tunda aka haifeta bata taba shiga tashin hankali irin wanan ba, bama tasan cewa akwai tashin hankali hakaba aduniyan nan daga zuwanta birthday yan sanda ne koyan menene sunwani kamata, Sameer dawasu officer guda biyune kawai a compound din yana musu magana, sauran suna waje wurin mota tsare da yaran dasuka kama, yanda Rahima ke kuka sosai tana kurma uban ihu tana kwalama Mummy kira yasa yadago kanshi ya kallesu, ko'ina na jikinta bari yake har lokacin dan kwalin kanta da riganta duk ajike ne sabida ruwan daya kwaramata tana kuka, babu abinda take tunawa sai maganganun Mummy karta sake tai abinda zaisa aganosu kokuma tai abinda zai tonamusu asiri idan Dady yaji ankamata ai saiya luma mata wuka aciki tamutu dama bayasonta yafison su Siddiqa. "dan Allah kasakeni natafi wurin Mummy na, ni wlh banmuku komiba, please please karku tafi dani kaji Abba na zai kasheni ne" zufa officer ya share da hannu daya tsabagen yanda take bashi wahala yasa yake zufa yace "ashe kinsan abinda kikeyi baida kyau, muje" janta yayi ya fitar da ita daga gidan zuwa inda sukai parking yay mota da ita, jefata yay cikin motan ganin irin mutanen dake cikin motan da aka kakkama sai warin shaye shaye suke yasa ta kifa kanta akan cinyarta tahau kuka sosai kaman za'a kasheta, Chris da batama lurada shi bane yanachan gaba tsaye yakutso kai yazo ya tsaya akanta yana kallonta tabashi tausayi dan yasan tadamu duk ta tsure, ahankali yace "Hey Beautiful a......." "don't call me beautiful I hate you Chris" tafada tana tashi tsaye daga kan kujeran cikeda masifa tana kuka sosai, tace "just thank God my hands aren't free da wlh saina waska maka mari mai gishiri, a dog like you" cikeda masifa dan shima he feels furious and frustrated as well yace "I love and respect you beautiful but I won't have you calling me names, I am not gonna tolerate that am 25 nasan nabaki nothing less than 5yrs so pay some Goddamn respect u lousy hausa spoilt brat" cikin kuka sosai da shegen muryan ta mai bala'in zaki da dadi tace "u are the lousy one hypocrite kawai and I said it you are a dog" azuciye yawani irin bugamata kanshi a goshi da karfi sabida yanda hannunshi suke a daure, baya luuu tayi tafadi a daidai baki bakin motar kaman wacce iska ya diva tai wani irin tumble kafanta ya malkwade tafado daga motar zuwa kasa daidai lokacin Sameer da all the eight NDLEA officers sun karaso wajen akan idanunsu ya bugamata kai a goshi, daidai kafan Sameer tafado tai wani irin kara goshinta na jini bayanta ya mugun bugu tafashe da kuka idanunta na juyawa, daya daga cikin officers ne ya shiga cikin motar, finciko Chris waje yayi ya zubamai Mari yace "how dare you hit a woman?" cikin fushi dajin haushin yanda officer ya marai agaban all his friends yace "Sir is personal issues besides she's my girlfriend you don't have to interfere" daya daga cikin officer ne yace "ahhh yaro kaidan iskane naga alama kanka na hayaki, kafasama yarinya goshi sanan kama fadamana we don't have to interfere" kulkin dake jikinshi ya zaro shima dayan haka suka shiga dukanshi yana ihu saida sukamai lilis yana ihu duk Sameer na kallonsu baice musu uppan ba sanan sukazo inda Rahima take agaban Sameer tana zaune tana kuka sosai, tana taba goshinta dake jini tana kallon jinin a hannunta tana kara kecewa da kuka kaman zata shida, daya daga cikin officers dinne yace "ke tashi ki shiga mota mukakai head quarter za'a dubaki?" makemusu kafada tayi tana kuka tace "ni yanzu zakuyi treating dina I can't feel my leg at all, am bleeding I don't want to die now pls" bushewa da dariya all the 8 officers sukayi daya daga cikinsu yace "you don't want to die shine kike shaye shaye kina shan su shisha da codeine that kills faster than anything you could think of, my friend stand up" yay maganan yana mikar da ita tsaye, wani irin ihu jin yanda kafarta yamata mugun ciwo tai tangal tangal zata fadi akasa ta daga kafarta daya sama tai baya hakan yasa Sameer dake bayanta yatare ta tafado in his arms, atsorace ta juyo dakai ta kallai tana kuka hawaye na bulbulowa ta gefen idanunta gabanta nafaduwa kaman zata mutu, dauke idanunshi yayi daga kallon datakemai kaman wacce keson karanta abu ahankali yadauketa kaman yadau paper da sauri tai wrapping hanuwanta around his neck, yana kallon gabanshi yake tafiya daidai harya karasa da ita wurin motar dasuke ciki, da ido daya yama wayanda aka kaman alamun su matsa, matsawa sukayi ya ijiyeta akan dan kujeran bencin wajen tana kuka ciki ciki hawaye na bulbulowa kaman famfo, kafarta na dama ya kama, hannu yasa yazare White takalmin dake kafarta dakeda dan tsini ya ijiye agefe yana kallon yanda ankle looks so reddish gawani leg chain data daura a kafar daya zubama ido for a while sai kyalli take abinku da farar fata, kafan harya kumbura kashin gefen ankle din yadawo tagaban kafan, wani irin fashewa da kuka tayi tana kallon kafar tace "innalillahi kululun kafana yadawo gaba shikenan zan mutu yau" ta fashe da kuka sosai, dariya officers din suka shigayi suna mata dariya, daga kafar yayi yarike kowa na cikin motar na kallonsu barinma Chris dayasan aikinshi ne, wrist din kafan yarike gam kafin yakama foot dinta yay wani irin twisting dayasa ta kwala mahaukacin ihu kaman ta sume tafado daga kan kujeran tana dukan hannun Sameer din tace "kabari dan Allah, wayyo Allah na Mummy na" sakin kafar yayi ahankali batare daya kalletaba yajuya ya kalli officers din yace "Dr should check the leg when u get to the headquarter, see you guys next time" yajuya yawuce ya shiga motarshi, shiga motocin su suma officers din sukayi, Officer biyu suka tsaya abaya tareda yan shaye shayen gudun karsuyi jumping su shiga titi in attempt to excape sukai headquarter dasu shikuma Sameer yay gida dan ya mugun gaji.



Parking yayi a compound dinsu yana kallon motar Nuru alamun yazo gida kenan baiyi mamaki ba dan yasan dukansu daga Nuru har Muhammad kullum da yamma insun taso daga aiki saisun biyo sun gaida Ummi dan da safe basa iya zuwa sabida zuwa aiki, bayan sunyi magrib saisuma Ummi Sallama su tafi gidajen su, motar Nuru dayagani yasa yagane Muhammad bai riga yataso daga wajen aikinshiba, flat dinshi yawuce dan he wants to shower kafin yaje wurin Ummi, wurin fridge dinshi yayi dake falon budewa yayi yadauko bottle water yabude yakafa abaki, bude kofanshi da akayi yasa yadan juyo while drinking the water ganin Nuru ne yasa yacigaba da shan ruwan, zare goran yayi daga baki hakan yasa Nuru daya karaso wajen yace "sannu da dawowa yayan mu ya aiki?" "Alhamdulillah fine, Muhammad bai dawoba?" gyadamai kai Nuru yayi yace "eh baidawo ba, wurinka nazo Ya Sameer amma naga you want to shower yanzu ka shigo bari na jiraka" dan murmushi yamai yace "alright give me just 5min okay" gyadamai kai Nuru yayi hakan yasa yawuce yay bedroom dinshi Nuru yabishi da kallo yana mugun son wanshi Sameer saidai bakajin cikinshi tun yana gani kaman kawai Ya Sameer baiso yay aurene har wakan Ummi shima yasoma zama a kunnenshi to the extend yanzu yasoma believing maybe wani matsala yakedashi saisa baya sha'awan auren according to Ummi.


Bude fridge din yayi yadauko vita milk yasa opener ya bude yamaida fridge din yarufe yadawo kan kujera yazauna yanasha yana kallon news.


Almost 10min Sameer yabata sanan yafito falon sanye da bathrobe fari ya zauna kusada Nuru yace "je kitchen ka hadamin coffee Noor" tashi Nuru yayi da sauri yace "to yayan mu" kitchen dinshi ya shiga that is so clean kana ganin kitchen din kasan ba'a cika amfani dashiba, cikin 5min yahada mai coffee yazubamai a mug yasa spoon da sugar yafito yakawo mai, karba yayi yace "thank you" ya ijiye dan yasan da zafi, kafin yadauka sipping kadan yayi ya ijiye yadan daga gira daya sama yace "not bad" fashewa da dariya Nuru yayi yace "kai Ya Sameer nai kokari fa sosai" shima dan murmushi yayi yace "yeah was just kidding, its actually taste good thumbs up" murmushi dukasu sukayi sanan yace "alright, let's talk, what is the matter?" dan shiru Nuru yayi kafin ahankali yace "Yaya Sameer yesterday I was busy inata nazarin abubuwa da dama" gyadamai kai Sameer yayi yana sake kai Coffee bakinshi giving him his fool attention, ganin haka yasa Nuru yace "uhmm Ya Sameer why don't you marry Asiya? Naga tana sonka"




Wani irin kallo Sameer yamai saida gabanshi yafadi da sauri yace "I mean bawai tana sonka ba but naga kuna shiri taku tazo daya please understand me kaji yayan mu, she is our cousin and tanada natsuwa, tana 300 level a school ga ilimin islamiyya what else?" "get out!" yadakama Nuru tsawan da saida yasa ya firgita, cikin fushi yace "u think sabida kai aure kanada gut din tunkarana kamin maganan aure harda fadamin wanda zan aura my sister Asiya, yaushe aka haifi Asiya? Is Asiya even ripe for marriage, you know me you know what I hate banson raini Noor, watch your tongue, now get out" tashi Nuru yayi ahankali dukyay wani iri he feel awful duk laifin Ummi ne saida ya gayamata yafi so tamai maganan da kanta bata aikoshi in disguise ba, ahankali yace "I'm sorry Yaya Sameer kayakuri" da yatsa Sameer yanunamai kofa babu alamun wasa kan idanunshi hakan yasa yajuya yafita da sauri, jingina yayi da kujera ya lumshe ido yana sauke ajiyan zuciya ranshi yabaci sosai. Karan da wayanshi yayi na shigowan sako yasa yadau wayar NDLEA ne yaga sunmai message.
" _Lieutenant Chairman asked us to call you, something come up u have to come to the headquarter please_ ".
[6/3, 9:42 AM] Marsy😘: 💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫



_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔



✍️ M Shakur





1️⃣7️⃣



Tashi yayi yawuce bedroom dinshi ranshi abace wasu kananun kaya ya dauko, Black jean yasaka sai wata Ash color riga short sleeve mai gajeren hannu yasaka, rigan nada V neck daya bayyanar da kwantaccen gashin kirjinshi, rigan ta kamashi sosai, kaman rigan zata barke ajikinshi sabida yanda ta bayyanar da kiranshi na full packs man, Black jacket yadauka yadaura kan rigan yasaka wani boot baki yadau car key dinshi, kana ganinshi kaga soja yafito daga flat dinshi yaso ya shiga wajen Ummi but no Inya dawo yaje, he don't want to waste anytime, motarshi ya shige yaja tareda danna horn mai gadi ya budemai gate yabar gidan.




Tashi Ummi tayi daga jikin window bayan taga taga fitanshi jikinta ya mugun yin sanyi takoma kan gado ta zauna ta buga uban tagumi cikeda damuwa ta daga hannayenta sama tace "wanan wani irin jarabawa ne Ya Allah meke damun Sameer ne dako kadan mace bata gabanshi?" tai dan shiru tasa hannu tai maza ta goge hawayen dake shirin zubomata, tasowa Nuru yayi yazo kusada ita yabata side hug cikeda damuwa yace "Ummi kidena damuwa okay, kidinga mai addu'a in sha Allahu har jikokin shi zaki gani nan bada jimawa ba kuwan" fuskar Nuru ta kalla tace "anya? Kaduba pa am sure sabida maganin dana gayamishi Baffa shi yakawomai ne yau da safe yasa yaki shigowa dan baisoma yasha, Noor ya zanyi da raina eh? Yayanku fa Noor duk ya girmeku nesa ba kusa ba, yabaka almost 8yrs but look at you now da Nabila batai having miscarriage ba da kanada yara biyu aduniya, I tot yanda na kawo maganan Asiya he will accept da gudu sabida cousin dinshi ce kuma naga suna shiri yarinyar na sonshi sosai, bazai wani sha wuyan neman aure ba dan da gudu Baffa zai bashi ita amma kalli abinda yama" ahankali Nuru yace "Ummi kibar maganan Asiyan nan, it won't work, ai dama tun kafin kiturani na gayamiki kice Yaya Sameer ya auri Asiya ai kaman kin kara koranshi daga zancen auren ne, Yaya Sameer dason girma tsiya inya auri Asiya ai kaman ya yankin ma kanshi ticket din raini ne, ni nasan dama bazai taba koda da wasa he will not accept maganan nan, kawai kiyitamai addu'a Ummi what goes around comes around, Yaya Sameer zaiyi aure one day one day" cikeda damuwa sosai Ummi tace "Ya Allah, Ya Allah kadubi lamarin nan nawa, Ya Allah ka karkata zuciyan Sameer zuwaga wata mace, Ya Allah kahadashi da wacce zaiso sosai, Allah ka aurarmin da yaron nan badanni ba badan halina ba" tasake share hawaye daya zubo mata rungumeta Nuru yayi yace "is okay Ummi ya isa hakanan" haka yacigaba da lallashinta har Muhammad shima yadawo duk suka taru suna bama maman nasu baki harsuka samu ta dawo normal tadan wartsake tabiye musu sunata hira.




Tunda aka shigo dasu headquarter anan reception aka zubesu duk wanda zai wuce saiya kallesu, gabaki dayansu akasa suka zauna bama abasu kujera ba, Rahima tai kuka har idanunta sun kumbura kaman zaka taba jini yafito, daukan sunayen su akayi gabaki dayan su saiga wata mata ta taho da kayan first aid box a hannunta tareda daya daga cikin officers din dasuka kawo su suka taho gaban Rahima. Rahima yanuna mata yace "ga wacce batason ta mutun nan amma take shaye shaye, duba kafan Dr, tai targade Lieutenant ya gyara mata dazu" murmushi Dr tayi ta tsugunna a gabanta tana tattaba kafan ahankali kafin ta bude first aid kit din tadauko wani man zafi ta shafa mata sama sama tace "ya gyaru kamai muscles pain take having, wanan balm din kuma will kill it nan bada jimawa ba" sakin kafan tayi auduga ta dauka ta daura kan goshin nata tana share mata jinin wajen tace "what is your name yanmata?" shiru Rahima tayi batare databata amsaba tai banza da ita hakan yasa Dr din ta kalli fuskarta tacigaba da aikinta tace "young girls kaman ke always think shaye shaye is a gateway to having fun, inspiration, zero worries da sauran, aganinku shaye shaye wayewa ne irin kema kin isan na, but my dear is a lie bahaka abin yakeba, yes nasan shaye shaye nasa ka manta da matsalolinka, ka manta da bakin ciki da duk wata damuwa data addabi zuciyarka, kaji kaman kai kadai Allah ya hallita a duniyan nan, kaji yes a yanzu u can stand up to anybody kodakam babanka ne, inkayi you can stand up against anyone and anything in fact u can even stand against the world, shaye shaye nabaka wanan karfin da boldness din da jarumtar aganin ku but my dear is not true, duk ba hakabane, shaye shaye is mess with the heart and mess with your brain the IQ dinki, baya komi illa destroying dan Adam, tundaga na lafiyan shi harda sauran su and kill u wulakantaccen killing ma, but you know you still have time, u are young, you are too beautiful karki bata rayuwanki akan wanan shaye shayen da kikejin dadinshi nayan mintoci, see duk abinda dadinshi ba dawwamamme bane den babu amfani yi, dadin da last for few hours ko for a day dadi ne? Ki natsu kituba Allah zai yafemiki kisan me kikeyi kokya samu rabauta" tana maganan tana shafa gyaramata injury din goshin nata sanan ta shiga hada kayanta, ahankali Rahima tasa hannu ta share hawayen dasuka cika idanunta suka sake zubowa sharr, ganin Dr looks friendly yasa murya chan kasa tace "I want to use the restroom" dagokai Dr tayi ta kalleta jin tamata magana for the first time, murmushi ta sakin mata tace "stand up muje na kaiki" ahankali ta tashi tana dafa bangon wurin tanadan dingishi suka wuce itada Dr din, officer yace "kuma two minutes nabaki" da Dr suka tafi daidai sunkai wajen bayin wani yafito daga wani office ya kwalama kira yace "Dr you are needed here" da sauri ta kalli Rahima tace "shiga this is the rest room, zakiga ladies side inkin shiga" tai magana tana tafiya, bude kofan Rahima tayi ta shiga rest room din, dan passage ne awajen dakeda two pathways dama da haggu da akwai kofofi, ko kadan bata lura da sign din ladies da gentlemen ba take nuna Wannene bayin maza dana mata ba tabude kofar dama ahankali tanadan dingishi ta shiga, maida kofar tayi tarufe tai ciki, saida tai dan tafiya sanan ta iso main falon bayin wasu jerin bayi guda shida ne sai wash hand basin da manya manyan mirror a bangon, da sauri takarasa tabude bayin farko ta shiga ta mayar ta rufe, bayin so clean babu datti kodaya kodan bayin maza ne saisa oho, but bayin mata dai always yacika datti, mayar da kofan tayi tarufe tasa sakata sanan ta daga riganta sama tasa hannu a aljihun bayan wandon ta taciro wayarta da tuntuni take wurin Allah yaso ta babu wanda ya kirata da asiri ta yatonu sun kwace dan duk an karbe wayan sauran, maida wayan silent tayi da sauri sanan taciro number Mummy tana goge kwallan datake yi tai dialing number har wayan ya katse ba'a daukaba, haka tasake kira shima ba'a daukaba fashewa tayi da kuka tayi mara kara tana taushe bakinta, ba karamin tashi hankalinta yayiba takira mummy sau 17 times bata dauka ba bakaramin tashi hankalinta yayi ba yanzu kwana zatayi a wurin nan, gashi an fara kiraye kirayen sallan magrib, share hawaye tasakeyi, ahankali tasa hannu ta sauke cover bayin, zama tai kan sitter ta rufe fuskarta da duka hannayenta tana kuka tajima ahaka sanan tai shiru ta share idanunta tana kallon wayan sanan ta shiga saka wasu nambobi tadanyi jimm tana kallon number kaman mai tunanin wani abu kafin ahankali tai dialing number tasa hannu ta share hawayen daya zubomata takara wayan a kunenta, har wayan tagama ringing ba'a
Showing 27001 words to 30000 words out of 212889 words