da faɗin, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Shikenan tuwona maina, yanzu abunda za'a yi, ki ɗan fara Kwankwasawa Alhj Mutallab da maganar kamun daga nan su Marmari su zo tambayar aure, don so nake kawai da sun zo, har lokacin biki a tsayar. Allah yasa dai kar Habbooba ta bamu matsala!" "Hajiya baki da matsala, Habbooba kuma babu matsala daga wajenta in Sha Allah." Layla dake gefen Hajiya Mariya sai jan gyalen lifayan data naɗe jikinta take yi tana faɗin, "Umm! Umm!!" Ita kuma haj Mariya sai kai mata duka take yi tana bige hannunta, sai da ta gama wayar sannan ta kalleta a fusace tare da soma magana cikin yaren Shuwa, "Mai yasa baki da hankali ne Layla? Kin san da wacce nake magana amma sai takura ni kike yi, baki bari in gama wayar tukun sannan kiyi min duk maganar da zaki yi min!" Turo baki kyakkyawar farar yarinyar tayi tare da faɗin, "Haba Umm, why always Habbooba? Komai Habbooba, duk abunda kika samu, Habbooba, idan kyauta za kiyi, Habbooba is the first person to received before everyone, haba Umm!" Layla ta ƙarisa maganar cikin ɗacin zuciya. "To yanzu kuma me nayi Layla?" Faɗin Hajiya Mariya tana mai zama kusa da Laylan. "Naji lokacin da kuke magana da Aunty Yagana a parlour, shine kika yi sauri kika dawo bedroom ɗinki, and then yanzu kuma kina magana da aunty Bilkin Kaduna, kuma i heard anything you were saying, it all about uniting Habbooba and that son of her's!" Janyota jikinta tayi tare da faɗin, "Haba Layla, ba wai nafi son Habbooba bane a kanki, kin ga you're just 18years, amma ita she's 27years, kin ga dole ita zan so na fara kawaswa a nan gidan tafi gidan nata mijin kamun ke. Be petient, in Sha Allah kema mijinki na nan zuwa soon!" Shuru Layla tayi bata ƙara cewa komai ba. Tayi haj Mariya tayi tare da fita daga bedroom ɗinta ta nufi na Habbooba, tun daga corridor ɗin da zai sadata da ɗakinta take jiyo sautin wakar _Allela Belela_ kamar zai fasa dodon kunnenta, sai data toshe kunnen sannan ta iya ƙarisawa har cikin ɗakin Habbooban sannan ta kai hannu ta zare socket ɗin radion ta jefar. Wata fara tass ɗin budurwa ce kwance a kan gado daga ita sai wani Short kalar baby pink wanda ya tsaya mata iya cinya, sai rigar short ɗin ta kamfanin Armani da ya kawo dai-dai inda short ɗin ya tsaya mata, gashinta baƙi siɗik mai uban tsayi daya barbazu akan gagon, rubutu take yi a kan wani jotter kuma a lokaci guda tana kallon screen ɗin iPhone X ɗinta, jin waƙar da take sauraro ya tsaya cak sai tayi saurin juyowa da sauri, kyakkyawa ce ta bugawa a jarida, gashinta ya watsu baya, wasu kuma suka rufe gefen fuskanta, hannu ta saka ta mayar da gashin baya tare da turo baki ganin mahaifiyarta ce da wannan aikin. "Habbooba." Mahaifiyar ta kira sunanta a hankali tare da zama a bakin gadon, cikin sauri Habbooba ta kawo kanta ta ɗaura a kan cinyar maman tata, "Ya Rasulullahi, Habbooba na hana ki ƙure sauti a ɗakinki, idan za kiji waka, ki riƙa saka sautin daidai kunnanki dan Allah!" "Umm, idan ban saka volume dayawa ba, waƙar bai min daɗi sosai." Faɗin Habbooba. Ajiyar zuciya Umm tayi tare da faɗin, "Habbooba!" Ɗagowa tayi ta kalli Umm ɗin jin yanda ta kira ta with seriousness, "Na'am, Umm!" "Kin san wannan?" Umm ta faɗi tare da nuna mata hoton Khalil lokacin yana _Las Vegas_, tsaye jikin wani ƙarfe hannunsa biyu sanye cikin aljihun wandonsa yana sanye cikin wata navy blue ɗin bodyhug irin highneck ɗin nan, murmushin kwance a fuskansa wanda ya bayyanar da 2dimples ɗinsa, ba ƙaramin kyau yayi ba. Ƙarɓan wayar tayi a hannun Umm tare da zoomin picture ɗin sosai tana faɗin, "Wow! He look familiar, amma na rasa inda na taɓa ganinsa. Yana da kyau sosai Umm." Wani murmushin jin daɗi Umm tayi tare da karɓan wayar sannan tace, "Future husband ɗinki ne!" Waro idanu Habbooba tayi tare da tashi zaune tace, "Umm, are you for real? Like da gaske kike Umm?" Dariya Umm tayi tare da faɗin, "Ni na taɓa yi maki ƙarya ne? Mahaifiyarsa ce ta buƙaci ya ƙara aure saboda bata son first wife ɗinsa da yake zaune da ita, shine ta zaɓe ki a matsayin matar da zai aura, kuma kin san ko shi ɗin ɗan wanene?" Girgiza kai Habbooba tayi gabanta na faɗuwa jin yana da mata, don it's obvious Shuwa basu ƙaunar kishiya! "Ɗan _late CJN Nurudden Muhammad_ ne, kuma kin san dai CJN Nurudden Muhammad mijin cousin ɗita ce, don da mahaifin haj Bilki, da Mahaifiyata, ubansu ɗaya, uwa ce kowa da tasa." Jinjina kai Habbooba tayi tare da faɗin, "Na tuna, na tuna inda na taɓa ganinsa, lokacin da muka je ta'aziyar mahaifinsa ne na taɓa ganinsa, he's a medical doctor ko?" Jinjina kai Umm tayi tare da faɗin, "Tabbas shine, kin gane sa." A sanyaye Habbooba tace, "Umm I love him, but yana da mata kika ce." Ta ƙarisa maganar cike da rauni. Kamo hannunta Umm tayi tare da faɗin, "Come on, sai kace ba Shuwa ba, Kar ki bani kunya mana, Shuwa ba'a san mu da tsoran kishiya ba, kishiya ko wacece ita bata bamu tsoro. Ni dama kuma amincewarki nake so, kuma baki san wani abu ba, ita matar tasa ma, sakinta za ayi don ita mahaifiyar tasa cewa tayi dole ya saki first wife ɗinsa, kuma da zarar anyi auren, _Las Vegas_ zaku wuce acan za kuyi zaman ku." Wani irin runguma Habbooba tayi wa Umm tare da faɗin, "Na amince Umm, zan aure shi kuma ni dama tun ganin da nayi masa na farko naji ina matuƙar sonsa." Shafa kanta Umm tayi tare da miƙewa fuskanta cike da murmushi ta bar ɗakin. Bayan kwana biyu! "Khalil ka san mai yasa nayi kiranka a gaban ƴan uwanka gasu gaba ɗaya?" Faɗin Hajiya tana yin nuna gasu, ya Abdullah, ya Abdul-Hakeem, ya Barrister, da kuma Aysha. Girgiza kai Khalil yayi, don shi da badan ritsa shi da aka yi ba, da yanzu haka yana hanyar Nassarawa wajen matarsa, "Yauwa, to na kiraka ne in kuma jaddada maka maganata akan sakin matarka, Ibrahim wallahi dole ne ka saki yarinyar nan, ƴaƴa kuma ni da kai na zan aika har Nassarawar a ɗauko min su, kar ka damu ba zan barka babu mace ba tunda ka riga ka saba da mata, na zaɓo maka cikin dangi, ba kuma ƴar kowa bace sai ƴar ƙanwata Habbooba, yarinya fara tas kyakkyawa da ita. Don haka idan ba so kake na ɗaga maka nono ba, dole ne ka saki yarinyar nan, ehe. Aure kowa ya san ba dole bane, shikuwa saki surah sukutum aka saukar a kansa, Allah da kansa shi ya halatta sakin aure! Kuma na riga nayi rantsuwa sai ka saki Saratu!" Kan Khalil a ƙasa babu abunda yake zubarwa face hawaye. Ya Abdullah gyaran murya yayi tare da faɗin, "Hajiya, Ta yiwu ɗaya daga cikin dalilan da ya sa ake kiran wannan sura da sunan surar saki (Ɗalak) shi ne irin hukunce hukuncen sakin da suke ƙunshe a cikinta makil, wanda wannan yana nuna mana irin la'akarin da shari'ar musulunci ta yi dangane da al'amarin saki, saboda irin hatsarin da yake da shi, domin abu ne wanda in har ba'a yi da gaske ba, kuma ba'a yi shi yanda musuluci ya zo da shi ba, sai ka samu ya taimaka wajen wargaza al'umma da tarbiyyar iyali, kana da haifar da gaba da kiyayya a tsakanin dangi. Kamar yanda rashin kiyaye hukuncin sakin ke iya haifar da aure kan aure, wanda daga karshe a dinga haife 'ya'ya marasa tabbas ɗin iyaye. Kamar yanda kuma, shi saki ba wani abu ne wanda shari'a ke ƙarfafa gudanar da shi ba, bil hasali ma shi ne halas wanda Allah ya fi ƙi, kamar yanda ya zo a mashahuriyar ruwaya daga Ma'asumai (A.S.) "Babu wani abu da Allah ya halatta kuma yake fushi da shi fiye da saki. Wannan ruwayar ta zo cikin Wasa'ilus shi'ah juzu'i na 15 shafi na 266. Sai dai kuma wani abin tambaya a nan shi ne, mene ne ya sa shari'a ta halatta yin saki ? Amsa a nan ita ce a irin hali na zaman yau da gobe na ma'aurata a wasu lokuta za ka samu cewa akwai wasu halaye waɗanda suke faruwa marasa daɗi wanda in da za'a tilasta ci gaba da zama da juna a tare da waɗannan halayen, sai mu samu rayuwa za ta yi ma wanda yake cutuwa, tsanani da kunci wanda zai iya kaiwa ga halaka da abin da ya yi kama da haka. To saboda Allah ne mahaliccin kowa da komai, kuma asanin abin da zai kai ya kawo, don haka ya kawo magani da mafita a duk lokacin da irin waɗannan matsaloli suka bijiro a tsakanin ma'aurata, wanda wannan magani shi ne saki, duk da cewa ba'a son al'amarin ya kai ga haka, sai ya zama dole. Musulunci addini ne da ya ƙunshi komai da komai don inganta rayuwar ɗan Adam a duniya da Lahira. Bai bar ɗan Adam ya yi amfani da hankali da tunaninsa kawai don tsara wa kansa makoma ba, saboda shi ɗan Adam mai rauni ne, mai son zuciya ne, mai haɗakma ne, mai rowa ne, kai ƙarewa ma mai butulci ne ga wanda Ya halicce shi. To in har zai yi butulci ga Mahaliccinsa, ta yaya zai tsara rayuwar da sauran abokan zamansa za su ji daɗi? Aure daya ne daga cikin ginshiƙan rayuwar al’umma, wannan ya sa Musulunci bai bar shi sasakai ba ƙa’idoji da dokoki ba. Kuma baya ga ƙa’idojin zamantakewa a tsakanin ma’auratan, duk da ba a fata, amma ya tsara yadda za a rabu idan aka kasa samun jituwa ko maslaha a tsakanin miji da matar. Saki a matsayin zaɓi na ƙarshe:
Ko da yake an halasta saki a Musulunci alama ce ta sassauci da aiki da tsarin shari'ar Musulunci, kiyaye haɗin kai na iyali yana ɗaukar fifiko don kare yara. Saboda wannan dalili, saki a koda yaushe zabin karshe ne, bayan gajiyar dukkan hanyoyin sulhu. Misali, Allah yana magana da maza yana tambayar su da su yi ƙoƙari don kiyaye auren, koda sun ƙi matansu: Ku zauna da su bisa tushen kyautatawa da adalci. To, idan kun ƙi su, akwai tsammãnin ku, ku ƙi wani abu, kuma Allah ya sanya albarka a cikinta. Surah 4 Aya 19
Haka nan ayar nan tana magana ne ga mata suna tambayarsu irin wannan: Idan mace ta ji tsoron zalunta ko tawaya daga bangaren mijinta, Bãbu laifi a kansu idan suka yi sulhu a tsakãninsu, Surah 4 Aya 128, wannan ayar tana magana ne ga dangi ko kuma al'umma don wannan manufa ta kubutar da wannan alaka, wanda Allah bai sauwake wa karya ba: Idan kun ji tsõron sãɓa a tsakãninsu, (biyu) masu sasantawa, daya daga danginsa, da sauran daga nata; idan suna fatan zaman lafiya, Allah zai daidaita su: Kuma Allah Masani ne, kuma Masani ne ga dukkan komai. Surah 4 Aya 35, Amma, idan bayan gajiyar dukkan hanyoyin sulhu, Ƙiyayyar da ke tsakanin miji da mata har yanzu ta fi haƙuri, sannan saki ya zama babu makawa. Ga kuma hazakar shari’ar Musulunci, wanda ke da amfani, maimakon hanyoyin da ba su dace ba, zuwa ga haƙiƙanin yanayi. Maƙasudin aure, da kuma duk wani ɓangare na rayuwar dan Adam, su ne don cimma farin ciki da nagarta. Don haka, lokacin da aka hana mutane hakkinsu na kashe auren da ba a yi daɗi ba, waɗannan biyun an keta su sosai. Wannan shine, kamar yadda ma'aurata za su rayu cikin wahala, wanda zai iya kai su ga rashin imani a aure. Don haka saki a cikin wannan yanayin - idan an auna har zuwa bala'in rarrabuwar iyali – zai zama ƙasa da bala'i.
Maza suna da hakkin saki. Idan mutum baya son kiyaye aurensa saboda wani dalili, sai ya saki matarsa ​​kuma ya biya mata kudi ta hanyar biyan ta abin da ake ce wa mut’a. Wannan kari ne akan abin da ake yi mata na kudi akai-akai, idan har tana da hakkin 'ya'yansu.
Saki ya fara aiki da zarar miji ya furta ko ya rubuta duk wata ka'idojin saki na shari'a kamar: ‘Na sake ki’ ko ‘kin sakeki’...da sauransu. Miji na iya yin wadannan ko dai da kansa ko kuma ta hanyar manzo (Ɗan aike).Idan har sha'awar mace ce ta yanke auren, lamarin ya zama daban. Dalilinta na iya zama cewa ta sami rashin lafiya, miji baya iya ciyar da ita kudi ko kuma ba ya da karfin jima'i. Za ta iya tabbatar da wadannan aibu a gaban alkali, sai alkali ya ba ta saki tare da samun cikakkiyar damar samun dukkan hakkokinta na kudi.
Hakanan, idan mijin ya kyautata mata amma ba ta son ci gaba saboda wani dalili na zuci, sai ta tambaya me ake ce masa khul’. Wannan yana nufin a ba da saki amma ba tare da samun dama ga haƙƙin kuɗi ba, da kuma biyawa mijin sadakin da ya riga ya biya akan aurenta. Hajiya, duk na kori maki wannan jawaban ne saboda kisan cewa shi fa kalmar saki ba abun da za ayi wasa dashi bane, A wasu lokuta, furta kalmar saki ya zama mara amfani. Daga cikin wadannan har da lokacin da miji yake:1.) Buguwa. 2.) Wani ya tilasta musu furta su. 3.) Cikin tsananin bacin rai har bai san abinda yake fada ba. 4.) A cikin yanayi mara kyau na hankali, kamar hauka na wucin gadi, farfadiya ko a cikin suma. A irin wadannan lokuta, saki banza ne. Kin ga kuma Khalil na ƙaunar matarsa, kece kawai kike son tilasta masa ya sake ta. Hajiya bari nayi maki wani tambaya dan Allah, shin a zaman da kika yi da matar Khalil na kimanin shekaru biyu da ɗoriya, shin kin taɓa ganin wani mummunar hali da take dashi? Shin ta taɓa zaginki? Ta taɓa dukanki? Ta taɓa hana ɗanki zuwa gareki ko kuma yi maki wani alkhairin? Bin bata girmamaki da yi maki biyayya?" Shuru Hajiya tayi, can kuma ta girgiza kai tare da faɗin, "Ko ɗaya, Saratu bata taɓa yi min ɗaya daga cikin abubuwan daka lissafo ba." "To kin gani Hajiya! Hakan na nufin baiwar Allahn nan bata yi maki komai ba, kawai laifin ƴar uwarta ne yake son shafarta. Hajiya dan girman ubangijin halitta, ki sassautawa zuciyarki ki bar maganar Khalil ya saki matarsa, wallahi Allah zai yi fushi dake idan har kika tilasta masa rabuwa da matarsa, don wallahi zaki iya haddasa ɓanna a bayan ƙasa, zata iya yuwuwa, ki tsinke igiyar dake tsakaninsu, amma kuma suje suna bibiyar juna a waje bayan babu aure tsakanin su, kuma kin ga idan har haka ta faru, wallahi kina da babban kamasho! Hajiya ina roƙon wannan Alfarmar, ki sassautawa Ibrahim kar ki raba shi da matarsa dan Allah!" Ya Abdallah ya ƙarisa maganar a tausashe. "Uhm! Naji bayanka Marmari, kuma na gamsu, sai dai nima ina da nawa sharuɗɗan." Gyara zama Ya Abdullahi yayi, Khalil wani sanyin rahama ne ya shiga ziyartar lungu da saƙon jikinsa jin Hajiya ta janye ƙudurin saki, he is willing to accept all her sharuɗɗa in har zata amince ya cigaba da zama da his light. "Na farko dai dole ne ya auri Habbooba, na biyu, kar ya kuskura ya wulaƙanta min ƴa saboda matarsa kuma kar ya bawa matarsa fuskan da zata wulaƙantamin ƴa saboda tana taƙamar ita ce matar so, na uku, yayi takakkiya har Maiduguri yaje ya nemo soyayyar Habbooba, don ita ba _matar shige_ bace, idan har ya cika duk wannan, na amince ya cigaba da zama da matarsa, zan yi azumi uku na rantsuwar da nayi." Faɗin Hajiya, "To kai kaji Khalil, shin ka amince na abunda Hajiya tace." Gabansa na bugun tara-tara ya ɗago ya kalli ya Abdallah, sannan ya kalli Hajiya tare da sunkuyar da kai ya furta, "Na amince da duk abunda kika ce Hajiya. Zan je Nassarawa na dawo da Sarah, bayan na dawo sai in tafi Maidugurin!"


( _Ni kuwa nace Uhmmm! To me zance ni Matar Sayyadeen banda uhm ɗin? Dan-dan-dan-dan-dan-dan! Akafta_ 🙆)



*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID
Showing 123001 words to 126000 words out of 129453 words