shiga wasu fine dogayen riguna yasaimata guda uku sai simple gown mai spaghetti hand guda biyu, daya orange daya black ash color, yadau mata cream, sai takalmi da kai tsaye yasaimata 37 dan yaga batada kafa, sanan shima yasai t-shirt da wando, yabiya kudi akamai packaging nasu yafito sanan yakoma dakinsu, har lokacin tana bayi bata fitoba, kayan ya ijiye mata kan gado sanan yawuce yafita daga dakin yakoma motarshi ya zauna, hannunshi yamika yadau wayarshi ya shiga saka wasu nambobi kafin yay dialing number, kusan ringing uku aka dauka, cikin wanan voice din nashi na nuna babu wasa aciki yace "This is Lieutenant Sameer Simran Sameer I want to speak to Governor of Gombe state please" yay shiru kafin ya janye wayan daga kunnenshi, ko minti biyar ba'a daukaba same number daya kira yakirashi back hakan yasa yay picking.....





Takai almost 15 minutes wanka take da ruwan zafi da sabulen data gani a bayin wanda hotel ya ijiye musu, tadau shampoo da hotel din ya ijiye musu ta jujjuye akan kitsontadaya tsufa sosai yafara warwarewa dan dama dogayen kalabane dudda bata wani iya wanke kaiba tarage dauda kan sanan tasake wanka tai brush data dade bata samu tayiba dan hotel sunyi providing nasu da new brush da tooth paste sanan tadau towel ta daura akirji tadau wani karami ta daura akanta dan ya tsane ruwan tafito tana sauke ajiyan zuciya kanta najuyawa, dan kadan tabude kofa ta leka ganin babu kowa adakin sai TV dake aiki shi kadai yasa tafito dasauri tsigan jikinta na tashi, ledan data hango akan gado da bakin kaya yadan leko haka data gani akan gado cikin leda yasa tabude kofan tayi kan gadon, ledan tadaga ta zazzage kayan wanan mai spaghetti hand din orange color idanunta suka sauka akai dan bazata iya saka sauran manyan dogayen rigunan ba, da sauri tadauka tasaka babu komi acikin jikinta rigan kawai tazura kaman ya aunata rigan yamata kyau sosai yakara haska fatarta, anan kasan dakin ta yarda towel din data cire dan batada karfin komawa bayi ta ijiye gawani mahaukacin sanyin dataji tafaraji sosai hakan yasa tahau kan gadon taja bargo ta kudundune sosai tana sauke ajiyan zuciya ko minti daya ba'ayiba bacci yay awon gaba da ita mai nauyin gaske.



Tareda Dr da receptionist din takiramai yadawo, Dr magidanci ne sosai dudda ba lallai ya haifi Sameer ba but Rahima kam ya haifeta, yana rike dawani dan babban kit da kayan aikinshi ke ciki, dan knocking kofar dakin Sameer yayi dan yasan yabarta tai wanka kafin yabude kofan ahankali ya shiga Dr biyeda shi yakafa mata idanu ganin baccinta take shrarawa ga towel akasa daga chan ta cikin gadon kuma kayan dayasayo musune bata mayar cikin ledan ba, maida idanunshi yayi kan fuskanta daya kara yin ja sosai kaman allergies din yakaru sai pink lips dinta dayay jajir shima na irin mai zazzabi, towel din data daura akanta yadan zame kasa hakan yabama gashin gaban kanta daman fitowa sun tattare and all coiled up kaman na karaman baby, kallon Dr yay yace "common in" shigowa Dr din yayi yana kallon Rahima dake bacci yace "is she the patient?" gyadamai kai Sameer yayi yakarasa gaban gadon ya daga towel din dake kasa ya shiga bathroom ya ijiye sanan yafito ya zauna kan kujera ya kalli Dr yace "kaduba ta" karasawa jikin gadon Dr yayi yabude kit dinshi dake kasa yadauko wani dan tocula yarike hannun yana kallon yanda fuskar nata yay wani strange red kaman jini yataru a fuskan yajuyo ya kalli Sameer da hankalinshi kekan TV yay wanan zaman nashi looking well compose and serious yace "yallabai yarinyar nan is her skin reddish haka kokuma bahaka bane?" yatsa Sameer yadan kada yadan kalli fuskarta kafin ya kalli Dr yace "she's not this reddish, just normal fair girl" gyadamai kai Dr yay yamaida hankalinshi kanta ya kunna torchlight dun dayake rikedashi yadan duka
yaja naman idanunta yabude idanunta ya haska da tocula hakan yasa tabude shanyayyun idanunta da sauri jin haske a kwayan idanunta, cire hannunshi Dr yayi daga fuskarta yace "sannu kin tashi, tashi ki zauna naduba ki, am a Dr, and am here naduba ki, sorry kinji tashi ki zauna muga" ahankali ta tashi ta zauna tana dafe kanta da kaman zai fadi akasa ta janye bargon daga jikinta, yanda Dr yaga tana rike kanta yasa yace "sannu" yay maganan yana dauko stethoscope da abun auna bp ya makala yakama hannunta yadaura ajijiyanta, wani irin tashi tsigan jikinta yayi hakan yasa tawani irin sosa wuyan ta cikeda gajiya da yanda tsigan jikinta ketashi ahankali Dr yace "sorry kinji" yadan juyo ya kalli Sameer dayay kaman baya jinsu idanunshi kan wayanshi dayake duba wani sako yace "officer yarinyar nan is suffering from chronic allergies she came in contact with kodai something da jikinta bayaso kokuma wani abinci taci da jikinta is trying to reject, and she is having maleria, akwai kuma yunwa tattare da ita, zan samata ruwa yanzu sabida karfin ta yadawo zanyi allura ciki dazaisa tadawo normal, sanan zan rubuta maka wasu magunguna da bandasu anan you should go and get them for her tasha sanan taci abinci and tasha fruits, anjima da daddare zan dawo nasake dubata in drip din yakare nacire mata" gyadamai kai Sameer yayi batare dayace komiba, Dr ya tsugunna yadauko wani drip ya sagale shi a jikin kan gado ya tsaya chak, sanan yadauko allura, tana ganin allura tabare baki takoma cikin gado da gudu tana kuka tace "dan Allah karkamin allura, in kanama iyayen ka karkamin kaji" kallonta Sameer yayi itama cikin kuka ta kallai tana girgiza kai hakan yasa towel din kanta yakarasa warwarewa yafadi akan gadon tace "dan Allah kar amin allura" dan dariya Dr yayi yace "opisa wanan kanwar takane ko Hajiyar ka zance anyi raguwa anan" yay maganan yana dan rage tsawonshi a gabanta, yamika hannu zai kamo hannunta takase komawa chan karshen gadon da sauri, wani mugun kallo Sameer yamata yace "give him your hand right away" gyadamai kai tayi kirjinta na bugawa sosai tana goge hawaye da dayan hannunta, tadawo inda take zaune ahankali ta zauna, hakan yasa Dr yakarbi hannun yana murmushi ganin yanda take kuka yace "yauwa muga hannun ahankali zan miki" sake bare baki tayi tace "to kabani magani wlh zansha Allah amma karka samin alluran nan ajikina" ta karbe hannunta ta boye hannun abayanta tafashe da kuka sosai tace "dan Allah kabarshi kabani magani zansha wlh wlh please" hada ido sukayi da Sameer wani mugun kallon dayamata yasa ta bashi hannunta tareda runtse idanunta da karfi, daure hannun Dr yayi da igiya sabida yasami vein sanan ya soka allura ahankali dudda hannunshi babu wani zafin kirki amma saida ta kurma ihu tace "Mummy, wayyo Mummy zafiii" dan dariya Dr yayi yace "a'a kace yar Mummy ce, saisa kikeda wanan uban rakin, to angama" bude idanunta tayi tana kallon hannun da Dr yamata fixing drip.
[6/30, 10:15 AM] Marsy😘: 48.....






Dr yadauko prescription sheet na hospital nashi yarubutamai magungunan sanan ya hada jakan yarufe yatashi yana gyara zaman eye glasses din idanunshi hakan yasa Sameer yatashi yamikamai hannu yace "thank you Dr" murmushi Dr yayi yace "bakomi saina dawo dubata anjima da night, makesure taci abinci yanzu dan saitaci abinci zata iyashan drugs dinan dazaka bata" ahankali Sameer yace "in sha Allah" sanan Dr yamusu sallama yawuce yafita tareda mayar musu da kofa yarufe, komawa Sameer yayi yazauna kan kujeran dayake kai yadaga land line din yakira hotel kitchen din dan kusa da landline din an rubuta various number places a hotel din kaman su reception, kitchen da bar, da sauransu, ringing daya kitchen din suka daga yace "I want fruit salad, anddd" yay shiru yadaga kai ya kalleta har lokacin hawaye take sharewa tana kallon hannun da aka makala mata drip din sai kawai ya dauke kai yace "fried rice with water, the one that's not cold" ya maida wayan ya ijiye, wayarshi ne dake kan jikinshi ya shiga ringing da sauri yadaga wayan ganin Ummi ne yasa yatuna bai sanar da ita bazai dawo gidaba kuma inba tafiya ba koyaje wani assignment a outside Abuja ba, baya taba fashin kwana agida, dudda Ummi na bacci da wuri amma yarasa ya akayi duk in bayanan take notising koda baidawo gida da wuri bane tasani, ajiye landline din yayi yadaga wayan yana kallo, answering call din yayi ahankali yace "Ummi na" yanda yafadi Ummi na saida Rahima tadago kai ta kallai cikeda mamaki dama wanan masifaffen sojan na ragema wani murya haka haladai mamanshi ne.


Cikeda dan bacin rai Ummi tace "I call to ask you one single question, just a question Sameer" dan faduwa gabanshi yayi dagaji yasan Ummi tai fushi dashi sosai, tace "na lura kasoma zama man of your own yanzu Sameer, you feel kai keda kanka you have the right to do duk yanda kaga dama, naji kuma nagane Sameer, tambayata itace incire idanuna ne akanka kawai na zuba maka ido?" shiru yayi yakasa amsata hakan ya mugun tunzurata ta dakamai tsawa. "answer me Sameer, nace in cire idanuna ne akanka na zuba maka idanu, dan I see no reason dazan dinga damuwa akan ka, sabida ka rainani Sameer kaga ka girma saika tashi bazaka kwana agidaba kuma kaki kira ka sanar dani eh Sameer and inama magana you kept mute kaman wanda yahadiyi dalma" cikeda damuwa ahankali yace "am sorry Ummi, please" tashi yayi akan kujeran yadan juyo hada ido sukayi da Rahima da tunda yafara wayan take kallonshi kaman yauta fara ganinshi harara ya balla mata yawuce yafita daga dakin, ya sauka chan kasa, garden din Hotel din yashiga yazauna kanwata kujera mai kyau tashan iska shi kadai awurin yasake dialing number Ummi din danta kashe cikin fushi jin baya amsata, saida wayan ke gabda katsewa ta dauka tai shiru batare datai magana ba hakan yasa cikin kwantacciyan murya irin ta lallashi yace "am sorry Ummi na, dan Allah kiyakuri kinji" cikin fushi tace "ban neman hakurin ka, just tell me kana ina yanzu haka?" dan jim yayi 1st policy din rayuwan shi shine baya karya ko zaka kasheshi baya karya, instead of yay karya to gwara yay shiru kawai yaki baka amsar tambayan ka koda zaka tsinemai ne. "kana jina kai shiru Sameer?" ahankali yace "ina Gombe Ummi, am sorry I was on my way coming back home da magrib jiya issue came up da dole I had to attend, Ummi am sorry karkiyi fushi dani kinji" cikin kakkausan murya Ummi tace "mekaje yi a gombe Sameer?" dan jim yayi kafin yace "aiki ne, anjima kadan zaki gani a news Ummi, news din will be a all kafafun yada labaran duniya" dan ajiyan zuciya tasauke tadamu da situation din Sameer saisa any abu nashi yake tadamata da hankali, jin tai shiru batace komiba yasa yace "I am sorry, rushing to the place nake saisa I couldn't call you nafada miki zanje aiki Ummi, kiyakuri kinji, kinyafe min?" ajiyan zuciya ta sauke tace "naji nayafema Allah maka albarka" murmushi yayi yaji wani sanyi aranshi tace "yaushe zaka dawo?" ahankali yace "tommorow or next tommorow" "okay daman Mu'az yadawo gida dazun nan wai ASUU sunje warning strike na 2weeks" gyadakai yayi yace "eh yafadamin yamini text, tunda yadawo gida tell him nace yaje farm house yataya su ishak aikin dana sasu" ahankali Ummi tace "tom zan gayamasa gamashi nan ya shigo yana jinka tunda yadawo yadaman wlh Sameer danai magana yace wai shine Auta haka autanni keyi, am fed up fa, ni yakoma school yazauna yajira su gama warning strike din tunda just 2weeks ne yafimin" dan murmushi Sameer yayi yace "put him on the phone Ummi" kafin ma Ummi tabashi wayan Mu'az ya fizge jin Sameer yace abashi, cikeda murna yana wani irin murmushi yace "Ya Sameer ina yini" yay maganan yana tashi daga kusada Ummi yay dinning da gudunshi Ummi tabisu da kallo tana murmushi tanason yanda yaranta keson junansu duka saisa ko kadan batama Sameer fada agabansu shima Mu'az shigowan shi kenan yanzun nan duk fadan datama Sameer ba a idanunshi bane.



Ahankali Mu'az yace "good morning Ya Sameer" anatse Sameer yace "morning kiddo, why are you disturbing Ummi?" kaman zaiyi kuka ashagwabe yace "Ya Sameer nifa kudi nakeso tabani waidan nace tabani Atm card dinta shine wai ina damunta bazata bayarba zan emptying account dinta" ahankali Sameer yace "tome zakai da kudi?" ashagwabe yace "aski zanyi fa, sanan da gyaran farce" gyadamai kai Sameer yayi yace "alright will transfer money for you, but kadena damun Ummi at her age bata bukatan damuwa sai kwanciyan hankali daga wajenmu, karka bari takara kawomin irin wanan complain din am I clear" gyadamai kai Mu'az yayi kafin ya saramai ya buga kafa akasa yace "Crystal clear Sir!" da sauri Ummi tace "wlh kafasamin tiles saika kawo kudin gyaran su" daga tachan bangaren Sameer yace "bama Ummu wayan" da sauri ya kaima Ummi wayan ta amsa ta kara a kunne yace "okay Ummi namai magana, inya kara damunki just let me know" hararan Mu'az din daya daura kanshi kan cinyarta tayi yana daddanna waya abinshi tace "balm din kafafu na yakare Soja, na aika su Noor da Muhammad basu samomin ba wlh, duk pharmacy dazasu babu" gyadamata kai yayi yace "idan zan dawo zan tahomiki dashi" murmushi tayi tace "shikenan nagode, Allah yay albarka, kome zakayi kadinga yi tsakani ga Allah kaji, abinda akayi tsakani ga Allah, Allah yafi sanya albarka cikinshi, Allah yay muku albarka gabaki daya, Allah ya tsaremin ku aduk inda kuke yakare min ku" ahankali dagashi har Mu'az dake kwance sukace Ameen sanan yace "saina kira anjima Ummi bye" "bye Son" katse wayan yayi yatashi daga Garden din yawuce cikin hotel din. Dakinsu yabude ya shiga kwance yaganta kan gadon tana bacci hankali kwance ta lulluba da bargo, tray da aka aiko musu abinci kusada gadonta yabi da kallo, tsugunnawa yayi yabude yaga ko kadan bata taba rice dinba sai bowl na fruits wanda yaga gane na fruits ne sabida chunks of pineapples dayagani acikin bowl din da fork kenan shi kawai tasha, maida rice din yay yarufe yatashi yasa hannunshi ahankali yadau kayan shi daya saya a boutique din dake hade da nata yabude bathroom din ya shiga ya maida kofan yarufe, wanka yayi yacire uniform dinshi ya kwashe farin riganshi da jacket dinshi datai hanging abayin yajefa cikin wani dan mini basket sanan yay wankan yadade yana wanka ya gama tsaf ya shirya cikin jean da rigan daya saya da suka mai kyau sosai sanan yafito rikeda basket din, yadau wayanshi, wallet da prescription note din yasaka a aljihu yadau car key yafita, saida yabiya laundry hotel din yabasu uniform din nashi dan su wanke mai sanan yafita ya shiga mota ya kunna wani gidan mai yafara zuwa yasha mai sanan yafito ya shiga gari dudda baiwani san kan gombe sosai ba gaban wani shago ya tsaya dayaga ana dinka hijabi yasai guda daya maroon mai hula da hannu sanan ya koma mota yacigaba da tafiya saida yaga wani babban pharmacy sanan yay parking ya shiga yasa yo duka magunguna ciki harda na wanda zata shafa a inda kuraje ya feso mata da kuma reddish din allergies din sanan yafito ya shiga wani super market another set od cloth yasaima kanshi da takalmi itama yasai mata takalmi sanan yawuce yakoma mota ya ijiye komi sanan ya shiga wani masallaci that is at the road side yay sallan la'asar yafito ya shiga mota yaja awani eatry ya tsaya yaci abinci sanan yaja mota yakoma hotel din, har lokacin tana bacci ajiye komi yayi yadau kayayyakin sawa su yasa a wardrobe din hotel din sanan ya zauna ya cicciro magungunan daya siyo mata yana karanta leaflet dinsu, maganin maleria ne dakuma na allergies din sai multuviate dazai bata apatite yakuma sa taci abinci, aijiyewa yayi yatashi yafita.[6/30, 10:16 AM] Marsy😘: 49&50




Bayan sallan magrib suka shigo Hotel din tareda Dr din sunadan taba hira, knocking Sameer yayi tana zaune kan gado rike da rice din dazu data kasaci mugun yunwa takeji but dukta yanda taso ta chusa abincin acikin tane takasa sai kallonshi take akan kafafunta knocking da akayi yasa ta dago kanta batare datace komiba dan batada karfin magana bata dade da tashi daga baccin bama, bude kofan Sameer yay ahankali suka hada ido ahankali ta saukar da kanta kasa duk in suka hada ido sai gabanta yafadi juyawa yayi ya kalli Dr yace "come in" shigowa Dr yayi yana kallon Rahima yace "iyye patient ke kadai wanan delicacy din ba tayi?" dan murmushi tayi batare data dago kantaba yakaraso gaban gadon yace "to kishi abincin mana" girgixa mai kai tayi tasa hannu ta share hawayen daya zubo mata ahankali tace "nakasa ci" cikeda damuwa Dr yace "ahh sorry bakida apatite ne, don't worry tunda yanzu kin tashi akwai magun gunan dazaki sha zaki sami apatite nan da zuwa gobe zaki warke ok, mezakici yanzu?" murya chan kasa kaman wata marainiya tace "sliced fruits" dan juyowa Dr yayi ya kalli Sameer dayay kaman baya jinsu yace "call the kitchen officer akawo mata fruits, she can't take those drugs on empty belly" landline Sameer yadauka ya shiga kiran su shikuma Dr yajuyo ya kalleta yace "ban hannunki ruwan yakare nacire miki" mikamai hannun tayi ahankali yacire mata sanan ya shiga dubata temperature ta yasauka sosai ba kaman dazu ba, knocking akayi Sameer yabada izinin shigowa fruits din aka kawo mata acikin wani bowl da aka daura akan tray aka rufe takawo har gaban Sameer da hannu yanuna mata Rahima takaimata tareda mata sannu da jiki ganin batada lpy sanan tajuya tafita Dr yace "farasha" farasha tayi ahankali shikuma Dr yajuya yaje wurin Sameer ya karbi magungunan sanan ya ballo wanda zatasha yadau bottle water yace "gashi sha" karba tayi gabanta na faduwa watsawa tayi abaki sanan tadau ruwa tasha tana tabe fuska Dr yace "good gurl, shanye fruits din to" cigaba da sha tayi bata wani bata lokaci ba ta shanye tass, Dr ya karbe plate din yadaura kan tray sanan yadau balm din tube din da Sameer yasayo a pharmacy yace "kinga wanan maganin kije kiyi wanka
Showing 81001 words to 84000 words out of 212889 words