halittar ubangiji. Kuma dai nafi matar kyau." Juyowa yayi gaba ɗaya ya kalleta daga sama har ƙasa tare da faɗin, "Eh Lallai babu shakka." Sai kuma ya bushe da dariya tare da faɗin, "Ga shawara idan zaki ɗauka, kije kuyi shawara ke da mai gadi ya samo ƙatuwar keji ya ajiye a ƙofar gate, bayan kin gama aikinki na cikin gida sai ki fita waje ki shiga kejin nan, wallahi ba ƙaramin kuɗi zaki samu ba, don duk wanda ya zo wucewa sai ya ajiye maku kuɗi." Kuka ta fashe dashi tare da faɗin, "Sai kace wata biranya zan shiga keji. Kuma turaren ma ba'a so." Tana gama faɗin haka ta juya Sarah tayi saurin kai hannu zata riƙota _Khalil_ ya riƙe hannun tare da faɗin, "Tsaya ki sha kallo." Sai da ta kai bakin ƙofa sannan ta juyo tare da faɗin, "Baza ka bani haƙuri ba? Ke kuma amarya ko ɗan irin cin-cin ɗin nan ma baza ki bani ba. To wallahi ban fita ko ina sai an bani turarena da cin-cin." Kallon juna _Khalil_ da Sarah suka yi suka fashe da dariya. _Khalil_ yace, "Ahaf, ba na faɗa maki ba. Ai mayya ce! Idan ban bata turaren ba sai ta lashe kurwata!" Murguɗa baki tayi tare da faɗin, "Eh naji ɗin komai zaka ce kace idan har za'a ban turaren." Kiss yayi ma Sarah a kumatu tare da faɗin, "Ina zuwa love, bari na ɗauko mata ta wuce ta bamu waje." Gyaɗa kai kawai Sarah tayi. Yana wucewa Laure ta matso kusa da Sarah tare da faɗin, "Wallahi ke kyakkyawa ce. Kin ganki kuwa? Wane kajuli (Kajol) ta ƙasar hindiya. Gaskiya ya _Khalil_ ya iya zaɓe yasin. Ku wani yare ne?" Murmushi Sarah tayi tare da faɗin, "Babana ɗan Nasarawa ne a wani ƙauye da ake kira _Wamba_" Riƙe haɓa Laure tayi da faɗin, " _Wamba_? Ni ban ma taɓa jin sunan garin ba. To mamanki fa?" Ko kamun ta bata amsa suka ji saukowar _Khalil_ hannunsa riƙe da kwalin turare guda biyu. Washe baki Laure tayi tare da faɗin, Alhamdulillahi ni Laure! Nagode ya Ibrahim" ta faɗi tun kan ya miƙa mata turaren. Taɓe baki _Khalil_ yayi tare da miƙa mata yace, "Sai a sakar min mara inyi fitsari." Amsa tayi bakin yaƙi rufo, haƙoran sunyi cirko-cirko a waje. "To, to a wuce a bani waje." Sai da ta kai ƙofa sannan tace, "Aunty Saro, sai nazo dan ya _Khalif_ ya fita." Da ƙarfi Khalil yace, "Kika ƙara kiran matata da wannan sunan sai na cire shegun haƙoran nan. Kuma kar in sake inga ƙafafunki a ɗakina." Dariya Sarah tayi tare da faɗin, "Amma ya kuke da ita?" Sai da ya kulle ƙofar ya saka key sannan ya dawo inda take ya rungume ta sannan ya ce, "ƴar uwa ce, lokacin da Hajiya taje Maiduguri aka haɗo ta da ita domin ta riƙa taimaka mata da wasu ayyukan. Ance dai abokiyar wasan mu ce, ban dai san asalin yanda muke da ita ba." Sarah tace, "Hajiya ƴar Maiduguri ce ko?" Zama yayi a kan kujera ya ɗaurata a kan cinyarsa tare da faɗin, "Mahaifinta Shuwa ne, mahaifiyarta kuma Kanuri, kuma duka tana jin yaren." Kallonsa tayi tare da faɗin, "Kai fa, kana jin yaren?" "Gwada yara min naji ko zan iya mayar maki?" Faɗin _Khalil_. "To ai ni ban iya ba." Sarah ta faɗi. Kwanto da kanta yayi a kan ƙirjinsa tare da faɗin, "Kar ki damu, wata rana zaki san ko inaji ko ban ji." "To baba fa, wani yare ne?" Sai da ya nuna kansa Sannan yace, "Babana?" "Eh babanmu." Ta bashi amsa tana nuna ita dashi. "Sorry babanmu har dake. Shi kuma Mahaifiyarsa bafulatana, mahaifinsa Kanuri." "Kai Kanuri ne kenan?" Faɗin Sarah. "Kwarai da gaske!" Ya bata amsa tare da miƙar da ita zuwa dinning sannan ya ɗauko basket ɗin da Laure ta kawo abinci ya ajiye a kan dinning ɗin sannan ya koma kitchen ya ɗauko kwan da ya soya. "Ni na soya wannan da kaina. Ci kiji?" Faɗin Khalil cike da farin ciki don ya soya kwai. Sarah kuwa tun kallon farko da tayi wa kwan taga tsakiya ya babbake. Hannu ta kai ta ɗan yago gefe inda bai ƙone ba ta saka a baki. Da sauri ta furzo shi jin magi har kwakwalwar kanta. "Ya dai?" Faɗin Khalil bayan yayi saurin zuwa inda take. Bata ce komai ba ta yanko ta saka masa a baki. Dakyar ya iya juriya ya haɗiye yana yamutsa fuska. "Wai wai wai! Daɗi!" Faɗin Khalil yana yin haka👌da hannu. "To maza cinye shi!" Ta faɗi tana masa tuni da plate ɗin da idanunta. "Kiyi haƙuri na kaiwa Madhu itama taci. Don duk abunda na saka a baki itama sai ta ci." "Wacece kuma haka?" Tayi saurin faɗa. Shi kuma yace, "Madhubala wutar kyau, masoyiyata kenan?" Tuni annurin fuskanta ya canza ta tsaya kawai tana kallonsa. Kumatunta yaja tare da faɗin, "Kishi, to mage na ce wacce na ɗauko all the way from Paris. Zaki sota sosai idan kin ganta. Very beautiful." Sai a lokacin ta saki fuska tare da faɗin, "Laa! Kaman ka san ina son mage sosai. Tana ina?" "Tana side ɗin Hajiya. Idan mun gama karyawa zan kai ki, ki gaida Hajiya sai mu ɗauko abun mu daga nan." Ya faɗi hakane tare da soma serving ɗinsu a plate ɗaya. Yana bata a baki tana bashi har suka kammala sannan suka kwashe kayan tare suka kai kitchen yana wanke-wanke tana ɗauraya har suka kammala. Towel ya ɗauko ya goge mata hannu dashi sannan suka fito parlour. "Bari na ɗauka maki babban mayafi sai muje wajen Hajiya." Ya faɗi hakan tare da nufar sama. Mintuna kaɗan ya dawo ɗauke da gyale. Da kanshi ya soma nannaɗa mata gyalen a kai dai-dai lokacin da suka ji door bell. A tare suka kalli ƙofar, sai da ya gama saka mata sannan ya nufi ƙofar ya buɗe. Ido huɗu suka yi da Aina'u tana sakar masa murmushi.



*KIRA ZUWA GA MARUBUTA*

_A matsayinka na ɗan Nigeria bai kamata kayi murnar Independence ba, bai kuma kamata kabar wani yayi ba!_
_dalilina kamarhaka_
_a satin daya_ _gabata an sace ɗalubai a jahar Zamfara, an kashe wasu a sakkoto, An harbe wasu a cikin Jos, a kaduna kuwa an tare jirgin ƙasa an kwashe mutanen cikinsa wanda har yau ba'a san inda sukeba!_
_kai yanzu ko tafiye tafiyen da akeyi da an daina saboda irin wannan matsalolin!_
_Kuma duk haka yana Faruwa ne saboda sakacinmu na mutanan AREWA, ko har kun manta da ƴan matan da aka sace a cikin jahar Barno state a shekarar 2014 su ɗari biyu da sabai'n da shida?!, ƴan matan ƴan matan chibok, toh haryanzu ba'a san inda saura suke ba..._
_Idan mukace AREWA muna magana ne da ƴaƴan cikinta waɗanda suka sami ɗaukaka koya take kama daga Ƴan social media, ƴan film, mawak'a, masu shirin barkwanci, tare da_ _*Marubutan mu*, mu taso mu buɗe baki muke_ _magantuwa, muyi amfani da wannan damar ta social media, kuna ganin celebrity ɗin nan na kudu daya mutu zargi suke akan kashe shi akayi ba tabbatarwa ba, amma ji yadda abun ke yawo a ƙasa baki ɗaya!_
_mu kuma ƴaƴa mata ake kwasa ake shiga jeji dasu, banda tsadar rayuwa, da azaba da ƙuncin da muke ciki, kidnapping, kwace, Haure, ana kashe mana ƴan uwan mu ɗaruruwa batare da munce komaiba!_
_shin da mukayi shirun gajiya_ _sukayi suka daina ko kuwa abin ta'azzara yayi?_
_a matsayinki/ka na *Marubuciya, Marubuci* ƴan AREWA ga dama tasamu, masu novel na kuɗi dama free, masu ɗaukakar cikin mu dama sabbin tasowa, magana ake aji murya iri ɗaya gabaɗaya a social media a yau first October dan already no more Independence, Dan girman Allah kar mu raina abin da zamuyi, koda baƙya update na novel kiyi koda shot writing akan matsalar dake faruwa!_
_kar mutsaya sai abi yazo kan ƙanwarka ƙanina babana ko mamana, Kaduna Zamfara Barno Kano da dukkan arewa muɗin duka abu ɗayane, dan Allah marubata mufito ƙwanmu da ƙwarƙwata mutaya ƴan uwanmu ƴan_ _social media isar da saƙo, tunda mu baiwar rubutu_ _ubangiji ya bamu muyi amfani da ita wajan yin gƴara._
_ubangiji yayi mana Jagora ya Allah ka sakawa duk wacce tayi ƙoƙarin tallafawa da gidan Aljannatul-Firdausi_.


*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_MATAR SAYYADEE_*

*Paid book 08128755583*
[10/2, 8:21 PM] AMINA KABIR CAPS: 🦜 *KANWAR MAZA* 🦜

*22*


Da sauri Sarah ta ƙariso wajen tana faɗin, "Lah, Ai'n kece? Shigo mana kin tsaya a waje kamar baƙuwa. Ke ɗaya ce?" Hanya Khalil ya bata ta shigo tare da faɗin, "Bamu san da zuwanki ba, ashe kina tafe" kai tsaye yayi maganar don har ga Allah bai so zuwanta ba don zata shiga haƙƙinsa na rashin bashi damar kasancewa da matarsa. Da kallo ta bishi tana ji kamar rungumesa saboda ƙaunarsa dake fuzgarta. Shi kuwa Khalil komawa yayi ya zauna tare da ɗaukar remote ya kunna tv ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya. "Ai'n mai zaki ci? Ki zauna mana." Wani kallo Khalil ya watsawa Ai'n ɗin tare da maida kallonsa izuwa ga Sarah yace, "Babe, ba girkin da za kiyi, saboda ban so kiyi stressing kanki shiyasa na fita da kaina na haɗa maki breakfast. Ohh nama manta, akwai sauran abincin da Aunty Maryam ta aiko mana dashi gashi can a dining. She should go and serve herself kamun mu dawo daga cikin gida wajen hajiya. Let go wife!" Ya faɗi hakan tare da kama hannun Sarah ya saka cikin nashi. Kallonta Sarah tayi tare da faɗin, "Aina'u bari muje mu dawo. Hajiya zanje na gaisar in dawo yanzu." Yaƙe tayi tare da faɗin, "Ok sai kun dawo." Suna fita Khalil ya saki tsaki tare da faɗin, "Killjoy?" "Wa?" Sarah ta tambaya tana kallonsa. "Ƙanwarki mana. Bata iya zuwa gidan amare ba. Ita da ake bari sai irin bayan sati biyun nan, duba fa ki gani ko 12:00 bai yi ba. Ni dai wallahi an shiga haƙƙina. Ɗaukar hutun wata guda nayi domin in huta tare da matata, amma naga alama ana son hanani more amarcina." Tsungulinsa tayi a hannu har sai da ya furta, "Auch! Mai nayi maki?" "Duk fa wanda zai zo ba kwana zai yi ba, dole zai tafi ya bar mu tare, to menene abun damuwar bayan we will always sleep together babu mai raba mu?" Cak ya tsaya yana kallonta tare da faɗin, "Haba, dagaske? Za ki biyani duk bashin soyayyar da aka hanani nunawa da ranar?" Dukan kafaɗunsa tayi tare da faɗin, "Wallahi happiness kana da negative mind. Ni ba abunda nake nufi kenan ba." "To ni kuma kinga abunda nake nufi kenan." Faɗin Khalil. Da sauri tayi gaba saboda kunyar da ya bata. Haɗawa yayi da gudu ya isketa tare da faɗin, "Yarinya kina da aiki, wai kunyata kike ji? Taɓ, kina ruwa can gaban breaker." Cak ta tsaya kasancewar sun iso daidai ƙofar part ɗin Hajiya. Shi ya ƙarisa tare da murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga bakinsa ɗauke da sallama. Gaba ɗayansu suna parlour ana hira, Hajiya, yaya Abdul-Hakeem, yaya Muhammad Kabir, Aunty Maryam, aunty Khairat, aunty Zakiyyah matar yaya Abdullahi, Nafeesa, Aysha, Laure, Aunty Jamila autarsu uncle Ameeru, sai ƴaƴansu da kuma kaɗan daga cikin sauran mutanen Maiduguri da basu koma ba. Juyawa Khalil yayi tare da faɗin, "Babe, shigo mana." Da sauri Aunty Khairat ta tsunguli aunty Maryam jin sunan da Khalil ya kira Sarah dashi suka bushe da dariya. Ita kuwa Sarah a kunyace ta shigo ɗakin kanta na kallon ƙasa ƙafafuwanta na harɗewa. Har ƙasa ta duƙa tare da faɗin, "Hajiya ina kwana?" Da murmushi a fuskar hajiya ta amsa tare da faɗin, "Zo taho nan kinji ƴata." Zama tayi kusa da ƙafafun Hajiya a kan capet sannan tabi kowa ɗaya bayan ɗaya ta gaida su, kowa ya amsa fuska cike da fara'a babu nuna wani kyara ko wulaƙanci. Khalil ɗin ma gaida waɗanda suka girme shi yayi, wanda ya girma kuma suka gaida shi. "Yayanmu ka iya zaɓe fa wallahi." Faɗin Nafeesa tana ƙara leƙo fuskan Sarah. "Kun san ni komai nawa mai kyau ne shiyasa matata sai da na hanga na waiga na zaɓota zuƙeƙiya gata nan." Aunty Zakiyyah matar ya Abdullahi tace, "Gaskiya Ibrahim baka da kunya, a gaban yayyin naka nake irin wannan magana haka." "To Aunty kuma ni mai nace? Yabon matata fa kawai nayi." Faɗin Khalil yana dariya. "Wai, Hajiya sai kinyi haƙuri don zaki ga rawar kai!" Gaba ɗaya aka kwashe da dariya. Saukowa ƙasa Khalil yayi tare da zama daidai inda Sarah take sannan yace, "Wife, na san baki san kowa a nan wajen ba idan aka cire Laure da tazo ɗakinmu ɗazu. Bari na fara ta kan wannan babbar aunty, (yayi nuni zuwa ga Aunty Zakiyyah), ita ce matar babban wanmu, sojane a Abuja yake aiki. Lokacin da papa yake dai rai, we all are living there duk dani zaman na hutune don a abroad nayi rayuwata kaf, Hajiya ce ta matsa na dawo saboda Allah ya rubuta sai na haɗu dake mun ƙunla alaƙa mai girma. Last year suka aurar da second daughter ɗinsu mai sunan Hajiya ana kiranta little hajjaju, very smart girl don ni ta biyo a kwakwalwa." "Ai ka san mu duka kwakwalan tunkiyoyi gare mu sai kai ɗan gwal" Faɗin yaya barrister. Waro idanu Khalil yayi tare da faɗin, "Ni ba haka nake nufi ba. Mine saurareni kiji." Ya ƙarisa maganar yana kallon Sarah, "Wannan sunansa ya Abdul-Hakeem, wannan itace matarsa Aunty Maryam wacce ta aiko mana da breakfast ɗazu, ƴarsu ɗaya Maimoon... Wannan kuma shine ya barrister, shi kuma kin ga matarsa nan, sunanta Aunty Khairat, ƴaƴansu biyu...." Haka ya dunga nuna mutanan parlour ɗin yana mata bayani. Ita dai kai kawai take ɗaga masa. Yanda aka amsheta kowa na nan-nan da ita ya saka ta mance da wata Aina'u. Shikuwa Khalil yana sane, addu'a kawai yake yi cikin zuciyarsa Allah yasa ta gaji da jira ta wuce gida. Ɓangaren Aina'u kuwa, bayan fitarsu babu inda bata buɗe ta duba ba, sai faɗin, "Kan bala'iiii!" Kawai take yi tana kwafa. Sai da ta gama tsaf sannan ta dawo parlour ta zauna a kan kujera tana girgije-girgije ƙafa, "Wallahi in har sunana Aina'u ɗiyar Lami da Nuhu, wallahi tallahi ba zan taɓa bari kiyi farin ciki ba, ba dai anyi auren ba, enjoy the first week of your marriage before the war begins!" Ta ƙarisa maganar tana mai rausayar da kai. Tun tana ƙirga mintuna har ta dawo awa. A can cikin gida kuwa, kirar sallar azahar ne ya fitar da mazan zuwa masallaci yayin da matan suka ɗauro alwala. Bayan kowa ya idar da Sallah, sai suka haɗu gaba ɗaya a dinning don har an kammala lunch. Kujerun dinning ɗin irin mai sha huɗu ne, kuma sun ɗauke gaba ɗaya don ma yaran an haɗa masu a parlour don suna da yawa. Khalil ƙafa ya tura ya shafo ƙafar Sarah, ɗagowa tayi suka haɗa idanu ya kashe mata idanu, gaba ɗaya a idanun Hajiya komai ya faru amma sai ta nuna kamar bata ga komai ba ta cigaba da cin abincinta. Zumbur Sarah ta miƙe tana faɗin, "Inna lillahi!" Gaba ɗaya aka haɗa baki wajen faɗin, "Mai ya faru?" Khalil kuwa har ya zagaya ta bayanta tare da jan kujeran da take kai baya. "Na manta ina da baƙuwa a ɗaki. Kuma tun ɗazu tana can tana jirana." Hajiya tace, "Laure maza haɗo mata abinci a basket ki tafin mata dashi." Khalil kuwa tsaki yayi a zuciyarsa don bai so ta tuna ba. Shima abincin da bai ƙarisa ci kenan ba yabi bayan matarsa. Kowa Sarah ta murɗa handle ta shiga, a zuciye Aina'u ta juyo zata fara ruwan bala'i sai ga Khalil ya shigo rai ɓutu-ɓutu. Washe baki Ai'n tayi tare da faɗin, "Kun jima, har nayi bacci na farka. Amma dai mancewa kuka yi nazo ko?" Ko kamun Sarah tayi magana caraf Khalil yace, "Ni na ɗauka ma kin wuce ai. Ashe kina nan kina jira." Sarah tace, "Kiyi haƙuri Aina'u wallahi mancewa nayi kina nan. Kinci abincin?" "Ban sani ba shegiya munafuka. Wato kin shigo cikin arziki har kin soma wulaƙanci. Kiyi, lokacinki ne. Nawa na nan zuwa." A Cikin zuciya tayi maganar, amma a zahiri sai cewa tayi, "Naci!"
Showing 66001 words to 69000 words out of 129453 words