hararan nan na ban yardaba tace "yan matan ki dai na dakin ki tana bacci yar gaban goshinki, mu ai bakison mu, Rahima dabake kika haifeta ba kikeso ita kadai" da sauri Siddiqa data karasa tashi zaune tace "Luba banhanaki irin wayan nan magangan....." hannu Mummy ta dagama Siddiqa tace "leave her, gaskiya tafadi, but am sorry kinji y'ata kema kinsan ina mugun sonku ko, me kikeso yanzu?" dan murmushi tayi tace "Mummy wanan dubai gowns dinan dakikasa kawarki tasayoma Auta" da sauri Mummy tace "angama zan sa akawo muku guda biyar biyar each, oya yanzu atashi ayi salla kuzo mu shiga kitchen yan albarka" da sauri Siddiqa tace "Auta, bari naje nakirata Abba yace mudingayi tare" hararanta Mummy tayi tace "agulma'u bil kisira, Ke kinmafi mai kisiri mai dummataini ce, to bazakije ba, wuce kije kiyi alwala kuyi salla mu shiga kitchen inta tashi zatai nata" wani kallo Siddiqa tama Mummy najin haushi saikuma ta tashi ya wuce bayi abinta, Mummy tana zaune tareda su duk sukai salla sanan ta tattara su sukai kitchen saida tasa suka fara shirye shiryen hada sanwa sanan tafito tai dakinta, wayarta dake kan mirror ta dauka tai dialing number Abba, ringing daya ya daga.

"Wifey" "na'am Alhaji, nace ba" anatse Abba yace "uhum ina jinki" kashe murya tayi tace "Abban su nace anjima da daddare Lieutenant zaizo wajen Rahima ne? Naga dazu yazo dama inaso nasani ne danna sashi a abinci zamu fara girki ne" daga tachan bangaren Abba yace "yeah I think tarema zamu dawo, dazu dayazo yana shigowa aka kirashi, shida Marshal ogansu sukaje supervising posts, so yacemin zaizo da night, kisada shi, tare zamu shigo, nima I thought bazan dadeba, anyway lemme just tell you abinda nazo yi a office kinsan menene" da sauri Mummy ta gyara zama tace "no Alhaji menene, bani insha? Wani contract kasamu ko mene?" dan dariya Abba yayi yace "No ba contract bane, dama nayi ordering wata mota ce" da sauri Mummy tace "mota Alhaji? Mezakai da mota gala da uban motoci" ahankali yace "ki rage murya kar yaranmu suji" da sauri MUMY ta kwantar da murya tace "na rage" Abba yace "actually Rahima nama ordering mota, so ya iso shine aka kira naje nai signing ne, luxus ce motar yar babba hakanan but ba chanchan ba anjima zamu dawo da ita" yay maganan sounding so excited, wani irin faduwa gaban Mummy ya shigayi ranta yay bala'in baci wani baki ciki yataso mata, jin tayi shiru yasa Abba yace "ya kika gani? Naga tai bala'in kokari duk tabi tadawo wani iri, ta lalace ta rame, ta kode kinga yau kwananta 5 batasha komiba, so I thought of lemme buy car for her hakan zai sata murna, murnan kuma zai mantar da ita komi yasata dawo normal, su Siddiqa kuma nasu motan in sha Allah kowaccen su duk ranan daurin aurenta ranan da za'a kaisu gidan miji da sabuwa motarsu za'a kaisu, kinsan yanzu abun zaiyi wani irine natara yara duk nabasu motocin kansu tun kafin suyi aure kaman batasu ne, ko Rahima ma wanan ne dalilin bata mota bawai dan shagaltarwa ko sangartarwa ba, akwai many ways dayakesa yaron barin hallaya marasa kyau, inhar kasamu yadena koda na kwana uku ne tokabashi tukwuicin dazaisa yaron yaji zaima iya barin dabi'un marasa kyau har abada kin gane wife" danne bakincikin da Mummy takeji tayi tai murmushin yake tace "wow Abban mu mungode, yau zakasa baby girl dina farin ciki, u have no idea yanda kasani farin ciki, thank you Alhaji, Allah yamaka albarka" har cikin zuciyanshi Abba yaji wani irin sanyi yanda Mummy tai farin cikin abinda yayi batare data batarai kota nuna wani irin haushin akan yasaima Rahima mota baisaima yaranshi ba, ahankali yakira sunanta. "Maryam dina" murya chan kasa tana danne duka bakin cikin datakeji tace "na'am Alhaji na" murya chan kasa Abba yace "I love you so much Maryam banjin akwai mace mai irin hallaiyan ki aduniyan nan ba, ni karan kaina nasan nayi dacen mata, nagode miki and I know I always promise you this, yanzu ma still zan kara promising naki, listen Maryam kome kikeso aduniyan nan, komeye shi, gida, kudi, fili ke koma menene inhar baifi karfina ba wlh saina miki shi you deserve this and even more, Ke mace ta gari ce" dan dariya tayi tace "haba Alhaji ni kadenamin godiya please, kake cewa komenakeso to mema bakamin ba, Alhaji kabude min manya manyan super market guda hudu anan Abuja, ka zuba ma'aikata kullum kudi shiga account dina yake, ka budemin spa, banda all this duk wata ana maka salary zaka bani kudi nima kyauta mekuma nake nema inhar am not greedy, indai nice I will always support you mijina, kaga kar yaran nan suyi shirme a kitchen nabarsu su kadai, bari naje saika dawo" katse wayan tayi da sauri ta jefar da wayan man gado ta kife kanta zuciyata na wani irin kuna kaman an watsa garwashi, tadade ranta bai baci hakaba, mikewa tayi tsaye tace "aiko I promise you yau zaku iso gidan nan ku tatrar da bakin cikin da baku taba tunani ba, wlh sainasa murnan ka takoma ciki" tai maganan tana bude kofa tafita, sake bude kofar dakin Rahima tayi ganin har lokacin bacci take yasa ta kalli agogon bangon dakin biyar saura ahankali tace "by 6" tawuce tai falo tsabagen bakin ciki kasa shiga kitchen din tayi tawani kwanta akan dogon kujera tana kallon agogon bango tana jiran 6 yayi.

Wuraren 5:50 Rahima tabude idanunta ahankali dasuka sanyi ja sabida baccin datashi, tashi ahankali tayi ta zauna tana yatsine fuska kaman zatai kuka tace "uhmm" daidai Mummy tazo wajen zata bude kofan ta shiga jin muryan ta yasa tai wani irin murmushi tareda taune lips tajuya ahankali sadaf sadaf takoma falo ta zauna.

Hannu tasa ahankali ta zare hijabin jikinta tanaji ko ina na jikinta namata ciwo, tashi tayi ahankali daka kan dadduman tadauke dadduman da hijabin nata ta wurgasu kan madubi tawuce ta shiga bayi fitsari tayi tai tsarki ta wanke hannunta sanan tasa toothpaste a toothbrush dinta ta shiga wanke bakinta dan ta tsani ta tashi daga bacci taji bakinta namata wani iri, wanke bakin tayi tsaf sanan ta debi ruwa ta wanke fuskanta taja towel ta share ruwan fuskan nata sanan tabude kofa ahankali tafito feeling headache kanta yawani saramata, hannu ta daura kan goshin nata tareda lumshe ido tana tsaye daga bakin bayin saida kan yadan lafa sanan tabude idanunta ahankali ta daga kafafun ta zata fara tafiya idanunta suka sauka akan kwalaban codeine guda uku dake kan side drawer gadonta an ajiyesu gasunan acike tap bawai empty bottles ba, ga karan weed guda uku gakuma light, wani irin racing heart dinta yayi she can't believe wat she is seeing, tsabagen mamaki da rudewa kulle idanunta tayi sanan tabude da sauri tasake kallon saman side drawer taga still dai suna wurin dawani irin sauri takarasa wajen wani irin zama tayi dirzhan akasa tana kallonsu kaman mai daukan karatu agaban Malam tana bude baki har wani yawu take hadiyewa kaman wacce aka gabatar mata da farfesun kan sa, hannunta har rawa yake tamika tadau kwalba daya na codeine din tarike a hannu jikinta har bari yaje bar bar kaman irin yaron daya ga abinci for the first time after like a whole year of starvation, kanta gabaki daya ya kwance kaman wacce akama baki ko kadan bata tunani all abinda zuciyanta idanuwanta gangan jikinta da ruhinta ke gani dakuma tunani shine wayannan kayan mayen, dawani irin sauri ta shiga bude codeine din wani irin cillar da marfin tayi ta daga sai bakinta tana sha tana nishi tana lumshe ido kaman yaron karami da akabama bobon dayagama kuka abashi, saida ta shanye shi tass sanan tawani irin cillar da bottle din tadau na biyun da gudu tana sauke ajiyan zuciya tabude ta yarda marfin takafa abaki saida ta kwalkwale tass sanan ta wurgar da bottle din vamatare da tasan inda take wurgawaba tadau 3rd bottle takafa abaki, harwani lumshe ido take tana sauke ajiyan zuciya gwanin ban tausayi tsabagen yanda tai kewansu fess ta shanye na ukun sanan ta cillar tawani irin yin doguwar gyatsa tana murmushi tai maza ta kwaso duka karan wiwikan tana kallonsu, kallon dakin nata tayi ganin babu komi na sha yasa tasake kallon side drawer, ganin lighter akai yasa tai shiru to kodai ta gwada smoking nashi ne ai taga Chris yay smoking nashi ranan yana shan codeine yana zukanshi wai mugun dadi kakeji, da sauri tamika hannu tadau lighter ya kyasta na wiwi wuta yakama ta yarda lighter takai wiwi baki ta zuko ahankali sanan ta fuzar tana lumshe ido tawani mike kafafu akasa tanajin dadin da bata tabajin irinshi ba.



Fitowa su Siddiqa sukayi daga kitchen rike da kulolin abincin dasuka dafa suka shiga jerawa kan dining, wani irin strange wari Siddiqa taji daya gauraye da kamshin abincin daya cika falon hakan yasa Siddiqa ta kalli Zeenatu dake kara rufe kulan abincin da kyau tace "Zeena bakiji wari ba?" da sauri Zeena ta dago daga abinda take tace "wari Ya Siddiqa? A'a ni banji wani wariba" da sauri Luba tawani yatsine hanci tana huroshi tace "huuuu nima naji warin wlh, kaman warin taba" Mummy dake kan kujera tana kallo tai kaman bataji suba tace "me haka? Astagafurullah lafiyan ki kuwa Luba kike kira mana sunan taba agida? Baku kukagama girki ba yanzu? Halama kun kona tukunya ne, ko wani abun barinma ke Luban nan mai shegen cinne cinne awuta, Common kuzo nan kusa mana zee World mu kalla Mahek" da sauri suka taho falon suka zazzauna dudda warin sai cigaba yake da damunsu amma Mummy tahansu magana sai labarin Mahek din take basu.


Yarda kara dayan wiwi data gamasha tayi, dukta bata carpet din dakin nata da tokan wiwi, lighter tadauka ta kunna na biyu ta shiga sha idanunta na mugun juyawa, jikinta nawani irin saki, tanajin ta a sama, sama kaman tana tafiya akan ruwa kifaye na lasan diddigen ta, silin din dakin take kallo tana zukan wiwi sai taga Maman ta sojoji sun sata kneel down, jikinta sai rawa yake wai tana tsoron bindiga tafashe da kuka, kyalkyacewa da dariya tayi tana zukan wiwi cikin wani slow murya tace "sooooja ci ubanta muuuguuuwaaa ceeeeee, batada imani kusada tsinto duwatsun kwata" takara kyalkyacewa da dariya ta mugun buguwa to the extend da bamata duniyan nan she is high....


Horn da Mummy taji na motar Abba yasa tawani irin tashi zaune da sauri tana yatsine hanci takalli su Siddiqa tace "Siddiqa are you sure kun kashe su gas da komi nima inatajin warin nan wlh yasoma hawa kaina" da sauri Luba da sauran suka tashi Zeenatu tace "Mummy wlh mun kashe komi nima warin ya isheni kaman taba" da sauri Siddiqa tace "kaman warin anan kona itacen magani" da sauri tai Mummy tace "kumuje kitchen nakara dai dubawa nagani" kitchen Mummy tayi yaran biyeda ita.
Shigowa gidan Abba yayi dawata sabuwar mota dall fara kujerun ko leda ba'a bareba, saiga motar Sameer shima ya shigo gidan dan tareda Abba suke, parking yayi yabude yafito yana sanye dawani farin bugaggiyar shadda data mugun yimai kyau kanshi babu hula, he looks very matured well compose a kayan kaman ka saceshi, karasowa inda yake Abba yayi yana murmushi yace "mu shiga ciki Son kagama an kusa kiran sallan magrib, kwanan nan dare na saurin yi, kaman ana period of shorter day longer night" gyadamai kai Sameer yayi yace "hakane Abba" daidai sun karaso hannu Abba yasa yabude kofar dakin taredayin babban sallaman nan nashi ya shiga ciki Sameer biyeda shi daidai su Mummy dasu Siddiqa sun fito daga kitchen, chak Abba ya tsaya tsaye a tsakiyan dakin sabida warin dayama hancinshi sallama Sameer ma haka, kafin Abba yay magana Mummy cikeda damuwa tace "sannu da zuwa Alhaji" , ta kalli Sameer daya tsaya chak tace "welcome Lieutenant" kafin da sauri ta kalli Abba cikin damuwa tace "Alhaji kataba ganin abu haka wai bakuji wariba kaman na taba taba kaman na kona saiwan magani, su Siddiqa sun gama girki yanzun nan nadauka sun kona abune but na shiga kitchen naduba ko'ina komi is fine narasa daga ina warin nan yake zuwa kuma sai tadamin da zuciya yake wlh" kafinma Abba yay magana Sameer ya kalli Siddiqa strictly babu alamun ko wasa daya akan fuskan shi yace "where is your sister? Rahima" ahankali Siddiqa tace "tana dakinta bacci take, har yanzu bata tashiba tun bayan mun gama basketball" da husky voice dinshi yace "take me to the room" da sauri Siddiqa tai hanyar corridor ko kadan bai damuba kai tsaye yabita Corridor sai a lokacin Abba ya iya daga kafa yabi bayanshi, Mummy ta kalli su Luba tace "menene duk aka tafi dakin autana? Kumuje" bin bayan Abba tayi su Luba biyeda ita, har gaban dakin Rahima Siddiqa taje sanan ta kalli Sameer tace "nanne dakinta" yanda mugun warin wiwi yacika corridor yasa Sameer yakarasa gaban dakin Abba da jikinshi yay wani irin sanyi tareda shi hannu yasa yabude kofan ahankali, baya Abba yayi zai fadi da sauri kowa yay ihu. "Abba!" rikeshi gam Sameer yayi yace "Abba calm down, don't panic" yay maganan yana shigo dashi cikin dakin ya jinginar dashi jikin kofa sanan ya kalli Rahima, har lokacin sillin din dakin take kallon ga karan wiwi na uku a hannunta ga kwalaben codeine data wawwatsar dasu kasan dakin tana wani irin buso hayaki ta hanci da bakinta sunayin saman dakin.


_this is the last free page, nabaku 30 pages free, BIN ABINDA ZUCIYA KESO novel ne one of it kind, gabaki daya daban yake da sauran littafai nai, is a blockbuster, I pour knowledge in this novel say I brag naji na yarda🤣_

_in kinaso kicigaba da karantawa zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank, saiki turo evidence of payment to my watsapp number 07012181461, sainai adding naki a group din danake posting BIN ABINDA ZUCIYA KESO zakuma ku iya turo kati MTN na dari uku marasa banki_

_ko Allah yasan irin effort and research dana saka a book dinan, some of my fans kun sani dan nayi tambayoyi kan shaye shaye kuka Bani amsoshin abubuwan da kuka sani, dan haka ba danniba bakuma dan halina ba, dan Allah ubangijina ni da ku kubiya just 300 kuyi subscribe ku karanta hankali kwance, ku ilmantu ku nishadan tu, dan duk wacce ta karanta batare data biyaba ban yafemata ba Allah zai sakamin_

_CHASING THE HEART CRAVINGS novel ne daya kunshi Soyayya, tuzuranci, Tausayi, drugs, addiction, rehabilitation, sugar Mummy, and many more, just pay and enjoy this book, I love you all_

_Awoof Bonus! Bonus! Bonus!_
_inhar kinzo zaki biyama mutane biyar zan barmiki akan dari bibbiyu instead of dari uku uku_
_in zaki biyama mutane goma, mutum takwas zaki biyamawa 2 nasamiki su free_
_mesa zakiyi satan novel? Just come pay for your friends and family akwai huge massive discount dazan miki inhar zaki biya wa mutum dayawa, this Awoof last for a whole week, daga next week Wednesday yay expire yay💃🏼💃🏼_31.

Arude Mummy da isowarta dakin kenan tadafe kirji ganin Rahima tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, innalillahi wa innailaihi raji'un, Abban su! Sameer! menene wanan a hannun Auta na? Kwalaben meya wayan nan akasa? Wiwi, taba, Rahima, Auta na" tai cikin dakin da gudu tai kan Rahima fizge karan wiwin tayi tayar akasa cikin ihu kaman wacce tasoma zarewa tace "Auta kina haukane tarbiyan da muka baki kenan? Wanan wani irin abin kunya ne kikeyi agidan mahaifinki eh? Agidan mahaifinki kike shaye shaye?" ko kadan Rahima batasan me Mummy ke cewaba idanunta kan wiwi ta da Mummy tayar akasa yanaci harya soma kona carpet din wurin, da sauri tai rarrafe tai wajen wiwi kaman wata tsohuwar mayya zatasa hannu tadau karan wiwi jikinta har rawa yake wani irin zuciya ta kwashi Abba yaji karfi yazomai ya tashi daga jikin kofan dayake, cikin wani irin kunan rai daidai tadau karan wiwi zatakai baki yasa kafa yay wani irin kwallo da ita saida bayanta ya bugu da wardrobe din dakin wiwin yafadi akasa ta buga bayanta awurin, kaman wacce bataji zafiba, bude idanunta tayi ahankali dasukai jajir, kaman wata wawiya tasa hannunta akasa tadafa ta tashi tsaye da kyar tana kalle kallen kasan dakin tana neman wiwin ta tana layi, so kawai take ta cigaba da sha tana ganin sojoji nabama maman ta wahala, ganin bamata san ya daketa ba haukanta take tana neman wiwi yasa Abba yawani fizgota ya jijjigata tareda dauketa da Mari ya kwala ihun kaman zai fasa gidan yakirata da kakkausan murya. "Rahimaaa!" dafe kuncinta tayi dan wanan karan marin ya shigeta kafin tasa hannayenta ta shiga dirza idanunta kaman wacce idanunta kemata kaikayi sanan ta cire hannun tabude idanunta da kyar tana zaro idanun dan bata ganida kyau kafin idanun su washe ta kalli Abba ido cikin ido, turo baki tayi cikin maye tace "wlh ka kara dukana saina rama mugu kawai azzalumi, angayama yanzu dane, bana tsoron ta mutu balle tai tsami, nice owlet, and I am a pj mask, bari kaga Halloween wind" tawani daga hannu tana huroma Abba iskan bakinta adole zata dagashi sama ta yar kaman yanda owlet keyi a cartoon din, ganin bai matsaba yana tsaye agabanta yasa tafashe da dariya tanunamai muscles dinta duka biyun tana zaro mai idanu, cikin fushi Abba yasake jijjigata yace "Rahima bazaki dawo hayyacin kiba, Rahima, Rahima Allaahumma ajirni fi musibati w......." kabar da hannun Abba tayi daga kan kafadarta tace "leave me alone this man, I hate you wlh, dama kowa baya sona dukkun tsaneni nima na tsaneku, kullum kaita dauremin fuska ka kira su Ya Siddiqa, Ya Lubabatu, da Ya Zeenatu kan kujera kusada kai amma bakako kallona, nima I don't need you kaji old man, Mummy na kadai nakeso, ita kadai, only Mummy, only Mummy" tai maganan tana washe baki duka fararen hakoranta awaje tana layi tace "I love my Mummy, Mummy I love, zankai ki all the 7 continent damuke dashi in the world, Europe, Asia, North America, South America, Antarctica, Australia yayyyy oya give them Mummy zannnnku legg work" yashiga rawa tana zanku agaban Abba sanan ta tsaya
Showing 54001 words to 57000 words out of 212889 words