Shagali tayi ta dirko sauran ukun ma suka diddirko kasa kana ganinsu kaga kwararrun yan duniya, sanan Shagali ta tashi ta daga Rahima dake kuka sosai ta kakkabe mata jiki tace "sannu kinji oya mu gudu mota na chan gaba" gudu sukahau yi Shagali na rikeda hannun Rahima dake shirin suma tana kuka kaman yarinya karama, sundan yi nisa Rahima ta zube akasa dan karfin ta yakare hakan yasa sauran suka tsaya suna tsaki sukace ce "wai mesa kika dauko wanan yar yarinyar shagali? Sai bata mata lokaci take" cikin jin haushi shagali tace "sonta nake baruwan ku, kuma dai naga taimaka muku nayi tomena cewa me yasa na daukota" ganin kaman suma tayi yasa Shagali ta dagata tagoyata abaya sukahau gudu kusan na na 45min sanan suka kai titi aiko saiga wata yar akwalan mota datai parking ita kadai akan hanyan da motoci basawani guduwa, da sauri wani mutumin yafito daga motar yabude musu baya suka shiga daya cikinsu ta shiga gaba, Shagali ta zauna kusada Rahima tace "bani ruwa in kanada shi" ruwa yamiki mata yace "Shagali ta Shagulgula dama ashe zan kara ganinki yau akwai holewa kenan" dariya shagali tayi tace "jamuje Bala" kunna motar mutumin yayi yaja itakuma ta debo ruwan ta watsama Rahima kan fuska hakan yasa tabude idanunta ganinta amota yasa tace "mun gudun?" fuskarta shagali ta shafa tace "eh mungudo yanzu zamuje musha dadi abinmu da sassafe saimu kaiki har gidanku ki kwaso mana kudade ko" turo baki Rahima tayi tace "yanzu zaku kaini" ahankali Shagali tace "a'a sai safiya zamuje yanzu sun riga sun kira yan gidanku kina zuwa za'a maidake gwara kibari gobe kinji" ahankali ta gyadamata kai tai shuru ko kadan she is not comfortable dasu haka taga sunkai wani uncompleted building a cikin wani anguwa da duk gine gine ne da ba'a gamaba, ya kashe motan suka fiffito Shagali tafito da ita tana tafiya ahankali suka shiga gidan rawa suka hauyi suna ihu mutumin ya shiga shigo musu da gorunan coke yana basu daidai biyu Shagali ta karba tazo inda Rahima ke zaune ta mika mata tareda kashe mata ido daya tace "ga coke, amma coke dinan yaji hadi nake gaya miki, so kisha kadan dan harkan manya ne you are too small for this, yanzu ma nabaki ne dan nasan kinyi kewan abin" karba tayi tarike tana kallonsu suna rawa sosai kaman ansaka musu waka suna rawa suna shan coke din harda mutumin daketa shafe shafe da Shagali, dauke kai tayi ta makure a bango ta kunshe ido har saida taji shiru sanan tabude idanun ahankali, ganinsu tayi duk sun baje akasa suna bacci suna munshari, kasa koda runtse ido tayi sabida sauro awurin ga kukan dasuke yi na bala'i, haka tazauna idanunta biyu ita kadai har asuba, sai wuraren asuba sanan tabude coke din dataji already marfin abude ne takafa abaki dan kishi takeji, wani shegen daci da dadi taji hakan yasa ta yatsine fuska tacireshi daga bakinta, sai bayan ta hadiye sanan taji wani dadi a bakinta kaman tasha bitter chocolate hakan yasa tadauka takafa abaki tanasha tana wani irin sauke ajiyan zuciya saida ta tada goran sanan ta yar tana yatsine fuska sai chan kuma tafara jin dadi, murmushi tayi kafin taji wani mahaukacin bacci na dibanta daganan kuma ba tasake sanin inda kanta yakeba.
39.
Wuraren 8 na safiya namijin yafara tashi ya bubbuga Shagali dake kusada shi yace "Shagali kutashi mutafi kafin masu gini suzo su ganmu anan" da sauri ta mike ta bubbuga sauran kawayen nata dake kwance gefenta kafin tai wurin Rahima dake bacci ta akasa ta bubbugata da hannu tana kiran sunanta. "Baby, Babygirl" bude idanu Rahima tayi kadan takara maidawa tarufe su tace "niki barni bacci" da sauri Shagali tace "baidai yar yarinyar nan ta shanye duka wanan mix dinba? Na shiga uku na lalace" kwashewa da dariya sauran matan sukayi daya daga cikinsu tace "da ke zata jira saikin cemata ta shanye sanan zata shanye, angayamiki sabon shigace, tunda kikaga yar yarinyar nan a gidan nan aito kinsan ta kware kan harkan, nidai tattara ta mutafi mota mubata ruwa kota iya bude ido tanuna mana gidansu mukaita tabamu kudi" dagata Shagali tayi suka jata har mota suka sata cikin mota duk suka shiga Shagali tadau ruwa ta zubamata a fuska sanan takafa mata goran ruwan a baki tana watsa mata a fuska, dan kurba tayi, bude ido tayi kadan, Shagali ta jijjigata da sauri ganin tabude ido tace "ke inane gidanku zamu maidake gida mu karbi kudi mu wucene" cikin maye tace "uhmmmm gidanmu, wurin Mummy na?" da sauri Shagali tace "eh inane gidan?" washe baki tayi tace "gidan Alhaji Sambo, number 1 Sambo Street GRA nanne gidan muuuuuu" tai wani uban ihu, da sauri direban yadauki hanyan itakuma tacigaba da bacci tana surutai har saida sukakai layin data fadi, baki Shagali tabude tace "ashe yar gidan masu kudi ce" a daidai address din data fadamasu yay parking, ruwa Shagali takara kwara mata a fuska tace "bude ido ke mun kawoki gida, ga gidanku nan" ahankali tabude idanunta dudda dishi dishi take gani bai hanata gane Gate din gidansu ba da sauri takara bude ido ta tashi tana tangadi tace "Mummy na, laaaa gidanmu" ta shiga neman abin bude kofar mota, budemata Shagali tayi tace "kiyi sauri ki kawomana kudin muna jiranki anan" gyadamata kai tayi tafita tana washe baki hartana fadi kasa ta tashi tsaye tana kakkabe jikinta tana kallon Gate dinsu, wani irin tura Gate din tayi Gate din yay kara kaman za'a balla hakan yasa gateman yafito da sauri yace "waye anan?" ganin Rahima ne yasa yay gum dan yasan zata iyamai rashin mutunci, ahankali Rahima ke tafiya tana tangadi tana kallon ko ina kafin cikeda murna ta kwala wani uban ihu. "Mummmyyyyyyyyy naaaaaa!"
Gabaki dayansu suna zaune a dakin Abba suna hira dan yau Abba yaji sauki sosai, jin murya kaman na Rahima ta kwala ma Mummy kira yasa duk sukai shiru Abba yace "sainaji kaman an kirak....." "Mummmyyyyyyyyy naaaaaa" Rahima tasake kwalama Mummy kira tana juyawa da sauri Mummy da Abba suka tashi Mummy tace "kaman muryan Auta na, meya faru ba 6 month kacemin zatayi a rehab ba ko an sallamota ne?" tai maganan tana bude kofa Abba biye da ita da sauran yaran duk sun kosa suga Rahima ce da gaske, sake kwalama Mummy kira Rahima tayi tace "Mummmyyyyyyyyy" da sauri Mummy tabude kofan falo tafito tai turus ta tsaya ganin Rahima sanye da uniform din rehab dayay datti sosai barin ma kasan wandon dakejan kasa dukta tattake shi, babu hijabi ajikinta sai hula, Abba yabi ta gefen ta yafito tareda saukowa daga dakalin barandar yana kallon Rahima kaman amafarki, ganin Abba yasa Rahima tafashe da dariya cikeda maye tace "laaaaaaaa Abba kadawo kaman tsoho wlh" tai maganan tana karasawa gabanshi inda ya tsaya churr kirjinshi na bugawa hudu hudu, hannu tasa akan gemunshi da fura fura ya cika tace "tsoho ne kai, kudi, bani kudi Abba" tai maganan tana tura hannunta a aljihun gaban jallabiyarshi tana lumshe ido kaman wacce bacci ke shirin tafiya da ita, warin da Abba yaji kaman na giya kona menene daga bakinta da numfashinta yasa yadan kawad dakai saikuma yadago kai ya kalleta cikin wani irin yanayi kaman wanda zai fashe da kuka, cikin raunanniyar murya mai nuna tsantsan ciwo yace "Rahima ya akayi kika dawo gida?" kyalkyacewa da dariya tayi cikeda maye tace "uhmmmm gudowa mukayi dasu Shagali, nahau kan gini nai tsalle nafadi tippppp akasa hahahahahha" ta kwashe da dariya kafin ta kama hannun Abban tace "Abba fitsari nakeji wlh tiles din bayin nan yay kal kal yau ka wanke ne?" tai maganan tana sakin hannunshi tsugunnawa tayi agaban Abba batare data cire wando ba tasaki fitsari awurin tana wakan fitsari "siiiiiiiiiiiii, fitsari futu futu, Mama da Baba suna kallona yayyyy yafitooo, agayara agayara fitsari zai shiga gidan takalmin Abba" tai maganan tana bin fitsarin datasaki da kallo dake gangarawa zai shiga takalmin dake kafan Abban ta tana washe baki cikeda mugun murna, wani irin juyawa Abba yayi cikin tsan tsan fushin daya dade baiyi irinshi ba yay ciki da sauri Mummy tabishi abaya ganin a yanayin daya juya yashiga daki tace "Alhaji kaga mezakayi eh? Kaga bakada lpy bakadade da farfadowa ba, so calm down and relax nasan duk inda Sameer yake rehabilitation centre sun riga sun kirashi, kabari ya iso ya mayar da ita please mijina karkamata wani abu, dan Allah kaji Abban su" ko kallon Mummy baiyiba tsabagen bacin rai yafada dakin Rahima yay wurin wardrobe dinta yabude kaman zai karya kofofin, babban akwatinta nasama yaciro ya yar akasa tareda budewa Mummy tabude baki tana kallonshi tace "Alhaji me haka? Koranta zakayi daga gidanne? Ina zata? Watake dashi aduniyan nan banda mu?" wajen kayan sawanta Abba yabude yadinga jido uban kayan da baisan iya yawan su ba da kalansu ba ya watsa akan akwatin haka yadin ga kwasan kayanta duk wanda hannunshi yasauka kai saiya jawo ya wurga a akwatin har akwatin ya cika yamaida akwatin yarufe yaja trolley yafito ya shiga dakinshi, drawer shi yabude yaciro wrappers din yan dubu dubu guda biyar yadauko car key duk mummy nabiye dashi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Alhaji, Abban su Abban su please talk to me my hysband dan Allah kaji, koran Rahima zakayi ne?" fitowa falon yayi yanajan akwatin batare dayabi takan Mummy ba Mummy biye dashi sukayi hanyar fita daga falon inda su Siddiqa dake gaban daki suka tsaya suna kallon Rahima, Mummy ta kwalama Siddiqa arude tace "Siddiqa kuzo kuga abinda babbanku yayi, baban ku yahado kayan Rahima a akwatin koranta zaiyi? Ina yakeso taje? Hannunka baya rube ka yanke kayar, addu'a zamu mata, addu'a makamim mumina, ka dauka Rahima itace jarabtar wanan Family namu, and I assure you babu abinda ya gagari Allah, dan Allah mijina karka korata instead ka maidata gidan Rehabilitation din" wurin kofa Abba yayi batare da maganganun Mummy sun shiga kanshi ba, da sauri Siddiqa ta tare Abban su Zeenatu ma haka duk suna kuka dan basu taba ganin mahaifin su yay fushi hakaba, ahankali Siddiqa tace "Abba mekakeyi ne ina zaka kai Rahima? Eh talk to me Abba na" cikin wani irin Kunan rai ya kalli Siddiqa yace "tashi daga gabana" yanda yama Siddiqa maganan saida gabanta yafadi da sauri suka matsamai yay wurin motarshi yabude boot ya wurga jakan ciki sanan yarufe yakoma gaba yabude motar ya kunna dantai warming sanan yadawo inda Rahima take tsugunne tai fitsari tana wasa dashi yazo wajen hannunta yakama ya finciketa ta mike tsaye tace "leave me Abba, bacci nakeji" ko takanta baibiba yajata ya wurgata a bayan mota saida kanta yabuge yamaida kofan yarufe, yakoma gaba ya shiga yatada motar gateman yabude mai yafita batare daya lura da motan su Shagali dake gaban gidansu kadan ba, wani irin fanfala uban gudu yake akan titi, ikon Allah ne kawai ke tafiya dashi saida yawuce zuba tawajejen hanyar Suleja ya tsaya awani babban farm house dinshi ya kashe motar ya fito ya shiga Rahima na cikin motar tana yaren da baiji, shiga cikin gidan yayi babban gidan gona ne dake daukeda bishiyoyi kala kala, ana kewan kifi da kaji masu kyau ciki, daga Gate ya tsaya ya shiga kwalama wani mutumi dake cikin dakin kaji kira cikin fushi. "Habu, Habu, Habu" da sauri wani dan mutumin dake cikin dakin kaji yana dubasu yajuyo jin ana kirashi ganin Abba yasa yafito da sauri yakaraso gaban Abba ya tsugunna cikeda girmamawa cikin hausan shi da bata fita da kyau tafi kaman da fulatanci yace "barka da zuwa Alhaji" cikin kunan rai Abba yace "Habu kataba bani labarin garinku dakace mini kauyen kayayau ne ko gwamnati batasan da itaba hakane?" gyadama Abba kai Habu yayi yace "kauyenmu asalin kauye ne aradu, ba wuta ba ruwa, ba waya, arafi muke wanka muyi wanki, adaji muke zuwa muyi bahaya, yawancin yan garinmu bama susan da akwai wani abu wai binni ba, wayanda kuma sukasan da binnin tsoron zuwa sukeyi wai cinye mutane kukeyi anan binni, konima wanan kaddaran nanne yafito dani daga garin dahar yau bansan akwai binni ba, sanan mutanen binnin nada kirki" ahankali Abba yace "gud, matarka nachan ko da yaranka guda tara daka fadamin?" da sauri ya gyadamai kai yace "I, duk suna chan taki yarda tadawo binni wai tanaso ku mutuwa ya kamata ta mutu a inda aka yanke mata cibiya, kudi albashina nakan raba biyu nakai mata rabi, tana saida su gyada dafaffiya, mascara, sanan baban d'ana jauro mun sayamai shanu ahirin da biyar yana kiwansu muna sayar da hura da nono a kauyen mu" gyadakai Abba yayi cikeda gamsuwa da bayanin shi yace "Habu kasan mesa nakemaka tambaya kan garinku yau?" da sauri Habu ya girgiza kai, Abba yace "kasan shaye shaye?" da sauri Habu ya gyadakai yace "nasani ba giya ba ahai ai tatil aita hauka ana layi akan hanya" gyadakai Abba yayi cikin wani irin bakin ciki yace "to Habu y'ata na shaye shaye, an kaita wurin magani tagudu, sonake kazo kashiga motar nan ka kaini garinku inaso nabama matarka rikon y'ata, inaso nakaita kauye, inda bazata tataba samun access to shaye shaye bane, bazata ga inda zata sayo abubuwan shaye shaye ba, danko namaidata Rehabilitation centre sake gudowa zatayi dan tariga tasan hanyan guduwa, kauyenku kauyen kayayau ne kuma irin wajen nake son mata harsai tayi wata ni shiddan nan tabar shaye shayen, tahakura dan kanta sanan zan koma na dauko ta, Rahima needs iron hand tana bukatan abu haka, by the time tai rayuwa irin wacce bata saba da itaba hankali zai shigeta dan kanta, zata gane gata ake mata a rehab datake samun gado ta kwana, tasamu shawa tai wanka, lokacin dataga batada wani option dayarage ta shiga rapi tai wanka, kokuma tasha ruwan rapi, kokuma ta kwanta tai bacci akan gadon kara ko kasa, tasha nono tai hamdala ta goge baki, tai kwadayin shaye shaye ta nemi inda zata samu tarasa, tai kewanmu takasa ganinmu wlh zata natsu, I believe tahakane kadai Rahima zata natsu tabar wanan mugun dabi'an na tir" da sauri Habu ya kalli Abba gabanshi nafaduwa dim dim yace "tooofah, saidai wani hanzari ba gudu ba garinmu akwai wani......." da sauri Abba yatare shi yace "zaka rikemin y'a ko ba zakayi ba na nemi wani wajen Habu?" Abba yay maganan cikin bacin rai, da sauri cikin kuma damuwa sosai Habu yace "zanyi wlh Alhaji, kaida kamin komi karufamini asiri, kabani ci, sha, tufafi da abin kwashewa na gagara maka wanan, wlh zanyi wlh" "gud rufo gidan mutafi banson jin wata magana" komawa yayi ciki da sauri yadauko key yafito yarufe gidan sanan yazo gaban mota Abba yabudemai ya shiga yarufo kofa Abba yakoma ya shiga motan yana kallon Rahima dake hauka sosai har lokacin tana wakoki, girgiza kai yayi hawaye yataru a idanunshi da sauri ya hadiye su yatada motan yaja, koshi kanshi Habu saida yaji tsoron irin gudun da Abba keyi, tun Rahima na haukanta hartai bacci.
Awa takwas yadauke su suka shigo garin Gombe, Habu nata nunamai hanyar kauyensu, suka dau wani hanya wacce itace hanyar kauyen, kauye da yadauke su kusan awa biyar sanan sukakai wani daji, ahankali Habu yace "dole zamu ajiye motan anan Alhaji mu karasa da kafa dan babu hanyar motar kuma, kauyen mu chan bayan dajin nanne saisa bama asan damu ba a Nigeria nan" saukowa Abba yayi batare daya damuba Habu ma yafito boot Abba yabude yaciro akwatinta yabama Habu yace "rike wanan" akai Habu yadaura sanan Abba yabude baya yajawo kafafun Rahima dake narka uban bacci, kuka tahauyi cikin Bacci tace "sakeni" kota kanta Abba baiyiba ya kulle motar yarike hannunta gam yahau janta bacci take dan taki bude ido bin Abba kawai take luuu kaman zata fadi tsabagen karfin mix din data sha tafiya kawai suke, har dare tamusu ahanyan nan amma ko darr Abba baiji aranshi ba, sunyi tafiya kusan na awa daya akafa sanan Abba yafara hango haske hasken fitilu Habu yace "mun iso, ga kararkaran mu chan" karasawa sukayi dudda darene amma all abubuwan da Abba ke gani shine bukkoki kusan hamsin ko dari azagaye, baiga ginin gini ba saidai ginin kara dasu bukkoki, sai gaishe gaishe Habu yake dayan kwararrun mutanen dake waje kafin yakarasa chan gaba wurin wasu bukka guda biyu da bishiya ke tsakanin su, sallama ya kwada. "Assalamu Alaykum mutan gidan nanan" daga ciki aka amsa. "muryan wa nikaji kaman mai gidana" dan dariya Habu yayi saiga wata mata tafito da daurin zanu a kugu babu riga ajikinta sai wani yaro agwai data rike akan cikinta yanshan dogon nonon ta dayakai cikin ta tsabagen tsawo dayan kuma yaron na wasadshi da hannu yana surutu irin na dadin nonon nan da yara keyi, bata da kiba sosai sai tsayi da gashin kanta data tufke kaman na yar bararoji, an kitse na gefe da gefen gaban kanta guda biyu jelar gashin har wajen kirjinta, saiga wata yarinya dazata fi Rahima tsayi itama rikeda fitila tana dagawa tana haska fuskokin su ganin Habu yasa matar da saka uban tsalle nonon na lilo da sauri dan karamin yaron ya saki nono ya juyo jin maman shi ta daka uban tsalle yana kalle kalle, matar tace "wayyo Allah na mai gida kadawo, Mairo kufito ga babban ku yadawo" wasu yarane suka dinga fitowa daga bukkan Abba ya saukar da kanshi kasa ganin babu riga a jikin matar, dudda baya ganin fuskokin su da kyau sabida darene bai hanashi ganin yaron dake shan mama ba, tsalle sukahau yi har wasu mutane suna fitowa daga bukkoki su suna lekowa, ganin haka Habu yace "bamu asabari muzauna magana zamuyi ba dawowa nayiba" da sauri ta kalli yarta tace "Mairo dauko as abari babbanku yazauna" da sauri yarinyar ta shiga ciki ba'a jimaba tafito da asabari ta shimfida Abba na kokarin zaunar da Rahima ta kwanta tana bude idanunta tana kallon kowa, zama matar tayi takalli yaran dasuke tsaitsaya suna kallon baban nasu duk maza gabaki daya kansu daya kaman yan shidda ta haifa, sai wani babba da yake sanye da kayan fulani da tsayinshi daya
Showing 66001 words to 69000 words out of 212889 words

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6Chapter 7Chapter 8Chapter 9Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23 Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30Chapter 31Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67Chapter 68Chapter 69Chapter 70Chapter 71