ka! Laure babu baki, ni da maƙoƙo da zazzagowar idanu, surukata kuma da aman tsutsotsi. Kai Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Allah mun tuba." Faɗin hajiya tana mai fashewa da kuka. "Hajiya kiyi haƙuri ki bar kuka, in Sha Allah, zasu samu sauƙi, ku taso mu tafi gida, to amma wa zai kwana da Laure tunda ba'a bata sallama ba?" Share hawaye Hajiya tayi tare da faɗin, "Tare da ita zamu tafi tunda itama bayan rashin maganar babu abunda ke damunta, kuma ba gida muka yi ba kai tsaye, zamu fara biyawa ta gidansu Uwata domin taho da ƙanwarta ta ɗan zauna damu kaga ni ba ishashshen lafiya ba, Laure kuma babu baki, dole ina neman mai taimako." "Kuma Hajiya sai a rasa wacce za'a ɗauko domin taimakon ki sai ƙanwar matar Khalil, a'a gaskiya Hajiya, don ni haka nan yarinyar bata kwanta min a rai ba." Faɗin yaya Abdul-Hakeem. "To ni ta kwanta min, kuma dole ka kaini gidan na taho da ita." Faɗin Hajiya tana hararensa. Bai kuma cewa komai ba ya juya ya ɗauki akwatin kayan haihuwar Nafeesa ya fita dashi, ita kuma Nafeesa ta rungumo babynta Hajiya a bayanta suka fito. Can gidan su Sarah kuwa, Aina'u ta gama shirinta tsaf don tana ganin komai ta tsakiyar tafin hannunta. Suna parking a ƙofar gidansu ta saki wani murmushi tare da faɗin, "This is the end of you Saratouh Nuhu!" Fitowa kawai Aina'u tayi da akwati a hannu ta fito waje, kallonta Abdul-Hakeem yayi ta yi yana mamakin dama ta san da zuwansu ne ganin ba tare da an shiga da sun shiga ciki ba, kuma basu tura kowa ba har ta fito. Da kanta ta buɗe boat ta saka kayanta a ciki tare da rufewa ta zagayo ta buɗe gidan baya ta shiga tare da rufe motar tana faɗin, "Hajiya ina wuni, ya kuma ƙarfin jikin?" Ita kanta Hajiyar ba ƙaramin mamaki tayi ba jin furucin Aina'u, "Ya akai tasan bani da lafiya?" Faɗin Hajiya cikin zuciya. Amma a fili sai cewa tayi, "Jiki Alhamdulillah Aina'u." Kallon jaririyar hannun Nafeesa tayi tare da faɗin, "An samu ƙaruwa? To Allah ya raya." Ba tare da tunanin komai ba Nafeesa ta miƙa mata jariyar, hannu biyu Aina'u ta amshi jinjirar tana mai faɗin, "kyakkyawa da ita!" Daidai nan yarinyar ta tsandara wani mahaukacin ihuu sai da ya Abdul-Hakeem dake driving ya juyo da sauri yana faɗin, "Lafiya?" Babu wanda ya bashi amsa sai miƙa hannu da Nafeesa tayi tare da amsar jinjirar, sai kuma tsit kamar an ɗauke ruwan sama. Aina'u kuwa wani murmushi tayi ganin kurwar ƴar na yawo a saman motar, can kuma sai ga fuskan *_Hell Ofulafula_* ya wani irin zaro harshe tare da lashe kurwar jinjiran yana mai jinjiwa Aina'un sannan fuskar tasa wanda Aina'u kaɗai ke gani ya ɓace. Khalil kuwa yana parking da gudu ya nufi side ɗinsu yana tsatstsallake step uku-uku har ya isa ƙofar ɗakin Sarah, cikinsa ne ya bada wani irin saurin kuuuuuuuuu tsabar wani dunƙulallan wari da ya shaƙa, amma stil haka ya tura ƙofar ya faɗa ɗakin. Tsalle ɗaya yayi ya isa inda take tare da rungumota gaba ɗaya a jikinsa.............





*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_MATAR SAYYADEE_*


🦜 *KANWAR MATATA* 🦜

*27*


"Mutuwa zan yi, mutuwa zan yi Khalil! Wannan ciwon nawa na tafiya ne. Ni kuma haka nawa ƙaddarar yake! Na shiga uku! Baka jin wani irin wari da ƙarnin da nake yi? Aunty Maryam ma ta kasa zama dani a ɗakin nan saboda wari da nake yi, na zama abun kyama!" Wasu irin hawaye ne suka wanke fuskan Khalil amma yayi saurin sharewa saboda baya don zuciyarta ya cigaba da karaya. "Sarah duk duniya idan sun kyamace ki, ni zan kyamace ki ne? Wallahi babu wannan ciwon aduniya da za kiyi na kyamace ki! Ba gani nan ba, kina buƙatar kulawar wani ne bayan nawa? Shin na gaza ne?? Sarah nayi alƙawarin muna tare for better for worse, babu abunda zai iya shiga tsakanina dake don wata lalura ta same ki. Yanzu zan ɗauke ki muje asibiti a duba min jikinki, bari na gyara miki jiki da ɗakin." Ya faɗi hakane tare da janyeta daga jikinsa ya sauka daga kan gadon, kallon wandon jikinsa yayi sai yaga gaba ɗaya tsutsotsin ne manne a jikin wandon, sunkuyar da kai Sarah tayi tana mai jin nauyinsa, ta san tabbas yana ƙaunarta sosai, amma bata taɓa tunanin zai iya yin abunda yake yi mata a yanzu ba, ba tare da kyama ba. Wandon ya cire ya rage daga shi sai boxer sannan ya cicciɓeta ya kaita bathroom yayi mata wanka, abunda ya matukar bashi tsoro shine, ganin yanda tsutsotsin suke ɓulɓulowa, ɗazu da ya wanke mata, su daina fitowa amma kuma yanzu idan yana wankowa kamar ƙara turosu ake yi. "Ya Ilahi!" Shine abunda Khalil ya furta tare da kinkimarta ya fito da ita ya zaunar akan resting chair sannan ya gyara gadon, yanzu kam Sarah ba kuka take yi ba, ido kawai take bin Khalil dashi tana jin wani irin ƙaunarsa na ƙara huda tsokar dake ƙirjinta da ilahirin jikinta har ji take tsigar jikinta na tashi ganin yanda yake nannaɗo zanin gado da hannunsa duk da kuwa tsutsar na taɓa jikinsa, tana kallon yanda tsokar jikinsa shima yake tashi amma a fuska baza ka taɓa ganin wani yanayi na kyama a tattare dashi ba. Wayarsa taga ya ɗauko yayi danne-danne kamun ya kwashi zanin yayin gadon yayi bayi dasu. Ya jima a bayin yana wanke zanin da hannunsa da ya saka handglove sannan ya sake ɗauraye jikinsa yayi wanka tare da ɗauro alwala don lokacin tuni har an idar da Sallar la'asar. Hajiya kuwa suna dawowa gida ta buɗe motar tare da kamo hannun Laure tana jin wani irin mugun tausayinta, da ace tunda ta taso ne bata jin magana da sauƙi da ace lokaci guda kwatsam ta samu lalurar, "Sannu kinji Laure, Allah ya baki lafiya." Ga mamakin Hajiya sai taga Lauren ta ɗaga kanta alamar ta amsa sannun hajiyan, "Laure! Laure, kin ji abunda nace kenan? Alhamdulillah jin Laure ya dawo." Da saurin Nafeesa da ya Abdul-Hakeem suka iso wajen suna faɗin, "Laure kina jin komai yanzu?" Ƙara gyaɗa kai Lauren tayi hawaye na zubo mata daga idanunta, Aina'u kuwa wani taɓe baki tayi don ita ce nan tayi magana da _Hell Ofulafu_ ta cikin tafin hannunta, akan ya dawo da jin Lauren ta yanda idan tayi mata magana za taji, kasancewar ya bata wani abu ta haɗiya idan har tana son wani abu ba sai ta kuma komawa Abia ba, tana matse hannun ta buɗe zai bayyana ta tsakiyar tafin hannunta. "Laure kiyi magana mana, ko baza ki iya ba?" Hajiya ta tambayeta tana mai riƙo hannunta biyu. "Girgiza kai Laure tayi alamar baza ta iya ba." Kuka Hajiya ta fashe dashi tare da faɗin, "Kiyi haƙuri Laure, yanda Allah ya buɗi kunnuwanki, haka zai buɗe bakinki nan kusa in Sha Allah! Muje ciki." Ta faɗi tare da janta gaba, Aina'u kuwa boat ta buɗe tare da ɗauko akwatin ta tabi bayan Nafeesa dake gabanta tana kalonta da gawar babynta dake hannunta tana dariya cikin zuciya. Ya Abdul-Hakeem kuma ɗakin matarsa ya nufa wacce itama tana can tashin hankali ya saukar mata da zazzafan zazzaɓi. Khalil yana idar da sallar la'asar ya koma bayan gidan tare da ɗauko buta da baho ya kawo gaban Sarah ya dunga tsiyaya mata ruwan har ta kammala alwala sannan ya mayar da komai bayin ya fito ya buɗe wardrobe ɗinta ya ɗauko mata hijjab tare da saka mata yace, "Mine kiyi sallah ki kai wa Allah kukanki, in Sha Allah zai yaye maki wannan cutar. Bari na sauka ƙasa na karɓo saƙo." Gyaɗa masa kai kawai tayi tare da kabbara sallar bayan ta kalli gabas a zaunen da take, shi kuma ya fice. Kallon motar ya Abdul-Hakeem yayi tare da faɗin, "Sun dawo kenan!" Cikin zuciya tare da nufar gate, leda ya karɓa a hannun wani matashin yaro irin masu delivery ɗin nan ya dawo cikin gidan ya nufi side ɗin Hajiya, gaba ɗaya a parlour ya same su, Hajiya ta zabga tagumi tare da zubawa Laure idanu. Kallon Laure yayi wacce lokaci guda ta zabge, duk wannan fara'ar da barkwancin sun tafi, sai kallon kowa take yi a firgice. "Ina wuni ya Khalil." Aina'u ta faɗi tana zuba murmushi don babu abunda bata gani ta cikin tafin hannunta, har wanka da alwalar da yayiwa Sarah yanzu da kuma fitar da yayi ya amshi saƙo, bama wannan ba, hatta yanda zuciyarsa ke bugawa da jinin dake zagaye ilahirin jikinsa tana kallon a yanzu haka. Kallon ɗaya yayiwa inda take ya kau da kai ba tare da ya amsa gaisuwarta ba. "Mu'azzam ba gaishe ka Ƙanwar matarka take yi ba!" Hajiya ta faɗi tare da ɗan ɓata rai. "Ita ɗin *_ƘANWAR MATATA_* ce kawai, bayan nan babu abunda muka haɗa Hajiya." Faɗin Khalil cikin zuciya, amma a zahiri sai cewa yayi, "Lafiya!" A tilastance tare da zama akan kujera yana mai fuskantar Laure yace, "Ƙawata ya jikin naki? Allah ya baki lafiya kinji! Ina sha Allah komai zai wuce." Ya faɗi hakane duk da yasan ba zata ji ba, amma ga mamakinsa sai taga ta gyaɗa masa kai tana hawaye. Da sauri ya kalli Hajiya, tun kan yayi magana hajiyan tace, "Cikin hukuncin ubangiji sai ga jin ya dawo, maganar ma nan kusa in Sha Allah." Da murmushi ya juya tare da kallonta yace, "Ki kwantar da hankalinki, in Sha Allah komai zai wuce, ji cigaba da addu'a. Wannan jarabawace daga Ubangijin halitta." Jinjina kai Laure tayi tana mai kallon Aina'u a sace, karaf sai suka haɗa idanu, wani mugun harara Aina'un ta sakar mata tayi saurin kawar da kai, don wani irin mugun tsoron Aina'un take yi, duk suka haɗa idanu sai gabanta ya yanke ya faɗi. "Sai kuma naji wani maganar tashin hankali Mu'azzam, dagaske ne matarka ba lafiya tana aman tsutsotsi?" Hajiya ta faɗi kamar ta fashe da kuka. Cike da damuwa Khalil yace, "Hakane Hajiya, yanzu ma asibiti zamu tafi da ita." Ko kamun Hajiya tayi magana Aina'u ta buga wani irin ihu miƙewa ta dafe ƙirji tare da fashewa da kuka tace, "Wayyoo Allah mun shiga uku, Sarah ce ke aman tsutsotsin?" Wani hararan gefen idanu Khalil yayi mata tare da faɗin, "As if she care!" A cikin zuciyarsa. Hajiya kuma ƙoƙarin kamo hannun Aina'un tayi amma ta goce tare da fita da gudu daga ɗakin, taɓe baki Khalil yayi tare da ajiye ledan da ya shigo dashi a gefe ya kai hannu ya ɗauki babyn Nafeesa akan kujera, tun shigowarsa yake satan kallon babyn, sai yake gani kamar babu rai a jikinta. Cikin dabara ya kai hannunsa saitin hancin babyn, amma bai ji alamun numfashi ba, taɓa pulse ɗin yarinyar ya kuma yi nan ma yaji baya harbawa, wani wawan ajiyar zuciya ya sauke tare da kallon Nafeesa ta gefen idanu, don ba ƙaramin tausayi ta bashi ba. Ba'a mamakin mutuwa, amma yayi mamakin mutuwar babyn Nafeesa, don ko da Nafeesa ta haifeta, lafiyarta ƙalau kuma akwai kuzari sosai a jikinta da ƙosashshen lafiya! Rufe babyn yayi har kai tare da shimfiɗar da ita a kan kujeran ba tare da ya kalli Nafeesa ba. Nafeesa kuwa kallo ɗaya tayiwa babyn da khalil ya ajiye taji zuciyarta ya buga da ƙarfi bata ma san lokacin da ta buga tsalle ta isa gaban kujeran da ya ajiye babyn ba. "Lafiya Khalilullah ka lulluɓe jaririyar har ka kamar wata gawa?" Faɗin Hajiya wacce gabanta ke faɗuwa kamar zai faso ƙirjinta ya faɗo don ta san idan har aka rufe ɗan adam har ka hakan na nufin babu shi. Girgiza kai Khalil yayi yana kallon tiles ɗin dake shimfiɗe, Hajiya bata san lokacin da ta furta, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Nafeesa kuwa kuka ta fashe dashi tana mai jijjiga hannun Khalil tana faɗin, "Don Allah kar kace min ta mutu, ka sake dubata da kyau, lafiya ƙalau muka baro asibiti, Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Na shiga uku!!" Faɗin Nafeesa tana kallon babyn nata, hannunta kuma yana kan na Khalil dake kallon ƙasa idanunsa sun cika da hawaye. Hajiya kai hannu tayi ta ɗauki jaririyar tana ƙara dubata, kuka ta fashe dashi bayan tabbatar da yarinyar ta koma, "Hajiya ƙarfafa mata guiwa za kiyi ba ki karya mata zuciya da kukanki ba, ita nata tayi kyau tunda bata ɗibi zunubin komai ba, mune abun jin ba ita ba. Allah yasa mai ceto ce. Nafeesa nasan abun da zafi, amma kiyi haƙuri, Allah da ya karɓe abunsa ya fiki sonta, ki gode masa ta hanyar yin tawakkali, kuma dama shi da kansa yace ba wai don munce munyi imani ba shikenan ba zai jarabce mu ba. Allah zai baki wata in Sha Allah, ai ba cewa akai baza ki ƙara haihuwa ba. Ki kwantar da hankalinki kinji, Allah ya baki haƙurin rashi!" Gyaɗa kai Nafeesa tayi zafafan hawaye suna kwaranyo mata, miƙewa yayi ya ɗauki kasar da ya shigo da ita ya fita daga ɗakin don zai iya zubar da hawaye idan yana kallonsu, "Allah mun gode maka, Allah kasa muci wannan jarabawar!" Ya faɗi tare da nufa side ɗin yaya Abdul-Hakeem. Knocking yayi, ba jimawa yaya Abdul-Hakeem ɗin ya buɗe masa ƙofa, "Lafiya Ibrahim?" Faɗin ya Abdul-Hakeem ɗin ganin yanayin Khalil ɗin. "Allah ya yiwa ƴar wajen Nafeesa rasuwa yanzu." Da sauri ya Abdul-Hakeem ɗin yace, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ba dai jinjirar ba?" Ko kamun Khalil yace wani abu har Aunty Maryam ta iso wajen gabanta na wani irin bugawar tsoro da tashin hankali, don duk a tunaninta Sarah ce ta mutu. "Wallahi kuwa ita, yanzu na shiga ɗakin, su basu ma sani ba sai da na ɗauki yarinyar na duba pulse ɗinta don tun da na kalleta sau ɗaya na fahimci babu rai a jikinta." "Wacece ta mutu?" Aunty Maryam ta faɗi a firgice. "Ƴar wajen Nafeesa ce." Ya Abdul-Hakeem ya bata amsa. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Ba yanzu kake faɗa min ta haihu ba? Mun shiga uku daga wannan sai wannan!" Khalil yace, "Haba Aunty Maryam, Kar kiyi saɓo mana!" Kuka Aunty Maryam ta fashe dashi daidai lokacin da wayar ya Abdul-Hakeem ɗin yayi ƙara. "Gama mijinta nan yana kirana." Ya faɗi tare da picking kiran shi kuma Khalil ya juya tare da nufa side ɗinsa. Aina'u na shiga parlourn Sarah ta fashe da dariya har da kyakyatawa tare da faɗin, "Su Mine da Happiness kenan, ai yanzu aka soma wasan wallahi, ina nan zuwa gare ka Khalil, wallahi sai na mayar da kai masarrafin talabijin!" Sama ta hau tare da tura ɗakin Sarah, da gudu ta fito tana mai danne ƙirjinta saboda wani uban wari daya busota, "Bala'iiiii, gaskiya _Hell Ofulafu_ ka iya aiki, wannan bala'in wari haka, ai ko Lami da babanmu masoyinta baza su iya jurewa ba balle kuma miji! Taɓ, sunanki sorry Saratu. Aini ko buɗe Ƙofar ban iya ƙara yi bare in shiga ciki. Allah dai ya ƙara azabar da yafi haka." Aina'u ta faɗi tare da saukowa ƙasa tana mayar da numfashi. Turo ƙofar Khalil yayi ya shigo, ganin Aina'u zaune akan kujera ya saka shi sakin wani malalacin murmushi tare da faɗin, "Hmm! Har kin gama ihun tashin hankali akan ƴar uwarki na aman tsutsotsi? Kin kasa isa wajenta ko? Dama na san baza ki iya ba, wacce ke ciwon da bai kai wannan ba kin kasa taimakonta sai wannan ne zaki taimaka mata! Nasan wallahi duk ƙaunarki da kuɗi, ko nawa zan baki, baza ki iya kula da ƴar uwarki ba, ban dai sani ba ko idan kinga tana shashshekar mutuwa za ki iya, to ina so ki sani, Ni ba zan taɓa gazawa ba da matata, zan mutune matsayin bawa mai hidimta mata! Ki fice min a ɗaki yanzun nan!! Ke _ƘANWAR MATATA_ ce amma ban san mai yasa ba, baki taɓa burgeni ba, ban sani ba ko hakan nada nasaba da nuna rashin son ƙulluwar auren mu da Sarah tun farko!" Yana gama faɗin hakan ya haura sama. Sai da gabansa ya faɗi jin warin ninkuwa yayi a kan nada, ga tsutsotsi ne nan faca-faca tun daga kan kujeran da take kai har ƙasa, ita kuma kifa kanta kawai tayi akan hannun kujeran tana shashshekar kuka don kukan
Showing 81001 words to 84000 words out of 129453 words