Ameeru, bigu biyu ya ɗaga tare da faɗin, "Tunda naga kiranka nasan ba alkhairi zaka faɗa min ba, don haka nan baka kira ka gaishe mu, balle kuma yanzu da kayi aure kana ganin kanmu ɗaya!" "Allah yayiwa Nafeesa rasuwa ta hanyar gobara, yanzu haka ina can gidanta!" Shine abunda Khalil ya faɗi tare da yanke kiran ba tare da ya bari uncle Ameeru ya dire salatin da ya ɗauko ba. Uncle Ameeru a gigice ya kira sauran ƴan uwansa a waya ya shaida masu, nan da nan suka haɗu suka yo gida wajen Hajiya maimakon su wuce can gidan Nafeesan kai tsaye, Hajiya najin sautikan muryansu yayin tahowarsu taji gabanta ya faɗi don ta san zuwansu ba alkhairi bane, ɗayan biyu ne, ko sun zo neman kuɗi ko kuma tijarar da suka saba yi mata. Babu sallama suka faɗa ɗakin kasancewar ƙofar buɗe take don Hajiya bata kulle ƙofa idan dai ba dare bane. "Bilkisu ashe abunda ya faru kenan? Allah ya jiƙan Nafeesa, oh! Yaushe-yaushe ƴarta ta koma, ashe itama tana tafe." Da sauri Hajiya ta miƙe tana faɗin, "Ban gane ba mai kuke faɗi ba. Nafeesar ce ta mutu? Nafeesa tawa?" Kallon-kallo aka shiga yi tsakanin su uncle Ameeru, don sun ɗauka ta san da mutuwar, Uncle Shamsu yace, "Kenan baki sani ba, ɗazun nan Khalil ya kira Ameeru yake faɗa masa gobara ta kama a gidan duk sun mutu har da mijin." Hannu Hajiya ta ɗaura akai tare da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Sau uku sannan ta faɗi ƙasa sumamma. Laure a sittin ta fita ta nufi side ɗin aunty Maryam ta shiga bugawa da ƙarfi, ya Abdul-Hakeem na fitowa ta kamo hannunsa ta dunga jansa har ɗakin Hajiya, da sauri ya nufi Hajiya yana jijjigata tare da tambayar mai ya faru da ita, uncle Ameeru ne ya shaida masa abunda ke faruwa, a gigice ya soma karanto Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, can kuma ya cicciɓi Hajiyar zuwa mota ya fita daga gidan zuwa asibiti shi da Laure, su uncle Ameeru kuma suka wuce gidan Nafeesan. A can Asibiti kuwa, jinin Hajiya yayi mugun hawa, ya Abdul-Hakeem bai bar asibitin ba sai da Hajiya ta farfaɗo aka saka mata drip da kuma alluran bacci, bai samu sallar gawa ba, domin yayyafawa naman ruwa kawai aka yi saboda yanda tayi dagwargwaje, Khalil ne yace ba sai Hajiya ta ganta ba, don ganin naman Nafeesa zai iya jefata cikin mummunar hali, ko shi da yake namiji kuma doctor ba ƙaramin tashin hankali yake ciki ba. Suna dawowa daga maƙabarta da ya halartu mutane da yawa, don maza da matan unguwan kowa sai bada shaidar alkhairin Nafeesa yake yi. Sosai ta samu shaida mai kyau daga ƴan unguwa da dangin mijinta, don surukarta har yanzu bata cikin hayyacinta, wani mugun tashin hankalin suka kuma taraswa, gawar Qasim mijin Nafeesa aka dawo da ita shima ya amsa kiran Ubangiji domin ba ƙaramin ƙuna yayi ba, ya riga ya dahu sosai. Khalil dai ba ƙaramin tashin hankali suka gani ba a ranar, yayi wani irin zuru-zuru kamar wanda ya shekara yana ciwo. Haka suka kuma yiwa Qasim sallah bayan an yayyafa masa ruwa, don shima namar jikinsa sai zagwanyewa yake yi, bayan sun kai shi makwancinsa sun dawo, sai suka shiga gidansu Qasim ɗin aka yiwa juna gaisuwar mutuwa sannan shi da Laure da ya Abdul-Hakeem suka wuce asibiti wajen Hajiya duk da ƙanwarta Aunty ya Gana da Aunty Yaana suna tare da ita. Gaba ɗaya duk wanda ka kalla tsakanin ya Abdul-Hakeem da Khalil ba wanda bai zama abun tausayi ba. Hajiya kuwa ta farfaɗo amma ko iya ɗago idanu bata yi, harshenta ma har so yayi ya soma karyewa! Khalil kallo ɗaya yayiwa Hajiyar yaji hawaye sun taru a idanunsa, da sauri yaju ya bar ɗakin. Aunty Yaana da yare tayi wa Laure magana akan ta zauna ta tsaya a tsaye kamar sanda. Zama tayi tana kallon Hajiya hawaye na zuba a idanunta. Hannuta Hajiya ta kamo tare da faɗin, "Laure da gaske Nafeesa ta mutu? Da gaske babu auta Laure?" Sunkuyar da kai Laure tayi tana hawaye, Aunty Yagana tace, "Haba ya Bilki, kullu nafsin za'ikatul maut! Ki daina saka damuwa aranki, Allah ya fiki son Nafeesa, na san abun da zafi, amma daurewa za kiyi, addu'ar ki kawai Nafeesa take bukata matsayin ki na uwa. Bp ɗinki ya hau sosai, idan kina wannan kukan da damuwa ba zai taɓa sauka ba. Dan Allah ya Bilki, kiyi haƙuri ki sakawa zuciyarki haƙurin rashi." Duk cikin yaren Kanuri tayi mata maganar. Sai kuma ta kalli Laure tare da faɗin, "Je kira Khalil yazo yayi mata allurar bacci!" Da sauri Hajiya ta ɗaga hannu alamar bata so tare da danƙe hannun Laure da ɗayan hannunta. Sarah ba ƙaramin wahala taci ba, ga yunwar dake nuƙurƙusan cikinta amma ko motsi ta kasa, ji take kamar ana hura wuta a jikinta saboda wani irin azabar zafi da take ji, ta kai gudun ac ɗin ɗakin gaba ɗaya amma bata daina jin zafin ba, ta haɗa da warware fanka zuwa number ɗin ƙarshe nan ma kamar ƙara hura wutar jikinta ake yi. Ta cire kayan jikinta gaba ɗaya ya rage daga ita sai bra da pampers ɗin da Khalil ya saka mata nan ma dai bata ji wani salama ba, daga ƙarshe sai da ta cire komai na jikinta ta kwanta flat a ƙasan tiles amma still babu wani salama sai ma ƙaruwa da zafin yake yi ga kuma fitsarin da ya zama mara control yana zubo mata, don bata sanin lokacin da take jinsa, zubowarsa kawai take ji, tsutsotsin nan kuwa sun yi faca-faca a tsakar ɗakin. Da kyar ta rarrafa ta faɗa bayi ta dunga kwarawa kanta ruwa a jiki, amma da ruwan ya sauka a jikinta sai taji kamar tafasasshen ruwan zafi ta kwarawa jikinta. Fitowa tayi daga bayin ta zauna daɓar a ƙasa tare da fashewa da kuka tana sosa jikinta saboda wani mahaukacin ƙaiƙayi da ta soma ji kamar an watsa mata karara. Khalil bashi ya shigo gidan ba sai gab magrib gabansa na faɗuwa saboda bai ƙaunar yaga Sarah cikin wani hali gashi ya barta ita kaɗai kuma ya san mahaukaciyar ƙanwarta ba zuwa dubata za tayi ba. Ɗauke numfashi yayi jin wani uban ƙarni, zarni, hamami, ɗoyi da warin da saman gaba ɗaya ya ɗauka. Haka ya daure ya ƙarisa don yasan shi ɗinne dai, idan bashi ba babu mai iya jurewa, yana tura ƙofar ɗakin Sarah na sakin wani mahaukacin gyatsa mai tafe da lafiyayyar tusa mai warin fitar hayyaci, tuni ɗakin yayi wani irin duum akan wanda yake yi. Cikin sauri ya nufeta ganinta tsirara kuma kwance a ƙasa tana susan jiki, "Mine Lafiya, mai ya faru dake!" Da hannu bibbiyu ta soma turesa tana faɗin, "Ka bar nan wajen, wari kake yi, warin jikinka zai kashe ni, ka tashi ka fita nace!" Da mamaki Khalil ya hau shinshina jikinsa yana kallon Sarah, sai kuma yace, "Ɗakin ne ke wari, bari na gyara miki jikinki na gyara ɗakin zaki daina ji." Faɗin Khalil, Aina'u daka ɗakin Hajiya tana kallon komai cikin tafin hannunta ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya tana ɓaɓɓaka mahaukacin dariya. Sarah kuwa duka ta shiga kai masa ta ko ina a jikinsa tana faɗin, "Ka fita nace, wari kake yi, kai abun kyama ne. Ka fita kabar ɗakin nan." Hannunta ya riƙo biyu tare da faɗin, "Naji zan fita, amma bari na gyara maki ɗakin tukun da jikinki." Ta jin haka sai tayi wuf ta miƙe ta shiga jifansa da duk abunda taci karo dashi a ɗakin har tayi sanadin fashe masa goshi. Fita yayi daga ɗakin yana mai matsanaicin jin tausayinta, ya bar gaba ɗaya abunda tayi masa yanzu matsayin depression ne ya kamata saboda halin da take ciki shi yasa take acting haka. Ɗakinsa ya koma yayiwa kansa dressing a goshi lokacin ana kwaɗa kiran sallah sai yayi alwala tare da wucewa masallaci. Sarah kuwa tun sanda aka soma kwaɗa kiran sallah sai taji gaba ɗaya zafin da take ji a jikinta ya kau, sai wani nannauyen bacci yayi gaba da ita. Lokacin da Khalil ya dawo daga masallaci, haka kawai ya yaji yana buƙatar jin karatun Alkur'ani, sai ya kunna ƙira'ar minshawi ya saka wayar a gaban aljihusa, kai tsaye ɗakin Sarah ya nufa, kwance ya sameta a ƙasa, a hankali ya tura ƙofar ya shiga, bai taɓa ta ba sai da ya gyara ɗakin tsaf sannan ya ajiye wayarsa da har a lokacin tana karatun ya cicciɓi Sarah yayi bayi da ita, daga can ɗakin hajiya kuwa, tun da Khalil ya kunna karatun nan ta daina ganinsa a tafin hannunta. Sarah na jinta a hannun Khalil ta buɗe idanunta da sauri tare da zabura, sai kuma ta mayar da idanu ta rufe, wanka yayi mata sannan ya saka ta ɗaura alwala sannan suka fito ya taimaka mata wajen saka pampers ya fiddo mata da kaya marasa nauyi ta saka ya bata hijjab ta tada sallah. Bata ƙara jin warin da Khalil ke yi mata ba saboda karatun da ya kunna, shima kuma bai ji mahaukacin warin ba, sai ya ɗauka saboda ya gyara ɗakin ne. Shi ya dafa masu indomie da kwai, sai da yaga ta ƙoshi tukun ya daina bata, sai taga ya jingina da gado yayi shuru, rai babu daɗi ta kallesa tare da faɗin, "Happiness, mai ke damunka?" Murmushin yaƙe yayi mata don bai ji zai iya faɗa mata Nafeesa ta rasu kuma Hajiya na kwance a asibiti ba, "Ina tunanin ki ne, Mine. Allah ya baki lafiya kinji!" Ya ƙarisa maganar yana kallonsa. Kallon indomie ɗin da tashi ta rage tayi tare da ƙarisowa wajensa ta saka hannu cikin plate ɗin ta dunga ɗebowa tana saka mashi a baki, ba daɗin indomie ɗin yake ji ba ko kaɗan, amma saboda bai son sosa mata rai sai yayi ta amsa har ya cinye. Kwanciya tayi a jikinsa tare da faɗin, "In Sha Allah zan warke" Ga mamakinta sai taji saukar hawayensa akan kafaɗanta, da sauri ta kallesa daidai lokacin da wayarsa ya hau ringing ɗin wakar _I miss You like crazy_, wani irin mahaukacin ihuu Sarah ta saki tare da toshe hancinta tana nuna masa waje alamar ya fita, da ɗumbin mamaki yake kallonta ita kuwa sai turashi take yi tana faɗin, "Fita nace! Fita daga ɗakin nan wari kake yi Ibrahim!!" Miƙewa yayi itama ta miƙe ta dunga turashi har waje sannan ta jawo ƙofar ɗakin ta rufe tare da zamewa jikin ƙofar ta soma wani irin kukan fitar hayyaci, har cikin zuciyarta bata jin daɗin abunda take masa, amma bata san mai yasa take jin wannan warin da ko ta ƙudurtawa zuciyarta zata jure sai ta kasa. Khalil ya jima a ƙofar yana mamaki, can kuma ya juya ya koma ɗakinsa. Wani irin tsallen murna Aina'u tayi daga ɗaki don tana ganin komai tun lokacin da karatun nan ya tsaya. Haka suka kwashi kwana goma suna yi, da ya shiga ɗakin domin gyarata zata hau ihu tana faɗin ya fita wari yake yi, tana kuma turashi da ƙarfi. Wani lokacin ƙarfi yake saka mata ya gyara mata jikinta da ɗakin sai ya ajiye mata abinci ya fita. Wani lokacin kuma sai ya bari sai tayi bacci sai ya shigo ya gyara ko ina don tana iya gyara jikinta ta canza pampers, zarnin fitsari da ƙarni da warin tsutsotsin naso ya kashe ɗakin don bata bari Khalil ɗin yayi abunda ya kamata. Kwanan Hajiya ashirin da uku aka sallamota, tunda suke asibitin ko sau ɗaya Laure bata taɓa sha'awar dawowa gidan ba, haka Aina'u bata taɓa taka ƙafarta taje asibitin ba. Ɓangaren Sarah sai abunda yayi gaba wajen kyaran Khalil, shi kuwa ko afuska bai taɓa nuna ɓarin rai ko ƙosawa da ita ba, sai ma wani irin nunkular kulawa da ya ƙara bata don duk tunaninsa depression ke damunta. Kamar daga sama sai ga Muneeba a gidan Sarah, sosai Khalil yayi murnar ganinta, har bedroom ɗin Sarah ya kaita, kuma a gaban idanun Muneeban ta yiwa Khalil ɗin koran kare, bayan fitarsa Muneeba ta hau Sarah da faɗa kamar ta ari baki, sai kawai Sarah ta fashe da kuka tare da faɗin, "To ni ya zanyi Muneeba, ina zan saka kaina! Ciwo duk yabi ya dame ni, tsutsotsi a gabana, wari da ƙarni gami da hamami a ɗakina. Mijina kuma duk lokacin da ya kusanto ni, wani irin ƙarni da hamami yake min!" Da idanu kawai Muneeba take bin Sarah, can kuma sai tace, "Sarah! Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!! Wani irin abu nake ji haka? Shin baba da Lami sun san wannan zancen kuwa? Ai wannan ba cutar da za ayi shuru da baki bane, dole iyaye suji don cutarki bai yi kala da cutar asibiti ba. Bari ki gani ina zuwa.." Tana gama faɗin haka ta mike tare da ɗaukar jakarta domin zuwa gida ta faɗawa mahaifiyarta abunda ake ciki domin tayiwa babanta magana ayi mata treatment na Islamic. Sai dai miƙewarta yayi dai-dai da miƙewar Aina'u da sauri tare da fitowa ta tsaya bakin gate, Muneeba na fito ta soma tafiya da sauri, sai kawai ji tayi an juyo da ita da auri tare da taɓa goshinta, "Ki kalli gabas kiyi ta tafiya kar ki ƙara waiwayar nan gidan!" Gyaɗa kai Muneeba tayi tare da kallon gabas ta hau tafiya ba tare da sanin inda ta nufa ba. Wani irin dariya Aina'u ta sheƙe dashi tare da faɗin, "Babu mai ja dani ya zauna lafiya, Khalil nawa ne ni ɗaya, don ni aka halicce shi, duk wacce tayi ƙoƙarin rabani dashi sai na ɗanɗana mata azaba, haka duk wacce tayi ƙoƙarin ceton Sarah sai na wulaƙanta rayuwarta!" Tana gama faɗin haka ta juyo ta dawo cikin gida. Cikin Sarah ya shiga na wata bakwai, still babu abunda ya canza, haka kuma Khalil shima bai taɓa canza mata ba. Aina'u ta kai maƙurar ɓacin rai ganin babu wani canji daga Khalil, sai kawai ta hau shirin tafiya Abia domin samun _Hell Ofulafu_ gaba da gaba domin tayi mai kankat.. Ranar wata asabar ta tafi, wannan karan ma Ugo ne yayi mata jagora bayan sun gama watsewarsu. Ba ƙaramin tsafi Hell yayi mata ba wannan karan, sannan sai da tayi masa alƙawarin jinin mutane goma, biyar jarirai, biyar kuma waɗanda suka soma tadawa ƴan shekaru uku zuwa goma. Sannan ya bata wani kwaɗo ƙarami yace ta haɗiye, idan har ta haɗiye duk wanda ta kalla tace yayi wani abu babu musu sai yayi, sannan kuma idan har tana son asirin da za ayiwa Khalil ya kama shi, sai ta kwanta da mahaifinta. "Idan har buƙatata zata biya ko Sarkin maka kace na kwanta dashi zan kwanta dashi." Shine abunda Aina'u tace. Kwananta uku a Abia ta juyo ta dawo Kaduna, bata sauka a ko ina ba sai gida lokacin ƙarfe biyu na dare. Banƙare ƙofar gidan tayi sannan ta shiga, ɗakin baba ta nufa kai tsaye tare da tura ƙofar ta shiga don shi bai saka sakata a ɗaki. A Zaune ta samu baban don tun lokacin da ta tura ƙofar gida ya farka, hannu ta kai ta kunna switch ɗin ɗakin tare da yin wani irin tsayuwan karuwai tana mitsi-mitsin da idanu, shi kuwa baba sai yaga gama ɗaya suffarta ta koma ta Lami sak lokacin da take amarya. Wani irin mugun sha'awa ce ta shiga fuzgar baba har bai san lokacin da ya miƙa mata hannu tare da faɗin, " _Elizabeth_" ba. Aina'u kuwa wani murmushi ta saki tare da kashe wutan ta nufe shi gadan-gadan. Cike da rashin imani Aina'u ta bari mahaifin da yayi sanadin kawota duniya ya kusanceta. Sai bayan komai ya nutsa baba ya sauko daga kan gadon a gigice ya kunna wuta, arba yayi da fuskar ƴarsa kuma autarsu tana saka brezia, hannu ya kai ya dafe saitin ƙirjinsa tare da soma nunata da hannu yana son yin magana amma bakinsa ya karkace. Take ya yanke jiki ya faɗi ƙasa rabin jikinsa gaba ɗaya ya mutu. Aina'u kuwa tana gama saka kaya ta tsallakesa ta bar ɗakin ta koma ɗakinsu. Da sassafe kamun kowa ya tashi ta bar gidan ta nufi gidansu Khalil. Sarah kuwa tun asuba ta soma jin wani irin mahaukacin ciwon mara wanda bai misaltuwa don naƙuda ta soma yi gadan-gadan duk da kuwa lokacin haihuwarta bai yi ba don cikin watansa bakwai, itace har safiya tana abu ɗaya, idan ta kai hannu gabanta tana jin gashi, amma haihuwa taƙi zuwa sai nuƙurƙusan azaba take yi. Aina'u na fitowa daga gida ta shafa tafin hannunta sai ga Sarah ta bayyana cikin halin naƙuda. Wani irin nishine ya taho mata, cikin sauri Aina'u ta haɗe yatsanta biyu ta kame gam, sai Sarah taji kamar an saka igiya an shaƙe wuyarta ga kuma kan ɗa daya soma turowa............
( _Anya Aina'u ƴar Adam ce kuwa_? 😭)
*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata
Showing 90001 words to 93000 words out of 129453 words
( _Anya Aina'u ƴar Adam ce kuwa_? 😭)
*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31 Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44