ranta. A wasu lokutan jarood baya ganin lefinta, ai tayi hakuri, hakurima me tsanani, amma de yasan be kamata tadinga gaya masa irin wad annan kalamanba, kodan darajar girmansa, a banza ya bata 10yrs. da ace tasan irin kunar da kalamanta ke masa a zuciya data rage musu tsauri garesa. Shimafa abun na damunsa kuma bashi yasama kansa ba ubangijine ya jarabcesa badan yana soba, bashi da yadda zeyi sede hakuri, a kullum yana rokon ubangiji ya sassauta masa wannan jarabawar yasan insha Allahu ze samu sassauci komin Daren dadewa saboda ubangiji maji rokon bawansa ne. Yafi 5mint tsaye kmr mutum mutumi yana kwallah, kana ya ciro wani kyakyawan farin kyalle daga aljihunsa se kamshi yake zubawa ya goge hawayensa. Jiki ba laka ya juya zebar dakin hajiya Zulaihat ta fito daga toilet din bayan taci kuka ta koshi ta wanke fuskarta a zatonta zuwa ynzu ya fice a dakin shiyasa ta fito. Dai-dai yana shirin fita tabi bayansa da kallo, ta saki wani tsuki ciki-ciki, batasan meyasa ba inde tana ganinsa se tayita Jin bakin cikin dake sata dole tayita tsuki, itafa wallahi daza a bata abun bugu zata iya masa bugun tsiya. Dai-dai Ya kai hannunsa handle din kofar dakin yaji fitowarta a hankali ya juyo, ya zubo mata idanuwa, a kallo daya ya fahimci kuka tayi data shiga toilet din, besan meyasa ba yana tsananin Jin tausanta sbda tayi hakuri, hakuri me tsanani dashi ba duk mace bace zata jure, amma ita ta jure saboda umarnin iyaye, shiyasa be tabajin haushinta ba a kan duk kalamanta garesa, Ada batayi masa wadannan kalaman a shekaru biyar dinnan ne ta fara masa wannan kalaman yasan hakurinta ne ya kare, kuma Gashi ba yadda zeyi sbda wannan Auren nasa da ita rabuwarsa zeyi wahala. idon Zulaihat dana Jarood suka sarke cikin na juna, Zulaihat Tayi hanzarin dauke idonta a kansa sbda bata jurar kallonsa eyes to eyes duk rashin kunyarta, sbda idanuwansa nada tsananin kwarjini. , ta karasa drawer din bedside ta zauna ta daura kafa daya kan daya, tana karkada kafa.  Zan fita.. Cewar jarood da yayi mgnr a gajarce murya babu karsashi.  Ina ruwana da fitarka ko inada case da fitarkane ni zulaiha? Me fitar Taka zata tsinana min? Abu daya nasani, nagaji da ganinka a dakina na kosa ka ficemin a daki malam.. mara Amfani kawai! Ta fadi Cikin tsiwa, tana wani yatsuna baki. Ba tare da JAROOD yace komi ba, amma kalmar ta, ta karshe ta bugesa, inda sabo yasaba. , ya juya ze bar dakin a karo na biyu, ubangiji ne kawai yasan me yakeji a zuciyarsa, samshi daman magana bata wani damesa ba, yanada miskilanci me tsanani irin na yayan gidan sarauta, sannan shi mutum ne me tsananin hakuri da danne abu a rai.  Uhm Daman ka dena wahalar da kanka a banza, dannasan bako Ina zakaje ba se gun neman magani& kayi hkri kawai ka dena wahalar banza saboda alamu ya nuna a haka zaka mutu&  jarood dake niyar fita ya tsinkayo muryar hajiya Zulaihat na fadin wannan kalaman, ba tare daya juyoba ya fice a dakin, wani dumi ya kuma lullubesa na zallar bakin ciki. Dabadan yanada karfin imaniba ya tabbatar da tini ya mutu da bakin cikin duniya. Direct ya nufa dayar kofar dazata kaisa part din hajiya Aisha jiki da zuciya ba laka. Tinda ya sako kansa babban falon hajiya aisha yaji wani kamshi me sanyaya zuciya ya cika masa hanci, se yaji kwatan bakin cikin daya kwaso a part din hajiya Zulaihat ya ragu a ransa. daman ita hajiya aisha yar kamshi ce ba a rabata da turare ako wani lokaci, domin itadin cikakkiyar yar medugurice kuma cikakkiyar yar duniya ce. Sak komi dake part din hajiya aisha haka yake a part din hajiya Zulaihat hatta da labulayyartama irin na part din hajiya Zulaihat ne, komi nasu iri daya haka Alhaji Jarood ya zuba musu ko ze chanza musu hk yake musu a tare yake musu komi hatta da motocinsu na hawa iri daya ne sak.  Ko ina tsaf-tsaf amma babu flower masu kayata guri&  jarood ya fadi a ransa se kara bin ko ina yake da ido kmr ya warke makanta, a zahiri ni senaga ko ina akwai flowers amma de bansan wani irin flower yake nufi ba bayan wadannan da Nike gani.  Inasan yara, dazan samesu sunfimun kaf dukiyarnan da Nike dashi&  jarood ya sake fadi a ransa, se kuma zuciyarsa tace  Kaida baka da Abunda za Asamu yaran ta sanadinsa? Kama denasa rai da samun yara& ka dauki kaddara, haka ubangiji ya tsara Maka rayuwarka tin FIL AZAL&  zuciyarsa ke basa wannan shawarwari& .. Hajiya aisha ce ta fito daga bedroom dinta, hannunta rike da wayarta, ita ta katse masa , shawarar da zuciyarsa ke basa. Tin shigowarsa taji, domin akwai abinda ke kara yana sanar dasu duk wanda yashigo part din, sannan ita hajiya aisha tasa wani abu da in jarood ya shigo zeyi kara, kara ta musamman. Hajiya aisha nada d an tsayi kadan tafi hajiya Zulaihat tsawo, sannan batada kiba kmr hajiya Zulaihat, ita hajiya aisha kibarta a kasa take, tanada mulmulallan duwawuka cikakku masu ban shaawa ga duk d ana miji. Bata da wani kyau a fuska itama harma hajiya Zulaihat ta dan fita kyau a fuska, hancinnan nata d an dus kmr an dasasa, Gashi tanada wawakeken baki, itama hajiya Zulaihat tanada babban baki amma sede na hajiya Aisha yafi nata girma,. Kwata-kwata ita hajiya Aisharma ko matsakaicin Kyaun a fuska bata dashi, zan iya cewa de ita mummunace ta karshe, qualities dinta daya, tanada mazaunai manya manya, shima dan tana Shan magani ne sukayi wannan uwar girman daman de akwai su ammafa ta kara dana shago, bakace waluk amma sede Tana bleaching na Innalillahi wa inna ilaihirraju un, wai Danma akwai Hutu da an samu matsala, ga kirjinnan nata a shafe, se d an kan nono tsuit ake gani ta cikin riga, kwata kwata bata da Nono, Kasancewar sanye take da doguwar Riga ta bacci red, wadda ta kwanta jikinta ya bani damar kare mata kallo. kanta babu dankwali, amma sede Tanada suma balefi, tadanfi hajiya Zulaihat suma da kadan. Ada tana Karin Gashi seda Alhaji jarood ya taka mata burki shine tadena, ta tsayawa gashinta, bleaching ma dan besan tanayi bane da tini ya taka mata burki, a haka yaganta fara ya aura, beyi tsammanin bleaching take ba, Kodan mashi baya wani kallonta sosai,.Hajiya Aisha nayin 2eyes da JAROOD ta washe wagegen black mouth dinta, labbannan nata baki suduk irin de yadda labban yan meduguri yake, amma ita nata bakin se naga yayi yawa. A kallah hajiya Aisha bazata wuce 33yrs ba amma Ido sekasha kota girma Hajiya Zulaihat sbda gabaki daya zubin tsofaffi gareta, ga bleaching ya cinye mata fata sosai. Tinda ta fito daga dakinta taketa bin jarood da ido Tana sakar masa murmushi irin na shu uman mata makirai. shima jarood yabita da ido , yayinda fara arta tasa yaji sanyi a ransa, Gashi data fito yaji wani uban kamshi ya doshesa.shiko a duniya yanasan kamshi ita kuma hajiya Aisha bata rabo da kamshi. Akasin hajiya Zulaikha da Bata da tunani Sena acita dan haka ko kamshinma bata damu dashiba.

 Barka da safiya Ranka ya jima, Alhajin Allah&  Cewar hajiya Aisha datayi maganar cikin iya magana, Sam muryarta bata da dadih, hasalima tanada babbar murya amma ta iya sarrafa harshenta, shiyasa A wasu lokutan take zama tauraruwa ga Jarood, Sam baya iya hanata abinda takeso garesa.  Barkade Hajiya Aisha yakike? Bade wata matsalar kou ? Cikin kissa Hajiya Aisha tace  eh babu ranka ya dade, tako ina a wadace muke a gidanka sede fatan Allah ubangiji ya kara arziki duniya da lahira& , ba abinda zamuce dakai se dumbin Adduah ,,Allah de ya kara maka lafiya&  jarood ya amsa da Amin, ç1k1n Jin dadih.  Mu karasa ka zauna ranka ya dade, mu karasa dinning dan daganinka kanajin yunwa.&  Hajiya Aisha ta fadi cikin ladabi kamar zata kwanta masa a kasa sbda kissa da kisisina da iya tafiyar da namiji.  Wlhi zan fita ne ina sauri,& daman nace bari in shigo ne in ga lafiyarku.. Cewar jarood daya karashe mgnr yana duba watch din hannunsa, yaga time ya tafi sosai.  Duk muna lafiya ranka shi dad e Dawisun Hajiya Aisha,,,amma se naga kmr bakayi break ba? Ko kayi de idonane be ganemin dai-dai ba? Ta karashe da tambayarsa cikin kulawa.  No, amma ba damuwa kawai zan wuce inna fita zanyi break a waje&  marairaicewa hajiya Aisha tayi tace  habade! Kanada mu kuma kayi break a waje? Meye amfaninmu? Gaskiya ka tsaya kayi break ko ba yawa kasa wani abu a cikinka, sbda nasan inka fita be zama Lallai ka tsaya ka kulamin da cikinka ba, nikuma Banasan ka azabtarmin da kanka da yunwa,,, nande ta dinga kanalnayesa da zancen kulawa, har tasamu ya amince suka isa dinning daman ta shiryama kanta abinda zatayi break dashi sannan tasan daman wasu lokutan a gunta yake break Tana sane da irin rikon sakainar kashin da hajiya Zulaihat kema Jarood ita kam sam bazata iya masa hakanba ko ba komai tana sanshi kuma ga daula Tana Ciki, taci hansin ta wanke dari tasaka. Seda tacika masa ciki taf da abinci, daman tasan yanasan dumamen tuwo shine abinci. Daya fiso yaci da safe, ita ma kuma tanaso sbda shi. Yaci dumamen Tuwon da farfesun kazar hausa, Sam bayacin kazar turawa kazar hausa kawai yakeci tin yana karami har zuwa yanzu, se naman dawisu yanaso sosai,. Se 11:10am ya bar part din hajiya Aisha sbda se jansa da hira takeyi, irin hirarnan ta nishadi har ya cika tumbinsa taf, sannan ta kula baya mood, dan haka shiyasa tadinga jansa da hira har tasamu ya dan saki ta sako hijjabi ta rakosa har compound din gidan, hannunta rike da wayoyinsa, tana masa hira yana murmushi amma fa a zuciyarsa cunkus take bawani armashi. Ba karamin girma gidan garesa ba, kusan get uku ne a gidan kafin suka karaso packing spaces, tako ina gidan ya tsaru , Gashi katoto, se shuke-shuke tako ina ga wasu part part wanda shi kansa me gidan be taba shigarsu ba. Ma aika maza se garzayowa suke suna zubewa suna gaidasa, a kallah ma aikatan dake gidan maza sunfi su dari. sbda shide namiji ne me masa gyara part dinsa, sbda hajiya Zulaihat bata gyara masa, se hajiya Aisha ke gyara masa tasa masa turaruka, shima se ranar girkinta, inko ba ita ke girkiba bata zuwa part dinsa, se tayi luf a dakinta tayita wayace wayacenta, daga ita se ubangiji sukasan dawa take wannan wayar, Gashi kullum wayarta na hannunta, ko ajiye waya batayi seda babban dalili, 24h takeyi a daki tana waya, wayar daseta kule a bedroom dinta take yinta.





This books is 1k 0542703718 Saadatu Abdullahi GT bank. 08101626484. Banda card VTU pls.





<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

FIL AZAL

<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß<Ø:ß

=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü=Ø–Ü

(Romantic and love story)



SAADATUBINTUABDULLAHI
'<Øýß(Writer of Kyautar Allah)



This book is 1k 08101626484.



Free page2

Seda ta rakosa har bakin motarsa dazasu fita a ciki. yayinda motocin dake jere a packing space din sukeda Yawan gaske, duk iya bin kwakwabina nakasa kirga motocin dake packing space din, yawansu yayi daga-daga da brain dina. Inada tabbacin acikin motocin akwai Wacce ba ataba hawanta ba. Abu daya na iya ganewa shine Yawancin motocin dake packing space din duk green da White se black, whites da black s din basufi a kirga ba. hakan ya kara tabbatarmin da yanasan green arayuwarsa. Tin kafin su karaso Malam Abdullahi wanzami ya isa inda suke, ya zube ya fara kwararoma JAROOD da hajiya Aisha gaisuwa. Kin amsawa JAROOD yayi , sede ita hajiya aishar ta amsa cikin isa, tanada mulki sosai, yan aiki nashan wahalarta, inda suke samun matsala kenan da JAROOD, Akasin hajiya zulaikha ita Sam bata da wulakanta d an Adam, kuma ita yadace tayi wulakancin sbda ita jinin sarauta ce, bayan haka kuma daga gidan masu Arziki ta fito,akasin hajiya Aisha wadda tafido daga gidan malam shehu, bahaushe yace dan talaka be iya samun guriba. hade rai JAROOD yayi yana kallon malam Abdullahi wanzan wanda yasha manyan kaya da nadin buzaye, hakan ya tabbatarmin dashi cikakken buzu ne, baka ganin komi a fuskarnan tasa se farar fatar idanuwansa kawai, ganin ç1k1n idanuwansa ya tabbatarmin dashidin ba yaro bane, Akalla ze iya kai 65yrz abunka da jikin buzaye sam baza kace yayi wannan shekarunba sannan yana tare da manyan mutane yanacin Arziki, shi kansa daka kallesa zakasan baya ç1k1n wahala yana ç1k1n daula jikinnan nasa ya kwanta luf-luf.  Baba banace maka dan Allah kadena tsugunnaminba, daga yau yazama rana ta karshe dan Allah ka girmeni ni yadace in dinga tsugunno maka bakai ba&  Cewar JAROOD dake mgnr rai abace, yafi sau akirga yana cema malam wanzan wato wanda yake kira da Baba yadena tsugunno masa amma sam yaki denawa,. Ganin ransa yabaci yasa Wanzan mikewa cikin hanzari hadi dacewa  Allah ya huci zuciyarka ranka ya dad e, baza akaraba&  hajiya aisha tayi caraf ta amshe da  Ai dole ne ya tsugunna maka ranka ya dad e saboda shima ai yasan matsayin ba daya ba&  wani wawan kallo JAROOD yabita dashi nan da nan kuwa ta shiga hayyacinta tayi kasa da kanta.  Agurinkine matsayinmu ba daya ba, agurin ubangiji ba wanda yafi wani, se wanda yafi tsoronsa, wallahi matsayin Baba agurina ya wuce tunaninki, dan haka kar in kara Jin maganar nan abakinki&  JAROOD ya karashe mgnrsa da muryar gargadi, idanuwansa nakan hajiya aishar. Hajiya aisha ta matukar jin zafin yadda JAROOD ya wulakantata agaban wanzan, daman itafa wallahi tincan ta tsani malam Abdullahi wanzan, ko anguwa zataje bataso JAROOD yace shi ze kaita, gaba daya ta tsanesa, bata taba tsanar wata halitta kmr shi ba aduniya, ta rasa dalilin dayasa ta masa wannan muguwar tsanar, amma ta danganta hakan da yanayin yadda JAROOD ke tsananin sanshi ya basa mukamin dakosu matansa be basu wannan mukaminba. Da Anyi magana kuma yace wai tinda yataso yaganshi Agidansu , tin Malam Abdullahi wanzan nada 7yrs yake tare da iyayen JAROOD A Agadez , kuma yakema mahaifin JAROOD me girma sarki hidima, har JAROOD ya girma ya mallaki hankalin kansa yazamana bashi da wani babban abokin dayafi Abdullahi wanzan, agidansu aka koya masa tuki, har yazama dreva din JAROOD yanzu, kuma babban Amininsa yafi kowa sanin waye JAROOD, ko iyayen JAROOD basusan wani abu akan JAROOD ba yadda Abdullahi wanzan yasani, iyayen JAROOD suna tsananin san JAROOD hakan ne yasa suke san Abdullahi wanzan.  Bazan karaba insha Allahu Ranka yadade&  Cewar Hajiya Aisha data danne bacin ranta ta fadi hakan cikin kwarewa a kissa. Batare da JAROOD yabi takanta ba sbda ta bata masa rai, ya mika hannu kawai ya amshi wayoyinsa a hannunta,. Wanzan ya amshi wayoyin a hannunsa shima beji dadin yadda JAROOD din yay1ma matarsa ba agabansa. Suka isa gaban dankareriyar motar dazasu fita da itan sabuwa dal kalar green se sheki takeyi tana walwali me kashe ido. Tasha bakin glashi. Wanzan na kokarin bude masa gaban motar JAROOD da kansa ya bude yashiga sam baya zama abayan mota inde malam din kejansa sede yazauna agaba saboda tafiya suke suna hira shida babban Amininsa.  Adawo lafiya ranka ya dade& Allah ya tsare&  Cewar hajiya aisha daketa sadda kai tanaso ta wanke lefinta. Ciki-ciki JAROOD ya amsa da  Ameen.. malam wanzan ya rufe masa kofar, ya zagaya ze nufi gefen dreva hajiya aisha ta watso masa wani kallo na kiyayya tanaji yanace mata  Semun dawo ranki ya dade&  ta masa banza ta juya ta nufa part dinta, tana tafe tana tsuki tana fadin.  Dreva yafi matanka na sunnah inba JAROOD ba an ina ake wannan gangancin& Mtwsss Allah de ya kyauta&  tana tafe tana matsifa ita kadai harta shige part dinta.



Malam wanzan yashiga yaja motar daman a kunne take Sbda AC, inde zasu fita toh se an kunna motar tayi kusan 30mnt akunne Se AC yayi sanyi a motar sosai, sbda Malam wanzan yafi kowa sanin yadda JAROOD kesan sanyin AC, ada malam wanzan inya Tuka JAROOD a mota na tafiyar 1H se yayi zazzabi saboda mugun sanyin dake Cikin Motar, tin be saba ba, yanzu ya saba da sanyin AC din. Yaja motar suka fice agidan motar yan sandan dake tsaronsa nabiye dasu abaya. JAROOD ya kalli malam wanzan daketa tuki cikin kwarewa da nutsuwa ya matukar iya tukin mota, se sanyin AÇ kawai ke aiki a motar da kamshin turaruka, turarukan dake gaban motar sunfi kala goma, duk malam wanzan ne yasiyesu yasa sbda yasan JAROOD nasan kamshi.  Yanzu Ina zamu? JAROOD ya jefoma Malam wanzan tambayar.  Zamu fara zuwa gün Giwar sarkine, takosa taganka wlhi ranka ya dade& takanas fa saboda kai tazo kasar nan&  (Se yanzu na fahimci har yanzu hausa bata gama ratsa malam wanzanba, dole dayayi magana ka fahimci shi ba cikakken bahaushe bane)

JAROOD yayi murmushi yace  Nima nakosa in ganta nasan saboda taganni tazo ka_ar ai&  malam wanzan yace  Ana ma magana& Ai ranka yadade Giwar sarki na tsananin sanka najima banga soyayyar uwa da d aba kmr Soyayyarka da Giwa, Allah de yasa ku rabu lafiya&  JAROOD ya amshe da  Amin ya Hayyu ya kayyum&  JAROOD yaci gaba dacewa  in muka bar gidan Amour (Love) Ina
Showing 3001 words to 6000 words out of 159605 words