GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*
_MATAR SAYYADEE_
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*38*
"Hajiya dan........." Ko kamu ya ƙarisa abun da yake shirin faɗa har Hajiya ta yanke wayarta. Hannu ya kai ya daki steari da ƙarfi tare da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Haba Hajiya!! Habaaa!!!" Ya jima kamun ya kunna motar ya sau hanya, "Wannan shi ake kira ga ƙoshi ga kwanan yunwa!" Ya faɗi bayyane, can kuma ya kuma ɗaukar wayar ya sake dailing number ɗin Sarah, " _The number you're trying to call is currently switched off, please try again later. Thank you_." Tsaki yayi tare da ajiye wayar a gefe ya nufi gida don bai san dame Ya Abdullah yazo ba. Tafiyar da zai yi ta mintuna sha biyar, amma saboda tsoro da tashin hankali cikin mintuna talatin da biyar ya iso layinsu. Tun da ya hango uban sojoji uwa saƙago sun tsatstsaya ya kuma tabbatarwa kansa ya LTG ya iso gidan. Horn yayi, mai gadi ya wangale gate shi kuma ya shiga tare da parking sannan ya fito yana tafiya sumimi-sumumi kamar an tsoma jaba a cikin koko. Tun da ya doshi ɗakin Hajiya yake jin koke-koken mata na fitowa daga ɗakin. Shahada yayi tare da ɗaga labule ya shiga. Turus ya tsaya yana kallon matan dake ɗakin tare da mamakin yaushe suka iso all the way from Maiduguri. Duƙawa yayi har ƙasa tare da soma gaishe su, yayin da kansa a ƙasa ya shiga gaida ya Abdullahi da tun shigowarsa kallo ɗaya kawai yayi masa ya kau da kai. "Wallahi, tallahi Hajiya baza mu taɓa yarda ba, sai an ɗauki mataki akan wannan abu da ƙanwar matar ya Khalil tayi masa, ta cuce mu ta raba mu da ƴar uwarmu, kema kuma tayi ƙoƙarin raba mu dake, baza mu yafe mata ba akan wannan abu da tayi mana. Hajiya ko gawan Nafeesa ban gani ba!" Ta ƙarisa maganar tare da fashewa da kuka mai ciwo. "Har da jaririyar da bata ji ba bata gani ba, yarinyar da bata jima da shaƙar iskar duniyar ba, wannan wani irin rashin imani ne haka!!" Aysha ta sake faɗi tana mai kwanciya akan cinyar Aunty Yagana, ƙanwar Hajiya. Shafa kanta Aunty Yaganar tayi tare da faɗin, "Aysha duk wacce imaninta zai bar jikinta har ta iya kwanciyar aure da mahaifinta, to wallahi babu abunda baza ta iya aikatawa ba, da a zamanin annabawa tazo, to tana ɗaya daga cikin wacce zata iya yunƙurin kashe Annabi! Wallahi Hajiya ina bayanki ɗari bisa ɗari, kar ki sake ki yarda matar Khalil ta dawo cikin gidan nan, mai za ayi da zuri'a irin tasu, zuri'ar matsafa, zuri'a karuwai ƴan dangi Arna!! Ai wallahi don dai kisa haramun ne, da ko ƴaƴan da Khalil suka haifa tare, shaƙe wuyansu kawai za ayi su mutu kowa ya huta. To sun tsotsi nonon tsiya!" Faɗin Aunty Yagana a mugun zuciye, don har ta kusan fin Hajiya ɗaukar zafi. Khalil lokacin guda yaji haushin Aunty Yagana ya rufesa jin abunda tace akan ƴaƴasa, nan da nan ya ɗaure fuska tamau. "Kayi abunda na umarce ka dashi ko kuwa???" Faɗin Hajiya tana watsawa Khalil harara. Ko kamun yayi wani yunƙurin yin magana tuni Aunty Falmata mai bin Aunty Yagana tace, "Ba magana ake yi maka ba don ubanka? Ko sai na taso ba na shaƙi wuyarka!" Ta ƙarisa da ƙarfi har sai da Khalil ya razana, "Hajiya wallahi, tallahi daga gidan nake, su kansu iyayenta basu san bata gidana ba, ashe dana koreta ba gida tayi ba, can dangin babanta ta nufa." Ya ƙarisa maganar a tausaye. "Dubi yanda yake wani rausayar da kai kamar maraya, to ubanka zaka ci, kuma dole ka rabu da yarinyar nan tun da ba tare aka haife ku ba. Yaro duk kabi ka zama wawa a kan mace!" Faɗin Aunty Yagana. "Uhm! Baku ji wata maganar banza da yake yi ba, wai ta tafi dangin mahaifinta. Ina ce nan Marmari yayi bincike lokacin auren naku, kowa cewa yake bai san asalin mahaifinta ba, su dai kawai tarewarsu suka gani a unguwar, kuma babu wanda ya taɓa ganin wani ko wata daga cikin ƴan uwansu yazo gidan, kaii Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'una, wannan fitina haka!" Hajiya ta faɗi har da buga cinya. Tun da suka fara magana ko tari ya Abdullahi bai yi ba yanzu da yayi gyaran murya tare da faɗin, "Hajiya, tun farko irin haka na guda shiyasa naƙi auren don zuciyata bai kwanta da ahalin ba, amma Hajiya kece ki kai ta tausata akan inyi haƙuri ayi auren tunda dai mutane huɗu sun bata shaida a kan ita matar Khalil ɗin, sannan kika ƙara da faɗin, laifin wani bai shafan wani. To Hajiya yanzu hakan ma haƙuri za kiyi tunda dai an riga an haɗa zuri'ar nan kuma laifi bana matar Khalil bane, na ƙanwar matarsa ce, kuma laifin ƙanwar matarsa babu yanda za ayi ya shafi matarsa, tunda ke shaida ce hatta ita kanta matar tasa ba barinta tayi ba. A bar abunda ya wuce ya wuce, sai a tari gaba kawai." Tsabar zuciyar Hajiya na tuƙuƙi, ta buɗe baki za tayi magana ta shaƙe da miyau, take ta hau wani irin mugun tari, idanunta na zubar da hawaye. Da sauri Laure ta nufi kitchen ta ɗauko bottle wata ta buɗe tare da kawowa Hajiyar, da sauri Hajiya ta karɓa ta kafa kai, sai da tasha rabi sannan ta ajiye goran tana mai da numfashin. Babu abunda kake ji a ɗakin sai "Sannu Hajiya!" Sai da ta lafa sosai sannan ta shiga faɗin, "Marmari idan har ka san ba zuwa kayi ka taimaka min muyi wannan yaƙin tare ba, to ka tashi ka koma tun yamma bata yi maka ba, don ka san wallahi, ba zan taɓa yarda Saratu ta kuma zama da Khalil ba in har nice na haifesa, idan kuma zai yi mani musu da gardama, sai in sallawa duniya shi!" "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Hajiya!" Khalil ya faɗi da ƙarfi har da dafe ƙirji yana zaro idanu. "Haba Ya Bilki, ai wannan furucin bai kamata ya fito daga bakinki ba matsayinki na uwa, idan ki kai haka ai sun ci riba. Hakan ma ba zata faru ba, Khalil ai me biyayya ne, ko ba haka ba Ibrahim, mai sunan ɗan gatan Allah!" Faɗin Aunty Yagana har da dariya. Sunkuyar da kai yayi tare da gyaɗa kan alamar eh. Aunty Falmata kuwa cewa tayi, "Yauwa Khalil, ko kai fa! Yanzu abunda za ayi, dubawa za kayi cikin dangi na nan ko na can Maiduguri, a kwai ƴan mata tsala-tsala, na san dai ba zai wuce kyal-kyal banzar matar nan taka bace kake ganin baza ka samu sama da ita ba kasancewar jajur kuma kyakkyawa, to akwai waɗanda suka fita komai a cikin dangin ubaka dana uwarka. Dangin ubanka akwai irin su, Ajaja, Gona, Am'an, yaba, yakaruu duk kyawawane duk da kuwa baƙaƙe ne, idan kuma basu yi maka ba, sai ka tafi dangin uwarka, ka san dai Shuwa ba baya ba wajen kyau, gasu Hindatu, Rakiya, Raliya dasu Aysha da Ameena, kai nayi tuya na mance da albasa, ga wannan ƴa ƴar wajen Mariya, _Habbooba_! Kai ita ma na zaɓa maka, Yarinya kamar India, yanda kasan ita tayi kanta tsabar kyau, ga gashi don san yana ɗaya daga cikin abubuwan dake tsole maku idanu ku maza." Caraf Hajiya tace, "Wallahi ni Habbooban ma tafi kwanciya min a rai, kawai ayi magana da iyayenta, idan sun amince sai ayi magana. So nake ayi komai cikin gaggawa, kuma ni wallahi na haƙura da zamansa a nan Nigeria kuma dama ni na matsa a kan ya dawo nan ɗin, to yanzu na haƙura, ana ɗaura auren sai ya tattara matarsa su koma cen _Las Vegas_ ɗinsa da zama." Da gefen idanu Ya Abdullahi ya kalli Hajiya tare da ɗan yin murmushin gefen baki tare da miƙewa yace, "Muje can side ɗin naka naga yarinyar!" Yana gama faɗin haka ya fice, da sauri gaba ɗaya mutanen ɗakin suka miƙe suka fito don suma duk abunda ake yin basu ga Aina'u ba. Jiki a sanyaye Khalil ya miƙe yabi bayan ya Abdullah zuwa side ɗinsa, shi ya saka key ya buɗe sannan ya shiga, ya Abdullahi yabi bayansa, su Hajiya kuma suka bi bayan ya Abdallah. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Kuna jin warin da nake ji kuwa a cikin ɗakin nan kamar gawa ta ruɓe?" Faɗin Nafeesa tana mai toshi hancinta. Gaba ɗaya sauran ma toshe hancinsu suka yi, "Allah yasa ba wannan shaiɗaniyar bace ta mutu a cikin gidan mu!" Hajiya ta faɗi. Cikin sauri Khalil ya nufi sama yana tsallake step bibbiyu. Ƙafa ya saka ya daki ƙofar ta bulle da ƙarfi, da wani uban sauri ya koma baya yana toshe hanci tare da zaro idanu, "Wa'innahu Sulaimanu!" Faɗin Aunty Yagana da aunty Falmata. "Ibrahim menene wannan ka ajiye a ɗakin ka." Ɗagowa Aina'u tayi cikin wa.i irin mugun azaba tare da faɗin, "Ku taimaka min, ku taimakeni Aina'u ce!" Kuka Hajiya ta fashe dashi tare da faɗin, "Wallahi tallahi jama'a mu kiyaye ALLAH! Mu kiyaye ALLAH jama'a!! Yanzu wannan yarinya Aina'u ce ta koma haka?" Kallonta Nafeesa take tayi cikin tsoro, ganin da tayi mata na ƙarshe shine ranar da tazo washa garin auren su Khalil. Yanzu kam ta lalace, tsirara take a cikin ɗakin, maƙogwaronta a waje, idanunta ya zazzago, ko ina a jikinta babu inda babu rami zuƙuƙu, duk inda tsokar ta yanko ta faɗo, tsutsotsi ke cunkusuwa a wajen suna cin sauran naman dake wajen. Gaba ɗaya Aina'u ta fice daga hayyacinta, gashin kanta duk ta gama fuzgar shi, haƙoranta duk jini ta gama tattaune leɓenta. Sai wani irin miƙewa take yi tana zabura sannan sai ta fasa ihu tare da kai hannu gabanta ta kwakwulo kunamu ta watsar a tsakar ɗakin sannan ta hau burgima tana buga kanta da bango. "Hajiya a fitar da yarinyar daga gidan nan, ta koma can gidan iyayenta dan Allah!" Fadin Nafeesa jikinta na wani irin rawar tashin hankalin ganin halin da Aina'u take ciki. Ya Abdallah kuwa girgiza kai yayi tare da saurin barin waje yana mai faɗin, "Hajiya yanzu yarinyar nan zata bar gidan nan, ku fito mu fita." Gaba ɗaya suka bi bayansa, Khalil kuwa sai da ya kalli Aina'u sannan yace, "Ban taɓa jin ɗigon tausayinki ba Aina'u, domin kuwa kin cutar dani matuƙa, Kuma idan har Hajiya tayi nasarar rabani da matata, hmmm!" Yana gama faɗin haka ya fice daga ɗakin da sauri hawaye na zubar masa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya Abdallah ya kirawo wani mai akori kura ya bashi 50k ya toshe hanci tare da saka glove, bayan lulluɓe jikin Aina'u ya kinkimeta ya saka a bayan akori kuran ya tada mota ya nufi jama'a road can gidansu Lami. Lokacin da aka shigo da Aina'u gidan, ihu Lami ta riƙa yi tana tuma a ƙasa, su Na'ima kuwa tsoron Allah ne ya ƙara huda zukatansu, duk da halin Aina'u sai da ta ɗan basu tausayi. Saboda tsananin warin da take yi, ɗaki ɗaya da akai masu ƙatoto saboda kiwo suka share sannan suka ajiye ta a ciki, babu abunda take yi sai tone-tonen abubuwan da tayi. Lami na jin sunan _Hell Ofulafu_ gabanta ya buga da ƙarfi ta fito daga ɗakin tana faɗin, "Rose Merry! Rose Merry ce kawai zata iya kai Aina'u wajen Hell! Yesu Almasihu ka kawo ƙarshe Rose a wannan rana mai albarka ta Sunday." Faɗin Lami tare da fizgar zanin dake kan igiya ta fita fuuuuuuuu. Saboda tsabar tashin hankali Lami ko abun hawa bai hau bata hau ba, haka tayi ta tafiya a ƙafa har ta isa gidan Rose Merry. Knocking ta hau yi a ƙofar gidan kamar zata ƙarya duk da kuwa akwai kwaɗo dake nuna alamun mutanan gidan basa nan, don anty Rose Merry idan ta tafi church duk Sunday bata dawowa sai bayan la'asar ko kuma gab la'asar. "Madam ai gidan a kulle yake, kalli padlock ɗin mana." Faɗin wata bayarabiyar mata mai ɗauke da ƙaton bawon gorunan magani a kai, sai a sannan ta kalli kwaɗon tare da kai hannu ta taɓa, zamewa tayi ta zauna akan dakalin gidan, don ji take ba zata iya taɓa tafiya ba tare da tayi ido huɗu da Rose Merry ba. Ta kusan awa ɗaya a wajen kamun Aunty Rose Merry ta ƙariso wajen cikin shigar farar atamfa mai ratsin sky blue, sai farar rigar less da kuma sky blue ɗin gwaggwaro. Tana ganin Lami ta washe baki tare da faɗin, "Elizabeth Akanchewa Uchendo, ƙawata, my childhood friend." "Stop that nonesense Rose Merry David Anthony! I came here to ask of what you did to my daughter! You've poisoned my daughter's heart Merry, Yesu Almasihu ya tsine maki, Ƙawancena dake babu alheri a ciki, ke guba ce, ke shaiɗaniya ce, kin kai min ƴata wajen azzalumin nan _Hell Ofulafu_, tun ranar farko da kika fara kai ni Abia na san wannan mugun mutum ne mara imani, duk tsafin da ake yi a gidanmu, baza su iya rashin imanin da Hell yake yi ba, yanzu na ƙara tabbatar da cewa kece kika kashe min ɗana Lukman, kuma ki sani, na rantse da tsafin Babana, You will pay for what you did!" Lami na gama faɗin haka ta juya zata bar wajen, da hannu ɗaya Aunty Rose ta jawo kafaɗanta tana wani irin murmushin mugunta, sai da ta juyo da Lami gaba ɗaya sannan ta kyasta babban yatsarta da kuma manuniya tare da faɗin, "Hey Elizabeth, do you think I came all the way from Nassarawa state to Kaduna, just because of our friendship? You're a fool, a big fool Elizabeth! Nazo Kaduna ne domin mijinki, don mijinki Elizabeth! Tun ranar da na fara ganin Nuhu, naji ina matuƙar ƙaunarsa, amma kuma sai kika min shigar sauri, sannan kuma kin tuna abunda Akanchewa Uchendo ina nufin mahaifinki yayi wa Babana, yayi masa asiri ya raba shi da mamana, ya raba shi da duka arzikinsa sannan ya mayar dashi makaho, Ni kuma gani har yanzu ban taɓa aure ba. Kina tunanin sai ni kuma in zuba maki idanu ki auri ɗan gidan malaman can, sannan kuma in barku kuyi zaman lafiya?" Sai ta girgiza kai tare da ɗaukar ƙafa ɗaya a kan dakali sannan tace, "Bari na faɗa maki abunda baki sani ba Elizabeth, nice sanadin lalacewar duka ƴaƴanki, Ni na kai sunanki wajen Hell, nayi amfani da kwaɗayin duniyarki, na saka Hell ya sakaki kika kai ƴaƴanki ga halaka, sannan ɗan ki tilo namiji na saka masa cutar sata da kuma shaye-shaye, ƴa ɗaya ce ta gagare ni, ita ce Saratu, Ni na saka Hell ya saka maki tsanar mijinki da jin haushinsa da kuma rashin ganin ƙimarsa, sannan Ni nasanwa mijinki karayar arziki bayan na nakasta ƙafarki, ƴarki kuma Aina'u, banyi mata komai ba, jinin mahaifinki ne ke yawo a jikinta, don ita ce tayo gadon ubanki gaba ɗaya har ta damesa ta shanye. Kuma Lami yanzu aka fara wasan a tsakanin mu. Ban san mai Aina'u tayi ba, amma tun da tace min tana so in haɗata da Hell na tabbatar Aina'u ɗiyarki ce, domin bata yada halinki dana mahaifinki ba. Mu zuba ni da ke Elizabeth!" Tana gama faɗin haka tayi wani murmushi tare da kaucewa ta nufi wajen ƙofa ta buɗe tare da shiga ta bugo ƙofa. Lami ta jima a tsaye tana jujjuya maganganun Rose Merry kamun taja jiki a sanyaye ta nufi gida. "Ai da zafi-zafi akan daki ƙarfe Hajiya Mariya, Ni dai idan har ba'a tsayarwa Habbooba miji ba, nayi wa Khalil kamu!" Faɗin Hajiya tana murmushi..............
_Kar ku damu, zamu haɗu gobe in Sha Allah. Na san nayi laifi kam_ 😬
*ðŸ‘GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👠ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA ðŸ‘👠fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👠Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*
_MATAR SAYYADEE_
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*39*
Cike da farin ciki Hajiya Mariya tace, "Hajiya Bilki wanene zai ƙi son haɗa jini dake? Ai wallahi ko an tsayarwa Habbooba miji, haƙuri za'a bashi, gida bai ƙoshi ba ba'a baiwa na dawa ba, balle kuma Habbooba bata da wani tsayayye miji. Ba'a jima da kammala degree ɗinta ba. Yanzu ne ta ɗan soma kula samarin ma." Wani ajiyar zuciyar farin ciki Hajiya ta sauke tare
Showing 120001 words to 123000 words out of 129453 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41 Chapter 42Chapter 43Chapter 44