ƙofar ɗakin na maza da kuma na mata. Sallama su Sarah suka yi kamun suka shiga ciki, da maɗaukakin mamaki Sarah ta take kallon jama'ar dake ɗakin suna zazzaune akan ƙatuwar carpet ɗin dake shimfiɗe a ɗakin sun zagaye wata farar tsohuwa mai mugun kwarjini da kuma kamala kasancewar mai riko da ibada, ta tsufa sosai, amma babu ruɗewa a tattare da ita saboda zuciya da gangan jikinta sun ginu ne akan Addinin Allah cikin tafarkin _SUNNAR MA'AIKI SAW_. Suna shigowa gaba ɗaya idanu ya koma kan Sarah da kuma ƴan biyu dake hannun Suhan, gyaran muryan Nnanne tayi, sai koma ya dawo cikin nutsuwarsa don sun san dokar, babu mai magana har sai an kammala cin abinci kamun nan ake gabatar da meeting na tsawon awanni biyu rak, a dunƙule Sarah ta gaishe da duk manyan wajen, cike kuma da sakin fuska suka amsa mata gaisuwarta sannan suka nemi waje suka zauna, daga nan ƴan aikin gidan wanda a ƙalla sun kai ashirin suka gabatar da abinci, daga kowa yayi serving kansa, tunda aka fara cin abinci babu wanda ya ƙara ko kwakwkwarar motsi har suka kammala sannan ƴan aiki suka ƙara zuwa suka kwashe komai. Nnanne kuwa tun da takai lomar abinci ɗaya baki take kallon Sarah har ta kammala baya yi cokali biyar kwarara ba. Shuru gaba ɗaya ɗakin yayi ana jiran Nnanne ta soma yin magana don hakane zai bawa Kowa damar yin magana, ita kuwa Nnanne taƙi magana sai kallon Sarah da take yi kawai babu kyaftawa, "Yarinya!" Ta faɗi slowly still tana kallon Sarah. A hankali Sarah ta ɗago tana kallon Nnanne, nan take taji wasu irin ruwan hawaye na kwaranyo mata akan fuskanta ganin gaba ɗaya ɗakin nan da take duk yawansu ƴan uwan mahaifinta ne. "Yarinya daga ina, kuma ke wacece?" Nnanne ta kuma jeho mata wata tambayar, Sai da Sarah taja majina kamun tace, "Sunana Sarah, mahaifina kuma sunansa Nuhu kuma a nan gidan aka haifesa." Ta faɗi hakan tana mai nuna Ba Nura (Mai kama da Baba Nuhu) tare da cigaba da faɗin, "Sak haka Babana yake" ta ƙarisa maganar tare da rushewa da kuka tuno halin da Baba yake ciki na mutum-gawa. Wani irin ajiyar zuciya Nnanne tayi tare da soma goge hawayen da yake shirin zubowa, matan ɗakin masu raunin zuciya har sun soma kuka, Nnanne miƙawa Sarah hannu tayi alamar ta taho kusa da ita, da rarrafe Sarah ta ƙarisa tare da rungumeta ta fashe da tsumamman kuka wanda ya taɓa zuciyar mutane da dama dake ɗakin. "Ina ɗana? Ina kika baro min Hussaini na!" Faɗin Nnanne cikin kuka. Ƙara kwakwuneta Sarah tayi tare da faɗin, "Ina can Kaduna, Yana can Nnanne kullum bashi da magana sai taku, duk lokacin da zai bani labarinku, cemin yake yi ba zai iya haɗa idanu daku ba saboda abunda ya aikata maku. Nnanne baba yana can kwance kamar gawa, ba magana babu motsi!" Sarah na kowa nan sai ta kuma fashewa da kuka sosai har tana ƙanƙame jikinta duk kukan gaba ɗaya da biyu take yinsa, tunowa take da halin da Baba yake ciki da kuma halin da take ciki yanzu, sai kukan ya zama biyu. Kuka Nnanne ta fashe dashi wanda ya tada hankalin dattijan dake ɗakin sai duk suka taso suka zagayeta suna bata baki. "Na janye dokar da na saka akan Hussaini, na janye wallahi. Kuje ku taho da ɗan uwanku, kuje Hassan ku taho dashi. Ina son ganinsa kamun na koma ga Allah. Na yafe masa har abada, na yafe maka Nuhuna." Ko wannensu sai da ya share guntun hawaye. Ba Lukman kuwa wani irin farin cikine ya lulluɓesa yana mai jin daɗin saukowar Nnanne, domin ba dadun ita ba, da tuni sun nemi Baba Nuhu a duk inda yake." Hannun Nnanne a kan Sarah tare da faɗin, "Jikanta kuma takwarata, bani labarin ɗana Nuhu!" Gyara zama Sarah tayi tare da faɗin, "Nnanne idan har kina da ƙarfin zuciyar ji, to ki saurareni sai dai labarin Babana ko kuma ince maki dukkanmu, ba labari bane mai daɗin ji!" Gaba ɗaya ɗakin wani irin tsit yayi na wasu daƙiƙu kamun Sarah taja wani numfashi tare da soma faɗin...., "Tun da nake ban taɓa ganin mutum mai haƙuri da sauƙin kai kamar mahaifina ba, mu shidda ya haifa mata sai namiji ɗaya, Na'ima, Nuratu, Hassana, Lukman (Tana faɗin sunan Lukman, Ba Lukman ya ɗago don ya san tabbas shi akai wa takwara) Marfu'a, Ni Saratu da kuma autarmu Aina'u......." Tun daga karayar arzikin baba, taɓarɓarewar tarbiyansu Na'ima da irin karuwancin da suka zuba sanadin huɗubar Lami, lalacewar Lukman, sanadin shiga islamiyarta, aikin da tayi a restaurant wanda shine sanadin haɗuwarta da Khalil, cikin da yayi mata zuwa zubewarsa, gwagwarmayar da aka yi kamun auran da kuma auren, farin cikin da ta samu a gidan zuwa ciwon da tayi na tsutsa da irin kulawar da Khalil ɗin ya bata har zuwan Aina'u gidan, haihuwarta, ciwon Baba (duk da bata faɗa masu sanadi ba don itama bata sani ba) da kuma iskanci da mulkin da Aina'u ta zuba har izuwa sanadin barowarta kaduna duk sai da ta zayyane masu tana kukan fitar hayyaci. Ba ita kaɗai ba, gaba ɗaya ɗakin yara da manya kuka suke yi, "Haka Nuhu yaga rayuwa? Yanzu ƴaƴan Nuhu ne suka yi karuwanci har da ƴaƴan shegu! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!!" Faɗin Nnanne tana mai dafe saitin zuciyarta, ɗaya hannunta kuma yana riƙe da hannun Sarah dake kuka. Gaba ɗaya ɗakin babu wanda bai ji mugun tausayi Sarah ba jin halin bala'in data shiga sanadin ƙanwarta ciki ɗaya! "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Nnanne!!" Ba Lukman ya faɗi da ƙarfi ganin Nnanne zata dungura don suma tayi. Nan da nan suka kwashe ta zuwa asibiti. Sai da Hajiya tayi sati tana jinya kamun aka sallame don jininta ne ya hau sosai, Sarah kuwa taga ƙaryar wani abu wai shi dangi, don kuwa irin jama'ar dake tururuwar zuwa ganinta sunfi ƙarfin a ƙirga, wannnan ya jata riiii zuwa gidansa, sai wancen ma yaja. Ɓangaren Hajiya kuwa, tun bayan tafiyar Sarah da kwana biyu wanda bata ma san bata gidan ba ta tashi tsaye sosai akan roƙon Allah, waya ta buga Maiduguri tare da faɗin buƙatunta wajen wani babban malamin musulunci tace a haɗa almajirai suyi mata sauka zata turo da abun sadaka ta waya, sannan ta kira malamin da yake masu saukar Qur'ani tun lokacin da Alai yake da rai, ta faɗa masa buƙatunta, kasancewar girma yà kama shi sosai, sai ya saka ƴaƴansa da almajirasa suka cika gidan Hajiya da karatu, ranar ba'a gidan Aina'u da Khalil suka kwana ba, ihu ta riƙa masa a kan su bar gidan, sai da aka haɗa kwanki goma ana sauka a gidan tare da buɗe gidan da hayaƙin shaiɗanu. A rana ta goma sha huɗu, Aina'u ta taso Khalil suka dawo gidan, kai tsaye ɗakin Hajiya ta nufa tana kwala kiran, "Bilkisu! Bilkisu!! Ki fito nan tsohuwar munafuka annaminiya" tana tafiya hannunta riƙe dana Khalil har parlourn Hajiya, da sauri Hajiya ta fito tana ƙarewa Aina'u dake riƙe da hannun Khalil kallo, "Menene haka nake gani Khalilullah!" Hajiya ta nuna hannun Aina'u dake riƙe dana Khalil fuskanta ɗauke da mamaki, " _ƙanwar matarka_ ce fa Ibrahim!" Wani wawan harara Aina'u ta jefi Hajiya dashi tare da yin wani irin dariyar ƴan iska sannan wani janyo Khalil ɗin tare da riƙo kansa ta haɗe bakinsu waje ɗaya. Da sauri Hajiya ta rintse idanunta gabanta na wani irin bugawa tana istigfari cikin zuciya. "Wallahi kika ƙara yin magana akan alaƙata da ɗanki, yanzu gabanki zan sutale masa wando kuma kina kallo zai yi amfani dani, wata ƙila na har rabo ya shiga tsakani!" Wasu irin zafafan hawayene suka shiga kwaranyo daga idanun Hajiya har tsikar jikinta na tashi, "Na taso maki da sha'awar shekaru ko? Kar ki damu idan ƙaiƙayi yake maki, inada mutane dai-dai dake da zasu iya biya maki buƙata." Wani irin kuka Hajiya ta fashe dashi mai ƙarfi kuma har wannan lokacin idanunta a rufe suke, "Ibrahim a gabanka, a gabanka _Ƙanwar matarka_ take faɗa min irin wannan maganar amma ka kasa ko tari mai ƙarfi, a gabanka Mu'azzam!!" Hajiya ta faɗi tana kuka. Khalil kuwa tunda ya sunkuyar da kanshi a ƙasa hawaye masu uban gudu suke sauka a akan tiles, ya kasa ko ɗagowa, jikinsa ne kawai ke karkarwa. "Ba kukanki nazo inji a nan ba, zuwa nayi inyi maki kashedi akan kar ki kuskura ki kuma kiran wasu ƴan iska gidan nan suzo suna yin tsaface-tsaface, kinji ko baki ji ba?" Wani irin haske ne ya gilma a fuskan Aina'u har sai da taji shock, Hajiya ta nuna mata ƙofar fita tare da faɗin, "Wa ya haifi ubanki da har zaki shigo cikin gidan ChiefJustice Nurudden kice zaki bawa matarsa order, fita kamun na saka a ƙarar da zuri'ar ku!" Hajiya ta faɗi a tsawace. Baya Hajiya tayi zata faɗi saboda wani gigitacen mari da Aina'u ta ɗauketa dashi tare da faɗin, "Kul! Kika ƙara ɗaga hannunki a jikina. In kwanta da ɗan naki in bashi natsuwa har sai da ya manta sunanki, shine zaki saka min da mari, ƙarya kike yi wallahi!" Hannu dafe da kunci Hajiya ta kalli Khalil da ya tarota tare da zaunar da ita a kan kujera, "Khalil har lalacewaka ta kai haka? A gaban idanunka _Ƙanwar matarka_ ta ɗaga hannu ta mare Ni." Jikin Khalil wani irin rawa yake yi har naman jikinsa na ɗagawa haƙorinsa na haɗuwa dana juna a lokacin guda gashin dake kwance a jikinsa suna wani irin mimmiƙewa, idanunsa kuwa sun koma wani irin abun tsoro saboda yanda suka kaɗa sukai jazur............
*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*
_MATAR SAYYADEE_
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*36*
Ganin yanda gaba ɗaya yanayinsa ya canza, sai ta soma ja da baya kaɗan-kaɗan tana kuma murza tafin hannunta a lokaci guda, sai dai gabanta ne ya yanke ya faɗi da ƙarfin tsiya jin bata ji wannan sanyin da ta saba ji ba a duk lokacin da ta murza tafin hannun, da saurin ta fiddo tafin hannun tana kallo gabanta na wani irin zullon tashin hankali, "Na shiga uku tafin hannuna yayi baƙi!" Ta faɗi da ƙarfi ganin har hayaƙi yake yi, a dai-dai wannan lokacin ne kuma Khalil ya wani irin shaƙo wuyanta tare da ɗagata ya buga a ƙasa dai-dai lokacin da Laure ta shigo parlourn da gudu tana faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Hajiya hayaƙi a ɗakinki." Cak ta tsaya tana mai kai hannu kan maƙogwaronta tare da kallon Hajiya da itama take kallonta cikin tsantsan mamaki da kuma farin ciki. Laure nuna bakinta tayi sannan ta nuna Hajiya cikin mamaki, hajiyan sai ta gyaɗa mata kai alamar eh tabbas taji fitar muryanta. Kuka Laure ta fashe dashi tare da kai goshinta ƙasa tayi sujada. Khalil kuwa wani
Showing 111001 words to 114000 words out of 129453 words
*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*
_MATAR SAYYADEE_
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*36*
Ganin yanda gaba ɗaya yanayinsa ya canza, sai ta soma ja da baya kaɗan-kaɗan tana kuma murza tafin hannunta a lokaci guda, sai dai gabanta ne ya yanke ya faɗi da ƙarfin tsiya jin bata ji wannan sanyin da ta saba ji ba a duk lokacin da ta murza tafin hannun, da saurin ta fiddo tafin hannun tana kallo gabanta na wani irin zullon tashin hankali, "Na shiga uku tafin hannuna yayi baƙi!" Ta faɗi da ƙarfi ganin har hayaƙi yake yi, a dai-dai wannan lokacin ne kuma Khalil ya wani irin shaƙo wuyanta tare da ɗagata ya buga a ƙasa dai-dai lokacin da Laure ta shigo parlourn da gudu tana faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Hajiya hayaƙi a ɗakinki." Cak ta tsaya tana mai kai hannu kan maƙogwaronta tare da kallon Hajiya da itama take kallonta cikin tsantsan mamaki da kuma farin ciki. Laure nuna bakinta tayi sannan ta nuna Hajiya cikin mamaki, hajiyan sai ta gyaɗa mata kai alamar eh tabbas taji fitar muryanta. Kuka Laure ta fashe dashi tare da kai goshinta ƙasa tayi sujada. Khalil kuwa wani
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38 Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44