kuma kamar wani wawa ya saki baki sai ɓaɓɓaka dariya yake yi. Sarah miƙewa tayi ta bar wajen zuciyarta na susa, duk da tasan babu aure tsakanin Aina'un da Khalil ɗin idan dai har ba mutuwa tayi ba, sai taji wani irin matsanaicin kishi da damuwa yanda Khalil ɗin ya manta tana wajen, da dane, Aina'u bata ma isa ta ƙariso inda suke ba balle har ta zauna kusa dashi, da bata jin daɗin yanda Khalil ɗin yake ɗaurewa Aina'un fuska ganin su Na'ima yanzu har wani respect yake basu matsayin yayyin matansa, amma kuma ya kasa sabawa da Aina'u, sai ta bar hakan matsayin rashin haɗuwar jini, amma yanzu lokaci guda da taga wannan sauyin duk sai taji matsanaicin damuwa ya kamata. Bayan ta hau sama sai ta canzawa twins pampers tare da saka masu kayan baccinsu sannan ta sayar dasu har bacci ya ɗauke su lokacin ƙarfe tara da mintuna biyar amma har yanzu Khalil bai dawo ba, kwanciya tayi tare da rufe idanu amma sai taji gaba ɗaya baccin yaƙi zuwa, tashi tayi ta sauka a kan gadon tare da fitowa ta tsaya daga nan sama tana hangen Khalil kusa da Aina'u kamar zasu shigewa juna yana nuna mata abu a waya suna dariya. Da sauri ta juya ta bar wajen saboda bata son kawo zargi a zaman aurenta dashi. Ko da ta koma ɗaki, sam bacci ya kasa zuwan mata sai juyi take yi tana saƙe-saƙe a zuciya tare da duba agogo a wayarta, sai da agogo ya buga ƙarfe ɗaya sannan taji buɗe ƙofar Khalil ya shigo ɗakin, tana jinsa ya shiga toilet yayi wanka kasancewar kullum zai kwanta sai yayi wanka, kayan bacci ya saka sannan ya hayo gadon tare da gyarawa twins kwanciya ya mayar dasu ƙarshen gadon ahankali gudun kar su tashi sannan ya jawo Sarah jikinsa ya rungume, duk tana jinsa sai tayi kamar bacci take yi har ta soma jin saukar numfashinsa alamar baccin ya ɗaukesa. Ajiyar zuciya ta sauke domin ta rasa wani irin tunani za tayi, sai wajajen ukun dare bacci yayi gaba da ita. Washa gari da sassafe bata nuna masa komai ba ta haɗa masa breakfast da duk abunda zai buƙata, haka kayan da zai saka bayan ya fito daga wanka. Ita ta taimaka masa ya saka kayan sannan yayiwa twins kiss a kumatu kasancewar basu farka ba sannan suka sauko ƙasa tayi serving ɗinsa ya karya. Sun rabu kamar kullum bayan yayi hugging ɗinta tare da yi mata kiss ita kuma tayi masa addu'ar Allah ya tsare sannan ya tafi. Da sauri Aina'u dake kallon komai a bangon ɗakinta dake shashin Hajiya ta fito cikin uban kwalliya tare da isa inda yake yana ƙoƙarin buɗe mota, "Manyan gari kenan, har za'a fita ba tare da an ganni ba!" Da sauri Khalil ya kalleta tare da faɗin, "I'm so sorry Ai'n, na kusa nayi latti ne shine nake sauri, kin san jiya mun sha hira, abunda ya makarar dani kenan." "Kar inzo yau kenan?" Faɗin Aina'u tana wani kashe idanu. Waro idanu Khalil yayi tare da faɗin, "Wa! Ai ko da har ɗakin Hajiya zan biyo ki, baki san yanda hira dake yake matuƙar sani nishaɗi ba ko? Kar ma ki fara min wannan wasan." Wani shu'umin dariya Aina'u tayi tare da faɗin, "Hakane! To mu fita tare ka ɗan rage min hanya nima dama fitan zan yi." Da sauri ya buɗe mata gaban mota sannan ya zagaya ya shiga mazaunin driver yaja motar suka bar gidan. Sakin labule Sarah tayi tare da jinginar da bayanta jikin window ɗin tana faɗin, "Ya Allah ka tausaya min kasa ba abunda nake tunani bane akan mijina da ƙanwata. Wunin ranar sukuku tayi sa, ƙarfe shida Khalilullah ya dawo kamar yanda ya saba, sai dai kuma tare suka dawo da Aina'u kamar yanda suka fita tare, kasancewar Sarah na ɗakinsa tana fesa airfreshner, sai tayi saurin ɗaga labulan window jin ƙarar motarsa, gabanta ne ya buga da ƙarfi ganin Aina'u ta fito daga motar hannunta ɗauke da wata ƙatuwar leda bakinnan kamar zai yage tsabar washesa da take yi. Sakin labulan tayi tare da saukowa ƙasa sauri, buɗe ƙofar Khalil yayi ya shigo fuska ɗauke da fara'a, ganin yanayin matar tata duk sai jikinsa yayi sanyi, gashi tayi bala'in kyau cikin wani Indian material da tayi ɗinkin straight gown dashi, gashin kanta kuma ta kama shi in a middle ponytail, jelar gar dokin wuyanta, fuskanta yaci makeup mai ɗaukar idanu, "Wife, lafiya naga fuskanki haka?" Maimakon ta bashi amsar tambayarsa, sai cewa tayi, "Ina kuka je kai da Aina'u? You left this house together and you also came back together." Murmushi yayi tare da faɗin, "Wai Aina'u? Rage mata hanya nayi wai zata wajen ƙawarta, luckily kuma sai muka sake haɗuwa shiyasa muka dawo tare." Sarah bata iya cewa komai ba sai kallonsa da ta riƙa yi, "Come on, smile!" Ya faɗi yana mai bata side hug. Yau ma dai irin na jiya aka kuma, Aina'u ta kuma zuwa kuma still sai 1am Khalil ya dawo ɗakin, abun na matuƙar damun Sarah a zuciya, sam bata samun kulawar Khalil yanzu, ya kai yanzu ko kwalliya tayi bai kallo bare ya yaba, girki kuma Aina'u ta koma yi masa, idan Sarah ta zuba masa abinci, sai yace mata Aina'u zata kawo masa, tun Sarah na daurewa kusan sati Uku, har ta zuciya wata rana taje har side ɗin Hajiya ta samu Aina'u a ɗaki bayan Khalil ya wuce asibiti, zaune take tana kallon tafin hannunta, ba kowa bane a ciki sai Khalil dake zaune yana duba petient, bata san da zuwan Sarah ba kasancewar ba ita take kallo ba a wannan lokacin, turo ƙofar da Sarah tayi ne ya dawo da ita cikin hayyacinta tayi saurin kallon ƙofar don tasan Hajiya da Laure ko giyan wake suka sha baza su shigo mata ɗaki ba, wani kallon banza ta watsawa Sarah da taga itace a ƙofar ɗakin, a zuciye Sarah ta ƙarisa ɗakin tare da ɗauke Aina'u da mari sannan ta nunata da yatsa tare da faɗin, "Dan ubanki ki tattara kayanki ki bar gidan nan, idan ba haka ba, sai na kakkaryaki, shegiya ƴar iska, na gama gane take-taken ki, so kike ki ɗauke min hankalin miji ko? Don baki da kunya mijina kike so? To wallahi ahir ɗinki! In the first place ma na kasa gane uban da kike yi cikin gidan nan tunda ba gidan ubanki bane, to ki saurareni da kyau, ki tattara ki bar gidan nan tun kan inyi maki watsi da kayanki wallahi. Wawuya shashasha!" Tun da Sarah ta fara magana har ta dire Aina'u ko tari bata yi ba sai ma wani murmushi da take yi, amma deep down ita kaɗai tasan mai take shiryawa cikin zuciyarta. Sarah kuwa fita tayi tare da banging ƙofar. Har akai kwana uku Sarah bata kuma ganin Aina'u ba, sai tayi tunanin ko taji abinda ta faɗa mata ne ta bar gidan, sai dai kuma gaba ɗaya ta kasa gane kan Khalil, don wani lokacin har mancewa yake yi idan zai kirata sai yace, "Aina'u." Sarah gaba ɗaya hankalinta ya tashi ta soma tunanin mai Aina'u tayiwa Khalil haka. A ran kwana na huɗu, kawai sai ganin Khalil tayi ɗauke da akwatin kaya, Aina'u a bayansa shikuma ransa a mugun ɓace, a nan gaban Aina'u ya hau Sarah da faɗa abunda bai taɓa yi ba, "Wannan wani irin haukane da jahilci! Ƙanwar taki kika kora a gidan nan saboda selfishness ɗinkin? Kin bani mamaki Saratu! To yanzu na dawo da ita da kaina, she will stay here with us." Yana gama faɗin haka ya ɗauki akwatin tare da kallon Aina'u yace, "Ai'n, follow me." Da sauri Sarah tasha gabansa tare da faɗin, "Aina'u bata da ɗaki a sama." "Let go of my way Sarah Nuhu! Kar ki ja inyi maki abunda ban taɓa yi maki shi ba a daran nan." Baki sake Sarah ke kallonsa, yayin da Aina'u ke wani irin shu'umin murmushi. A gaban idanunta Aina'u ta bi bayan Khalil suka haura sama. Da daddare bayan Khalil ya dawo ɗakin Sara, don yau sun kai kusan 2am suna hira da Ai'n kamun ya dawo ɗakin Sarah. Sai da ya gama komai ya hawo kan gadon sannan Sarah ta miƙe ta zauna tare da kunna bedside lamp tare da faɗin, "Ka tashi za muyi magana Please!" A raunane tayi maganar yanda zai ji tausayinta, amma ko juyowa bai yi ba don juya mata baya yayi abunda bai taɓa faruwa ba tunda suka yi aure. Ƙara maimaita abunda tace tayi a karo na biyu, a fusace ya juyo tare da faɗin, "Baccin baza ki bari inyi cikin salama ba? Wato kin ɗauko wani hali da ba naki ba kin ɗaurawa kanki ba? Saboda tsabar kishi da rashin sanin ya kamata, shine za ki riƙa kishi da ƙanwarki ciki ɗaya, Aina'u fa ƙanwarki ce, _Ƙanwar matata!_ kin taɓa jin inda miji ya auri ƙanwar matarsa uwa ɗaya uba ɗaya kuma ba mutuwa tayi ba? Ni dalla malama kin isheni!" Yana gama faɗin haka ya fita daga ɗakin tare da bugo mata ƙofar da ƙarfi sai da twins suka firgita tare da tsala ihu. Aina'u kuwa daga ɗakinsa tana kallon komai, daga ita sai wata ƴar iskan rigar bacci da babu komai a ciki ta fito ta tsaya a bakin ƙofa, Khalil na zuwa wajen ta jawo hannunsa tare da shigo dashi ɗakin sannan ta murza key. Narai-narai tayi da fuska tare da shafa fuskansa zuwa ƙirjinsa ta shiga faɗin, "Kayi haƙuri ta hanaka bacci ko? Kar ka damu idan ita bata sonka, Ni ina sonka kuma zan kula da kai." Wani irin babu daɗi Khalil ya dunga ji amma bai san mai yasa ba ya kasa hanata abunda take yi, hannunsa ta kamo ta zaunar dashi a bakin gado tare da zama akan cinyarsa ta kamo ƙeyarsa tare da haɗe bakinsu waje ɗaya. Da sauri Khalil ya rufe idanu gabansa na faɗuwa da ƙarfi, can kuma ta ɗaga shi tare da turasa ya kwanta flat sannan ta hau kanshi ta shiga kissing ɗinsa, shi kuwa Khalil bai son lokacin da ya biye mata ba..........
_Na san yau zan sha caccaka, wallahi har gabana faɗuwa yake wajen rubuta page ɗin nan saboda nasan akwai wanda zasu tsine min tabbas, amma don Allah abunda nake so daku, kar ku kalli wannan page ɗin a wani mahanga ta daban, wallahi ko Khalil da Sarah + Hajiya suna addu'a da sauke Qur'ani kullum, abunda Allah ya rubuta sai ya faru, mutum bai taɓa wuce ƙaddararsa, Fiyayyan mahalicci ma asiri ya kamasa balle wani kashi Khalil_
*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*
*_MATAR SAYYADEE_*
*Paid book 08128755583*
🦜 *KANWAR MATATA* 🦜
*32*
Gaba ɗaya Khalil ya rasa control ɗinsa, Aina'u ta juye masa kamar Sarah, yunƙurawa yayi tare da juyata ya koma kanta tare da birkice mata, sai sararaba sai da ya samu natsuwa sannan ya koma gefe, Aina'u kuwa cikin zuciyarta cewa tayi, "Na rantse da Yesu Almasihu babu uban da ya isa ya rabamu tunda na ɗanɗani zumanka, shegiya ƴar iska ashe ta san daɗin da take kwasa shiyasa kullum tana naniƙe da kai babu dare babu rana." Da sauri ta tashi zaune tana kallon Khalil da yaja zanin gado ya rufe jikinsa yana shashshekar kuka kamar wani ƙaramin yaro, "Heart, mai ya faru kake kuka?" Ta faɗi tana mai kai hannu jikinsa, wani irin tureta yayi da hannunsa ba tare da ya juyo ba yana mai jin baƙin ciki da dana sani har da na haihuwarsa da Hajiya tayi kasancewar ya kusanci Ƙanwar Matarsa wanda har ga Allah shi bai san yanda aka yi hakan ta faru ba, don gaba ɗaya Aina'u koma masa Sarah tayi, sai tunaninsa gaba ɗaya ya gushe, kuma bai dawo cikin hayyacinsa ba har sai da ya biya buƙatarsa da ita. Wani irin durowa Aina'u tayi tare da duƙawa ƙarƙashin gadon da suke kai, sai taga still tukunyar tsafinta nasan kuma bai canza kala ba, ɗagowa tayi ta kalli Khalil ɗin da har wannan lokacin shashshekar kukan yake yi yayi ruf da ciki, a hankali ta kuma duƙawa ta tura hannunta cikin tukunyar har sa da tsintsiyar hannunta ya shige sannan ta ɗago tare da hawa gadon, tun daga kan ƙeyarsa take shafa masa hannunta har zuwa kan ƙirjinsa, nan take ya mirgino tare da zuba mata idanu, still sai ta kuma rikiɗemasa zuwa Sarah, "Ina matuƙar ƙaunarki, sosai fa!" Ya faɗi yana mai kai hannu ya shafo fuskanta, caraf ta riƙe hannun tana mai jin wani irin sanyi a cikin zuciyarta don da tayi tunanin tsafin da tayi masa ya lalatace, ɗaura kansa tayi a ƙirjinsa tana yi masa tafiyar tsutsa a cikin kunne zuwa bayan kunnansa har bacci ya ɗaukesa, tana ganin haka ta ajiye kansa a kan pillow a hankali tare da sauka daga kan gadon ta kunna hasken ɗakin sannan ta jawo wannan tukunyar dake ƙarƙashin gado ta fito dashi tare da tsoma hannu ta ɗauko wannan mutum-mutumin itacen nan ta hau kan gadon tare da kaisa saitin ƙirjin Khalil, wannan baƙin ruwan ya riƙa ɗiga akai, sai da ruwan ya mamaye ƙirjin sannan Aina'u ta zaro wani abu mai kama da mashi ta ɗaga tare da cakawa da ƙarfi a ƙirjin wannan mutum-mutumin sai da Khalil dake bacci yayi wani irin zabura tare da dafe ƙirji, amma yana arba da fuskan Aina'u sai ya sakar mata murmushin tare da miƙa mata hannu alamar tazo garesa duk da yana kallon abinda ke hannunta amma bai iya ko ƙare masa kallo ba balle ya tanka. Sauka tayi ba tare da ta isa wajensa ba ta mayar da komai cikin ƙarƙashin gadon sannan ta kashe wutan ɗakin ta hau kan gadon ta shige jikinsa, a cikin daren nan sai da ta ƙara naiman Khalil sau uku sannan tayi bacci. Ɓangaren Sarah kuwa, raya darenta tayi da kuka, don yanda taga rana haka taga dare, idanunta yayi luhu-luhu, ji tayi sam baza ta iya jure rashin Khalil a kusa da ita ba, ta riga ta gama yanke shawarar zata cewa Khalil ko ita ko Aina'u, kuma ta san a irin ƙaunar da yake yi mata, itan zai zaɓa. A kunnanta akai kiran sallah, saukowa tayi daga kan gadon ta nufi bayi ta ɗauro alwala tare da tada sallah, bayan ta idar da sallar, sai ta miƙe ta hau gado saboda wani irin bacci dake fuzgar kasancewar bata samu bacci ba. Tana kwanciya baccin yayi gaba da ita. Can cikin baccinta taji ihun kukan Sam'an, da sauri ta tashi zaune tare da jawosa jikinta ta hau shayar dashi, shima Sauban kamar an tsikaresa sai ya tashi. Ko data gama shayar dasu, wayarta ta jawo ta kunna, da sauri ta diro daga kan gadon ganin bakwai da mintuna arba'in tare da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Breakfast ɗin Happiness." Tana gama faɗin haka ta fice ko sauraran su twins dake kuka saboda ta fita bata yi ba, jawo ƙofar tayi tare da soma saukowa daga steirs ɗin da sauri, saura steps huɗu ta sauko gaba ɗaya ta tsaya turus tana kallon ikon Allah, zaune Khalil yake a kan dinning, Aina'u kuma cikin wani irin shigar ɗaukar hankali tsaye a bayansa ta turo hannayenta ta saman kafaɗansa tana saka masa Irish a plate, daga nesa ma zaka ɗauka rungumesa tayi. Sarah har wani jiri taji yana neman yar da ita tayi saurin riƙe ƙarfen dake gefenta tana maimaita, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Cikin zuciyarta. "Ka cinye tass, ban so ka fita da yunwa." Faɗin Aina'u cikin kunnen Khalil ɗin har da ɗan cizon fatar saman kunnensa, shi kuma Khalil wani irin yaji yaja tare da cafko hannun Aina'un ya zagayo da ita tare da jan kujeran baya ya ɗaurata a kan cinyarsa sannan ya zagayo hannunsa ya rungumeta tare da faɗin, "Abincin kike so inci kuwa? Bari dai in baki tukwuicin daɗin da kika bani jiya!" A firgice suka juya gaba ɗaya suna kallon Sarah data kwatsatsa wani irin ihuuu tare da gungurowa saboda ƙafarta da ya kasa riƙeta sakamakon abunda taji ta kuma gani. Da sauri Khalil ya ture Aina'u dake jikinsa tare da ƙarisawa wajen Sarah har da haɗawa da gudu, jijjigata ya soma yi yana kiran sunanta da ƙarfi, Aina'u kuwa folding hannunta tayi tana kallonsu
Showing 99001 words to 102000 words out of 129453 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34 Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44