Lukman yace, sai ince ɗansa namiji yake nema." Da mamaki Khalil ya kalli Lami tare da faɗin, "Mama dama kina da ɗa namiji?" Gyaɗa kai tayi tare da share guntun hawaye tana kuma jin tsoron da kunyar faɗin Lukman ya mutu da kuma sanadin mutuwar tasa don ko ƴan uwansa basu sani ba, daga ita sai ƙawarta Aunty Rose Merry suka san komai, su Na'ima kuwa sun ɗauka yana can yawon banza da sace-sacen da ya saba. Khalil bai ƙara cewa komai ba sai juyawa da yayi ya kalli baba dake ta ƙoƙarin magana amma babu baki, kuma ba kowa yake kira ba sai Aina'u yana faɗin, "Allah ya isa tsakanina da Aina'u" su Khalil kuma Aina'un kawai suke ji shima kuma cikin karyewar harce sai kalmar yake yi masu kamar Aliyu. Bayan fitan Khalil daga ɗakin sai Lami ta juyo ta kalli Sarah tare da faɗin, "Sarah, kin san kuwa har yanzu babu wanda yasan inda Aina'u take! Yau watanni uku kenan rabon da na saka ta a idanu." Da sauri Sarah ta kalli Lami tare da faɗin, "Wai dama baku san tana gidana ba? Ai tana can wajen Hajiya, Maman Khalil." Da mamaki Lami tace, "Gidanki? Tun yaushe?" Sarah tace, "Ai ta jima, zata kai kusan watanni ukun da kwanaki, duk da nima sai in haɗa sati biyu ban ganta ba." Riƙe haɓa Lami tayi tare da faɗin, "Lallai Aina'u! Yanzu kuma ta san babanku ba lafiya amma ta rasa zuwa duba shi." Watsa hannu Sarah tayi tare da faɗin, "Ohooo! Ta damu dashi ne? Ni wallahi Lami, wani lokacin Aina'u tsoro take bani. Tana da mugun hali." Wani irin jijjiga baba ya fara yi yana watsa hannunsa na dama alamar dai magana yake yi amma babu mai gane abunda yake cewa, kuma Sarah yake kallo yana watsa hannun. Fadi yake Sarah ta kori Aina'u a gidanta, amma kuma bata gane ba sai kukan da take yi ganin yanda ya burkice, fita tayi da gudu tayi office ɗin Khalil, yana ciki yana duba wata petient ta afka tare da kamo hannunsa zuwa ɗakin baban. Allurar bacci yayi masa, nan da nan baccin ya kwashesa, sannan Khalil yace duk su fita daga ɗakin su bar shi ya huta. Aina'u kuwa kwananta goma a ɗakin Hajiya babu ci babu sha sai ƙarban azaba daga hannun _Hell Ofulafu_ take yi babu ƙaƙƙautawa. Dukan safe daban, na rana da ban, haka na dare. Kuma har wannan lokacin Hajiya bata san da dawowarta ba, ba ƙaramin alwashi da mugun nufi Aina'u take yi ba a zuciyarta duk lokacin da ta samu sassauci da yafiyar Hell, wani irin tsanar Sarah ta kuma ji ya ninku a zuciyarta. Watan su Sarah ɗaya a asibiti aka sallame su, idan kaga twins baza ka taɓa cewa bakwaini bane, sun yi ƙiba abunsu, haka ma Sarah ta ƙara cika tayi kyau, baba ma an sallame shi duk da jikin na nan dai jiya i yau, sai dai Khalil yace zai riƙa zuwa har gida yana yi masa gashi wanda in Sha Allah zai taimakawa jikin nasa. Satin na zagayo da sallamar su aka yi wani gagarumin taron sunan twins, _Sam'an_ da _Sauban_. Irin kyaututtukan da Sarah ta samu faɗi ɓata baki, a gaban idanun Aina'u akai komai, don ta samu sassaucin azabar, sai jinya jikinta da take yi yanzu, tayi wani irin rama da baƙi, haushi da tsanar kowa take yi a gidan, hotunan Khalilullah dake wayanta kawai take kallo taji sanyi azuciya. Khalil ya maida komai nasa da sunan Sam'an da Sauban, wani irin mahaukacin soyayya yake gwadawa Sarah da ƴaƴanta. Khalil ya bawa su Na'ima miliyan biyu-biyu kowaccen su har da Lami, sannan ya saya masu wani four bedroom flat a Jama'a road, tare da saka dukkansu a islamiyya kuma Alhamdulillah duk sun fara zuwa kuma natsuwa ta soma shiga jikinsu. Hajiya damuwarta ɗaya, ta rasa abunda ke mata daɗi a duniya, wani irin abu take ji ya tsaya mata a zuciya amma ta rasa menene wannan abun, sai ta zauna shuru tana tunani, duk tabi ta rame ita da ya Abdul-Hakeem. Kuma har yanzu ta kasa tambayarsa akan matarsa da kuma zaman gida da yake yi babu aiki. Aina'u kuwa ta warke garas, sai dai tsafinta ba zai taɓa ƙara amfani ba sai nan da shekara ɗaya, haka Hell ya faɗa mata. Baiwar Allah Sarah kuwa, yanzu bata da damuwar komai, ta warke garas kamar bata taɓa ciwo ba, tun da ta haihu bata ƙara ganin tsutsotsin nan ko guda ɗaya daga jikinta ba, sannan wannan warin da mijinta yake yi mata duk babu. Wani irin soyayya suke shimfiɗawa wanda ko lokacin da take amarya basu yi ba. Twins sun shiga wata shidda da haihuwa, yara tubarkalla don har tsayuwa suna yi idan suka kama abu, kamanninsu ya ƙara fitowa sosai da Khalil, ga wayau. Sun san Laure sosai don itace mai taya Sarah raino, amma kuma abunda ke matukar bawa Sarah mamaki shine, ko muryan Aina'u suka ji gaba ɗaya rikicewa suke yi suna kuka, Sam'an shi har wani kakkafewa yake yi..........



_Asha weekend lafiya 🤩_

*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_MATAR SAYYADEE_*

*Paid book 08128755583*

🦜 *KANWAR MATATA* 🦜

*31*


Tsaye take a tsakiyar ɗakin tana wani irin dariya mai tafe da hawaye baƙin ciki da kuma farin ciki lokaci guda, domin bayan tsawon shekara ɗaya har da wata uku, jiya da daddare _Hell Ofulafu_ ya dawo mata da makamanta, yanzu tana iya ganin komai ta tsakiyar tafin hannunta, sannan tana iya magana da _Hell_ da wannan mummunar halittar duk ta tafin hannun nata. Tsafinta ya ninku yanzu ta yanda tana iya ganin mutum idan taso har a jikin bango, sannan ta jikin bangon zata iya yi masa duk abunda taga dama, yanzu haka ma, tana kallon Sam'an da Sauban dake tsere a parlour, pampers ne kawai a jikinsu, tuntuni Sarah ke so tayi masu wanka amma da wannan yayi can, sai wancen ya zille yayi can, Khalil na zaune kan kujera sai dariya yake yi mata kuma yaƙi tashi ya taimaka ya kamo mata su, shekaransu ɗaya da wata uku cif, amma wayansu ya zarce tunanin mai karatu, ga magana a bakinsu kamar uwar aku. Idan Sarah ko Khalil suna so su tantancesu, sai su kira suna, misali sai suce Sam'an! To Sam'an ɗin ne zai juyo Sauban kuma harkan gabansa zai cigaba dayi kasancewar ko ita kanta Sarah sai tayi dagaske take bambance su, daga baya kamar sun gane, idan aka ce Sauban ko Sam'an, sai gaba ɗaya su juyo. Khalil ruɗewa yake yi sai ya shiga tambayar Sarah, "Dan Allah wanene Sam'an, wanene Sauban a cikinsu?" Taɓe baki take yi tare da faɗin, "Ka gano da kanka ai kai babansu ne, idan a waje aka tambaye ka yaya za kayi?" Sai Khalil yace, "To ai shiyasa nake son ki bambance min tunda ke kina gane su gudun kar inji kunya watarana!" Idan ya faɗi hakan sai ta nuna su ɗaya bayan ɗaya, ita kanta tana ganesu ne da ɗabi'unsu, Sauban yana da faram-faram kuma yana da dogon fuska, Sam'an kuma bai cika faram-faram ba, kuma fuskansa bata kai ta Sauban ɗin tsayi ba duk da shima dogon fuskan garesa, babu abunda suka ɗauko na Sarah idan ka cire dimple, amma bayan haka kaf kamannin Khalil suka yo. Wani kalan murtuke fuska Aina'u tayi ganin yanda Sarah da Khalil suke wasa suna zagaye parlourn su da ƴan biyun nasu. "Wannan shine ƙarshe farin cikinki a cikin gidan nan, ni Aina'u sai na baƙanta maki fiye da yanda kika baƙanta min, sai na wulaƙanta rayuwarki, sai na saka ki hawayen jini, sai na ruguza zuciyarki, sai na ɓalɓalta rayuwarki dana ƴaƴanki, sai na kashe ki da baƙin ciki, sai nayi kwanciyar aure da mijinki a gaban idanunki, sai na zama kishiyarki, na kuma ƙasƙantar dake. Babu aure tsakanina da mijinki, amma na rantse da Ubangijin mu Yesu Almasihu mai ceto, sai nayi tarayya da mijinki kuma a cikin gidan nan a gaban uban kowa, kuma duk wanda yace zai kawo mi shamaƙi ko shishshigi, sai na kashe shi!" Tana gama faɗin haka ta ɗauko wani icce wanda aka ɗaɗɗaure shi kamar ƴar tsana sannan ta jawo wani tulu daga ƙasan gado mai ɗauke da wani irin baƙin ruwa mai kauri sannan ta ambaci sunan Khalil sau uku sannan ta tsunduma iccen nan har sai da guiwar hannunta ya shige ciki sannan ta fiddo hannun, wani mugun murmushi ta saki tare da saka ɗayan hannunta ta fizgi gashin kanta sannan ta tura a cikin ramin idanun wannan iccen da ya koma ƴar tsana amma bana itace ba, sannan ta tsaki saitin zuciyar ƴar tsanar nan har sai da hannunta ya lume tare da ambatan sunanta sau uku sannan ta saki ƴar tsanan cikin tulun ya bata sautin 'tsumbul', sai ta mayar da tulun ƙarkashin gado tare da duƙawa ƙasan guiwowinta ta leƙa ƙarƙashin gadon ta jawo wasu ƴan tsanar guda biyar, ɗaya bayan ɗaya ta riƙa tsaka wani abu mai tsini a ƙahon zuciyarsu sannan ta jefa cikin tulun nan ta miƙe tana jin wani irin matsanaicin farin ciki ganin gaba ɗaya ɗakin ya turniƙe da hayaƙi da kuma wani irin duhu, can kuma bayan mintuna talatin komai ya washe, kuma dama _Hell_ yace idan har hakan ta faru bayan kammala aikinta, to hakan na nufin aikinta yayi! Khalil ya kai hannu zai cafki Sarah dake ƙoƙarin kama Sam'an yaji wani irin abu kamar mashi ya soki zuciyarsa da ƙarfi, wani irin baya yayi zai faɗi Sarah ta kai hannu ta riƙosa amma duk da haka sai da suka kai ƙasa saboda gaba ɗaya jikinsa ne ya saki. A ruɗe ta shiga kiran sunansa tana jijjigasa har hawaye ya wanke fuskanta, ƴan biyu kamar sun san abinda ke faruwa sai suma suka zagaye Khalil ɗin suna jijjiga cikinsa, shi kuwa duk yana jinsu, amma sai ya rasa shin a wani duniya yake, a hankali yaji zafin zuciyar na raguwa, can kuma sai ya soma jin wani baƙon al'amari na shiga zuciyarsa, kuma ya rasa shin farin ciki yake yi ko akasin haka. Zuwa can sai ya miƙe da sauri yana mai riƙe kansa, "Happy lafiya? Mai ke damunka?" Sarah ta faɗi tana mai kai hannu goshinsa, twins ma da gwarancinsu suka haɗa baki suka ce, "apy yafila? (Happy lafiya?)" Murmushi Khalil yayi tare da dungure masu kai yana faɗin, "Dan gidanku, daddy ba apy ba." Murmushi ƙarfin hali Sarah tayi don gaba ɗaya hankalinta bai jikinta, duniya bata ƙaunar Khalil yayi ciwo don bai iya ciwo ba. Kamun yayi yana jimawa, amma kuma idan ya tashi yi, kamar ba zai yi raiba haka yake. Tashi yayi tare da faɗin, "Kaina ne ya ɗan sara min, amma nasan ina shan magani zai tafi, bari naje na ɗan huta kamun lokacin sallah yayi." Gyaɗa masa kai kawai Sarah tayi jiki duk sake. Kumatunta ya kama tare da faɗin, "Smile now! Ba mutuwa zanyi ba, muna nan tare mutuwar ma baza ta raba mu ba, tare zata ɗauke mu." Duk da haka yaƙe kawai tayi, shi kuma ya hau sama ya barsu nan parlour. Jiki a sanyaye Sarah ta wuni, aikin ma dai kawai yinsa take yi. Shi kuwa Khalil, koda ya koma ɗakinsa, bai iya baccin ba, tunani kawai ya riƙa yi, can kuma ya sauko don haka nan yaji yana son zuwa side ɗin Hajiya. Saukowa yayi lokacin Sarah na ɗaya parlourn ita da yara, ba tare da ya neme su ba ya fice abunda bai taɓa yi ba. Ita kuwa Sarah bata san da fitarsa ba, ta ɗauka har a wannan lokacin yana sama a ɗakinsa. Aina'u kuma tana fitowa daga ɗakita, kai tsaye ɗakin Hajiya tayi hannunta riƙe da wani baƙin padlock, ba tare da knocking ba ta murɗa handle ɗin ƙofar da ƙarfi tare da faɗin, "Hajiya!" A razane kasancewar ita nata sihirin _Hell_ yace sai ta firgita tukun zai kamata. A razane Hajiyar ta juyo, cikin sauri Aina'u ta ɗaga padlock ɗin tare da datse shi tana dariyar samun nasara. "Aina'u kina buƙatar wani abu ne?" Hajiyan ta samu kanta da faɗin haka. Aina'u kuwa domin tabbatarwa sai cewa tayi, "Buɗe bakinki ki tsaya a haka." Nan take Hajiyar tayi kamar yanda Aina'un tace. Wani irin dariya Aina'u ta saki tare da faɗin, "To rufe bakin." Tuf Hajiya ta rufe tana mai bin Aina'u da idanu. Zaro mata idanu Aina'u tayi tare da faɗin, "Bar kallo na!" Da sauri Hajiya ta sunkuyar da kai ita kuma Aina'u ta maka mata harara tare da faɗin, "Da ace lokacin da na kira ki a waya domin ki dakatar da ɗanki ga auren yayata, kin dakatar, da yanzu kina zaune cikin lumana babu tashin hankali, amma tunda baki yi hakan ba, yanzu aka soma wasan!" Tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin tare da fitowa parlour dai-dai lokacin da Khalil ya turo ƙofa ya shigo, idanu huɗu suka yi da juna, wani irin ajiyar zuciya Khalil ya sauke tare da sakarwa Aina'u wani irin murmushi wanda ya kusa sumar da ita. "Aina'u!" Ya kira sunansa cikin wani irin salo, "Na'am Khalilullah mijin Saratu!" Ajiyar zuciya ya kuma saki for the second time sannan ya zauna tare da faɗin, "Zauna mana Ai'n." Yanda ya gajerta sunanta sai taji kamar duk duniya babu wanda ya iya kiran sunan kamarsa, zama tayi daf dashi kasancewar a 2sitter ya zauna, fuskantar yayi tare da faɗin, "Oh, Ai'n kamar ba cikin gidan nan kike ba, ko zuwa wajen ƴar uwarki bakya yi balle a haɗu a gaisa." Wani farrrrr da idanu tayi tare da faɗin, "To ai ku ɗinne love bird, sam baku buƙatar irin mu masu hana ruwa gudu kusa daku, kullum kafi son ganinka naniƙe jikin matarka." Kau da maganar yayi tare da faɗin, "To yanzu dai muna gayyatarki shashinmu domin taya mu hira." "As you wish, your excellency!" Dariya Khalil yayi tare da faɗin, "Sai kace wani gomna. Mu dai muna jiranki, na miƙa maki katin gayyata kullum da daddare kike zuwa kina taya mu hira!" Faɗin Khalil. "An gama ranka ya daɗe." Faɗin Aina'u. Daga nan Aina'u ta riƙa jansa da hira, sai ga Khalil har da kyakyatawa. Kamar yanda Khalil ya buƙata, da daddare sai ga Aina'u cikin wani irin mahaukacin kwalliyar ɗaukar hankali, gaba ɗaya suka kan dinning suna cin abinci ta murɗa handle ta shigo, Khalil ne ya fara juyawa fuskansa ɗauke da murmushi yana mai faɗin, "Ƙariso nan Aina'u ayi dinner ɗin dake. Sauban na riƙe a wajensa, jin muryan Aina'u duk sai ya rikice yana neman guduwa wajen uwarsa, Sam'an dake wajenta riƙe hannunta yayi gaam jikinsa na rawa. Sarah kuwa murmushi tayi tare da faɗin, "Aina'u kenan, kamar ba gida ɗaya muke ba! Ko kin koma gida ne?" Taɓe baki Aina'un tayi tare da faɗin, "Baki so gani na bane kawai." Ta faɗi hakane tare da jawo kujeran kusa da Khalil ta zauna a kai tare da kallon Khalil ɗin tare da narke fuska. tana mai faɗin, "To ayi serving ɗina mana, ko da kaina zanyi." Cikin sauri Khalil ya miƙe tare da ajiye Sauban, shi kuwa dama abunda yake jira kenan da gudu ya nufi gun mamarsa yana kuka, ita kuwa Sarah wani irin maɗaukakin mamaki ne ya rufeta ganin yanda jikin Khalil yake rawa don kawai zai zubawa Aina'u da basu taɓa ga macijiba abinci. Sai kawai ta zuba idanu tana kallon ikon Allah. "Ai'n ga couscous, ga jellof rice, wanne za'a zuba maki?" Ɗaga idanu sama tayi tare da faɗin, "Wanda kake ci shi zaka zuba min." Jellof rice ɗin ya zuba mata tare da kaza sannan ya ki plate ɗin har gabanta tare da faɗin, "Gashi _Ƙanwar matata_" wani irin ƙululun baƙin cikine ya mamaye zuciyar Aina'u jin sunan da ya kira ta dashi wai _Ƙanwar matata_! "Nafi gaban haka wallahi!" Aina'u ta faɗi cikin zuciya, amma a zahiri sai tayi wani irin murmushi tare da kallon yanayin Sarah ta gefen idanu, abun yayi wa Aina'u daɗi ganin confusion a idanun Saran. Spoon ta saka ta ɗebo abincin tare da sakawa a baki, lunshe idanu tayi jin wani daɗi da ya mamaye kunnuwanta don Sarah gwana ce wajen iya girki duk da ba yi suke yi a gida ba. Aina'u na cin abinci a lokaci guda kuma tana jan Khalil da hira, shi
Showing 96001 words to 99000 words out of 129453 words