'Ya mace! GARKUWAR MATA ðŸ‘👠fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👠Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
*_MATAR SAYYADEE_*
*Paid book 08128755583*
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*30*
Numfashinta ne ya soma ɗauke, idanuwanta kuma suka soma rufewa ga wani irin azababbiyar azabar da take ji a ƙasanta. Hannu ta kai ƙasanta ta kuma taɓo gashin kan babynta daya soma turowa, wani irin ƙarfine ya kuma zuwa mata, da ƙarfi ta furta, "La'ilaha illalah Muhammadur Rasulullah, Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Take taji kamar hannun da ya shaƙi wuyarta an janye shi da ƙarfi, a wani irin nishi tayi mai ƙarfi daidai lokacin da Khalil ya turo ƙofar, da gudu ya ƙarisa tare da taro babyn da yayi fut ya fito, idanunta ne ya soma rufewa kuma ga wani kan babyn na ƙoƙarin fitowa amma kuma ƙarfinta ya soma ƙarewa saboda wahalar da tasha, cinyarta ya soma bugu bayan ya ajiye jaririn dake tsandara kuka akan gado, cicibarta yayi ya kwantar akan resting chair ɗin dake ɗakin ya soma ƙoƙarin cetonta, da taimakonsa Sarah ta kuma sunkuto ɗayan jaririn, yana fitowa ita kuwa ta sume. Rasa inda zai saka kansa yayi, sai ya mance gaba ɗaya taimakon da zai yi mata, da sauri ya fita daga ɗakin ya koma nashi ɗakin ya dawo hannunsa ɗauke da sabuwar reza ya yanke cibin yaran, basu da muguwar ƙanƙanta kamar ba bakwainiba, kuma dukansu maza kamar Khalil ɗin yayi kaki. Ruwa ya shafawa Sarah a fuskanta yana goga tafin ƙafarta har ta farfaɗo, rungumeta yayi tare da faɗin, "Kin gama min komai Sarah, thank you, thank you Soo much mine, mai kike so a duniyar nan inyi maki shi yanzu nan?" Murmushi tayi tare da faɗin, "Ka cigaba da sona har bayan raina, kar ka juya min baya a kowani irin hali!" Ta ƙarisa maganar tana mai shafa fuskansa. Hannu ya kama yayi kissing sannan yace, "Kin riga kin daɗe da samun wannan Sarah, Khalil naki ne ke ɗaya har abada. Tashi mu tafi asibiti a duba min ke." Aina'u gudu take yi akan titi kamar mahaukaciya domin Sarah na fara salati hotonta ya ɓace a tafin hannunta na _Hell Ofulafu_ da wannan mummunar halittar ya bayyana gaba ɗaya fuskansu ɓutu-ɓutu, mummunar halittar nan ya soma magana da ƙarfi, "Kar ki kuskura ki bari a fita da jariran nan daga gidan nan, idan ba haka ba zaki fuskanci hukunci har na tsawon shekara ɗaya, Hell ba zai ƙara amsa buƙatunki ba, don idan har suka bar gidan, jinin jariran bazai shawu ma Hell ba, kasancewar sun shaƙi iskar waje." Yana gama faɗin haka suka ɓace ita kuma ta hau buga uban sauri, cikin ikon ubangiji duk keken da ta tsayar sai yace mata ba zai je unguwar ba. Kawai sai ta hau gudu kamar mahaukaciya a kan titi. Khalil fita yayi ya nufi ɗakin Hajiya jikinsa har rawa yake yi tsabar murna, murɗa handle ɗin yayi don ƙofar a rufe take, tun da Aina'u ta nufi Abi, Hajiya ta tsiri rufe shashinta, shiga yayi amma babu kowa a parlour, kai tsaye ɗakin hajiyan ya nufa, zaune ya same su ita da Laure sun yi jigum-jigum. "Hajiya Sarah ta sauka! Kin samu mazaje har biyu!" Out of excitement ya faɗi. Hajiya ta mance rabon da tayi murna a rayuwarta irin yau, Laure kuwa kuka ta fashe dashi tare da fita da gudu ta nufi part ɗin Khalil ɗin, so take tayi magana ta nunawa Khalil irin farin cikin da take ciki, amma kuma babu bakin maganar, Hajiya Kuma ƙasa ta nufa tare da yin sujada sannan ta ɗago tare da fashewa da kuka tana faɗin, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Allah ubangiji ya raya bisa sunnar ma'aiki ya kuma karesu daga dukkan sharrin mutum da aljan. Muje Mu'azzam inga jikokin nawa!" Ta ƙarisa maganar tana mai share hawaye. "Hajiya ai ɗauki hijjab ɗinki kawai don daga nan asibiti muka yi. Yaran da uwar suna buƙatar kulawar likitoci." Juyawa Hajiya tayi ta ɗauki hijjab har da na Laure sannan tabi bayan Khalil, a can ɗaki kuwa, Laure har ta soma gyara jinin Sarah da ya lalata ɗakin, abun mamaki kuma babu tsutsa ko ɗaya. Hajiya ɗaukar ƴaƴan tayi duka biyun ta rungume a jikinta tana jin wani irin ƙaunarsu na ratsa jikinta, "Sannu kinji, Allah yayi maki albarka uwata, sannu da ƙoƙari." Murmushi kawai Sarah tayi tare da sunkuyar da kai ƙasa. "Ɗauko mata mayafinta mu wuce asibitin." Faɗin Hajiya tana kallon Khalil ɗin, da sauri ya ɗauko hijjab a cikin wardrobe ya saka mata tare da miƙar da ita tsaye sannan ya ɗauko silipas ya saka mata. Sai da Hajiya ta saka masu kayan sanyi sannan ta miƙawa Khalil Hassan yayi masa kiran sallah a kunna tare da yi masa huɗuba da sunansa, (Ibrahim Khalil) Hussaini kuma ya saka masa sunan mahaifin Sarah (Nuhu). Hajiya riƙe da Hassan, Laure kuma ɗauke da Hussain suka fita daga ɗakin, Khalil ya kama hannun Sarah suka sauka ƙasa tare da fita daga ɗakin gaba ɗaya suka nufi parking space. A gidan baya ta zauna ita da Hajiya, shi kuma da Laure a gaba, kamar ance ya kalli ƙasa, sai ya hango kwalin _Mastika gum_ a ƙasa, da sauri ya kai hannu ya ɗauko tare da ɓare kwalin ya ɗau ɗaya ya jefa a baki yana murmushi don har ya manta rabon daya kai chewing gum bakinsa. Suna fita daga gidan keke napep ɗin da Aina'u ke ciki ya tsaya, zuciyarta sai da tayi wani irin tsalle ganin motar Khalil ya fito daga cikin gida, ko kamun ta yunkura motar Khalil ta kusa bakin titi don gidan yana gaba da titi ne. Haɗa kai tayi da guiwa tare da fashewa da kukan baƙin ciki. Juyowa mai napep ɗin yayi tare da faɗin, "Lafiya baiwar Allah?" Ba tare da tace komai ba ta fito daga napep ɗin saboda tsabar rashin imani ta bugi goshinsa da tafin hannunta tare da faɗin, " _Hell_ ga jinin wannan matsayin sassaucin hukuncinka gareni." Da sauri mai napep ɗin nan yaja kekensa ya bar layin don ya tsorata da abinda Aina'u tace, sai dai yana zuwa titin bypass, trailer tabi ta kansa. Aina'u kuwa shiga cikin gidan tayi rai a mugun ɓace ta nufi side ɗin Hajiya. A can asibiti kuwa, jariran a incubator aka saka su sannan itama uwar aka shiga kula da jikinta, sai dai aka mata ɗinki uku sannan aka saka mata ƙarin ruwa domin taji ƙarfin jikinta. Hajiya kuwa ta ɗauki waya ta dunga kiran dangi da abokan arziki tana shaida masu matar Khalil ta samu ƙaruwan ƴan biyu. Khalil kuwa bayan Sarah ta samu barci, sai ya sulale ya fita domin zuwa can gidansu Sarah ya shaida masu Sarah ta haihu. Wajajen ƙarfe goman Safiya, gaba ɗaya suna zaune tsakar gida suna karyawa, Na'ima ta kalli Lami tare da faɗin, "Lami baza ki duba baba? Tun safe ban ni ɗuriyarsa ba, ko wa'azin da ya saba kunnawa banji ya kunna ba." Taɓe baki tayi tare da faɗin, "Yesu ne yayi min maganinsa! Ai ba ƙaramin addu'a nake yi ba akan Nuhu ya daina kashe mana kunne da wannan karatu da wa'azin nan da yake saka mana ba, har fata nake Allah yasa Tv ɗin ya lalace ko kuma ya faɗo daga saman ya fashe." Miƙewa Na'ima tayi tare da nufa ɗakin baban ta ɗaga labule, wani irin ihuu ta saka tare da faɗin, "Baba ya mutu mun shiga uku!" Ai a sittin daga Lamin har sauran suka nufo ɗakin don ganin halin da yake ciki. Gashi nan dai kamar me rai kamar kuma gawa! Baki a karkace, hannu a lankwashe, ƙafa ɗaya da hannu a shanye. "Yes......" Da ƙarfi Hassana tace, "Dalla Lami ki rufe mana baki, baba na cikin wannan halin shine kike ƙoƙarin kira mana Yesu, Allah dai ya tsinewa wannan addini da kika koma!" Da sauri Lami tace, "Zan ci ubanki idan kika zagi addinina, ai gwara ni kowa yasan ba addinin sallah nake yi ba, kuma duk Sunday sai naje Church, ku Kuma fa? Sai dai kullum ayi ta faɗi a baki mu musulmai ne, amma ko sau ɗaya ba'a yin sallar!" A fusace Marfu'a tace, "Dan Allah Lami ku bar wannan maganar aji da lafiyar baba." Daidai nan suka jiyo sallamar Khalil a ƙofar gida don tun yana hanya yake kiran layin baba amma ba'a ɗagawa kasancewar bargo ya rufe wayar shiyasa su Aina'u basu ji ringing ɗin ba. "Kamar muryan mijin Sarah!" Faɗin Na'ima tare da fitowa daga ɗakin ta nufi kwar gida, "Alhamdulillah!" Faɗin Na'ima bayan taga Khalil ɗin tsaye a ƙofar gida, "Shigo Khalil, Allah ne ya turo mana kai wallahi. Babane babu lafiya yana can kwance gaba ɗaya rabin jikinsa ya shanye." Da sauri yace, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Tare da gitta Na'iman ya wuce ciki da sauri. Hassana da Marfu'a sai sharan hawaye suke yi ganin kamar babu rai a jikin baban, suna ganin Khalil suka matsa suka bashi hanya. Cicciɓan baba yayi tare da fito dashi daga ɗakin ya nufi mota, gaba ɗaya suka rufa masa baya har da Lami wacce ko arzikin mayafi babu a jikinta, hatta su Na'iman ma babu mayafin a jikinsu. Lami, baba Hassana da Marfu'a a baya, Na'ima kuma ta zauna gaba ita da Nuratu. Sai da suka hau titi sannan Khalil ya ɗan juyo ya kalli Lami tare da faɗin, "Mama, Sarah ta sauka, ta samu ƴan biyu duk maza yau da safe, dan girman Allah kar a faɗa mata halin da baba yake ciki don itama tana can asibitin ita da yaran don an saka su a kwalba ne kasancewar basu isa watannin haihuwa ba." Gaba ɗayansu cike da mamaki da kuma farin ciki suka furta, "Ƴan biyu! Inna lillahi, Hassana ashe Sarah ce zata riga ki." Na'ima ta ƙarisa da faɗin haka, Lami kuwa cewa tayi, "Yesu Almasihu nagode maka da wannan kyauta da kai min, a lokacin da ka kwace lafiyan mijina, sai kayi min kyauta da jika har biyu." Tana gama faɗin haka sai ta hau waƙa, " _Yayi! Yayi!! Yesu yayi!!! Yayi, yayi...._" "Ke dallah Lami ana jimamin halin baba kin zo kin wani dame mu da zancen banza! Yesun me? Mu Allah ne zai cecemu ba wani yesunki ba!" Faɗin Marfu'a dake kusa da ita. Lami kuwa sai da ta saka bayan hannu ta bugi Marfu'an sannan tace, " _Ya Allah mai-iko duka, Uban Ubangijinmu Isa Almasihu, wanda ba ya son mutuwar mai-zunubi ba, amma ya fi son shi juyo ga barin muguntassa, shi kuma yi rai; Ya bada iko da umurni ga masu-bautansa su furta, su fadi kuma ga mutanensa da su ke tuba da neman gafarar zunubansu. Allah ke gafartawa, yana kwancewa dukan masu-tuba da gaskiya, masu-bada gaskiya ga bisharassa mai-tsarki ba da munafunchi ba. Domin mu roke shi, shi ba mu tuba mai-gaskiya, da Ruhunsa Mai-tsarki, domin abubuwan da mu ke yi yanzu su gamshe shi; kuma sauran ranmu da ke nan gaba shiyi tsabta da tsarki, domin hakkanan a-karewa mu zo chikkin farin cikinsa na har abada, ta wurin Isa Almasihu Ubangijinmu. Ubangiji kar kayi duba ga saɓon yarinyata, ka yafe mata a cikin yafiyarka mai girma! Ka juyo da hankali da tunaninta ta gane gaskiya a cikin addinin ka ya Yesu Almasihu! Mijina kuma ka bashi lafiya da juriya duk da ya ɓace daga gaskiya, kar kayi duba da laifinsa, ka samu a cikin aljanna gaba ɗaya, Amin._" Wani irin dariya ne ya kusa kufcewa Khalil jin yanda surukar tasa ta dage da iya ƙarfinta tana addu'arsu ta kirista, gefe guda kuma yana jimamin rashin hankali irin na ƴan uwan matan nasa. "Ubangiji ba ya kare mu da komawa addininki Lami! Duk da nasan ba kullum nake sallah ba, amma bana fatan in mutu a cikin addinin Kirista, ai na taɓa jin wani wa'azi akan duk wanda yace La'ilaha illalah Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi, ba zai taɓa dauwama a wuta ba, so ina da hope ɗin zan shiga ko da kuwa wuta na fara shiga." Faɗin Marfu'a, da sauri Khalil ya juyo kuma hakan yayi daidai da wani uban burki da ya taka duk sai da suka tsorata, "Ke wacce irin jahila ce? Kina hauka ne? Kin san mecece wutar ubangiji kuwa? Ƙarya kike yi wallahi, baza ki taɓa iya jurewa azabar Allah ba, kar ki kuskura ki ƙara faɗin wannan kalmar, kiyi fatan ko hucin wuta kada Allah yasa kiji bare ki shiga ko da kuwa na daƙiƙa ɗaya ne! Wai tsaya, dukan ku kun taɓa zaman aji na islamiyya kuwa?" Girgiza kai suka yi gaba ɗaya. Dogon tsaki Khalil yaja tare da faɗin, "Akwai babban matsala!" Yana gama faɗin haka ya kunna motar tare da cigaba da tafiya ransa a ɓace. Har suka isa asibitinsa babu wanda ya ƙara ko tari, nan da nan aka shiga da baba emergency, sakamakon gwaje-gwajen da akai masa ya nuna jininsa yayi mugun hawa, wanda hakan yayi sanadin faɗuwarsa har ya samu mutuwar ɓarin jiki, ga kuma ciwon zuciya da ya kai matakin stage C. Sosai Khalil ya girgiza da ganin haka, abunda ya kawo ransa shine halin da ƴaƴansa da kuma matarsa ya kaisa wannan stage ɗin saboda tara abu a zuciya. Aina'u na shiga ɗaki ta soma jin wani irin kuuwa a kunnanta har sai da ta saka hannu biyu ta toshe kunnan tare da durƙushewa a ƙasa, can ta soma ji ana ɓarke kayan jikinta, sai da aka mata tsirara sannan aka kwara mata wani irin balaƴenƴen ruwan sayi mai ƙanƙara-ƙanƙara a jiki sannan aka shiga zubaba mata bulalan doki a jikin, yanda ƙaran dukan ke fita zaka fahimci ba wai mutum ko aljani ɗaya bane ke dukan, da wannan yace waaap, sai wannan yace shauuuu! Ba ƙaramin duka taci ba, don tun da ta shiga ciki ake dukanta har wajajan goman Safiya, ta suma yafi sau a ƙirga, gaba ɗaya jikini yayi ruɗu-ruɗu, sannan kuma aka shafe jikin da gishiri da yaji. Tsabar azaba Aina'u zawo ta dunga saki a kwance a ƙasan tiles. A can asibiti kuwa, duk wanda ya kalli yanda baba ya koma lokaci guda sai ka tausaya masa, ido ya juye, hannun da ƙafa na ɓarin dama sun shanye, harce kuma ya karye, basu Na'ima kaɗai ba, hatta Lami sai da ta fashe da kuka. Khalil jan su Na'iman gefe yayi ya shiga yi masu nasiha mai ratsa jiki, sannan ya shaida masu abubuwan da suke aikatawa ne ya jefa baba a cikin halin da yake ciki, sannan yayi masu alƙawarin idan har sun tuba sun komawa Allah duk sun daina yawace-yawacen da suke yi, shi kuma yayi masu alƙawarin akan su sai inda ƙarfinsa ya ƙare, kuma daga yau in dai kuɗi suke nema to su tambayesa, sannan ya bawa kowaccen su damar nemo sana'ar da zata riƙa yi shikuma daga nera ɗaya zuwa miliyan biyu zai bawa kowaccen su ta kama sana'a domin rufawa kai asiri, ya ƙara da faɗa masu duk wacce ta natsu a cikinsu in Sha Allah tana zaune Allah zai kawo mata mijin marainiya ya aurenta. Sannan kuma yace dukkansu sai sun koma islamiyya. Lami ma ya kirata gefe yayi ta rioƙonta akan dan girman Allah ta daina ingiza ƴaƴanta suna yin karuwanci, idan har kuɗi take buƙata tana da number ɗinsa ta kira ko nawa take da buƙata shi kuma yayi alƙawarin zai bata. Ranar dai kowa jigum-jigum ya kwana, Lami kuwa lokacin da Khalil ya kaita ɗakin da babies ɗin suke, kamar ta ɗebesu haka taji, wani irin ƙaunar yaran ya shigeta. Sarah kuwa ganin daga ƴan uwan nata har Lami duk sun koma wani silent, sai taji wani irin daɗi da natsuwa ya kamata. Babu wanda ya faɗa mata baba na asibitin har sai da ya kwana goma, Duk yanda suka ɗauka Sarah zata tashi hankalinta, sai suka ga tashin hankali yafi kwatancesu, kuka kuwa kwana tayi tana yi, yaran kuwa ƙin zuwa tayi ta basu nono saboda haushin Khalil da take ji na ɓoye mata mutuwa har biyu da kuma rashin lafiyar baban, don mutuwar Rabo ɗan wajen Na'ima da kuma Nafeesa, duk a ranar aka faɗa mata, tayi kuka kamar ranta zai bar jikinta har sai da jininta ya sake hawa. Dakyar Hajiya da Khalil suka lallasheta. Lami kuwa hankalinta gaba ɗaya ya koma wajen Aina'u ganin bata ganta a asibiti ba, rabon da ta saka Aina'un a idanunta ma har ta manta, duk a tunaninta tana wajen yawace-yawacen banzanta ne, haka nan sai taji hankalinta ya mugun tashi don ko lokacin da su Na'iman suke tashen yawon bin maza, basu wuce kwana uku ko sati a waje, sannan duk ranar duniya sai sunyi waya da ita, amma Aina'u kusan watanni uku kenan rabon da ta ganta kuma babu kiran waya, ko Lamin ta kira ta a waya bata ɗauka. Tagumi Lami ta zabga tana kallon baba da ya koma kamar wani tsumma, a hakan ma wai don yana Asibitin da ake kula dashi kenan! Ƙara kunnanta tayi zuwa bakin baba ganin magana yake yi amma bata jin abunda yake furtawa, don harcen ya riga ya karye. Sarah dake kusa dashi don kullum tana tare dashi, anan kuma take kwana duk da Lami da Na'ima suma suna nan, itama ta kawo nata kunnan amma bata fahimta ba, fita tayi ta kirawo Khalil domin yazo yaji ko shi zai gane, ko da Khalil yazo ya kara nashi kunnan, sai yaji kamar yana cewa Aliyu cikin karyewar harce, sai ya ɗago ya kalli Lami tare da faɗin, "Mama Ni dai ji nayi kamar yana faɗin Aliyu, kuna da wani ne mai suna haka?" Girgiza kai tayi tare da faɗin, "Gaskiya babu, da dai ma
Showing 93001 words to 96000 words out of 129453 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32 Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44