ka iya canzawa Laure." Faɗin Aina'u tana hararen Lauren. "Ke Aina'u!" Faɗin Sarah a tsawace da sauri Hajiya ta ɗagawa Sarah hannu tare da faɗin, "Bana son in ƙara jin komai daga bakin kowa, ku tashi ku tafi ɗakunan ku. Sarƙa kuma zasu fito domin duk wanda ya ɗauka ba dai ya sayar ba, don duk inda yake sai an kama shi ko kama ta." Gaba ɗaya kowa ya tashi guiwa sage ya bar ɗakin. Suna shiga ɗaki Sarah ta ɗaga hannu ta wanke fuskan Aina'u da mari tare da faɗin, "Wallahi baki isa ki kashe min aure ba, kina hauka ne? Ko baki san Laure ƴar uwarsu bace da har zaki jefeta da wannan mummunar ƙazafin? To bari kiji, ba zan iya da iskancinki ba, ki shiga ɗaki ki tattaro duk wani abu naki kizo ki wuce gida, ina zaune cikin rufin asirina kizo ki tada min hankali, to ba zai yiwu ba. Dama ba wani uban abun kike tsinana min ba, maza tattaro kayanki ga kuɗin mota ki bar min gidana." Hannu akan fuska Aina'u tace, "Ni kika mara Saratu har kina faɗin in bar maki gidanki? To zan tafi, amma sai kinyi nadama mafi muni a rayuwarki! Baki san true colour ɗina ba, amma zan fito maki dashi. Ba dai miji kike taƙama dashi ba, mu zuba mu gani, gaki ga mijin nan." Tana gama faɗin haka ta shige cikin ɗayan parlour ɗin da zai sadata da ɗakinta. Jakarta ta kinkimo ta fito bayan ta canza kaya ta shafa aboniki a idanunta, nan da nan idanunwan suka kaɗa su kai jazur kamar taci kuka ta ƙoshi. Bata taras da Sarah a parlourn ba, sai kawai ta saka kai ta fita daga ɗakin. Sai da ta ajiye akwatinta sannan ta buɗe ta ɗauki wani abu cikin wani ƙatoton box tare da nufa side ɗin Hajiya, Laure ta taras a parlour sai da ta dungure mata kai sannan ta wuce bedroom ɗin Hajiya tare yin knocking haɗe da sallama. Daga ciki Hajiya ta bada izinin shiga, tura ƙofar tayi tare da zama a ƙasa tana kallon tiles ɗin dake shimfiɗe, Hajiya dake tsakiyar gado tana duba wasu kaya ta kalleta tare da faɗin, "Aina'u lafiya?" Kuka Aina'u ta fashe dashi tare da faɗin, "Hajiya kiyi haƙuri, amma yanda kika ɗauke kika riƙe ni tamkar ƴarki ya saka ba zan iya bari a haɗa baki dani a cuceki ba, ga sarƙan ki, Saratu ce ta sace tare da haɗin bakin ƴar aikinki Laure.........."



_Dan Allah kuyi haƙuri bana jin daɗi ne shiyasa kuka jini shuru. Yanzu ma cewa nayi bari nayi naku ko kaɗan ne yafi babu_

*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_MATAR SAYYADEE_*

*Paid book 08128755583*


🦜 *KANWAR MATATA* 🦜

*25*


"Yanzu haka Hajiya ta koreni daga gidan nan saboda na faɗa mata gaskiya abunda take yi bata kyautawa. Yanzu hakan sarƙan nan bata nan na ɗauko shi na kawo maki ba. Nasan za kiyi mamaki mai yasa na tona mata asiri tana matsayin ƴar uwata, to nayi hakan ne saboda na tseratar da ita ganin tayi aure gidan mutunci, bana so aurenta ya mutu sanadin abubuwan da take aikatawa. Shi kansa Khalil ɗin ba jin daɗin zama da ita yake yi ba, a wannan ɗan zaman da nayi na fuskanci haka, kullum cikin ƙorafi take yi masa akan dole sai ya saya mata gida a wani waje ita bata san zama waje ɗaya da uwar miji da matar ƙani ko wa, tafi son zama ita kaɗai ta wala. Hajiya baki ga irin ɓarnar kuɗin da Sarah take yi ba da dukiyar ɗanki, duk abunda tace kamar ta shanye shi, jiki na rawa yake yi mata. Hajiya sai fa kun tashi tsaye sosai akan Khalil!" Hajiya baki sake take bin Aina'u da kallo tana mamakin ƙaramar yarinya irin wannan da hassada da kuma iya tsaro zantukan ƙanzon kurege, don tun daga furucinta na farko ta fuskanci inda ta dosa, babu abunda ke damunta illa tsantsan hassada da mugun hali. "Ina so tambayarki." Hajiya ta faɗi still tana kallon Aina'un. Gyara zama Aina'u tayi har da matsar hawaye tare da faɗin, "Ina jinki Hajiya." "Ke da Saratu uwa ɗaya uba ɗaya kuke?" Jinjina kai Aina'u tayi tare da faɗin, "Uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya da ita Hajiya, halin ne kawai ba ɗaya ba." Hajiya tsuke fuska tayi tare da faɗin, "Tabbas kuwa hali ba ɗaya ba. Amma Allah yayi wadaran naka ya lalace! Yanzu saboda lalacewa da rashin hankali da tunani, ƴar uwarki ciki ɗaya kike yiwa baƙin ciki da hassada? Duk wani mai hankali idan yaji wannan magana da kika yi ya san cewa ke munafuka ce kuma baki ƙaunar ƴar uwarki. Ina matsayin uwar mijinta, shine zaki zo kina faɗamin maganganun ɓatanci akan ƴar uwarki saboda naji haushinta! To ki sani, na san wacece Saratu, tun lokacin da aka kawota cikin gidan nan nake lura tare da karantarta, yarinya ce mai natsuwa da hankali. Laure kuma shekaru bakwai kenan muna tare da ita, bata taɓa ɗaukar min ko mayafi ba balle kuma sarƙa. Bata ma san darajarsa, kuma yanda nasan tarbiyyarta da halinta baza ta taɓa amincewa a haɗa baki da ita ba domin a cutar dani. Kuma ni tun ɗazu na fahimci ke kika ɗau sarƙoƙin nan saboda yanda kika riƙa tada jijiyoyin wuya, na rabu dake ne domin inga iya gudun ruwanki don na riga na san baza su taɓa saiduwar maki ba duk inda za kije don sai kin bata risiti (receipt). Kalle ni da kyau, mahaifiyarki ma na haifeta, baki isa kiyi min makirci da wayau ba, kuma auren Khalil da uwata Saratu, mutuwace zata raba shi in Sha Allah. Ba Saratu da take ƴar uwarki ba, Ni kai na mahaifiyar Khalil ban amince ki ƙara tako ƙafarki cikin gidan nan ba. Kuma kin san dai ina da ƴaƴa hukumomi ko? Tashi ki ɓace min da gani tun kamun na wanke fuskanki da mari!" Aina'u da baƙin ciki tarkon da ta ɗana bai kama ba ta miƙe tana yiwa Hajiya wani irin kallo sannan ta juya fuuu ta fita tare da rufo ƙofar da ƙarfi. Laure na zaune ta zubawa talabijin idanu taji saukar mahaukacin rankwashi a tsakiyar ka sai da ta kwanta flat a ƙasa tsabar gigicewa. Dawowa tayi daidai kanta tare da faɗin, "Sai na zama ajalinki, shegiya mummuna!" Tana baro part ɗin ta tsaya tana mamaki domin bata taɓa kawowa a ranta wannan makircin da ta haɗa ba zai yi aiki ba. "Hajiya kin jawowa kanki bala'i da masifa da tashin hankali! Kin yi kuskure tura hannunki a ramin maciji kuma wallahi sai ya ɗanɗana maki zafin dafinsa...." Tana gama faɗin haka ta ja akwatinta ta wuce ta bar gidan. Bayan fitar Aina'u a ɗakin Hajiya, Hajiya ta zabga tagumi tare da faɗin, "Duniya ina zaki damu ne? Ɗan uwanka ciki ɗaya amma shine ke yi maka hassada da baƙin ciki, kai Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Allah kasa mu cika da imani, Saratu ce dai zama daram dam a gidan nan in Sha Allah!" Wani ajiyar zuciya Sarah ta saki lokacin da ta tabbatar Aina'u ta bar gidan. Kitchen ta shiga domin haɗawa Khalil abinci don ya kusa dawowa. Bayan ta kammala girkin ta haura sama ta cancaɗa wanka ta saka wata doguwar rigar shadda pink colour wanda yasha aiki da baƙin zare, ɗaurin ɗan kwali tayi mai kyau sannan ta fesa turare ta ƙara kallon fuskanta a madubi ta saki murmushi tare da fita ta sauko ƙasa ta zauna a kan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya tana kallon tanƙameman plasma tv ɗinta dake haska film ɗin _Mohabbatain_ a tashar Bollywood. Da sauri ta miƙe jin ƙarar door bell, buɗe Ƙofar tayi tana kallonsa. Shima kallon nata yake yi daga sama har ƙasa yana faɗin "Ma sha Allah!" Cikin zuciyarsa. Hannu ta kai ta karɓi jacket ɗin hannunsa da ya ratayo tare da kai bakinta saitin kumatunsa ta sakar masa kiss tare hura masa fuska tace, "Kar fa a cinye ni." Hannu ya kai zai cafkota tayi saurin ja baya tana dariya, "Ki tsaya ki gani idan ba'a cinyekin ba." Gwalo tayi masa tare da faɗin, "Ka kama ni idan zaka iy....." Ko kamun ta rufe baki har ya iso inda take ya cafki hannunta biyu tare da haɗata da ƙirjinsa yana mai faɗin, "Ni da zan iya haɗiye kin ma da na huta da kewarki, kullum na fita aiki sai kin hanani sukuni, domin da zarar na bar gida, kece kike min gizo a ko ina." Hannun ta saka ta rungumosa tare da faɗin, "To ni dai matsalata kar dai garin yi maka gizo kaje kaga wata macen ka ɗauka nice kawai kace mata, Ina son ki! Tabbas zuciyata zata buga daga nan." Janyeta yayi daga jikinsa tare da kama hannunta suka nufi sama yana mai faɗin, "Wannan kalmar mai tsada ga macen biyu kawai nake furtawa, Hajiya da kuma ke, bayan ku, babu macen nan gaskiya." Ƙanƙame hannunsa tayi tare da faɗin, "Ina son ka, ina sonka sosai." Bakinsa ya kai dai-dai kunnanta tare da faɗin, "Muje ciki a nuna min!" Tsungulinsa tayi a damtsensa tare da yin dariya. Bayan kwana biyu, Khalil ya fahimci Aina'u bata gidan, hakan ba ƙaramin daɗi yayi masa ba, amma ko a fuska bai nunawa Sarah ba, kuma bai taɓa yi mata maganar ya akai baya ganin Aina'un ba, ita ma kuma bata yi masa maganar ba. "Aunty Rose Merry, ina son don Allah ki kai ni wajen _Hell Ofulafula_ da kike bani labarinsa, amma kar ki bari ko Lami ta sani, ya zama sirri tsakanin mu kamar yanda muka saba." Aina'u ta faɗi bayan ta kamo hannun Aunty Rose Merry ɗin bibbiyu. Aunty Rose Merry da kallon mamaki ta bita tare da faɗin, "Lili mai za kije kiyi a wajen _Hell Ofulafula_? Kin san wanene Hell kuwa? Ko daga jin sunansa kawai ya isa ya firgita ki, ganinsa kuwa, kamar bala'i ne a wajenki." Aunty Rose Merry ta girgiza kai tare da cigaba da faɗin, "Baza ki iya da Hell ba, dokokinsa nada tsauri, bazan baki wannan shawarar ba, domin zai saka ki aikata wani mummunar abu mai girma wanda Yesu Almasihu ba zai yafe maki ba, gwara dai kije wajen _Iya fulowa_, itama ta iya aiki sosai. Wai ma menene za kiyi? Wa kike so ayi wa wani abun!" Faɗin Aunty Rose Merry. Sake hannunta Aina'u tayi tare da ɓata rai ta juya baya tana faɗin, "To shikenan! Amma ni duk abunda kika saka ni, ina yi maki kai tsaye, har babana na cutar saboda ke, amma ni baza ki iya mun ɗan ƙaramin alfarmar nan ba, ashe soyayyar da kike min na ƙarya ne, saboda ke na koma addinin Christian, na kwana arba'in da biyar a cikin ɗakin duhu daga Ni sai pastor William yana min wankan zunubi tare da amfani dani, ya aske min gashin kaina, ya saka na kwanta kamar dabba ina shan nonon kare duk saboda ke, amma shine baza ki iya min wannan ƙaramin abun ba. Shikenan!" Ta ƙarisa maganar tana mai fashewa da kuka. Jawota Aunty Rose Merry tayi tare da faɗin, "Kiyi haƙuri Lili, ba dai _Hell Ofulafu_ kike son zuwa ba?" Gyaɗa kai Aina'u tayi tana share hawayen fuskanta, "To ki kwantar da hankalinki, zan kai ki wajensa, sai dai tafiya ne mai nisa, don a Abia yake can wani ƙauye mai nisan gaske, kuma shi bai jin yaren Hausa, bai jin English, sai Igbo, yoruba da ifem." Wani murmushi Aina'u tayi tare da faɗin, "Wannan ba matsala bane Aunty, ba sai kin raka ni ba, kiyi kwatanci kawai." Shuru Aunty Rose Merry tayi mai tsayi kamun ta saki ajiyar zuciya ta soma zayyano mata kwatanci tsaf har da yanda zata samu tafintan da zai riƙa faɗa mata abunda Hell yace da kuma ita abunda zata ce masa. Bayan kwana biyu Aina'u ta shirya kuɗi tsaf tare da ɗaukar hanyar Abia ba tare da sanin kowa ba idan aka cire aunty Rose Merry, awanni goma sha ɗaya da rabi suka yi a mota kamun suka isa kuma cikin dare. Aina'u ta zauna, ta mike ta rasa inda zata saka kanta saboda gajiyar zaman mota. Taji waƙa a wayarta har na Allah ya isa Kasancewar ta tafi da power bank har taji ya fita a cikin ranta. Hotel ta kama ta kwana, washa gari da sassafe ta nemi wanda Aunty Rose Merry ta Bata number ɗinsa, sai da suka yi ciniki ta bashi 50k kuma ita za tayi masa kuɗin motar zuwa can sannan suka ɗauki shatar mota zuwa *_Asaokpuaja_*. Tafiyar awa Shidda ce ta kai su can, nan ma ɗin mai motar jiransu yayi a bakin wani hanya sabida mota baza ta iya shiga ba, nan ma suka soma cin uban tafiya, sai da suka yi tafiyar awa ɗaya da rabi sannan suka isa wani ƙatoton baƙin gunki wanda aka yi masa penti da jar kala, da mugun gudu Aina'u ta koma bayan Ugo ta ɓoye saboda yanda gunkin ya tsoratata da girmansa, "Una no hear wetin I say before we come here? I tell u say make u no fear if you see anything, because _Hell Ofulafo_ dey look you through here." Yayi mata nuni da ramin hancin gunkin. Ai sai Aina'u ta ƙara kiɗimewa! Wani sautin mara daɗi ciki wani harcen yare ya soma magana a kausashe, take Ugo ya kai ƙasa tare da yin sujada sau uku sannan ya miƙe ya harɗe hannayensa kamar mai neman gafar ya shiga magana cikin yare na kusan sakan sittin sannan ya yuyo ya kalli Aina'u tare da soma yi mata magana da gurɓataccen turanci, "Hell yace ace maki idan baki shirya ba, ki koma gida, idan kuma kika ƙara tsorata anan wajen sai ya maida fuskanki tana kallon ƙeyarki, idan kuma kin shirya kiyi sujada a gaban gunkin nan sau uku." A take Aina'u taji duk wani tsoron da take ji ya fece musamman da ta tuno korar karen da Sarah tayi mata daga gidanta. Zubewa tayi tare da yiwa gunkin sujada sau uku, ana ukun ba tare da ta ɗago ba taji wani irin guguwa mai ƙarfi ya taho ya lulluɓesu, bata kuma buɗe idanunta ba sai a gaban wani garjejen tsohon inyamure jikinsa gaba ɗaya guraye ne, ya kasance irin zabiyan nan ne, domin idanunsa ma basa tsayuwa waje ɗaya. Gaba ɗaya jikinsa yayi ƙuda-ƙuda. Kallo ɗaya yayi wa Aina'u ta soma jin wani irin zawo. Wani mummunar dariya ya ɓarke da ita tare da soma surkulle cikin yaruka daban-daban. Wani ƙatoton tulu ne ya bayyana a gabansa, kallon Aina'u yayi sannan ya kalli tukun sai ga Aina'u cikin tulun, gaba ɗaya komai ya faru ne cikin daƙiƙu biyu. Jan zare ya ɗauko tare da jan mayafi ya kulle tulun tare da ɗauresa. Da sauri Ugo ya miƙe tare da yiwa _Hell Ofulafu_ sujada sannan ya soma tafiya da baya da baya har ya fuce. Sai da Aina'u ta kwana bakwai cikin tulun nan sannan tulun ya face sai gata a watse a ƙasa daga ita sai ɗaurin ƙirji da baƙin zani da jan ɗan kwalin da bai rufe tsakiyar kanta ba. Sai da ta kwashi mintuna talatin tana kwance ko motsi bata yi sannan _Hell Ofulafu_ ya miƙa tare da ɗaga hannu sama sai ga ƙaramin tulu a hannunsa, hannunsa mai tsini ya caka a jikin tulun, take ya soma tsiyayar da jini mai kauri da wari shi kuma ya shiga zagaye Aina'u da tulun sau bakwai. A firgice ta farka tana mai buɗe baki tana shan jinin nan dake tsiyayowa daga cikin tulun. Bayan ya gama wannan ya jawo wata tulun mai ɗauke da wani irin ruwa mai ya ajiye a inda take tare da saka hannu ya fizge zanin jikinta da ƙarfi. Wani abu ya ɗauko mai kama da kofi sannan ya ɗaga hannunsa sama sai ga wata murtukekiyar bulala, idan ya tsiyaya mata ruwan sai ya shauɗa mata bulalan sau biyar a ko ina na jikinta. Sai ruwan nan ya ƙare tas a jikinta, gaba ɗaya jikin nata yayi wani irin ruɗu-ruɗu. Aina'u tayi suma ya kai goma saboda azaba. Ugo na gefe yana kallon komai, kuma dama ya san sai _Hell Ofulafu_ yayi mata hakan, ta hakane yake cire sauran imanin dake jikin duk wanda ya kawo kansa wajensa. Shi da
Showing 75001 words to 78000 words out of 129453 words