zamuje? Malam wanzan ya juyo ya kalli JAROOD kana ya maida hankalinsa ga tukinsa yana fadin.  Kasan inda zamuje mana ranka yadade, koka manta in tuna maka? JAROOD ya numfasa yace  Aah ina sane, amma gaskiya baza muje ba&  malam wanzan yasake juyowa ya kalli JAROOD akaro na biyu yace  Saboda me ranka ya dade ? Cikin gajiyawa JAROOD yace  Wallahi nagaji, nagaji da yawon neman maganinnan, wasuma da muke zuwa gunsufa ba malaman addini bane wallahi ni ganinsu nakeyi kamar bokaye, gaskiya Ina tsoron kada garin san neman lafiyata in bace ga hanyar ubangijina, kaga in tashi a tutar babu ba duniya kuma ba lahira, wlhi inajin tsoron Allah baba&  malam wanzan ya jinjina kai yana me nazarin kalaman JAROOD kana yace  hakane ranka ya dade, ka kwantar da hankalinka, duk wanda zamuje gurinsu senayi bincike an tabbatarmin da malamaine na Allah da Annabi Muhammadu SAW, bawai bokaye ba& wasu kuma masu bada maganin gargajiya ne&  JAROOD ya amshe da  Amma kuma shine ka kaini gün wanda yasani na Auri Hajiya Aisha dasunan za asamu waraka inna Aureta? Kaga watoma yasan gaibu kenan, Gashi kuma ba nasara, ubangiji na kuma nuna mana bawanda yasan gaibu seshi, kuma ba wanda ya isa ya bani lafiya Se ubangijin daya jarabceni da wannan ciwon, dan Allah mu hakura mu Fawwalawa Ubangiji komi wlhi dogaro ga Allah ya isar min komi kawai na hakura&  JAROOD ya karashe mgnr yana kwantar da seat =ØºÜ din dayake ya d anyi baya kadan, se sauke ajiyar zuciya yakeyi yayinda yakeji kmr zuciyarsa zata kone saboda zafi da tukikin da take masa, maganganun hajiya Zulaikha kawai ke yawo a kogon zuciyar tasa. Cikin tattausar lafazi malam wanzan yace  Ranka ya dade dan Allah kabari muci gaba da gwadawa inaji ajikina wata rana za a dace, kuma ubangiji yaga zuciyarmu muna rokon lafiyarka agaresa kuma muna neman magani, shi dakansa yace katashi in taimakeka, Allah yafimu sanin kanmu, ba haka Aka haifekaba yi maka Abunnan Akayi, marasa imanine suka maka wannan mugun sihirin, ka kwantar da hankalinka ranka ya dade mun tsaida Allah daya munsan ze temakemu insha Allahu wannan problem din ze zama labari, amma fa semun dage da Adduah kuma da neman maganin , kafin ubangiji ya sauke cuta saboda san da yake mana seda ya sauke mana maganinta,, insha Allahu Aski yazo gaban goshi dan Allah ranka yadade karka Sare karfin guiwarka nima kasaremin tawa&  JAROOD daketa sauraransa kuma yana tunano maganganun hajiya Zulaikha. Yanaso yasamu lafiya saboda bejin dadin abinda hajiya Zulaikha ke masa Gashi ba halin yasaketa, sbda mahaifinta yace duk randa tarabu da JAROOD toh tsinuwarsa ta tabbata agareta kuma karta sake ta Tunkaro masa gida.  Shikenan Baba Allah ya tabbatarmin da Alkhairi&  Cewar JAROOD. Malam wanzan yaji dadin abinda yace ya amshe da  Yawwa kokaifa yallabai, Amin ya Rabbih& wallahi nasan me kakeji ranka ya dade ga mata har mata ka tara Amma baka basu wutaaaa.. JAROOD yayi dariya yace  Babana kuma Aminina&  malam wanzan ma dariyar yayi yana Cewa  Eh mana ai gaskiya nafadi ka tara kaya ba injin, amma insha Allahu kwanan nan Injin ze fara aiki&  JAROOD ya amshe da  Amin ya Rabbih Allah ya amince& nida Kaifa baba marabar kadan ce&  JAROOD ya karashe maganarsa yana kwashewa da dariya ç1k1n zolaya , inde suna tare da Malam wanzan se yaji Rabin damuwarsa ta gudu. Malam wanzan ya bushe da dariyar shima yana fadin .  Gyan-gyan nake jina ai yanzu gashima harna Ajiye y a, nayima Giwar sarki takwara&  JAROOD yayi dariya yace  Au namanta fa, amma yar taka nawa take koni da haihuwa nakeyi ai da yanzu nahaifi wadda tafita wallahi&  cikin barkwanci suke maganar. Malam wanzan daketa dariya har yanzu yace  Tinima kuwa ranka ya dade, da kyar nasamu Nima wallahi, in baka mantaba kusan mata goma sha biyu na Aura muka rabu duk basu haihuba sbda matsalar daga gareni ne, se yanzu ubangiji yasa dana Auri wannan matar tawa ta karshe Nasamu na haifa y a daya shekararta goma sha hudu yanzu, kaga komi ai hikimar ubangiji ne akaina ma yakamata kaga ishara, duk gun me maganin da mukaje cewa akeyi bazan taba haihuwa ba, asibitocin daka kaini da kanka har kasar waje sunfi akirga,,, Kagani se yanzu ubangiji yabani haihuwar, kaima inaji ajikina zan dauki d anka a hannuna insha Allahu&  JAROOD ya jinjina kai yayinda yakejin dadin hirar tasu yace  Allah ya nunamin randa zan hau duri inyi sukuwa&  JAROOD ya fadi ko kunyar malam wanzan beji ba sbda Amininsa ne sun Saba irin wannan maganar. Malam wanzan ya kuma kwashewa da dariya kana ya amsa da  Amin ai kai daga ganinka bazaka ragama duri ba& Yanda kake labcecennan ai nasan itama Gimbiyar labceciya ce&  JAROOD da nishadi ke kwance Akan fuskarsa yace  Ai nida Kaina innaje wanka Abarnan nabani tsoro innaga girmanta, kai kaga Abaaa lafceciya& Kai Allah ya ragema Aya zakiii&  malam wanzan yasake dariya yace  Wannan Ayar kam da zakinta& wannan inta mike yaya kenan, Inka shiga gunnan Yanda yakeda mugun dadih da ruwa-ruwa kamar fadama ai inaga seka kusa kashe yar mutane.. JAROOD ya tashi zaune yana dariya yana fadin  Sekace de wani Mugu& Amma nide inaso ka fassaramin yadda gun yake da dadinnan da kullum in muna magana seka fadi gun nada dadih nifa ko shaawah baya bani&  malam wanzan yace  Ai duk yadda zan gaya maka dadinsa baza gane ba nan gaba da kanka zaka gayamin yadda kaji dadin nasa, Kaiii inka fara sukuwa agunnan zakaji kamar karka fito sbda dadinsa& Kabari kawai lokaci na nan zuwa&  JAROOD daketa murmushi yace  Allah ya tabbatar, malam wanzan ya amsa da  Amin& . Suna tafe suna hirarsu ta nishadi har suka iso Anguwar sarki inda gidan Sarki yake sauka inyazo Nigeria a kaduna. Babban gida ne wanda ya amsa sunansa tako ina an kewaye gidan da zanen sarauta da adon sarauta yan sanda zagaye da gidan suna tsaron gidan, wannan sarkin ba karabutin sarki bane, sarkine ga Kudi ga Mulki, kuma Gadon sarautar yayi bawai asama yasameta ba, masu abune da Abunsu. Packing motar malam wanzan yayi a babban packing space din gidan. A tare suka fito da JAROOD daga motar, nanfa mutanen dake zagaye da gidan suka fara zubewa suna miko masa gaisuwa yanata binsu yana amsawa cikin safin fuska. Yafi karfin 30mnt a waje yanata amsa gaisuwar ma aikatan wadanda ke sanye da irin kayan da ma aikatan gidan sarauta kesawa. Da kyar JAROOD yasamu ya nufa part din mahaifiyarsa, gidan babba ne sosai girmansa ya wuce lissafina. Allah-Allah JAROOD yakeyi ya isa falon nata domin yayi ido biyu da mahaifiyar tasa. Nanma yanata cin karo da maaikata abunka da gidan sarauta. Afalon mahaifiyarsa yahadu da Jakadiyar mahaifiyarsa hajiya sabuwa tsohuwa ce amma ba sosai ba sbda tana cikin hutu. Suka gaisa da JAROOD ya tambayeta  Awani Falo Giwar sarki take? Jakadiya ta amsa masa da  Tana falon sama, tinda ta tashi daga bacci da asubahi tay1 sallah yau bata koma bacci ba sbda tanaso taganka&  murmushi JAROOD yayi hadi dacewa  Okay&  ya nufa Saman ita kuma jakadiya ta nufa hanyar fita daga falon. Ko ina ya tsaru da kayan alatu ado iri daban-daban na gidan sarauta, se kamshi kawai ke tashi tako ina domin itama Hajiya Fatima batason kazanta tanasan kamshi agunta JAROOD yagaji san kamshi. Da sallama yashiga falon nata wanda ya tsaru yaji luntsuma-luntsuma din kujeru na alfarma kalar Ligt brown,. Wata farar mace na hango gishingide akasan carpet ta tada hannunta da tin-tin irin na sarauta, sauratarma ta mutanen Agadez. kyakyawa ce sosai dukda ta manyanta amma hakan be hana bayyanar tsananin kyaunta ba, kai dagani kasan itadin cikakkiyar buzuwa ce wadda ta amsa sunanta na buzaye, Sak ita JAROOD ya biyo amma gaskiya yafita kyau, ko alaunin fata ze tabbatar maka dasu ba yan nigeria bane. Tanajin sallamarsa ta amsa ta tashi zaune tasha doguwar rigar Abaya wacce tasha ado tako ina ta daura dankwalin Abayar akanta, wuyanta sanye da sarkar danyen gold da hannayenta. bakaramin amsarta Abayar tayi ba, hancinta zir har baka ga karamin baki, sak de kamarta da JAROOD tanada karamar fuska wato baby face, hutu ya ratsata tako ina, jikinnan kamar ataba jini ya bulbulo, se glowing takeyi Tana shekin kyau da fitar da wani shu umin siririn kyau, ita bame qiba bace kuma ba siririya bace, babbar macece amma sam bata tsufa ba sbda Akwai gyara irin na yan Niger uwa uba kuma ga Hutu.  Vie moi& (rayuwata) hajiya Fatima ta fadi da siririyar muryarta cikin harshen French, se murmushi takeyi wushiryarta tasama da kasa ta bayyana yar siririya, Abinda ya rabasu da JAROOD kenan shi beda wushirya amma yafita kyau da farar fata ma duka. Wani irin murmushi JAROOD ya saki na zallar murnar ganinta dajin dadin sunan data kirasa dashi, tin yana karami daman haka takece masa RAYUWATA. ya karaso ya kamo hannayenta yayi kissing kana ya tsugunna ya gaidata da harshen French  Bonjour mon premier amour,(good morning first love) hajiya fatima tayi murmushi zatayi magana JAROOD yace  Kiyi hausa Amour (Love)&  murmushi hajiya fatima tayi cikin hausarta da bata kware ba, saboda ita cikakkiyar buzuwa ce, tace  Kasan hausar nan da wahala&  JAROOD yace  Da haka zaki Iya Ai Amour.. ta jinjina kai tace  Haka ne& Yana sameku ya JAROOD dina yake da iyalinsa? Murmushi JAROOD yayi daya ganta dukse taji damuwarsa ta gushe.  Alhamdulillahi Amour, ya gajiyar hanya ya kuka baro Mon Pere?(My father) hajiya fatima ta amsa da  Lafiya lau yaso mu taho tare amma hakan be samu ba, ayyuka sun masa yawa, baka tambayi su Mardiya da sajeeda ba seka fara da tambayar babanka&  duk cikin rashin kwarewa ahausa take maganar. Mardiya da sajida kannen JAROOD ne su uku kawai mahaifiyarsu da mahaifinsu suka haifa duk suna gidan Aurensu.  Ai daman yanzu zan tambayesu Amour, yasu Mardiya da sajida ya kuma mamana? Cewar JAROOD da yayi mgnr yana murmushi. Hajiya fatima tadan hade rai sbda mgnrsa ta karshe.  Lafiya lau.. tabashi amsa agajarce. Murmushi JAROOD yayi yafi kowa sanin duk duniya ba wacce mamanshi ta tsana kamar Abokiyar zamanta, wato Amaryarta Hajiya Sadiya.  Yaya jikin naka? Har yanzu Anata Fama ko? Gashi shekaru nata tafiya kwance tashi asarar me rai&  JAROOD ya sadda kansa kasa yace  Ehe wallahi Amour har yanzu anata fama, insha Allahu, Allah ze kawo sauki&  jinjina kai kawai tayi nan da nan yanayinta ya sake sauyawa tace  Wallahi Sadiya tacuceni , ni nasan ita tamaka wannan mugun asirin, duk inda mukaje cewa akeyi itace tayi wannan kullin saboda taga ita bata taba haihuwa ba, seni nahaihu kuma nahaifa d ana miji, da mata biyu, shine ta kashemin namijin yadda bazaka moruwa, Allah ya isa tsakanina da Hajiya Sadiya, wata shara ar nida ita se munje lahira&  hajiya fatima ta karashe tana sharar kwallah. Cikin muryar kwantar da hankali JAROOD yace  Ki kwantar da hankalinki Amour, kinga fa ba atabbatar ita tamin asirinba, ni nadauka jarrabawar ubangiji ne kawai, insha Allah seya yayemin Amour bawanda yasan gaibu se Allah, duk lalube ake Cikin duhu&  humming kawai hajiya fatima tayi tace  kai yarone JAROOD nafika sanin wacece hajiya sadiya ta azabtar dani tin kana ciki ubangijine ya rubuta sena haifeka JAROOD &  JAROOD yace  Haka ne Amour toh Abar masa komi shi yasan yadda zeyi dani&  ya karashe yana kokarin danne damuwarsa saboda yadda yaga mahaifiyarsa nacikin damuwa.  shikenan Allah ya kawo mafita&  hajiya fatima ta fadi, daman ita macece me hakuri da saukin kai. JAROOD ya amsa da Amin.  Wanzan yacemin ansamu wani me maganin kou ? Hajiya fatima ta jefo masa tambayar. JAROOD ya amsa da  Ehe Amour, amma nagaji da ziryar neman maganinnan&   Me nema ai baya gajiyawa JAROOD, ka jure insha Allahu wata rana za adace, inata maka adduah bana bacci sbda kai wallahi& yanzu tinda nazo ma tare zamuje gun masu maganin&  Cewar Hajiya fatima. JAROOD yace  Toh shikenan Amour&  sukaci gaba da hira irin ta d a da uwa ç1k1n So da kauna.

Anan gidan yayi azahar tare da mahaifiyarsa sukaci abincin rana, se hira sukeyi taso da kauna, sukayi video call shida mahaifinsa ta wayar mahaifiyarsa. Se wuraren 3;pm suka bar gidan shida Malam Abdullahi wanzan , hajiya fatima taso sutafi tare gun maganin amma JAROOD yaki da kyar yasamu ta hakura bata biyosunba sun rabu Akan ze dawo zuwa dare.



 Wai har Ina ne gun me maganin? JAROOD ya tambaya malam wanzan dake driving tin Dazu sunata tafiya har sunyi tafiyar 1H amma basu isa ba. Malam wanzan yana driving yace  Mun kusa isa, ,, JAROOD yace  Wani irin gurine wannan amma dagani dajine kou ? Malam Abdullahi yace  Ehe amma ba daji sosai ba, karka damu ranka ya dade mun kusa isa&  cikin gajiyawa JAROOD yace  Wallahi nagaji da zakan motarnan..gaba daya ma nagaji da yawon neman maganinnan&  ya karashe kmr ze fashe da kuka.  Insha Allahu wata rana se labari, kwanan nan zaka hau Aiki kama hajiya babba ciki ka dawo kama hajiya karama ciki&  Cikin kwarin guiwa malam wanzan ya fadi hakan. JAROOD yayi murmushi kawai. Yace  Allah amince &   Amin.. Cewar malam wanzan.  Inka samu masallaci mu tsaya muyi sallah&  Cewar JAROOD malam wanzan Yace  Toh ranka ya dade&  tafiyar 2H sukayi suka isa wani masallaci acikin gari, sukayi packing da motar securities dinsa. sukayi sallar la asar suka idar sukaci gaba da tafiya acikin wani kasurgumin kauye dake Cikin zariya.  Tafiya kamar ta barin kasa.. Cewar JAROOD daya gaji da tafiyar, seya kwantar da kujera ya tasar ya rasa ma yazeyi dukya gaji saboda be saba tafiya me nisa ba a mota sede ajirgi.  Mun kusa insha Allahu&  Cewar malam wanzan. Jarood yaci gaba da mita  Ai da kawai jirgi muka hau dakasan da nisa har haka&  Malam wanzan de yayi shiru se basa hakuri yakeyi danya kula yagajine. Seda suka kara tafiyar 20mnt kana suka isa wani d an karamin gida Awani daji gabaki daya dajin gidanne kawai gida adajin, gabas da yamma bawani gida se wannan gidan, mutanen dake zaune awajen gidan sunyi layi sunfi mutane dari uku, kama daga kan jinsin maza da mata, amma gaskiya mata sunfi yawa sun baibaye ko ina ga manyan mutane tako Ina, anyi packing motoci sunfi motoci dari biyu ata farfajiyar bukkar gidan.  Wani irin gida ne wannan kamar gidan matsafa? Dan duk mutumin dake shuka alkhairi baze baro ç1k1n gari ba yadawo daji&  Cewar JAROOD daya fadi mgnr yana kallon gidan yana kallon malam wanzan. Malam wanzan ya bude baki zeyi mgna JAROOD yaga wani mutum ya fito daga gidan hannunsa rike da wani jan kyalle irin na tsafi. Haka kawai JAROOD yaji sam hankalinsa be kwanta ba gaskiya.  Gidan bada maganine ranka ya dade bakaga mutane tankanba&  JAROOD ya girgiza Kai yace  Gaskiya wallahi ban yadda da gidannan ba, nan gidan matsafa ne, dagani ba Aikin ubangiji ake shukawa ba a gidannan& ajuya mota kawai ka mayar dani Gidan Amour maza cikin hanzari kafin gari ya fara duhu kasarnan ba lafiya bace da ita&  malam wanzan ya kalli JAROOD yace  Haba ranka ya dade musha wannan doguwar tafiyar kuma kace mu juya? Dan Allah ka fita muje kashiga kagani bawai gidan tsafi bane gidan maganin gargajiya ne, shiga kawai zamuyi nariga naje jiya nakama mana layi yanzu shiga kawai zamuyi&   wallahi bazan shiga ba& dan Allah mu juya kawai wallahi nagaji , bazan kara dawowa ba gun wani neman magani daga yau wallahi, nariga na hakura& @ JAROOD ya fadi. Malam wanzan yashiga lallaminsa da lallabasa kan yashiga amma JAROOD yayi f1r yaki, wanzan yayi-yayi JAROOD ya tubure. Dole suka juyo da motar suka dawo kaduna ran Wanzan adagule, sam ba haka yasoba, yaso ace su shiga su amshi maganin yanaji ajikinsa za adace. Amma JAROOD yaki, hakan ba karamin batama wanzan rai yayi ba. A anguwar sarki sukayi sallar Magriba, awajen gidan kana suka nufa falon Hajiya Fatima atare shida JAROOD, daman Hajiya fatima tanata kiran malam wanzan saboda tasan inta kira JAROOD bezama lallai yana kusa da wayarsa ba, sbda shi ba ma abocin waya bane, amma yana kiran mahaifiyarsa sede itadin tafiso takira malam wanzan, tafi sabuwa da hakan. amma JAROOD inyaga kiran mahaifiyarsa yana dauka.  Malam ina

zakaje? JAROOD ya juyo ya kalli malam wanzan ya jefo masa tambayar, ganin yanaya binsa zuwa falon mahaifiyarsa.





This book is 1k 08101626484.





<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

FIL AZAL

<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

(Romantic and love story)



https://chat.whatsapp.com/CyBhsjJtnx7C5FWgP88xX1



SAADATUBINTUABDULLAHI
'<Øýß(Writer of Kyautar Allah)



This book is 1k 08101626484.

Free page3

Malam wanzan ya kalli JAROOD yasan dalilin dayasa ya masa wannan tambayar.  Zanje gun uwata ne nima mu gaisa ,ko angaya maka kai kadai keda Giwar
Showing 6001 words to 9000 words out of 159605 words