ruwan hannunshi da alamu bayi ya shiga yana ganinsu da hannu yamusu alamu su zaunar da ita kan kujeran, daukanta chass Binta da Asabe sukayi suka zaunar da ita kan kujeran machine din, nurse din tazo da sauri ta kulle hannunta da belt din jikin kujeran, Asabe ta kulle kafafuwanta da belt dinsu datake ta shurewa tana ihu, ko motsi bata iyayi da hannu da kafafunta hakan yasa tafashe da kuka kaman zata mutu. "wayyo Allah na Mummy, Mummy, Mummy zasu kasheni, Abba, ya Siddiqa, na shiga uku na lalace, innalillahi wa innailaihi raji'un" dawowa tagabanta Dr yayi yace "calm down number 16, bakiso kar amiki?" da sauri ta gyadamai kai tana kuka sosai yace "to okay naji amma dena kuka in kinaso na kwance ki" shiru tayi kaman ruwa ya cinye ta yace "gud, bude bakinki to kawai na duba saiki tafi" yay maganan yana komawa tabayanta, ahankali tabude mai bakinta tana sauke ajiyan zuciya, torch yadauka yana haska bakin yace "gud girl yanzun nan zaki tafi, rufe idanunki akwai abinda saikin rufe ido zan iya gani abakin ki kina rufewa zan gani kitafi".
How to subscribe
Pay 300 to my account number 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din BIN ABINDA ZUCIYA KESO






Gyadamai kai tayi ta runtse idanunta gam, wani abu yasa yadaura akan bakinta bakinta ya kame sanan abun ya danne harshen ta ta yanda takasa motsi da harshen in anyway, da sauri ta bude idanun tana kokarin tai magana takasa, jikinta ko ina na rawa takasa motsi, ahankali Dr yace "I know, I know, just calm down bazamu wuce 30min ba zamu gama kitafi kije kici abinci okay just relax" yay maganan yana daukan wani farin pipe din roba yajonashi da machine din dake tsotso da washing toxin daga jikin mutum sanan yashiga yakawo bakin pipe din bakinta ya shiga turawa cikin bakinta yana kallon computer dake nuna mai inda pipe din yakai a cikin jikinta, yanda Rahima take zaro ido jikinta nabari zaka zaci zare mata rai akeyi sai wani irin nishi take babu halin motsi, saida yagama zura pipe din yakai har cikinta sanan ya danna wani button a jikin kujeran kujeran yadawo gado yazamto tana kwance, murmushi Dr dake tsaye kanta yayi yace "alright yanzu zamu fara are you ready number 16?" wani irin kyafkyafta idanu Rahima tayi da hawaye suka shiga fitowa, wani button Dr ya danna a jikin machine din pipe din bakinta yafara kara kaman irin ana zuko Bobo dake gab da karewa a goranshi, wani irin lankwashewa Rahima keyi hawaye na zuba daga idanunta, ita kadai tasan irin azaban datakeji, jitake yi kaman ana wanke cikin cikinta da sabulu ana dauraya, combination of uncomfortable and painful haka takeji kaman ana kasheta, almost 1hr Dr yadauka yana detoxing nata kafin ya kashe machine din yazaro roban ahankali ya ijiye, sanan yacire abinda yakama bakinta dashi kasama magana tayi sai ajiyan zuciya takeyi tana kuka, hannunshi yasa ya bude daure mata hannu da kafa da akayi sanan yasa hannu yadagota zaune tareda kwalamata Nurse kira da sauri ta shigo yace "take her to dinning tai having breakfast dinta and make sure she takes lot of water" gyadamai kai Nurse tayi takama hannunta tace "sauko mutafi" saukowa tayi tai luuu zata fadi da sauri Nurse ta tareta jitake kaman ba jikinta ba, tadaiga nurse din tarike ta gam an fitar da ita daga dakin wata nurse ta shiga da wata dakin, dinning Nurse din ta kaita ta zaunar da ita kan kujera, jiri ma take gani hakan yasa ta kifa kanta kan table din tana kallon mutanen dasuka cika wajen duk sun saka Uniform kaman ita sunacin abinci wasu na soshe soshe kaman mahaukata, daga ta Nurse din tayi ta ijiye mata wani abinci da in her life batasan sunan abincin ba, sai wasu kwayoyin magunguna a dan karamin rober tace "oya tashi kici kisha inba hakaba jiri zaita damunki, yi maza ci" ganin tayi kaman batajita ba yasa ta kwalama su Binta da Asabe kira da sauri sukazo wajen wani mugun kallo Asabe tamata tace "ci abinci" ahankali tadau spoon tafara cin abincin dataji amai ne kawai yake tasomata tanaci amma haka suka tasata agaba ta cinye da karfi da yaji sanan suka bata magani taci zata kwanta suka hanata danko kadan batajin dadin jikinta saida tai kusan minti goma zaune har lokacin idanunta juyawa sukeyi sanan Nurse ta dagata tace "muje kiyi bacci" kaita daki sukayi tahau kan gado da kyar sanan nurse ta rufa mata bargonta lumshe ido tayi tai shiru babu wani abu na jikinta datake jinshi daidai wani irin tausayi kawai taji tabama kanta hakan yasa ta fashe dawani mugun kuka tana shesheka ita kadai cikin bargo, Nurse ba tace mata komiba suka wuce suka fita, haka ta dinga kuka tarasa waya kawota wurin nan, bama tasan inane ba, tarasa ya akayi ina Mummy tasan cewa Mummy batasan tazo nanba, gashi sun kwakule mata ciki jinta take wani iri gabaki daya, she is so lonely, ga all matan datake gani da Uniform irin nata duk sai ahankali, soshe soshe taga sunayi, haka tai kuka tai kuka tai kuka idanunta sukai luhu luhu sanan bacci yay awon gaba da ita. Duk wacce takaranta batare data biyaba, Allah ya isa.


38.



Bayan sati daya!

Sannu Sannu Abba kesamun sauki, dudda abin kanzaman mai da wuni lpy da daddare zazzabi yarufe shi, koya kwana lpy da rana jikin ya rikice haka yake lallabawa, tuni yakarbi sick leave awajen aiki, dan yanzu mataimakin shi shiyahau kan kujeran chief judge din high court, yaranshi kullum suna tareda shi adaki, ko Mummy tasan yaran sunason mahaifinsu to the extreme saisa suke bata tausayi yanda duk sukai zuru zurun sabida rashin lpy shi, another thing data kara lura dashi shine duka yaran basu damu da itaba ayanda suka shaku suka kuma damu da baban su basu shaku da ita hakaba, karfa abun yazamto tana kokarin bata yar wata agarin haka tarasa soyayyan nata lura da hakan yasa duk in suna zaune su kadai ko tare da baban su zata shiga cikinsu taita jansu jiki tana musu hira nai dadi, tsawon one week dinan Sadiq din Siddiqa yazo yagaida Abba yafi sau uku, while Sameer bai samu yazoba dan washe garin ranan dayakai Rahima Rehabilitation Centre yana zuwa office aka turashi wani assignment maiduguri dazai daukeshi 1 week.



Yau lahadi, tun safe as usual akai mata detox dinta taci kuka takoshi idanun nan sunyi suntum suntum akasa taci breakfast dinta dan dole, saida taci dan dolenta kullum wasu irin abinci ake bata da bata sansu ba kuma kullum sai sun tasata agaba tai wanka ga shan magani safe, rana dare, saida tai almost 30min a dinning sanan aka maida ta daki akace taje tai bacci, bacci tayi sai wuraren 1 ta tashi, tana kalle kalle.



Shigowa Sameer yayi rehab Centre da motarshi, parking motar yayi a parking space yana kallon premises din da kaman bakowa komi kal kal kafin yabude motar yafito yana sanye dawata blue shadda dayasha aikin hannu yana baza uban kamshi kanshi ba hula danshi gaskiya ba ma'abocin son hula bane, wayarshi yadauka yamaida kofar motar yarufe sanan yawuce reception yana takun nan daidai, yana shiga kafin ma yakarasa receptionist din ta gaida shi. "welcome Sir. What can we do for you sir?" ahankali yace "I came for a visit, want to see a patient" da sauri tace "your name sir" ahankali yace "Lieutenant Sameer Simran Sameer" da sauri ta shiga database dinsu nan tagani sanan ta kalli security that is at the door tace "Bala take him to visit room" sanan ta kallai tace "you will see her in a bit sir" gyadamata kai yayi yawuce Bala yakaishi har wani daki dakenan hadadde harda TV ga kujeru biyu ga table a tsakiyan su, ga water dispenser wayarshi yaciro yana dubawa.


Landlines din ward receptionist din takira wata nurse tadauka tace "Nurse patient number 16 have a visitor, take her to visit room" gyadamata kai Nurse din tayi tace "OK" tajuya tana kallon Rahima data tashi daga bacci tun dazu ta tashi zaune ta kifa kanta jikin window tana kallon waje yanda bishiyoyi da flawan backyard din keta kadawa sabida iskan da akeyi kaman za'ai ruwan sama, karasawa wajen gadon tayi ta tsaya akanta tace "number 16" ko kallonta Rahima batayiba dama tasan bazata kalleta ba dan gabaki dayansu yanzu tadena musu magana cikin patients dinsu kuwa har yau magana baitaba hadata da wataba dudda tana ganin wata datake yawan kallonta intaje wanka ko dinning amma ko kallon kirki basu isheta ba, ahankali tace "kizo ana kiranki come with me" ko kallonta Rahima batayi ba bakumata da alamun tashi hakan yasa nurse din ta kwalama Asabe kira. "Asabe, Binta" tanajin haka ta sauko daga gadon tana balla mata harara da kumburarrun idanunta, ta mugun rame sai fari data kara kaman mara jini kitson ta ya tsufa sosai dan gashin gaban kanta yasoma zarewa yana warware kanshi yana kwanciya dan tanada coily hair daman sosai kaman gashin jaririya, hulan kanta ta gyara batare data kalletaba hakan yasa Nurse din takama hannunta, ahankali take tafiya dan batada karfi ko kadan cikinta daman tunda aka fara mata detox dinan ya hargitse kaman ba nataba, agaban wani daki taga sun tsaya da aka rubuta visit a sama sanan nurse din tasa hannunta tabude kofan, karan bude kofa da Sameer yaji yasa yadago kanshi yana rike da waya ahannu, tundaga kan crock shoe kafarta yake kallo har zuwa wandon da rigan dayamata yakuma dan mata yawa wani irin kyau tarame bana wasaba kafin ahankali yasauke idanunshi kan fuskarta dayay ja tsabagen kuka kaman jini zaifito, idanunta sun kumbura sunyi suntum suntum sunyi jaajir gashin idanun duksun tattare looking so moist, idanunta sun kode, shigo da ita ciki Nurse din tayi ta kawota har wurin kujeran sanan ta kalli Sameer cikeda girmamawa tace "welcome Sir," gyadamata kai Sameer yayi tajuya tafita tarufo musu kofa, tsayawa tayi awajen atsaye batare data dagokai ta kallai ba sai kallon takalman kafafun ta takeyi takasa hada ido dashi, kallonta yayi from head to toe sanan ya mayarda kanshi kan wayanshi yacigaba da danne dannen wayanshi, takai almost 20min atsaye bata zauna ba, batace uppan ba, ga kanta akasa kafin taja wani uban ajiyan zuciya tafashe da kuka sosai tasa hannunta akan idanunta tanayi kaman zata shide, dago kanshi yayi ya kalleta yanda take kukan kaman wacce aka zane sanan yadan tabe baki yatashi tareda daukan wayanshi da carkey daya ijiye kan table yajefasu cikin aljihu gaban riganshi yayi hanyar kofa yabude kofan yafita batare daya sake koda kallonta ba, da sauri tajuya tabishi tabude kofan tafito yana cikin tafiya adan corridor taji takama hannunshi gam hakan yasa ya tsaya chak tareda juyowa yazuba mata idanunshi dababu alamun wasa cikinsu, fashewa tayi da kuka sosai gabaki dayan wurin ya dau karan kukan ta tace "ka maidani gidanmu, ka kaini wurin Mummy na" yanda take kukan yasa Nurse data shiga wani office awurin tafito tazo wajen da saurita, jin sahun tafiya yasa Rahima tajuyo tana ganin Nurse takara damke hannunshi gam gam tana kallon fuskan shi tace "dan Allah ka kaini wurin Mummy na kaji, please ka kaini dan Allah karka bari su tafi dani please, wlh banson wurin nan dan Allah kaji" ganin Nurse ta iso wajen yasa takoma dayan gefenshi talabe tana kuka sosai tana ihu kallon nurse din yayi yace "don't you have any female security here?" da sauri tace "we have sir" "call them suzo su tafi da ita ciki" yafada sounding a lil bit bitter, wani irin dan banzan ihu tasaki. "noooo, dan Allah in kanama Allah ka kaini gidanmu, wlh bansan wajen nan" wani mugun kallo yamata da idanunshi yanuna mata hannunshi, ahankali tasake shi cike da tsoron shi tana kuka sosai tana tsaye gab dashi jikinta narawa ko minti biyu ba'a yiba saiga Binta da Asabe tana ganin tasake damke hannunshi tana neman shigewa jikinshi da hannu daya Asabe ta dagata sama sukai ciki da ita tana kwala ihu tana juyowa tana mikama Sameer hannu, mugun kallo ya watsa mata yajuya yafice daga wurin, saida yaga Dr sanan yabar Centre.



Aranan da daddare yaje yagaida Abba dayasoma jin sauki sosai, Mummy kaman zata hadiyeshi da kallo amman tunda ya kalleta sau daya ya gaidata bai sake bata second look ba haryay briefing Abban kan Rahima tasoma samun lafiya and she is responding to treatment, Abba yaji dadi ranan, yaji dadi wani sabon karfi yaji ya shigeshi har saida yafita sallan isha'i tareda da Sameer shida rabon shi daya fita masallaci harya manta amma news din Rahima yabashi karfi.






Wasa wasa Kwanaki nata tafiya, yau satin Rahima uku a Rehabilitation Centre, tun ranan da Sameer yazo yadubata babu wanda yakara zuwa yaduba ta daga gida, babu ranan duniyan dabazatai kuka ba, and Alhamdulillah ana bata kulawa sosai ita kanta tanajin chaji ajikinta amma tsabagen yanda ta tsani wurin da abubuwan da ake mata aciki yasa taji babu abinda takeso kaman ta ganta a gidansu.



Yauma kaman kullum da sassafe aka tadasu suje wanka, tana cikin bayi tana wanka taga anbude labule an shigo, baki tabude zatai ihu tana jan towel dinta danta rufe jikinta matar datashigo tasa hannu ta rufe mata baki tareda rage murya tace "listen to me, kina ihu Asabe zasuzo nan, so kiyi shiru ba jikinki na shigo nagani ba ko wani abu magana nazo namiki" da sauri ta gyadamata kai tana kokarin daure towel dinta, janye hannun matan tayi daga kan bakinta tabi boobs dinta da kallo takai hannunta zata taba da sauri Rahima ta koma gefe hartana neman fadi matan ta riketa tana washe mata baki, tana sosa kai, idanunta bakin kirin hakama lebenta, tureta Rahima tayi tana turo baki tace "niki saken" sakinta matan tayi tana soshe soshe tace "dalla sabida ina sonki ne dan kinada kyau saisa ma nace bari nazo nataimake ki nidama last 2weeks duka duka shegen mijina bayan ya dannamin saki yakawo ni nan, tunda nazo kullum nake ganinki kina kuka bakima kowa magana, kullum ke kadai" tai shiru tareda daga hammatan ta tana sosawa kaman mahaukaciya, yatsine fuska Rahima tayi cikeda kyaman ta takoma baya dan ganinta take kaman mahaukaciya, dariya tayi ta sauke hannunta tace "kinga nan wurin kashemu sukeyi, inba hakaba antaba raba nawa da abinda kesashi jin dadi, shaye shaye fa, inhar zasuce zasu rabamu da shaye shaye to su rabamu da shan ruwa ko cin abinci man, ruwa baya kore damuwa ko bakin ciki amma shaye shaye kina sha wayyooo matsala da bakin ciki bye bye, bana wanan soshe soshen da amman sabida ban samu Cociene dina na shaka ba na 2weeks anan wurin shine nafara haka kaman mahaukaciya, kullum suyita kada kuka da maburgi acikina dan bantan uba" tai shiru tana kwakulo hancita tana lumshe ido tsabagen yanda abin kdmata dadi, tace "yau zamu gudu mubar gidan nan da daddare, akwai wani supplier na saurayina kuma da zaizo ya kwashemu da daddare amota anan baya, haurawa zamuyi kin gane, electric fence ne but zamu baza bargunan mu akai, in kinaso zanje dake kema ki gudu amma zaki biyani dubu goma inkin yarda" da sauri Rahima tazo kusada ita tace "eh zan biyaki Allah, Mummy na zamu kira muna fita zata turomiki kudin, da gaske dan Allah zaki fitar dani ko karya kikemin?" murmushi matar tamata tasa hannuwanta duka biyun tana sosa kai tace "eh kibarmin komi a hannuna nasan wurin nan lungu da sako, nine number 00, amma sunana Shagali" da sauri Rahima tace "Shagali?" gyadamata kai matar tayi tana sosa kunne tace "eh Shagali sunana, yanzu wuce kifita, karfe takwas nadare nurses ke fita shift dazaran ta dakin ku tafita kifito kawai zaki ganni kibar komi a hannuna" da sauri Rahima ta gyadamata kai tana murmushi tace "nagode" wuyan ta ta shafa tace "kinada kyau ga kira saisa zan taimaka miki, u look so innocent, wuce kifita kar Binta ko Asabe sukamamu" ko damuwa ma batayi da batagama wankan da kyau ba tafito tana murmushi ta ijiye sabulu da soap a box dinta tawuce ward dinsu.


Inkika karanta batare dakin biyaba Allah ya isa, zaki biyani ranan da bakida shi.
How to subscribe
Pay 300 to 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to my watsapp number 07012181461 sainai adding naki a group din BIN ABINDA ZUCIYA KESO.
Ranan har Nurses saida suka dinga mamakin ta ganin ranan ne rana ta farko da batai kukaba, batai gardaman shan magungunan taba har akai magrib, dama ba ruwanta da Salla dan tunda aka kawota ko hanyar masallaci bata taba biba sai agogon bango ward din take kallo, agogon nabugawa karfe 8 dot taga nurse din dakin ta tashi daga kan kujera, ta dau wayarta da wani littafi tawuce tafita da sauri ta diro daga gadon sauran yan dakin suka bitada kallo hararan su tayi tace "sa'idawa mutum bazaije yay fitsari lafiya bakuma yanzu adai rage" tabude kofa tafita tana fita tahango Shagali awurin kofar wajen da hannu tamata alama tazo da gudu tai wajen hannunta Shagali takama sukai wata hanya da batasan da ita ba tunda aka kawota Rahab centre, hanyar lungu ne haka suketa gudu itada Shagali har suka bullo backyard wajen masallaci wasu mata guda uku tagani awurin suna fitowa tace kowaya tsugunna Rahima tahau kansu ta dane kan fence, tsugunawa sukayi Shagali tasaki hannun Rahima data rike tace "hau bayansu ki dirka kijiramu" hawa bayansu tayi amma dudda haka batakai tsawon ginin ba dan bata da wani tsawo hakan yasa Shagali tahau ta cincidata sama ta taka bargon dasuka shimfida kan electric fence din ta mike tsaye gabanta na faduwa hango uban tsawon ginin dasuke cewa ta dirka ga wajen daji duk ciyayi, da sauri murya kasa kasa gudun kar ajisu Shagali tace "wai bazaki dirka ba sai an kamamu wai babygirl?" fashewa Rahima tayi da kuka tana neman tsugunnawa dan tanada fear of height tace "am scared bazan iyaba" wani irin tunkudata shagali tayi aiko ta kwala uban ihu tafadi tipp akasa tasaki kuka sosai, hawa fence din
Showing 63001 words to 66000 words out of 212889 words