tareda rike kwankwaso takawo fuskarta kusadana Abba tana kallon kwayan idanunshi har harshinta na gogan nashi tana busamai warin wiwi datake yi, cikin mugun fitsarin da shaye shaye kesawa tace "kaiko mugun, bakasona bansonka, I hate you! I hate you! I hate you" tai maganan tana turashi baya ta hanyar sa hannayenta akan kirjinshi ta tureshi da karfi, da sauri Siddiqa tace "Rahima!" dakuwa Rahima tamata tace "babu ruwanki dani jaririyar kunkuru tom" komawa baya Abba yayi yana kallonta kirjinshi nawani irin bugawa dabai tabayiba yana kallonta, biyoshi tayi tazo har inda yake tsaye kusada Sameer da yatsa tanuna shi tace "ka kara zuwa nan wlh saina zaneka ciki dabai, mugu kwai, wicked man, wlh bansonka" wani irin fadawa jikin bango Abba yayi kaman wanda aka tura any kalman I hate you na Rahima nasa zuciyarshi bugawa, wani irin nishi ya shigayi da baki trying to control yanda numfashi ke fita daga kirjinshi yana kallonta yana bude baki dan kaman nostrils dinshi sunmai kadan wajen fitar da numfashi, ganin haka yasa Sameer da sauri yarike shi yace "Abba Abba, listen Abba calm down kaji, batasan metake cewaba, bata hayyacin ta, don't allow her words gets to you, muje kafita daga dakin he falo ka huta" hannu Abba yasa kan kirjinshi yana bubbugawa yana wani irin lumshe ido kaman wanda ke shirin mutuwa, da sauri Mummy tazo wajenshi tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, Alhaji" da sauri Sameer yadago kai ya kalli Zeenatu dahar tafara kuka duk suna kallon yanda Abban nasu yakeyi yace "kawomin ruwa" wani irin tari Abba yashiga yi yay kasa kafafunshi na lankwashewa zai fadi da sauri Sameer yatare shi tareda zaunawa yadaura kanshi kan cinyarshi yadan dago kafan nashi sama sabida mugun tarin dayakeyi, ruwa Zeenatu takawo da gudu tabama Sameer, karban ruwan Sameer yayi yabude yakafa abakin Abba yazuba ruwan, tari sosai Abba ya shiga yi ruwan na fitowa kafin ruf yarufe idanunshi kaman wanda ya mutu ko suma, ihu Zeenatu tayi tace "Abba, Abba, Mummy Abba na menene" da sauri su Siddiqa da Luba suka karaso suka duk tsugunna suka zagaye su suna kuka "Abba, Abba" tsawa Sameer yadaka musu cikin fushi yace "ku fita! Out! he need air ba mutuwa yayiba, he's under shock, just a mild heart attack, ku fita kutafi dakinku" da sauri Mummy dake tsaye kansu jikinta na rawa tace "kufita kufita kunji me yayanku yace baban ku needs air, Siddiqa ki dauko wayana kan gado ki kira likitan baban ku kice yazo yanzu he is sick" da sauri suka fita suka rufo kofar Mummy ta fashe da kuka sosai tadau pillow gadon Rahima tana kallon Rahima dake tsaye tana kirga silin din dakin da yatsun tana layi bamatasan me akeyiba, kaima Sameer filon tayi tana kuka sosai ta ijiye akasa tace "sakanshi anan Sameer ya kwanta" ahankali Sameer ya kwantar dashi yana kwancemai neck tie din wuyanshi, fashewa da kuka sosai Mummy tayi ta tashi tai kan Rahima kifa mata Mari tayi ta jijjigata tana kuka tace "sokike ki kashe babanki? So kike ki kaishi lahira tun kafin lokacin shi yayi, Rahima waya lalata ki haka eh?" ta kalli Sameer cikin kuka daya dago kai yana kallonsu tace "wlh Sameer dazu ina kitchen naga tafice tsakar gida I tot maybe tafita kwaso shanyan kayanta ne fita kikayi ko?" ta jijjiga Rahima cikin fushi tace "kananun samari nan dakike dashi da basu gama balaga ba su suka kawo miki kwayoyin nan ko Rahima wani kudi kika basu dan nasan bakida ko anini" Mummy tafashe da kuka kaman mai shirin shidewa tace "to kodai ciki suka miki?" da sauri Sameer ya kalleta, ta gefen ido Mummy taga yana kallonta hakan yasa tasan yes! She just hit the right spot, hakan yasa ta cigaba cikin kunan rai tace "I've noticed kwanan nan bakida aiki sai bacci, bacci, bacci, Rahima look at you, you are just 20yrs but kinmafi babban yarku Siddiqa komi na y'a mace, kinfi yayyunki cikan nono, hips da sauransu, zuwa kike maza na kama miki suna matse kiko, dama ranan da wata yar ajinku ta tareni danaje dropping naki a department dinku tacemin taganki agidan wani dan ajinku dake zama offkay kuna wasa yana kama jikinki taga ku shiga daki sai yamma kika fito sanye dawata riga daban dana wanda kika shiga dashi, nama yarinyar fada na karyatata na zageta dan nasan baki taba dawowa gida dawani kaya dabamu muka saimiki ba yasa ban yardaba, Rahima NDLEA suka kamaki still shima ban yardaba dannasan birthday party kikace min zaki na classmate dinku ashe kinyi irin bacin nan, kin lalace, bin maza, shaye shaye dukke kadai wani irin JARABTA (M Shakur book) dahar zaki iya kunna sigari ne ma ko wiwi agidan ubanki, gidan iyayen ki kinashaye shaye, innalillahi wa innailaihi raji'un, me kikeso mufadi ma Allah akan tarbiyan da muka baki, mahaifinki ya killaceki yahanaki zuwa school, yahanaki fita ashe jira kawai kike yabar gida na sakan daya kiyi abinda ranki keso, dama baccin karyane eh Rahima? Ban taba dukanki ba amma yau kinyi kuskure wlh saina zaneki Auta, saina zaneki auta" Mummy tai maganan tana rufeta da duka tako ina Rahima na tureta tana turo baki kaman ma batajin dukan, Sameer na kallonsu baice ko uppan ba ko kyafta ido bayayi Rahiman yake kallo, daddaggewa Rahiman tayi ta tura Mummy cikin maye Mummy tai baya da gangan tawani irin fada kan jikin Sameer dake shafama Abba ruwa a goshi, unexpectedly yajita kanshi before you know it Mummy tafashe dawani mahaukacin kuka sosai tana kara shiga jikin Sameer din, tunda take aduniya tsawon shekaru hamsin da hudu zuwa hamsin da biyar kenan bata tabajin kamshin turare mai dadi kaman irin kamshin da Sameer keyiba, chusa kanta tayi awuyanshi kaman sabuwar vampire tana kuka tana goga fuskarta a thick neck dinshi tace "zan mutu Sameer Rahima zata kashe iyayenta da bakin ciki, innalillahi wa innailaihi raji'un" tureta Sameer yayi daga jikinshi da sauri cikin wani irin yanayi yatashi tsaye da sauri yana kakkabe jikinshi hakan yasa Mummy kaman wacce hankalinta ya gushe ta kwanta warwas akasa tana kuka harda birgima kaman irin bama tasan me tayiba dinan, fashewa dawani mahaukacin dariya Rahima tayi tafara rawa tana juya jiki kaman wacce taje dancing school, motsin da Abba yayi yana kokarin bude ido yasa da sauri Sameer ya tsugunna akanshi yarike hannunshi tareda kiran sunanshi. "Abba, Abba am right here open your eyes" tsagaita kukan Mummy tayi ta taso da sauri tazo dayan side din Abba, hannunshi takama tace "Alhaji gani nima katashi kaji" ahankali Abba yabude ido tareda sauke wani irin ajiyan zuciya, idanunshi ya sauke akan Rahima dake rawa sosai kaman an kunna disco, da yatsa yanuna ta cikin muryanshi da bata fita sosai yace "s....s......son t.....a" yakasa karasa maganan yay shiru sabida yanda numfashi kemai mugun wuya duk wanda ya ganshi yasan yana bukatan oxygen, cikin kokartawa da jarumta yace "he......her......take......her t......to.....re.....hab....." ganin yakasa karashe maganan yasa Sameer ya girgiza mai kai yace "stop talking Abba you need rest, nakaita rehabilitation centre?" gyadamai kai Abba yayi ahankali yace "n.....n..." da sauri Sameer yace "now?" gyadamai kai Abba yayi da sauri, ahankali yace "okay calm down" tashi 32 & 33


Girziga kai kawai yayi cikin mugun takaicin yakarama motan wani uban gudu, saida yakai Gwagwalada sanan ya yanki wata hanya suka cigaba da tafiya tanamai hauka saichan kuma tai shiru, agaban wani tangamemen gate din wani building yay horn, building an rubuta HOPE REHABILITATION CENTRE, masu gadi dake sanye da kayan security kusan su ukune suka budemai babban gate din ya shiga da motar ciki, wani hadadden gini ne bana wasaba babu kowa sai wuta dayacika ko'ina a compound din ya haska ko'ina kaman rana, parking yayi a inda aka tanada dan parking ya kashe motan sanan yajuyo ya kalleta ahankali yaga bacci take shaka abunta a kwance, gashinta ya zubo ta wuyanta ta tuge hijabin tayar ta tattake shi akasan motan da kafafuwanta, ajiyan zuciya yasauke sanan yabude motan ahankali yafito ya zagayo ta bayan ya tsaya yana shirin bude kofan da sauri daya daga cikin security yataho wajen daidai yabude marfin bayan motan yana kallonta. "Barka da zuwa yallabai" security yagaida Sameer yana lekawa cikin motan, gyadamai kai Sameer yayi hakan yasa security yace "akawo gado ne Yallabai?" da sauri Sameer yace "yeah" da gudu security yajuya ya shiga cikin building din ko minti daya ba'ayiba sai gashi yafito tareda wasu nurses guda uku dake sanye da kaya blue riga da wando sun gunguro gadon sukayo inda Sameer yake suka tsaya tareda gaidashi. "good evening Sir, what can we do for you sir?" Rahima yanuna musu dake kwance kan kujera tana bacci, da sauri buyi daga cikin nurses din suka zagaya ta dayan bangaren daya kuma ta tsaya inda Sameer yake suka bude kofan, hannunta dayan takama tajawo sauran biyun na kokarin kama kafafun ta tabude ido tarrr kaman wacce aka tsikara. ihu tayi tareda shurin su da kafa, "ammmmn ku, dan ubanku shegu masu kama da jemagen jalingo wlh kuka tabani saina karyamuku kashin mara" tashi tayi ta zauna ta daga hannu zata dakesu tana hararan su tace "kizo kugani wlh" tsayawa sukai chak suna kallonta, hakan yasa Sameer yadanja tsaki ya kalli nurse din dake gefenshi tanayi kaman ma tsoron kamo Rahiman take yace "excuse me" da sauri ta matsa gefe yazo wajen, da idanunshi dasukai jajir tsabagen bacin rai ya kalleta, harara ta ballaramai tana dan lumshe ido tsabagen baccin dake cinta ta nunamai hannunta tana turo baki tace "kataba ni saina kwakulemaka dogon hancin nan naka mai kama da giant tattasai" murmushi duka nurses din sukayi suna gimtse dariyan databasu, shigowa motan yayi hakan yasa takoma baya da sauri zata gudu ganin haka yasa sauran nurses din suka miko hannu zasu chapketa ihu tayi. "wayyooo a hhhhhhh" tawani irin yin tsalle azabure gudun karsu kamata tafada jikin Sameer tareda tahau kan ciyarshi ta zauna daram kaman irin yaro ya zauna kan cinyan babban nan tashiga wurgama nurses din kafafunta tanaso ta hambari nurses din tace "kuzo, kuzo kuga, I will smash you all" ko kadan bamatasan ta zauna kan jikin Sameer ba, yanda ta zauna kan cinyarshi saida yadanji wani iri ahankali yadaga hannunshi yakama shoulder dinta gam yanaso yatashi, jin ankamata yasa tajuyo da sauri ta kallai, hararanshi tayi tana kyafkyafta idanu cikin maye tace "kaiiii, wana kama? Tom tom tomlikitan" bakinta tabude tareda kawo bakinta da sauri ta daura kan dogon hancinshi dataga yafi komi tsayi a fuskarshi, tashi tsigan jikinshi yayi da sauri ya tureta baya, fashewa da dariya tayi tahau tsalle akan cinyarshi tace "laaaaaa hancinka sanyi wlh" ta fashe da dariya saikuma takara matsowa tana kallon idanunshi tace "bari nakara ice cream ne, ice cream ne ashe amma daskararre" tasake bude bakinta zata daura kan hancinshi da sauri yatureta da karfi yafita daga motan da sauri tareda janyota yafito da ita waje, kokawa ta shiga yi dashi yadauketa da karfi ya kwantar da ita kan gadon, tanajinta kan gado tai ajiyan zuciya tareda shafa cikinta tana kallon taurarin sama tace "hmmmmm twinkle twinkle little starrr" matsowa nurse din tayi cikeda dubara ta makale hannunta a belt din dake jikin gadon tama dayan hannun ma haka sanan suka shiga gungurata tana dariya kaman mahaukaciya tana surutu tana kirga taurarin sama tana wakoki daban daban, binsu abaya Sameer yayi har suka shiga wajen, babban reception ne, babu kowa sai two receptionist din wajen dake aiki agaban system saikuma TV dake aiki, wajen yahadu kaman ba a Nigeria ba, wani kofa suka bude suka shiga suka juyo sukece "come with us sir" binsu yayi wani babban dining ne da jerin kujeru da tables saikuma food court inda zasuje su karbi abinci sudawo su zauna ne wurin, wani kofa suka kara budewa nan yaga dogon ward inda almost 25 patients ke kwance ga wasu milk color riga da wando uniform ajikinsu, nurse daya dake tareda Sameer tace "this is ladies ward, chan dayan bangaren nanne male ward" tana maganan suka bude wani daki dake dauke da check up bed suka daurata akai, daya daga cikinsu ta shiga hada allura dayan kuma ta shiga ciki ba'a wani jimaba tafito tareda wani magidancin Dr da akalla zaikai seventy yrs, yay wajen Rahima dake kan gado tana ihu sabida alluran da aka mata a vein din hannu, da sauri Dr ya matsa ya janyo wani dogon abu dakeda rami a tsakiya yasa nurses suka dagota ta zauna tana turesu tana nunasu da hannu. "ku saken, ku saken, Mummy mummy kin gansu ko" ta fashe da kuka sosai kafin tafara kwaro uban amai yana shiga cikin abun, amai kawai takeyi bana wasaba jingina da bango Sameer yayi yana kallonta yanda duk suka taru akanta, ringing da wayarshi yayi yasa yaciro wayar ganin Ummi ne yasa yabude kofa yafita daga wajen, chan dinning yatafi zama yayi kan daya daga cikin kujerun wajen yay dialing number nata yakara wayan akunenshi dauka Ummi tayi tace "Soja na kana inane? Kanenka da matayen su sunzo gaishemu, Princess sai nemanka take, ga Asiya nan ma tazo zata mana sati sunyi mid semester, where are you Son? Anata liyafa baka" dan ajiyan zuciya yasauke ahankali yace "am very far Ummi, I will come back late, you guys should eat karku damu dani" murya chan kasa Ummi tace "Tom shikenan, saika dawo, Allah ya taimaka" ahankali yace "Ameen bye Ummi" katse wayan yayi yatashi yafita, chan wajen masu gadi yaje ya tambaya inane masallaci dan baiyi magrib ba gashi yanzu 9 anmayi isha'i chan backyard yakashi alwala yayi yashiga masallacin wurin yay salla sanan yafito yadawo ciki, yana shigowa reception din yaga nurse daya da alamu shi tafito nema tana ganinshi tai murmushi tace "please come with me, Dr want to see you" gyadamata kai yayi yabi bayanta har office din Dr, sanan Nurse din tajuya tafita, zama yayi kan kujeran da Dr ke nunamai yace "please sit" zama yayi sanan Dr yay yan rubuce rubuce a file din daya rubuta abubuwan Rahiman, anatse Dr yace "why are you just bringing your sister now? Lokacin da shaye shaye na gab da deteriorate system dinta?" ahankali Sameer yace "how?" gyara zama Dr yayi yace "base on the short investigation that I run on this gurl yanzun nan, yarinyar nan takai nothing less than 8 to 9yrs tana shaye shayen nan so trust me her rehabilitation process is not a process dat will take her just 1month, this gurl zatai spending nothing less than 6 to 1yr undergoing different process and treatment kafin asami lafiya tabar shaye shayen tass" shiru Sameer yayi yana kallonshi kafin yace "what are the processes?" ajiyan zuciya Dr ya sauke yace "normally in aka kawomana patient that is just suffering from irin 1month addiction or 2weeks hakanan nan, irin sababbin yan shaye shaye yawanci irin wayan nan ma bama admitting nasu saidai sudinga zuwa as an out patient muna dubasu muna basu maganin dayakamata suna sha."





Yadan yi shiru tareda mika hannunshi yadau bottle water ya kurba sanan ya mayar ya ajiye yace "muna basu appointment in sunzo mu dubasu mubasu magunguna su tafi, this your sister now, give me her name ma" Sameer yace "Rahima Sambo Rikadawa" rubuta sunan Dr yayi yace "rehabilitation treatment program din da sister ka ke bugata mainly guda biyar ne;
_1- Drug Screening and addiction assessment_
_2- Medical detox_
_3- psychological treatment_
_4- Educational sessions dakuma_
_5- supportive services_
Yace "kasan Rehabilitation is the process of combining pharmacological (prescription medications) and psychotherapeutic treatments to address substance abuse disorders, wani zubin inhar akace za'abar dan shaye shaye shi kadai anamai wa'azi yadena shaye shaye bazai taba iyawa bane, he needs support daga medical facilities why because all his organs, his system are use to the substances dayake abusing, saisa nace maka abu nafarko dazamu fara mata shine _drugs screening and addiction assessment_ zamuyi screening nata musan wasu kwayoyin shaye shaye tasa sha kagane? Musan wasu substance da wani substance take abusing, dole musan wanne takesha dan inmunsan wanda takesha ne zamusan magungunan dazaima jikinta aiki, bayan munsan wanan sai muyi accessing addiction dinta, how strong kwadayin, bukatan, jaraban son shan kayan mayen ke taso mata, every hour take sha koko zata iya yin kwana daya bata sha ba, kokuma a each 24hrs tana sha yakai sau biyu sau uku? Idan muka gane kan wanan the next thing damukema patient shine _medical detox_ though bazan ma karyaba all our patients sun tsani wanan medical detox din dan its makes them uncomfortable, baida dadinyi, wasuma sunce is painful but is one of the very vital step da rehabilitation centre can not do without, Medical detox din munayin shi ne dan zamu wanke cikin jikinta, by removing toxins (harmful substance) da impurities from her body na abubuwan datake sha, in a nutshell shi wanan detox din zamu washing away all kayan mayen ne na cikin jikinta mu wanketa taciki tsaf ya zamto babu sauran kwayoyin mayen ajikinta, sai _psychological treatment_, wanan zai zama ko everyweek ko everyday depending on yanda mukaga progress dinta dole zata dinga ganin psychologist suna magana, suna tattaunawa tana fadamishi how she feels today dadai sauran su hakan ma yana determining musan how far we have gone with the treatment akwai progress ko babu, sai _educational sessions_ ana kowa musu karatu, health education kenan, za'a basu ilimi da knowledge
asanarsai ka karo mata hardasu toothbrush da cream dinta da toothpaste, sabulon wanka, sponge da kuma hijab sabida salla, but most importantly karka manta da pant and bra sai pad this 3 things she can't get them here" dan gyadamata kai Sameer yayi batare daya kalleta ba ya shiga mota yatada yaja aka budemai Gate yafita daga gidan yafita daga Street din har zuwa shagon datamai kwatance, parking yayi agaban shagon ya shigo yana kalle kalle, breziyoyi ne da panties kala kala ashagon, tsayawa ma yayi chak batare dayasan wani abu zai daukar mata ba this is the first time in his life dayake sayan pant bra da pad toshi baida kanwa ko Yaya bama ataba aikanshi irin abun nan ba, ganin yanda ya tsaya chak yasa madam din shagon wacce take bayerabiya
Showing 57001 words to 60000 words out of 212889 words