ya nufi wardrobe ya ɗauko hijjab ɗin ta ya saka mata sannan suka fito, a cikin mota ma karatun ya kunna, yana kallon Sarah yanda ta kwantar da kanta jikin kujera tare da lumshe idanu. Suna isa ya shiga da ita lab ya ɗibi jininta ya bada ayi gwaje-gwaje sannan suka fito suka nufi X-ray room, nan ma sai da yayi examining Virgina ɗinta sosai. Kusan test kala goma aka yi mata, basu suka dawo gida ba sai past 10, wasu tests ɗin sun fito a ranar, wasu kuma sai bayan 8days zasu fito, wanda suka fito a ranar guda huɗu ne, kuma gama ɗayansu komai normal, guda ɗaya ne ma a ɗan ga yest infection kaɗan shima kuma na ciki ne, babyn cikinta lafiya ƙalau. Suna dawowa gida ya sake yi mata wanka ya canza mata pampers tayi sallar isha'i sannan suka ci abincin da ya tsaya ya saya masu a restaurant. Yana son faɗa mata ɗan wajen Na'ima ya rasu amma bai son hankalinta ya tashi, don sun yi waya da baba daga baya, kuma ya faɗawa baban bata da lafiya sai dai bai faɗa masa asalin ciwon ba, baban yace masa ba sai tazo ba, tayi zamanta kawai zai faɗa masu bata da lafiya. Haka suka kwanta ba tare da ya faɗa mata ba. Bai ji kyamarta ba, yanda suka saba kwana haka suka kwanta kwance a kan ƙirjinsa, can cikin dare ya jisa sharkaf, cikin sauri ya tashi ya kunna bedside lamp, cike da mamaki yake kallon uban fitsarin da Sarah ta lafta duk da pampers ɗin jikinta ga kuma tsutsotsin nan sun fara fitowa. Tagumi ya zuba yana kallonta tana bacci peacefully bata ma san mai ke faruwa ba, hawaye ne suka gangaro masa na tausayinta, ya jima yana kallonta kamun ya sauka daga kan gadon ya cire boxer ɗin jikinsa don ya jiƙe sharkaf, bayi ya shiga ya wanke jikinsa sannan ya dawo ya soma tashin ta a hankali, miƙa ta soma yi, sai ji tayi hannunta ya sauka a kan lema, da sauri ta ware idanunta tare da tashi zaune tana mai faɗin, "Happiness, fitsari kwance nayi? Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Na shiga uku!!" Tausayi ta bashi sosai, sai kawai ya sunkuceta ya kaita bayin ya ajiye a tub sannan ya fito ya kwashe zanin gadon ya kai bayin tare da ɗauko wani ƙaramin towel da ruwa da liquid soap ya goge katifar sosai sannan ya saki fanka tare da kwasar janin gadon ya shigo dashi bayin ya zuba a bucket sannan ya isa gareta, babu abunda take yi tunda ya ajiyeta sai kuka, "Wallahi tallahi zaki ɓata min rai Sarah! Kanki farau ko ƙarau? Haba! Baki san kukanki na tada min da hankali ba?" Yana gama faɗin haka ya shiga cire kayan dake jikinta, sosai yaji tsoro lokacin da ya cire pampers ɗin jikinta gaba wannan jajayan mitsi-mitsin tsutsotsin sun koma canza colour, wasu sunyi green, wasu yellow-yellow, wasu kuma farare. Bai bari ta gani ba ya ajiye pampers ɗin sannan ya wasa ruwa ya shiga cuɗa jikinta. Sai da ya gama mata wankan sannan ya dawo da ita ɗakin ya ajiyeta a kan gado inda babu lema ya saka mata wani pampers ɗin tare da kayan bacci sannan ya mayar da ita ɗakinsa ya rufeta da bargo ya dawo nata ɗakin ya wanke kayan nan tsaf sannan ya koma ɗakinsa ya kwanta tare da jawota jikinsa. Aina'u dake ɗakin can side ɗin Hajiya tana kallon komai ta tsakiyar tafin hannunta, bata san lokacin da ta jefi mirror da wayarta dake gefensa ba, sai ji kake tatsatsatsatsa! Tafin hannunta ta matsa da ƙarfi, wannan karon _Hell Ofulafu_ bai bayyana ba, wannan mummunar halittar ne ya bayyana tare da faɗin, "Kina da wutar ciki Aina'u, duk abunda muka ce zamu yi, za muyi shi, shin bamu cika maki biyu daga ciki bane? Rabo ya mutu, Abdul-Hakeem ya saki Maryam, yanzu saura warin da za'a turawa Khalil, korar Abdul-Hakeem daga aiki, mutuwar Nafeesa da kuma mantar da LTD Abdullah da Muhammad Kabiru cewar suna da uwa da ƴan uwa a Kaduna. Kar ki ƙara neman mu akan wannan buƙatar, sai dai idan wata buƙatar ke gare ki." Yana gama faɗin haka ya ɓace. Ajiyar zuciya Aina'u ta sauke tare da kwanciya rub da ciki, can kuma ta miƙe ta buɗe zip ɗin jakarta ta ɗauko murɗin wiwi ta saka a baki tare da kunna lighter ta hau zuƙa, sai da tasha murɗi uku sannan ta kora codine kwalba ɗaya sannan ta faɗi yarab a kan gadon ta hau bacci. Bayan kwana uku, sam Hajiya bata lura aunty Maryam bata gidan ba, don tare suka tafi da Moon, ya Abdul-Hakeem kuwa yayi wani irin zugewa, don washa garin ranar da ya saki aunty Maryam aka dakatar dashi daga aiki, Hajiya kuma ta kasa tambayar ina Aunty Maryam ɗin duk da kuwa bata ganinta, wani irin mahaukacin tsoron Aina'u take yi, idan ta ganta gabanta faɗuwa yake yi, Nafeesa ma haka, wannan dalilin ne ya saka ta tattara tabi mijinta duk da dama shima abunda yake so kenan, don dangi sun taso shi gaba akan ta dawo gidan auranta. Zaune Hajiya tare a kan kujera ta rasa abunda ke damunta, ga Laure dake gefenta wacce lokaci bayan lokaci take saka bayan hannu ta share hawayeta, tayi wani irin mugun rama, hatta a fuska sai ƙasusuwa suka fito mata, babu komai a fuskan dai idanu da haƙora yaƙaƙau! Fitowa Aina'u tayi daga ɗakin da Hajiya ta ware mata tana fito, babu wanda ya iya ɗago idanu ya kalleta a cikinsu, "Hajiya ko kin san wannan abun dake hannuna?" Faɗin Aina'u tana mai kai mazaunanta akan kujera, ɗagowa Hajiya tayi ta kalli hannun nata tare da girgiza kai. Sakawa a baki Aina'u tayi tare da kunna lighter ta kai kan wiwi ɗin tayi masa wani irin zuƙa tare da faɗin, "Wiwi ce!" Zaro idanu Hajiya tayi tare da yin gum, Laure kuwa babu inda jikinta baya rawa ga warin hayaƙin mara daɗi mai tada zuciya kuma babu wanda ya isa ya tashi a cikinsu. Sai da tasha murɗi biyu sannan ta kwanta akan three sitter tare ɗaura ƙafa akan saman kujeran tana kallon Tv, can kuma ta juyo ta kalli Laure tare da faɗin, "Ke, tashi ki canza min channel zuwa MBC action." Da sauri Laure ta tashi ta nufi wajen TV ɗin daidai lokacin da Khalil yayi sallama ya shigo ɗakin domin shaidawa Hajiya yana son shi da Sarah su tafi India domin a duba masa jikinta, don gaba ɗaya result ɗin tasa-tasan da aka yi mata a asibitin bai nuna tana ɗauke da matsalar komai ba. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, Hajiya! Warin wiwi fa nake ji a ɗakin nan." Da sauri Laure da hajiyan suka kalli juna sannan suka kalli Aina'u da ta wani irin ɗaure fuska. "Hajiya......." Tun kamun ya ƙarisa Hajiya tayi saurin faɗin, "Ni dalla ka isheni da magana, to ni nasha wiwin!" Zaro idanu Khalil yayi, sai kuma ya mayar da dubansa izuwa wajen Aina'u tare da faɗin, "Dan ubanki kece kika sha wiwin ko?" A watse ta kallesa tare da faɗin, "Hajiya ce tasha, ko baka ji ta baka amsa ba." Wani wawan mari Khalil ya ɗauke fuskan Aina'un dashi tare da faɗin, "Dan ubanki zo ki bar gidan nan tun da ba gidan ubanki bane......"








*👭GARKUWAR MATA*
*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu za ki yi godiya, sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki. Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*
*GA*
*Kadan daga cikin abubuwan da muke sayarwa*
Rage tumbi💯
Nono💯
Sanyi💯
Karin kiba💯
girmar hips💯
Ni'ima💯
Sabulai💯
Humra💯
Turarukan wuta💯
Matsi💯
Miski💯
Dilka💯
Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki
GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari
DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI
*08089965176*
*07084653262*


*_MATAR SAYYADEE_*

*Paid book 08128755583*


🦜 *KANWAR MATATA* 🦜

*29*


"To sannu ɗan masu gida! Wai kai Khalilullah mai yasa baka da kawaici ne a rayuwarka? Ƙanwar matarka ce fa! Ai ko don uwata ka raga mata. Gaskiya ka ɗauki hakki, kuma ka bata haƙuri." Faɗin Hajiya rai a ɓace. Nuna Aina'u dake riƙe da kunci yayi da hannu tare da faɗin, "Wannan ɗin zan bawa haƙuri? Kiyi haƙuri Hajiya, ban taɓa tsallake umarninki ba, amma yau kam bazan iya abunda kika umarceni da nayi ba. Hajiya hayaƙi ma ba sonsa kike yi na sani, Laure ko ina da tabbacin bata ma taɓa ganin wiwi ba bare ta kai bakinta, yarinyar dake fama da kanta ma ina taga lokacin shan wiwi! Nayi imani da Allah Aina'u ce tasha wiwin nan, kuma a yau ɗin nan kuma ba yanzu ba, sai ta bar gidan nan wallahi!" Da ƙarfi Hajiya tace, "To kuwa za kayi kaffara don Aina'u babu inda za taje wallahi! Wiwi dai ni nasha gama sauranta nan." Faɗin Hajiya ta hau waige-waigen inda zata hango saurin da Aina'u ta har a parlourn, da sauri tace, "Yauwa gashi nan!" A tare suka kai jiki, ita ta kai hannu, shi kuma ya kai ƙafa ya take sauran guntun wiwin don kada Hajiya ta kai hannu ta ɗauka. "Ai Hajiya da sauri kika yi kika rigasa ɗauka, kin ga idan kika kunna kika yi zuƙa ɗaya a gabansa wata ƙila yafi gasgata maganarki." Wani irin shaƙa Khalil ya kai mata tare da faɗin, "Hajiya zan kashe yarinyar nan sai dai nima a kashe ni." Da sauri Hajiya ta taso ta hau kiciniyar kwace hannun Khalil a wuyan Aina'un da har idanunta sun soma firfitowa, "Wallahi idan baka saki wuyar yarinyar nan ba zan tsine maka Ibrahim." Wani irin wurgi da ita yayi sai da kanta ya bugu da Centre table ɗin dake ɗakin ji kake tatsatsatsatsa ya fashe, take jini ya hau tsartuwa a kan Aina'u wacce tuni ta sulale ta sume, hannu Hajiya ta ɗaura a kai tare da faɗin, "La'ilaha illalah, Muhammadur Rasulullah Sallallahu alaihi Wasallam, Khalilullah!" Da sauri Khalil ya bar ɗakin a zuciye, don shi ko a jikinsa duk da uban jinin da yaga Aina'un na zubarwa. Daga nan fita yayi daga gidan gaba ɗaya domin cuku-cukun passport ɗin Sarah. Hajiya kuwa gaba ɗaya ta ruɗe sai kiran sunan Khalil da ya jima da barin gidan take yi, Laure dake zaune itama ko motsi bata yi ba, addu'a kawai take yi a zuciya Allah yasa daga suman da tayi ta wuce barzahu kowa ya huta. Ruwa fridge Hajiya ta ɗauko ta fasa a fuskan Aina'un, a gigice ta farfaɗo tana zazzaro idanu, can kuma ta tashi da sauri jini na ɗiga ta wuce ɗakin dake mallakinta ta rufo ƙofa, bata damu da ciwon jikinta ba ta matsa tafin hannunta da ƙarfi sai ga Khalil ya bayyana a immigration office suna magana da wani, wani irin zaro idanu tayi tare da faɗin, "Barin ƙasar? To ai sai kuyi tafiyar in gani duk da kuwa na san idan asibitocin duniyar zaku zaga, Sarah baza ta taɓa samun lafiya ba." Tafin hannun ta kuma matsawa, sai ga wannan mummunar halittar ya bayyana fuska a ɗaure tare da faɗin, "To uwar ƴan ƙorafi, menene kuma yanzu?" Kallon gefe tayi tare da kai hannu ta ɗauki kwalbar turaren dake kan mirror ta fasa sannan yanki hannunta na dama tare da tsiyaya jinin a fuskan wannan mummunar halittar sannan ta ɗuka akan guiwowinta tare da faɗin, "Dan tsarkin tsafin _Hell Ofulafu_ ka taimakeni kamar yanda Khalil ya zubar min da jini, ina so shima ya ɗanɗana ɗacin da naji wajen yin kuka da idanunsa, ina son a yau ayi kukan mutuwa a cikin gidan nan, sannan a hana Khalil fita daga ƙasar nan da matarsa, bama ƙasar nan ba, a kasar masa da tunanin nemawa matarsa magani ko da a wajen Kaduna ne!" Ta ƙarisa maganar ne tare da tara kanta dake tsiyayar jini a tafin hannunta, yayin da mummunar halittar nan ya saka harshe yana lashe duk wani jini dake ɗiga a jikinta. Sai da ya gama lashewa sannan ya shiga ɓaɓɓaka mahaukacin dariya tare da turo hannu ya dafa kanta sannan ya ɓace. Lumshe idanu tayi tare da faɗawa bayi don ta san ɓacewar yana nufin buƙatarta zai biya. Khalil yana tsaye yaji kamar an kwaɗa masa guduma akai yayi saurin dafe kan tare da tsugunawa. "Lafiya Khalilullah?" Abokinsa yayi saurin ɗukawa tare da faɗin haka. Bai ce komai ba, amma ya daɗe yana jin wani irin wuuuu a cikin kansa kamun ya miƙe ba tare da yace komai ba ya nufi wajen motarsa, "Ibrahim! Ibrahim!!" Abokinsa yayi kiransa yana bin bayansa, amma ko sauraran bai yi ba ya buɗe motarsa tare da shiga yaja ya bar wajen, sai da yayi nisa da immigration office ɗin sannan ya soma jin wasai a cikin kansa. Aina'u kuwa canza kaya tayi tare da yiwa kanta dressing sannan ta kunna wiwi tasha tare codine saboda zuciyarta da yayi zafi, sai da ta zuƙi wiwi ta fesar sannan tace, "Na rantse da girman Yesu Almasihu, ba don tsananin son da nake maka ba, da wannan marin da fasa kan da kamin ba zai tafi a banza. Da sai na kashe ka a yau ɗin nan, amma duk da haka, You'll pay for it!" Nafeesa na kitchen tana dafa pasta, Qasim na parlour yana kallon Tv kwance akan resting chair dake parlourn yana jiranta ta kawo abuncin, don tun da suka tashi basu ci komai ba, "Honey kin kusa?" Ya faɗi da ƙarfi ta yanda Nafeesan zata ji daga kitchen ɗin, "Soon in Sha Allah!" Faɗin Nafeesa tana mai saka carot da ta gama wankewa, a gigice ta saki ludayin dake hannuta tare da buɗe baki za tayi ihu, cak bakin ya tsaya a buɗe ba tare da ihun ya fito ba, jininta babu inda baya rawa ga fitsarin tsoro dake zirarowo daga jikinta ganin halitta mafi muni a gabanta, harce ya fiddo kamar na maciji ya caki wuyanta ya shiga tsotse jinin jikinta, sai da ya tsotse kaf sannan ta faɗi ƙasa yaraf, shi kuma ya kai hannu ya cire pipe ɗin gas ɗin tare da haɗa gobara a kitchen ɗin sannan ya ɓace ɓat. Da mugun gudu Qasim ya fito daga parlourn jin wani irin warin gas na bala'i, yana tura ƙofar kitchen gas yayi wani irin uban tsalle ya bugi fuskansa, kan kace kwabo gaba ɗaya gidan ya kama da wuta, gas ɗin nan kuwa haka ya dunga tsalle yana faɗawa gidan maƙota. Kasancewar layine na masu kuɗi, tuni har a kira ƴan kwana-kwana na Private, kuma cikin ƙanƙanin lokaci suka iso suka fara aikinsu. Sai da aka fara cire wutan unguwar gaba ɗaya sannan aka shiga kashe wutan, mutane goma sha shida ne suka yi mummunar ƙonewa, daga ciki har da Qasim mijin Nafeesa, gaba ɗaya tun daga kai har tafin ƙafa ya ƙone, ana taɓa jikinsa fata ke biyowa, Nafeesa kuwa tattare dagwargwajajen namanta aka yi, don wasu ma dun manne a jikin tiles da wuƙa aka kankaro, babu abunda ke tashi unguwar sai koke-koken mutane. Ƴan uwan Qasim kamar zasu haukace, wasu suka nufi asibitin da aka kai shi, wasu kuma suna tare da dagwargwajajen naman Nafeesa, ya LTG Abdullah suka kira, sai dai number ɗinsa bai shiga don jiya ya bar ƙasan zuwa China. Mayar da aƙalan kiran suka yi zuwa ya Abdul-Hakeem, shikuma ya kashe wayarsa gaba ɗaya saboda tashin hankalin da yake ciki, Khalilullah da driving zai dawo gida wayarsa ta hau ringing, sai da yayi parking saboda bai ɗaga kira idan yana driving sannan yayi picking, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" Shine abunda ya dunga maimaitawa har ya sauke wayar a kunnansa, haɗa kai da steri yayi wasu zafafan hawaye na zubo masa daga idanunsa, ya jima yana hawaye kamun yayiwa motar key ya nufi can gidan Qasim ɗin. Tun daga nesa da layin yake hango hayaƙi da ƙauri duk da an samu nasarar kashe wutan, parking yayi ya nufi inda ƴan uwan Qasim suke, maza huɗu ne da mata biyu, matan sai rusa kuka suke yi, mazan kuma sunyi jigum-jigum suna kallon naman Nafeesa. Kai tsaye wajen dagwargwajajen naman yayi tare da duƙawa yana kallo wasu maƙudan hawaye na zirarowa daga idanunsa, jikinsa har rawa yake yi tsabar tashin hankali, "Allah ya jiƙanki Nafeesa, Allah yasa kina cikin rahamarsa, Annabi yasan da zuwanki." Yana kawowa nan ya fashe da kuka tare da saka tafin hannunsa ya rufe fuskansa. Sai da Mukhtar wan Qasim ya ɗagosa tare da janyesa gefe yana bubbuga kafaɗunsa alamar rarrashi. Haɗa kai da bango Khalil yayi, hawaye sun kasa tsayuwa daga idanunsa, dakyar ya iya controlling kansa ya fiddo wayarsa daga aljihu tare da dialing number ya Abdullah, wayar bai shiga, sai ya kira layin ya Abdul-Hakeem, shi kuma switchoff, sai ya mayar da akalar kiran zuwa layin uncle
Showing 87001 words to 90000 words out of 129453 words