yayi ya kalli Sarah tare da nuna mata ƙofa yace, "Get out of this house right now, and don't forget to go with your kids!" Hawaye kawai Sarah keyi tana kallonsa, irin kallon kar kayi min haka. Juya baya yayi yana hawaye gabansa na wani irin faɗuwa. Sarah kuwa wani irin kuka ne ya kufce mata, da sauri ta ƙarisa kusa dashi ta ɗuka tare da riƙe ƙafafunsa ta shiga faɗin, "Happiness, Kar Kayi min haka, ka manta alƙawarin da kayi min? Ka manta kace min zamu kasance tare, for better for worse, ka mance kace baza ka taɓa bari nayi hawayen baƙin ciki ba, ka manta kace an halicceni ne domin ka, kai ma Kuma an halicce ka ne domin ni? Ka dubi girman Allah ko don Sam'an da Sauban ka barni a ɗakin mijina." Da ƙarfi Aina'u tace, "Capital NO! You're more welcome. Park your things and get lost!" "Da mijina nake magana ba dake ba Aina'u!" Sarah ta faɗi da ƙarfi. Wani shu'umin murmushi Aina'u tayi tare da faɗin, "To ai shi kansa mijin da umarnina yake amfani. Ko baki san ni nace ya kore ki ba?" Sarah bata bata amsa ba ta cigaba da yiwa Khalil magiya. Tureta Khalil yayi tare da faɗin, "Please Sarah, don't make things worse, just do as I said." Yana gama faɗin haka ya tashi ya fita. Aina'u sai da tayi mata gwalo sannan ta fice daga ɗakin, "Sarah ki tashi kawai ki tafi kar ƴar iskan nan ta saka Khalil ya yanke igiyoyin aurenki dake kansa." Wata zuciyar ta faɗa mata haka. Da sauri ta tattare kayan ta zuba a akwati ta zuge zip tare da saka hijjab sannan ta jawo akwatin zuwa parlour ta ɗauki Sam'an ta riƙe Sauban kuma ta goya shi, sai da ta ƙarewa parlourn kallo sannan ta murɗa handle ta fita tana kuka, tana zuwan wajen gate, kamar ance ta juyo, sai ta ganshi a bayanta yana hawaye, buɗe hannunta yayi tare da saka mata Atm card ɗinsa tare da faɗin, "Current account, date of birth ɗinki ne pin ɗin. Ki kular min da kanki da yaranmu." Caraf Sarah ta rike hannun tana kuka tana girgiza masa kai, shima hawayen yake yi tare da ƙoƙarin kwatar hannunsa, da kyar ya zame hannun tare da yiwa Sam'an kiss a goshi yace, "I'm going to miss you son, ku tayani neman gafarar mummynku." Yana gama faɗin haka ya juya da sauri. Kuka sosai Sarah tayi ta rusawa kamun ta juya tare da jan akwatin suka fice daga gidan..........


( _Wannan scene ɗin ya taɓa min Heart 😭 da gaskiyar Sarah da tace Aina'u ƴar wuta ce_)

*Kuyi haƙuri da rashin ganin update jiya, transformer ɗin mu ce ta buga*



*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*





*_MATAR SAYYADEE_*

*Paid book 08128755583*
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜

*34*


Sai da ta juyo ta kuma ƙarewa gidan kallo sannan ta soma tafiya tana hawaye, kasancewar gidan babu nisa da bakin titi nan da nan ta iso bakin titin tana nishi don ba ƙaramin kaya bane a cikin akwatin har da atamfofinta na lefe kusan kala ashirin a ciki wanda ba'a ɗinka ba, don ta kwashe wasu ta saka cikin wardrobe da kuma wasu akwatinan don da maƙil yake da kaya, yanzu kuma ga kayanta dana su Sauban a ciki sannan kuma ga goyo ga kuma Sam'an dake hannu. Tsaye tayi a bakin titin tana tunanin inda zata, don ji tayi gaba ɗaya bata ƙaunar komawa gidansu, gashi kuma babu wani wajen da take dashi da zata je. "Lafiya state!" Ta faɗi a bayyane tare da saurin nufa wani shagon pos dake bakin titin ta ciri dubu hamsin tana yin hamdala a zuciya saboda taimakonta da Allah yayi wajen sa Khalil ɗin ya kawo mata ATMcard ɗinsa da yanzu bata san yanda za tayi ba don ita bata samu sararin da ta ɗauko nata ATM ɗin ba da kuma kuɗinta da take ajiye a ɗakin duk lokacin da Khalil ɗin yayi mata kyauta. Napep ta tsayar tace masa tashar kawo ze kaita, shi dakansa ya fito ya saka mata akwatin a ciki sannan ta shiga, har cikin tashar ya kaita tare da fiddo mata da kayanta sannan ta biya shi hakkinsa ta ja akwatin ta soma tafiya, nan da nan aka soma tambayarta inda zata, "Nasarawa zani!" Da sauri wani tsoho a ciki yace, "Taho nan muje dama ke kawai muke jira motar ta cika." Hamdala tayi cikin zuciyarta jin saura mutun ɗaya, don ta bala'in ƙosawa ta bar kaduna. Bayan kowa ya bada kuɗin mota tare da rubuta address da number waya da suna sannan driver yaja motar suka ɗau hanya. Sai da suka hau hanya sosai sannan gabanta ya hau faɗuwa kasancewar bata taɓa zuwa ba, sunan garin da unguwan kawai take ji a bakin baba, ga kuma ƴan biyu da suke ta yi mata kuka a cikin motar, sai wajajen ƙarfe biyar suka isa, daga nan ta roƙi mai motar akan y taimaka mata wanba zata kuma bata san garin ba, nan ya sakata a motar wamba, ko da suka isa wamba, da tambaya aka kawota layin abakwa da take ji baba Nuhu na yawan ambata matsayin layinsu. Kalle-kalle kawai take yi ta rasa inda zata nufa, gashi isha'i ake neman yi don garin ya soma duhu, wajen wani gindin bishiya ta nufa inda ta hango dattijai su bakwai a zaune a kan tabarma, da kyar take tafiya, Sauban yayi bacci a bayanta, Sam'an shima haka sagale a kafaɗanta, ga kuma ƙatuwar akwati tana ja. Har ƙasa ta ɗuka bayan tayi sallama sun amsa mata, sai duk suka zuba mata idanu suna kallonta da mamaki, gashi dai bata yi kama da mabaraciya ba balle suyi tunanin bara tazo yi. "Sannunku da hutawa baba, Ina wuni?" Faɗin Sarah, sai gaba ɗaya suka amsa mata da "Lafiya ƙalau." Cikin gurɓatacciyar hausarsu. "Baba dan Allah tambaya nake yi, ina neman gidan wani ana ce masa Nuhu, amma ya jima da barin garin nan." Kallo-kallo suka shiga yi, can kuma ɗaya daga ciki yayi wa na kusa dashi magana a kunne, sai wanda aka yiwa maganar a kunne yace, "Nuhu? Shekarunsa nawa da barin nan, kuma kin tabbata ɗan nan ɗin ne?" Shuru Sarah tayi na ƴan wasu daƙiƙu kamun tace, "Eh to, a yanda dai yake bamu labari ya tabbatar mana dashi haifaffan nan ne, kuma yace sunan unguwarmu layin abakwa, sunan mahaifinsa Murtala, mahaifiyarsa kuma Zainabu! Sannan kuma ya bar garin nan shekaru talatin da huɗu kenan, ya bar garin ne saboda ƴan uwansa basu so ya auri budurwar da yake so kasancewar ta kirista mai suna Elizabeth ana yi mata inkiya da (Lami)." Gaba ɗaya wajen suka ɗauka da faɗin, "La'ilaha illalah Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallama! Wannan ai Nuhu na wajen mu take magana a kai!" Ɗaya daga cikinsu ya ƙarisa maganar da faɗin haka. "Ke yarinya ya kuke dashi?" Tun kamun tayi magana wanda ke ɗan gab da ita yace, "Tun da yarinyar ta ɗuka anan nake kallon fuskanta, babu hoton wanda na gani a kwance a fuskanta sai na ɗan uwana Nuhu." Ya ƙarisa maganar yana share guntun hawaye. "Ƴarsa ce ni!" Sarah ta faɗi muryanta na cracking. Su uku dake wajen suka miƙe a tare tare da faɗin, "Taso yarinya, gida kika zo, duk nan iyayenki ne." Wani irin sanyi da salama Sarah taji yana shiga jikinta. Miƙewa tayi ta soma bin bayansu kasancewar ɗayan ya ɗauki akwatin yayi gaba, sai ya kasance yaran ne kawai a hannunta da ƙaramin handbag ɗin da ta saya a lokacin da suka sauka. Ƙatoton gidane irin na da ɗin nan wanda aka yi sa da ginin ƙasa, sai dai yasha gyara da abubuwan zamani, kuma akwai wasu gina-gine guda biyu a tsakiyar gidan da aka yi su da cement blocks. Ɗaya daga cikin ginin bulo suka nufa mai kyau dashi, Sarah sai kalle-kalle take yi hannunta dafe da bayan Sam'an dake kwance a kafaɗanta. Hannu ya saka ya murɗa handle ɗin ƙofar tare da yin sallama sannan ya shiga. Babu kowa a parlourn sai fankar sama dake gudu sosai. "Zauna mana, suna cikine, bari na kira su." Ya faɗi hakan yana mai nuna mata kujera sannan ya bi wani ɗan dogon hanya a parlourn. Sarah kuwa kamun ta zauna sai da ta gama ƙarewa tsaftaccen parlourn mai ɗauke da set ɗin kujeru da kuma Tv bango 32 inches da idanu sannan ta shimfiɗar da Sam'an a kan 3sitter tare da kwanto Sauban sannan ta zauna ta rungumesa tana cigaba da ƙarewa parlourn kallo har idanunta suka sauka akan wani ƙatoton hoto a jikin bangon ɗaki ta bangon arewa, ƙurawa hoton idanun tayi duk da kuwa irin Black and White ɗin nan ne, su huɗu ne reras a jikin hoton, waro idanu tayi sosai tana ƙara kallon hoton da kyau, baba Nuhu ne zaune a kan wata farar kujeran ƙarfe shigen irin ta sarauta, sai wani ta gefen hagunsa mai irin kamanninsa babu bambanci yana murmushi sannan ya dafa mai kama dashi sak ɗin nan dake zaune a kan kujera, sai wannan mutumin da ya kawota cikin ɗakin da take yanzu a ta gefen wanda ya dafa baba Nuhu ya ɗan leƙo shima yana murmushi, sai shima mai kama dashi sak ta hannun damar wanda ke zaune a kan kujera ya turo hulan kansa gaba tulun gashin da ya tara ya fito ta baya da kuma gefe-gefe kansa stil shima yana murmushi, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, kaii! Kenan da baba da wannan mai kama dashi ɗin ƴan biyu ne, shima kuma wannan da ya kawo ni nan shima ɗin ƴan biyune kenan? Kenan anan nayi gadon ƴan biyu, ikon Allah!" Cike da tsantsan mamaki tayi maganar a bayyane. Daga ƙarshe sai ta tashi ta isa wajen hoton tana kallo daga tsaye. Da wani irin ihuu da murna taji an rungumeta ta baya, da sauri ta waigo tana mai cin karo da fuskan wata kyakkyawar yarinya mai kama da ita, gaba ɗayansu waro idanu suka yi suna mai shafa fuskansu suna kuma dariya at the same time, "Sunana Suhana, yarinyar wannan dake zaune a hotonan!" Suhana ta faɗi tana mai nuna hoton wanda ke zaune, don ita Sarah a tunaninta ma shine baba Nuhu, sai Suhana ta nuna shi matsayin mahaifinta, sai ta fahimci baba Nuhu shine na tsayan. "Abbana da Abbanki are twins!" Suhana ta kuma faɗi tana dariya tare da kamo hannun Sarah wacce ke ta kallon fuskar Suhana kuma murmushi yaƙi barin fuskanta. "Uwar surutu, kin tsareta da surutun ko? Ai sai ki wuce ki haɗa mata ruwan zafi a bayi tayi wanka taji daɗin jikinta sai taci abinci." Faɗin wannan da ya kawo ta cikin gidan cikin yaren _Nindire_, bayansa kuma wata kyakkyawar mata ce mai fara'a sosai, haƙorinta guda ɗaya na gefen dama na Makka ne sai kyalli yake yi. "Wallahi ga kama nan, ai surprise zamu bawa su Ya Hassan da Nnanne, sai da safe tukun duk zasu ganta." Faɗin matar tana kallon Suhana tare da faɗin, "Saura kuma kije ki faɗa masu, don na sanki da tsinannan surutu!" Turo baki Suhan tayi tare da faɗin, "kaji ta ko Ba Lukman!" Da sauri Sarah ta kalli wanda Suhan ɗin ta kira da Ba Lukman tana murmushi gano ashe wanta Lukman sunan wannan ɗin baba ya saka masa. "Baki faɗa mana sunanki ba yarinya!" Faɗin Ba Lukman. Sunkuyar da kai Sarah tayi tare da faɗin, "Sunana Saratu!" Da sauri ba Lukman yace, "Kai! Kai!! Kai!!! Suna mai girma da daraja Nuhu ya saka maki, ai sunan wacce ta riƙe mu duka kenan har shi bayan mutuwar mahaifiyarmu, kuma ita ɗin ƙanwace ga mahaifiyarmu uwa ɗaya uba ɗaya." Murmushi Sarah tayi yayin da matar Ba Lukman ta nufi inda twins suke tana kallonsu, "Tubarkalla ma sha Allah! Kaga ƴaƴa kyawawa kamar su suka yi kansu, ni wannan ma ai sun fiku nuna kamanni, taɓ! Zan iya bambance su kuwa?" Ta faɗi cikin yare, Sarah da bata jin ko zo in kashe ka, sai binsu da idanu take yi. Ba Lukman ma ƙarisawa kusa dasu yayi yana kallonsu cike da ƙaunarsu daidai lokacin da Sauban ya farka yana mai furta, "Mummyyyy, I want to piii." Ko kamun tayi wani motsi har Suhana ta isa wajen tare da sunkutoshi, shi kuwa bai mata ƙiwa ba, don suna matukar kama da Sarah shiyasa bai gane ba Sarah bace ta ɗauke shi, po ta ɗauko wankakke tas kamar ba'a komai a ciki ta ɗaurasa a kai, tana kallon fuskansa, "Momma, har da pupu zan yi!" Dariya Suhana tayi tare da faɗin, "To kayi!" Kallonta Sauban yayi ta yi kamar yana so ya gano ba mummynsa bace, sai da ya gama kashin ta wanke masa, wajen mayar masa da wando suka soma faɗa don yaƙi sam ya mayar da wandon, daga ƙarshe sai ya lankwashe ƙafar yana kuka, leƙowa Suhana tayi tare da faɗin, "Yaƙi yarda in mayar masa da wando." Sarah nufar akwatinsu tayi ta kwantar tare da fiddo masa wani wandon ta miƙawa Suhan tana mai faɗin, "Ai su haka suke, idan suka yi pupu basu taɓa yarda su mayar da wandon jikinsu sai dai wani." "Yaran nawa ashe ƴan gayu ne!" Faɗin Suhana bayan ta karɓi wandon. "Saratu ki shiga wancen bayin kiyi wanka sai kizo kici abinci." Kai sunkuye Sarah tace, "To Baba!" Ta ƙarisa maganar tare da cire hijjab ɗin jikinta ta ninke ta ajiye a hannun kujera sannan ta nufi bayi. Suhana na dawowa parlourn Sam'an shima ya tashi, sai ta haɗa su ta rungume duka a jikinta. Bayan Sarah ta fito daga wanka, sai Suhana ta nuna mata ɗakin da zata shiga domin tayi shiri ita kuma ta nufi bayi da twins domin yi masu wanka. Sarah tana shiga ɗakin, ko mai bata shafa ba, riga kawai ta zura tare shimfiɗa dardumar da ta gani a gefen gado tare shimfiɗawa ta saka hijjab ta tada sallah, sai da tayi na magrib da isha sannan ta kuma tada sallah tayi raka'a biyu, a sujadarta na ƙarshe ta shiga kwararo bukatun tana kuka sosai. Ta jima a sujada tana kai kukanta ga mahaliccinta......



_Anticipate a long page tomorrow, wallahi har yanzu ban jin daɗi, Wannan ma dakyar nayi_




*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_K'ANWAR MATATA ISN'T FREE, PAY #500 VIA THIS ACCOUNT NUMBER 0592412800 ZULFAU SAID GTBANK AND SEND YOUR EVIDENCE OF PAYMENT THROUGH THIS NUMBER 08128755583_*

_MATAR SAYYADEE_






🦜 *KANWAR MATATA* 🦜

*35*



Bayan ta idar da sallar, sai ta jingina da gado tana tunanin Khalil hawaye na zubo mata, hannu ta
Showing 108001 words to 111000 words out of 129453 words