yayi mugun sanyi ganin tsohuwa na hawaye. Hannunta Sarah ta dafa tare da faɗin, "Hajiya kiyi haƙuri, amma ni a tunanina ba hakannan ba su ya Abdallah zasu ƙaurace maki har na tsawon shekara ɗaya da watanni! Hajiya addu'a da roƙon Allah har da sadaka zaki fara daga yau akan Allah ya karkato maki da dukkan hankalinsu a kanki, in Sha idan muka miƙawa Allah lamuranmu da kyakkyawar yaƙini, in Sha Allah zai yaye mana damuwarmu, Hajiya gaba ɗaya mun mance da Allah shiyasa shima ya mance damu, kuma na tabbata idan muka koma garesa zai amshi buƙatunmu da hannu bibbiyu. Hajiya ban san cewar duk tsawon shekarun nan aikin banza nake yi ba wajen raya darena da kuka ba sai yau da na shigo ɓangaren nan na tarar da Laure na ganawa da ubangijinta tare da ƙasƙantar da kanta tana kuka. Hajiya muyi koyi da Laure in Sha Allah duk matsalolinmu zasu gushe!" Shuru Hajiya tayi tana sauraren Sarah cike da jin kunya da kuma dana sani akan rashin kai kukanta tuntuni zuwa ga mahalicci, sai hakan ya tuno mata da marigayi (Nuruddeen Muhammad) mahaifinsu Khalil, da wani abu ya shige masa duhu ko kuma yana fuskantar matsaloli, nan da nan yake ƙara nau'ikan ibadu akan wanda yake yi, dama kuma azumin litinin da Alhamis ya zame masa jiki da kuma sallar dare, sai ya ƙara ninkawa, almajirai yake tarawa fiye da ɗari kuma ya shiga cikinsu su sauke ƙur'ani sau goma a cikin sati guda, sannan ya shiga sadaka a masallatai tare da gidajen maru, maƙowa kuwa kyautatawarsu daban take, hakan ne ya saka duk tuggun da ƴan uwansa suke binsa dashi yake koma masu. Kuma ƙa'ida ne lokaci da yake raye, tun su Khalil na ƙanana sai ya haɗa kansu har matan sun sauke ƙur'ani duk bayan kwana goma, bayan rasuwarsa da kuma yanayin aikinsu gami da mai da hankali kan tsantsan boko ya saka suka watsar da komi, kuma Lokacin da yake da rai, kullum gidan cikin sauraren karatun Alƙur'ani ake. Ajiyar zuciya Hajiya ta sauke tare da kallon Sarah tace, "Tabbas Saratu duk abunda kika faɗi hakane. Wato lokacin da mahaifinsu Khalil yake da rai, wallahi kullum cikin gidan nan karatun Alƙur'ani ake saurare, sannan duk bayan wani lokaci, Alai sai ya tara almajirai anyi saukar ƙur'ani da sadaka, bayan rasuwarsa ne komai ya watse!" "Hajiya a shawarce, ya kamata komai da ake yi cikin gidan nan ya dawo har abada." Faɗin Sarah. "In Sha Allah, uwata. Nagode maki sosai da tunatarwarki uwata, Allah yayi maki albarka." Faɗin Hajiya. Sarah ta amsa da ameen tare da miƙewa ta fita daga ɗakin, a parlour, su twins na ganin mahaifiyarsu sai suka bar jikin Laure da sauri tare da ƙarisowa wajenta, Sarah tayi-tayi su koma a atafau suka ƙi, haka nan ta koma side ɗinta dasu, babu kowa a parlour sai tayi saurin shigewa ɗaki don kallo kujeran dake parlourn zai iya saka ta faɗi ta mutu, don gaba ɗaya hoton Khalil da Sarah take gani tsirara a kan kujerar. Aina'u kuwa duk abubuwan da Sarah ta tattauna da Hajiya tana kallon komai daga ɗaki, wani ƙuƙulun takaici ne ya tokare mata waya ganin Sarah tun ba'a je ko ina ba tana son lalata mata shirinta. Tashi tayi ta kullo ƙofar kasancewar ko da Khalil ya bar parlourn ɗazu, ɗakin Sarah ya shige ya kulle kansa, sai ta ɗuka ta fiddo wannan tukunyar tare da tura hannun ciki ta ɗauko wannan mutum-mutumin na itace ta matse saitin zuciyarsa da ƙarfi tare da tsundumawa cikin tulun sannan ta kuma cirowa ta ƙara danna ƙirjinsa sannan ta saki daga sama ya faɗa tsumbul a cikin tulun tare da mayar da tulun ƙasan gado sannan ta shafa tsakiyar tafin hannunta sai ga hoton fadwa ƴar wajen Marfu'a, Bobo da Nana ƴan wajen Hassana, mimi ƴa guda da ta ragewa Na'ima, Sai Sultee da haidar ƴaƴan Nuratu. Wani murmushi tayi tare da zana maciji a hannunta, nan take macijin ya soma motsi tare da tafiya da sauri-sauri, ɗaya bayan ɗaya macijn nan ya dunga saransu suna zuba ihu kasancewar gaba daya suna wasa ne a tsakar gidan, yayin da iyayensu suke makarantar dake gaban gidan kaɗan, Na'ima ce kawai bata je saboda fama da ciwon kai da take yi kwana biyu, Lami kuma tana ɗaki ta saki ac tana sharar barci don bata jima da dawowa gidan ba daga gidan Aunty Rose Merry. Da gudu Na'ima ta fito jin wani irin mahaukacin ihu da Mimi ta saki sakamakon saran maciji, dai-dai nan Lami itama ta fito da sauri, a kan idanunsu macijin ya sulale yabi bayan flowers ya ɓace amma su basu ga ɓacewar nasa ba. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" "Lord of Jesus!" A tare Lami da Na'ima suka faɗi haka sannan suka yi kan ƴaƴan da gudu suna jijjigasu, cikin ƙanƙanin lokaci har fatan jikinsu ta sauya kala ta koma green yayin da baƙin kumfa ke fita daga bakunansu suna wani irin jijjiga, kuka Na'ima ta fashe dashi tare da ɗaura hannu a kai, can kuma ta nufi gate da gudu ta fita ko mayafi babu tana kuka tana faɗin a taimaka mata, tare suka dawo da maza biyar cikin gida, inda yaran suke ta kaisu tana kuka, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Mai ya same su?" Gaba ɗaya suka faɗi suna mai isa kusa da yaran tare da taɓa su. "Macijine ya sare su, nima ihunsu naji na fito sai naga macijin da sauri yabi bayan flowers ɗin na." Ɗaya daga cikin su ya nufi bayan flowers ɗin yana dubawa, "Tabbas kuwa! Ga saɓarshi nan a nan wajen!" Ya faɗi yana mai ɗago saɓar macijin. Huɗun da suke kan yaran suka kalli juna bayan tabbatar da babu sauran numfashi a jikin yara, "Yaro yi min bayani, sun mutu ko?" Faɗin Lami tana mai duƙowa tare da taɓa wuyan Mimi dake daf da ita. "Iya sai dai haƙuri, Allah ya riga ya ɗauki rayuwar waɗannan ƴaƴan." "Yesuuuuuu! Wannan azaba da jarabawar ya isa haka! Muna yabonka Ya Allah: mun dauki cewa kai ne Ubangiji. Dukan duniya tana yi maka sujadda, Uba Ma-dauwami. Agareka Malaïku duka suna tada murya, da Sammai da Ikoki duka da ke cikinsu. A gareka Charubin da Sarafin kullayomi suna tada muriya. Mai-tsarki, Mai-tsarki, Mai-tsarki: Ubangiji Allah Mai-runduna. Samma da kasa cike su ke da Sarautar darajarka. Jama’a masu daraja ta zamaninka tana yabonka. Managarcin zumunta ta Annabawa tana yabonka. Jama’a mai-daraja ta Masu-shahada suna yabonka. Ekklisiya mai-tsarki cikin dukan iyakar duniya tana shaidanka: Ya Uba mai-sarauta mara-iyaka: Danka kuma mai-girma, mai-gaskiya, ma-kadaici: Ruhu Mai-tsarki kuma Mai-taimako. Kai ne Sarkin Daraja: Ya Almasihu. Kai ne Da matabaci na Uba. Sa’anda ka dauka ma kanka ka ceci mutane, ba ka yi kyamar cikin buduruwa ba. Sa’anda ka yi nasara da zafin mutuwa, ka budi Mulkin Samma ga masu-bada gaskiya duka. Kana zaune ga hanun damar Allah (Astagfutullah) a cikin darajar Uba. Muna bada gaskiya za ka zo ka zama mai-shari’anmu. Muna rokonka fa, ka taimaki bayinka: wandanda ka fanshe su da jininka mai-daraja: Ka maishe su a-cikin lissafin tsarkakanka, a-cikin daraja ta har abada. Ya Ubangiji ka ceci jama’arka, ka sa ma gadonka albarka. Ka malke su: ka ɗaɗɗaga su har abada. Yo da gobe muna girmama ka; Muna sujadda ga sunanka kuma kullum ba matuka. Ya Ubangiji da yardarka ka tsare mu kar mu mutu da zunubi. Ya Ubangiji ka yi mana jinkai: ka yi mana jinkai. Ya Ubangiji ka bar jinkanka shi rufto mana: da shike ban gaskiyarmu tana gareka. Ya Ubangiji, a-gareka na bada gaskiya, kada ka bar ni na rude har abada. Wannan yara da suka koma izuwa gareka a yau, ka hura ruhinsu a cikin tsarkinka, ka yafesu a cikin irin yafiya naka, mu kuma ka karemu kar muyi mutuwa irin nasu, Yaaa Yesu Almasihu uba!" Kallon-kallo mutanan nan suka shiga yi, don duk a tunaninsu Lami musulmace duk ganin da suke yi mata, sai yaji da suka ji uban yabo da ta kwararo suka fahimta, "Ashe aljihun baya ce!" Ɗayan ya kalli ƴan uwansa ya faɗi, shi kuma mai riƙe da fatar maciji yace, "To Allah ya ƙara nauyin ƙasa!" A fusace Na'ima tace, "To ba amin ba! Wannan wani irin Magana ce haka kuke yi? Ai ko da ace a cikin addinin Kirista aka haifi su Mimi bai kamata kuce haka ba tunda dai basu san komai ba, kuma ko yanzu a makarantar Annabi Ibrahim zasu tashi in Sha Allah! Balle kuma Ni uwarsu acikin musulunci aka haife ni kuma, na furta kalmar Ashhadu Allah ilaha Illallah, Wa Ashhadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu!" Da sauri mutumin yace, "Allah ya baki haƙuri, kiyi haƙuri dan Allah!" Na'ima bata kuma cewa komai ba sai kukan da take yi. Ita ta riƙa ɗaukar ƴaƴan tana kaisu ɗaki tare da rufesu har kai, bata yarda ko gawa ɗaya Lami ta taɓa ba, sai da ta kulle ɗakin sannan ta fito sanye da hijjab tana kuka ta nufi makarantarsu, shugabar makarantar ta sanarwar komai tare da roƙonta akan tazo tayiwa yaran wanka ta shiryasu. Sosai shugaban makarantar mai suna Malama Nusaiba ta tausaya mata tare da lallashinta ta kuma bata baki sannan ta kira su Nuratu don saura mintuna goma a tashi a islamiyar, suma sai da tayi masu nasiha mai ratsa jiki sannan ta shaida masu abunda ke faruwa, kuka suka fashe dashi duka, bata hanasu ba kasancewar ba kururuwa suke yi ba. Tare suka koma gidan har da Malama, kuma kamar yanda Na'ima ta buƙata, malamar ce tayi masu wanka sannan ta suturtasu da kikkafani. Khalil na kwance yayi ruf da ciki akan gado, ya rasa duniya mai ke yi masa daɗi, gaba ɗaya ji yake ya tsani kansa gaba, "Why am I even alive?" Be san sanda ya faɗi hakan ba yana mai kaiwa katifa nausuka kamar zararre! Burum Aina'u ta faɗo ɗakin tare da kama ƙugu tana kallonsa idanu a ƙanƙance, da sauri ya miƙe zaune yana kallonta gabansa na faɗuwa don duk lokacin da ta zuba masa idanu haka, matsanaicin tsoronta yake ji har gabansa na bugawa da sauri-sauri. Nuna kanta tayi tare da faɗin, "Ni! Ni zaka wulaƙanta Khalil saboda kaga matarka da ƴaƴanka? Wato idan mutuwa zanyi sai dai in mutu ko? Ka san cewar ban kawo ba, amma saboda tsabar iskanci da wulaƙanci shine ka sauka ka barni da wahala ko?" Ko mai Khalil bai iya ce mata ba, ji yake ƙirjinsa yayi masa wani irin zafi da ƙunci, hawaye ne yaji suna neman zubowa amma bai basu sararin haka ba, yana jin mugun tsanar Aina'u kamar ya kasheta, amma yana jin sam ko afuska ba zai iya nuna mata hakan ba, duk haushi da tsanar da yake yi mata, idan har suka haɗa idanu sai yaji komai ya washe. "Ina magana ka min shuru! Mahaukaciya ka mayar dani ko kuma me?" Ta faɗi a tsawace. Sam Khalil bai tsorata da tsawarta ba, amma yana ɗagowa suka haɗa idanu da Aina'u be san lokacin da ya furta, "Kiyi haƙuri dan Allah" ba. Harararsa tayi tare da faɗin, "Idan kana so inyi haƙuri in yafe maka, ka tashi yanzu ka sauka ƙasa ka samu ruɓaɓɓiyar matarsa ka koreta ita da ƴaƴanta, idan ba haka ba kuma...." Ta ƙarisa maganar tare da jan ɗan yatsarta akan kuyanta. Ƙura mata idanu Khalil yayi ko kyaftawa bai yi ba, wani uban tsawar ta kuma daka masa tare da faɗin, "Ko baka ji bane?" Da sauri ya miƙe tare da faɗin, "As you wish Ai'n!" Yana gama faɗin haka ya gittata ya fita daga ɗakin. Wani irin tsalle Aina'u ta daka tare da faɗin, "Yyyesss!" Khalil na fita daga ɗakin wasu zafafan hawaye suka shiga zubowa daga idanunsa har zuwa kan ƙirjinsa, kamar kwai ya fashe a cikinsa haka ya riƙa takawa har zuwa ƙofar ɗakin Sarah. Ya jima tsaye kamun ya saka hannu ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga, duƙe take a bakin gado tana sakawa Sam'an wando, da farin ciki gami da ihu yace, "Daddy!" Yana mai nuna shi da hannu. Da sauri Sarah ta waiga tana kallon Khalil ɗin dake bakin ƙofa yana kallon ƙasa hawaye na tsiyayo masa har yana ɗiga a ƙasa. Kallon su Sam'an tayi tare da faɗin, "You two should go and play in the parlour, will meet you there in the next two minutes!" Da sauri Sauban yace, "With daddy?" Ya faɗi hakane yana mai nunasa da hannu. Ɗaga masa kai tayi tare da sauko dashi daga kan gado, dukkansu sai da suka yi shaking hannun daddynsu, har zasu wucesa sai ya dawo dasu baya ya rungume a jikinsa tare da fashewa da kuka yana mai shafa fuskansu. Sarah ce ta ƙariso wajen itama kukan take yi sosai tare da kama hannunsu ta fitar dasu sannan ta jawo ƙofar ta rufe. Kallonsa ta riƙa yi hawaye na zubar mata, shi kuma kansa a ƙasa yana zubda hawaye kuma ya kasa ɗagowa ya kalleta, "Happiness!" Ta kira sunansa a hankali. Da wani irin ƙarfi ya jawota jikinsa ya rungume ƙas tare da sakin kuka kamar yaro, irin ruƙon da yayi mata sai da taji kamar haƙarƙarinta zai ɓaɓɓalle, "Ɗan sassauta kaɗan." Sarah ta faɗi muryanta na rawa don wani irin shauƙi da missing ɗin mijinta ne ya dirar mata, "Saraaah!" Ya kirayi sunanta cikin wani irin raunataccen murya tare da riƙeta gam-gam yana jin wani irin natsuwa na mamayesa, don ba zai iya tuna when last ya riƙeta haka ba. "Sarah meke faruwa damu! Sarah na haukace, ban cikin hayyacina, ban san meke faruwa dani ba, ina jin kamar an ɗauke Khalil ɗin dake cikin jikina, Saratuuuuuu." Ya ƙarasa kiran sunansa tare da fashewa da kuka jikinsa na rawa. Wani irin tausayinsa ne ya mamaye zuciyarta, soyayya da ƙaunarsa na kuma ruruwa a zuciyarta, a lokaci guda kuma tana aikawa Aina'u da kwandon tsinuwa na raba tsakaninsu da tayi. Don Sarah duk wannan abubuwan dake faruwa har ganinsa turmi da taɓaryan da tayi da Aina'u, bai taɓa sakawa taji ta tsaneshi ba, saboda tayi imani duk abunda yake yi ba'a cikin hayyacinsa yake ba, sai dai baƙin ciki da takaici kam ta ɗebe shi iya ɗiba, don ta tabbata da za'a gwada zuciyarta, za'a tabbatar ta samu matsala, Hassan jini kuwa idan yana kaiwa million, to nata sai ya wuce, don babu ranar da bata kwana ta kuma tashi da ciwon kai mai tsanani. "Addu'a itace makamin mumini daddyn twins, ka tashi tsaye ka kai kukanka gaban Ubangiji! Ka rage bacci ka raya darenka wajen roƙon ubangiji, ka yawaita saurarar karatun Alƙur'ani in Sha Allah duk wani abun da yake damunka a zuciyarka zai yaye kuma zaka samu sauƙi. Mun samu jin daɗin duniya, mun bar ubangiji shiyasa Allah ya barmu, amma idan muka miƙa wuya zuwa ga mahalicci, komai zai wuce kamar ba'a yi ba." Ƙara rungumeta yayi tare da faɗin, "Hakane! Hakane!! Maganar ki haka take Mine." Sun kusa mintuna biyar a haka suna jin bugun zuciyar juna kumun zuwa can yayi saurin janyeta a jikinsa ya nufi wardrobe tare da soma zubo da kayan sawanta dana su twins a kan gado kuma a lokaci guda yana kuka. Da sauri ta nufesa tare da kamo hannunsa tana faɗin, "Haolii menene haka? Mai yasa kake fiddo mana da kayan sawarmu?" Fincike hannunsa tayi ba tare da yace mata komai ba ya cigaba da fito da kayan kuma yana hawaye. Ƙara kamo hannun nasa tayi tare da faɗin, "Menene haka Khalil!" Da ƙarfi yace,"Ki sake ni Mine, ki sake ni dan Allah!" Ya faɗi tare da sakin rigar da ya ɗauko ya zauna a bakin gadon tare da riƙe kansa yana kuka. Duƙawa tayi a gabansa itama tana kukan tare da soma faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir!" Tun tana maimaitawa ita kaɗai har shima Khalil ɗin ya ɗauka, duk sai suka cika ɗakin da faɗin, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un." Aina'u dake ɗaki tana kallon komai a tafin hannunta ta kwaso da uban gudu har tana a dungure a steirs, ko kamun ta ida dungurowa ta saka yatsa ta caki tafin hannunta da ƙarfi, a take Khalil dake zaune ya zabura da ƙarfi tare da ture Sarah ya shiga faɗin, "Tashi! Ki tashi ki kwashi duka kayanki ku bar min gida ke da yaranki sai na neme ki!! Ki tashi nace!!!" A kiɗime Sarah ta tashi don ba ƙaramin ruɗewa tayi ba da jin wawan tsawar da ya buga mata. Ƙaton akwatinta ya jawo tare da soma loda kayanta dana yaran a ciki dai-dai lokacin da Aina'u ta banko ƙofar ɗakin ta shigo tana huci, "Wato kai kake haɗa mata kayan ko? To zo ka fice ta haɗa da hannunta." Idanu jazir Sarah ta kalli Aina'u tare da faɗin, "Aina'u ke ƴar wuta ce babu tantama! Baza ki taɓa gamawa da duniya lafiya. Fir'auna Kina samanki yake Aina'u. Uwa da uba ɗaya suka haife mu, amma wallahi tallahi billahil azeem bazan taɓa yafe maki ba ko da zanga kabarinki naci da wuta! Kin shiga tsakani na da mijina, kin shiga tsakani uwa da ƴaƴanta, Aina'u mutuwarki abun tsoro ce wallahi." Wani irin shu'umin murmushi Aina'u tayi tare da kallon Khalil tace, "Kana jin abunda take faɗi baza ka ɗau mataki ba?" Khalil dai bai ce komai ba, Sarah kuma a zuciye ta ƙarisa wajen Aina'u tare da wanke fuskanta da mari hagu da dama tare da fashewa da kuka tana faɗin, "Allah ya tsine maki Aina'u, Allah ya tsine maki albarka muguwa azzaluma, mara imani! A kafuran ma ke dutse ce, makamashin wutan jahannama! Yanzu baki ji komai ba Aina'u? Ki kwanta da mijina agaba da ƴaƴana Aina'u! Mijin yarki Aina'u!! Anya akwai tsoka a ƙirjinki kuwa? Aina'u ke ƴar wuta ce!" Wani kallo Aina'u tayiwa Khalil tare da faɗin, "Kamar yanda ta ɗaga hannu ta wanke fuskata da mari, haka nake so ka ɗaga naka hannun ka wanke fuskanta da mari, ka nuna mata babu wanda ya isa ya taɓa ni a gabanka ya zauna lafiya ko uban wanene kuwa!" Da sauri Khalil ya ce, "Aina'u......" "Don as I said!" Ta katse shi da ƙarfi. Juyawa
Showing 105001 words to 108000 words out of 129453 words
Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36 Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44