ba
Jikinta a sanyaye kuma a dari-dari kirjinta na
bugawa 'ta shiga gidan ta yi sallama da
dakusasshiyar muryarta da kuka ya dusheta tun
daren jiya ba a amsa mata ba, ta shiga tana jin
motsin ruwa a bandaki ta " shige cikin‘dakin.
Hajiya Kaka na yashe kan dardumarta da carbi a
hannunta tana barci ta tsallaketa ta shiga can
uwar dakinta ta haye gadon ta yi kwanciyarta, ta
yi lamo, barci ya gagareta,
tana jin Hajiya Atine wato‘kanwar Hajiya Kaka da
suke zaune tare a gidan tun mutuwar nata mijin
yaranta mata sun yi aure kowacce- na gidan nata
mijin. Amira'na kallon Hajiya ta shigo: tana
laluben mayafinta a' gefen gadonda alama fita
take shirin yi. Salati Hajiya Atine ta yi cikin
razana jin ta taba hannun mutum a da‘i dai
lokacin Amira ta ji wata irin faduwar gaba‘harsai'
da hanjin cikinta suka juya. ‘ Wayé anan.?” "
Hajiya Atine ’ta fada cikin murya mai cike da
tsoro Yan da Amira taga ta sandare a tsaye
muryarta‘ na rawa ta san ba karamar firgiti ta yi
ba, dan haka cikin Sauri ta ce ‘ “Nice Amira.”
Gudun kada hajiya Atine ta qarasa ‘ sumewa.
Hajiya Atine ta .matso da alamun tsoron da take
ji ya rage Sai dai mamaki.
“Wacce Amira.
Ta fada lokacin da take sake haske fuskarta
hasken rana daya hudu ta cikin windon dakin ya
taimaka mata Wajen ganin fuskar Amira ita kam
ta kasa furta kowacce kalma salatin da Hajiya
Atine ketayi da tafa hannaye shi ne abin da ya
farkar Hajiya Kaka daga gyangyadin da take ta
mike da sauri ta nufi cikin dakin da zaninta a
hannu take tambaya; ' meya
faru. Hajiya Atine ta dora da cewa
“Mai zan gani.?” Hajiya Kaka sai tambaya take yi.
Shashshekar kukan Amira ce ta
matsawa sai dai matsalar rashin gani sosai yasa
Hasken daya shigo ya kasa wadatar da ganinta
ga abin da Hajiya Atine ke nuna mata.~Ta juya
ga Hajiya Atine
“Wa ye haka ne Atinc kin san ba gani nake sosai
ba, a dakin nan kin ji gaya min - wacece ta shigo
mana gida kike ta nuna min kina nanata salati.”
Haji Atine ta ce
“Au baki ganeta ba Amira ce fa ‘
amaryar da muka kai daren jiya.” ‘ Hajiya Kaka ta
matsa. “Amira dai ta wajen basiru.”
Hajiya Arine. tace Eh ita ce.”
Hajiya Kaka ta ce “Kema dai Atine idon naki yaya
dai, mai zai kawo Amira cikin gidan' nan ki duba
dai da kyau yanzu_ haka cikin yaran Maikudine
kin san suna‘ kama. Ta sake matsawa ta kama
Amira.
“Wacce yarinya ce? Yi mgagana.” Amira cikin
murya kuka ta ce.nice Hajiya Alhaj Saminu
yasakeni
.jiya ta rafka salati ‘cikin daga murya daga
karshe ma sai ta fashe da kuka.' ‘ ‘
Cikin muryar .kukan take fadin. “Wannan yaron
ya cucemu Allah ya isa tsakanin’mu dashi, yanzu
a ce a kai yarinyar jiya jiyan nan ya sako mana
itasaboda shi ba dan arzi'ki bane badan wannan
abin kunyar da me ya yi kama.”
Ta ja ‘ajiyar zuciya ta face majina ta dubi Amira
wadda tun da ta soma maganar take razgar
kuka? zuciyarta kamar zata faso a Kirji ta fito
abin da yafi yi mata‘daci a yanzu yaya
mahaifiyarta zata ji , idan ta samu Wannnan
mummUnan labarin.?
Tana tausayin kanta tana tausayin mahaifiyarta
domin tana da tabbacin ba bayan itakanta babu
wanda zai ji dacin abin da ya sameta sama da
Ummant
Hajiya Kaka ta, ce“Me kika yi maSa haka Amira
ya sako ki
Amira tayi shiru kawai ita kadai tasan irin dacin
da take ji cikin ranta.
Hajiya Kaka cikin fada lna miki magana kin ‘yi
min shiru.”
Amira taji tamkar ta shake tsohowar .har zuwa
barzaho ta Bita da wani irin kallo, ‘Duk bake kika
janyo ba, ki ka dauke“ni kika kai ni wajen
malamin da babu imani a Zuciyarsa ya cuceni ya
cuci rayuwata ya rabani da abinda duk wata ‘ya
mace take tun Kaho ta kai gidan mijinta kin yi
sanadin Shiga rayuwata a biyu babu.”
Abinda Amira ke fada ke nan a cikin zuciyarta shi
ma kuma abin da ya dace ta fadawa Hajiya Kaka
a daidai wannan lokacin da take sauraran
muryarta na daka mata tsawa sai dai furtar da
furucin tamkar BANKADAR mafarin sirrin
zuciyarta ne da ya dace .ta barwa cikinta ta
shanye' shi ita daya domin budeshi sai yaf1 sakin
da Alhaji Saminu' ya yi mata ciwo a zuciyar
iyayenta kamar yanda ya zame mata dacin
rayuwa da ' ba zai taba gogewa a rayuwarta.
Hajiya Kaka ta jijjiga kafadarta.
“Ki yi magana mana, Amira kin barni da zulumin
zuciya ina ta magana sai zare min idanu kike yi.”
Amira ta saki rushewa da kuka.
“Hajiya. ban mishi komai ‘ba menene zan yi masa
a daren amarcina jiya da yau
kadai kawai‘ da asuba ya shigo ya ce ya sake,
ni.” hajia Kaka ta dafa kafadarta ta 'yi shiru.
“Amira kwantar da hankalinki dani yake‘zancen, ai
zama bai kama ni ba, bari na, canza zanin jikina.”
Amira na kwance ciwon kan yana ,. dada tsanani
tana kallon Hajiya Kaka ta canza kayan jikinta‘
har da murtsika mai a fatarta ta daura dankwalin
ta lullufa mayafinta ta deBo kudi da goronta ta'
zuba a ‘yar‘ _ Karamar jakarta ta dauko flask cike
da ruwan zafi ta ajiye agaban Amira. . “Ta shi
maza ki sha shayi yanzu zan je wajen malam
Balarabe na gaya masa ai sai kin koma dakinki,
idan ma matarsa ce ta yi masa asiri zai karya
shi, ta shi maza ki daina‘; kukan da ni suke
zancen.”
kuma ya yi shi da ya taimaka miki da addu’a har
sai da a kayi auren ya kuma mutu. - Amira ta
katse da cewa, ba shi‘ ya sa na
aureshi ba, da ba zata iya bayyana mata‘
gundarin aika ,aikar da ya yi mata.ba,‘ wannan
sirrin zuciyarta ne. Hajiya Kaka ta Ja salati.
“Wato madallah, turke zaki yi masa ai ya taimaka
kwarai wannan sakin dai
ina ga matarsa da matsafa ta hada ki ta yi nata
shirin ranar da kika tare.” ’
Hajiya Atine ce ta katse mata zancen. Hajiya
Atine ta ce.
“Ai ni hajiya tun da naga Amira na ji zancen saki
cikina ya murda nake ta tsuga gudawa dana flto
na ajiye buta sai cikina ya Kara hautsinewa sai
yanzu na samu kaina amma Hajiya wannan
lamarin ba na zama ‘ bane, a kirawo Basiru kawai
ya je ya sami
mijin adaidaita ta koma dakin mijinta tun kafin
jama’a su farga da zuwanta a zo a yi mata
sharrin da zata kasa aurowa a gari.”
Hajiya Kaka ta ce, “To ai aikin gama ya gama me
dungurumgum ya‘yi mata saki uku.”
Tare da hada baki ita da Hajiya Atine suka yi
salati. Amira ji take yi duk surutunsa ya cika
mata kunne burinta su flta su barta ta samu
kadaici ko dan ciwon kan da yake
barazanar tarwatsa kwanyar kanta.
* * * *-
Malam balarabe lokacin da ya gama biyan
bukatarsa da Amira ya shiga cikin wani irin
yanayi na fargaba cike da kokwanton sabanin
yadda ya Saba ‘yi a can baya duk yarinyar da ya
yi amfani da ita baya_' sake jin wani abu da zai
daga
kanta yawancinsu ma suke sake kawo kansu gare
shi fargaba daya shiga ransa. '
a ‘Saf1yar da yake cikin ketawa Amira mutuncin
ya ji wani’ motsi na alamun an. shigo dakin sai
dai halin da yake ciki bai bar" . shi, ya gane
kowaye ya shigo ba; tantama' yaga abin da yake
aikatawa; '
Dan lokacin da ya‘ gama samun ; nutsuwa da irin
kasalar data rufeshi ‘ wadda tabaWa Amira,
damar gudawa 'daga gareshi duk DA bai samu
danar tsareta ta gyara jikinta dagaBacin da yaga
ta yi da jini ba.
A hankali kuma barci mai dadi ya yi awon gaba
da shi sai dai bai ji ma yana yin ‘ barcinba ya
farka a wartsake yanajin wata. irin faduwar gaba
domin ' Kamshin turan daya mamaye dakin tun
daga "
Nuradderr yake saka ran zuwanshi a
. yau din tun da ya dawo daga tafiyar da ya yi
'sun yi maya da shi ya kuma ce masa zai zo.
yau din sai dai bai yi zaton shi cikin irin wannan
duku dukun safiyar ba.
, Hankalin shi ya ta shi ainun yana saBa
babbar rigarsa ya fito kofar gida ya tarar da
Malam Yahya zaune akan Kujera da .
alkur’ani a hannunshi yana karantawa da alama
har yanzu almajiransa basu dawo sun shiga
makarantar ba. Ya kwalawa Malam Yahya kira.
Malam Yahya ya taho ya mika masa hannu suna
gaisawa Malam ya rike hannunshi ya jashi zuwa
can gefe in da yake ' tabbacin babu mai jin abin
da za su tattauna cikin murya mai kama da rada
ya ce. “Malam Yahya Nura ya zo gidan nanne? ‘
Malam yahya ya ce
“Ya zo
“Ya zo kace?"’ ,
Malam ya fada hade da zaro idanuwa ‘ waje Tuni
Malam Yahya ya shirya abin da zai fada masa
domin yana gudun sharri da' mugun hali irin na:
Malam‘ a kan son rufawa malam Asirinshi zai iya
yiwa Nura koma menene saboda haka sai ya ce
“Nura ya zo amma fa an so a yi abin kunya,
Malam Allah ya kiyaye, tare da shi muka shiga
soron na ce bari na yi masa iso kawai sai na
bankadowa idona abinda yafi Karfin ganina.
Na dawo na ce masa kana barci sannan ya shiga
motarsa ya tafi
Malam ya sauke a jiyar zuciya har da kirji ya
lumshe ido ya bude su hade da
hamdala. ‘
malam yahya ya Ce, “Sai dai fa adaina wannan
harkar malam an girma akwai yara da sUrukai bai
daceba, ma yanda. yarinyar ta fito banda ba yara
a kusa Aida sai aji kunya- . Malam’ya hade
fuska. “To insha Allah za a kiyaye gaba Allah ya
sake rufa mana asiri Malam Yahya ya biShi da
kallo kawai ‘yadda yake wani ‘cin-magani Cike
da kwarjini idan ka ganshi sai ka ramse irin
malamin nanne masu tsoron Allah wadanda suka
san hakkin ‘yan uwanSu babu cuta‘ba cutarwa a
zukatansu. Malam kam Akuya ne kawai da fatar
Kura.
******
Matsanancin ciwon kai ne ya hana NUradden
sukuni tun da ya fito zuwa
shagonsu dake kan titin Aminu kano dole ya mike
ya koma office dinsa dake kusa da shagon nasa
sai dai zaman nasa anan din ma ya kasa samar
masa da jin dadin yanayin jikin nasa take ya
yankewa kansa shawarar ' ya koma gida
ya'kwanta a makeken gadonsa . k0 ya samu
barci.
Ya kulle office din ya nufi gida.
Tun kafin 'ya karasa shigowa gidan yake jiyo
muryar Bahijja tare da‘ wani‘ wanda bai shaida
kowaye-shi ba. Hira suke yi suna kyakyata-
dariya duk: sallamar da yayi ba wanda ya‘ jishi~
Bare ya . masa. '
Ya sanya Kafarsa a tsakar gidan idanuwanshi
suka yi~ karo da dattin ‘ tsakar gidan ‘kayan
wanke Wanke robobin almajirai watse duk ganin
haka ya
bai iya gigin shiga in da take ba saboda baya son
ganin abin zai taba zuciyarsa wanda ya jima da
sanin zuwan nasa ba zai yi amfani ba, tun da. k0
ya tsawatar ba zata ji .ba. - Sai da ya ji tamkar
ya koma da baya amma yanda yakejinnan nan
fita wani gurin ma aiki ne a tare da shi.
Yasa mukulli ya bude dakinsa ya shiga ya kwanta
duk da haka yana iya jin “ hayaniyarsu tamkar a
tsakiyar kanshi ji yake yi kamar ya ta shi ya je ya
kore su amma ba zai iya jure hayaniya da Bacin
ran Bahijja ba.
Haka ya hada da addu’ar Allah yasa .barci ya
dauke shi. .
Bai jima da kwanciya ba ya ji an turo
qofar an shigo bai iya k0 motsi ba bare ya daga
kai ya ga Wanda, ya shigo din.
‘ “Nura menene haka kawai dan ka Shigo gida ka
ganni dasu Salfu sai kafara fushi har ka jima da
shigowa baka neme ni ba.'
Kalamanta sun sa ya gane ita ce ta shigo Bahijja.
Bai tanka mata ba saboda yana jin kamar ba ma
zai iya daga'kansana ya yi magana ba, ta sake
tunzura‘jin ya yi mata shiru
“Sai dai duk abin .zakay1 ka yi amma ba zaka
rabani da mutane a’ mutum....
Bata Karasa abinda .take shirin fada ba ya daga
mata hannu hade da cewa.
“Naji yi hakuri dan Allah banjin dadi ne kije kuyi
hirarku
Ta tafa hannuwa ta murguda baki. '
“Ta fita
Ta‘juya ta fita tukukin Bacin rai da
maganganunta suka cika masa kai' suka hana"
shi samun sukunin da suka tunzora zuciyarsa har
ya samu kwarin gwaiwar mikewa da adu,a yake
jin kamar Bazai iya ba. Ya dauki mukullin
motarsa ya fita da sauri saboda jirin da yake
dibarshi sama sama.
Tana hangensa yanda taga idanunshi sun canza
launi ta dan firgita da yanayinshi. Ta san bai
wuce ya ce zai shigo da kanshi ya kori su Sabi’u
ba, ita ma ta gama shirya maganganun da zata
fada masa muddin ya ce zai ci- mutuncinsu ga
mamakima‘kawai sai ta ga ya nufi hanyar fita‘
'daga gidan‘ihakan yafiye mata dan haka. bata bi
ta kashi da abinda ya dameshi ba dukbasu sha
mata
kai ba.
‘kawai yake sai ta miketa kara masa karfin fanka
ta ce, 'tana zuwa can kicin dinta ta nufa ta dauko
Kifi wanda ta san yana mutukar so ta wanke bata
bar kicin din ba sai da ta kammala yi masa
farfesun kifin ta fito ta tarar tuni ya yi nisa a
barci ta ce ‘ “A yi ta aiki ba hutu zirga zirga ce
kawai cikin ranar nan ta haddasa masa .ciwon.’ ‘
Ta fita ta barshi tana Karasa ayyukanta na tsakar
gidan kiran sallar la’asar ne ya farkar da shi daga
'barccin da‘ ya dauki lokaci , yanayi tamkar
wanda. ya sauke wani nannauyan kaya haka "ya
ji kanshi ya yi masa sayau ba‘ciwon kai ba
alamunshi. sai ~kasala datamamayeshi. . Ya
mike hajiya ta shigo tana cewa. “Yanzu nake
shirin‘ na tasheka ashe ma
ka farka.”
Ya mutstseke idanuwansa. “Kiran sallah na ji.”
Hajiya ta ce “Idan ka idar da sallar sai ka zo kaci
abinci kasha magani ga shi can na ‘bayar an siyo
maka.”
Yace “To Inna ciwon 'kan ma ya sauka.” ’
Ya fita yana alwala ita kam tana shimfida
dardumar sallah.
Ya fita zuwa masallaci ya zo wucewa ta Kofar
gidan su abokinshi Yusif Wanda aminin shi ne da
kafin ya yi mishi gargade akan malam Balarabe
tuni ya zame tsakaninsu dagawa juna harmu ne
kawai yau da Nura ya hangoshi da sauri ya nufe
inda yake sannan ya mika mishi hannu suka
gaisa ya ce “Kai ma masallaci zaka nufa.”
Cike da mamaki yusif ya amsawa Nuradden suka
nufi masallaci tare suka yi sallah suna taBa hira
duk da mamakin da yake dankare a zuciyar Yusif
domin ya fitar da ran a kwai ranar da zasu kuma
yin irin wannan zaman tare.
*****
Hankalin malam balarabe ya gaza kwanciya tun
ranar daya ketawa Amira mutunci.
Da yake malam Yahya ya sanar da‘ shi Nura bai
gamsu ba zuciyarshi ta shiga ‘zargin da wasi
wasi musamman ’ cikin kwanaki nan domin bai
sake saka Nura a idonsa ba har ya yi tafiya ya
dawo ya wuce Abuja ya sake dawowa k0 da
wayarshi ma bai kumaji ba. .
Abin da Nura bai taba yi masa ke nan ba. Nura
baya kwana da wuni bai ziyarce shi
ba, idan kuwa '"Zai 'yi taflya sai ya zo ya sanar
da shi, ya kumayi masa alkairi' mai tarin yawa,
haka ida baya gari baya gajiya da turo miShi kudi
ta account din shi sannan idan ya dawo Zai zo
ya sanar da'shi ya hado masa da , tarin tsaraba
mafi yawancin turarukan da' yake amfani dasu,a
jikinshi " masu tsada Nuraddcn ne ke kawo masa
abin
’" da ya tuna wanda ba zai manta ba, tun ranar
da ya zo yana tare da Amira bai sake zuwa' in
‘da yake ba, k0 ya yi masa waya k0 ya tura
masa da kudi tsawan wata hudu, ke nan, gashi
duk iya bincikensa na sihiri ya kasa gane Nuran
ya gansu k0 bai ganSu ‘ba, abu'daya yake
ganewa ya Shigo 'gidan Wannan kuwa Malam
Yahya ya gaya ‘ masa
' Abu na ’biyu Amira data tsaya mishi cikin rai
tsayuwa irin wacce babu wata diya
dibarsa abin ya sani na gaskiya tun ranar da ta
soma zuwa ya gama hada mata aikin da Alhaji
Saminu zai aureta sauran zuwan ma Kirkirar
matashi ya yi ne dan ya samu biyan bukatarsa ya
kuma biya, ita' ma ta yi aurenta in banda radun
zuciya mai zai sa ya damu da tunaninta. .‘yana
jin tausayinta har cikin ransa baya son ya sake yi
mata wani abu na cutarwa bayan wanda ya yi
mata a baya, da wannan yabar zuciyarsa tana
walagigi cikin son ta da ya kasa ganewa menen
zuciyarsa ke damunshi da shi.”
Wata safiyar Lahadi, ce Malam ya je dauren aure
wani dan abokinsa ' tare‘ da jama’ar shi dake
take bayansa, ,jama’a da. dama wajen dauren
auren Kokari suke. su-
gaisa da Malam wadanSu kuma son ganinshi
kawai suke ido da saboda shahara da,
' Sunansa ya yi ‘yawa kunnuwan jama’a da
dama. da kyar‘ya samu hanyar fitowa daga
wajen dauren auren suka shiga mota tare da
jama,arsa har direban ya- soma tafiya ya ce,
Gidan Nuradden muka nufa.’ 'Direban ya ce “An
gama da‘ izinin allah
Nuraddcn bai dawo gidan ba sai dare bayan-yayi‘
sallar isha’i' a masallacin“; '; unguwarsu. tare da
abokinsa; Sun taBa hira kawai ya ji yana fargabar
zuwa gidan ‘kamar..yanda ya 'faru da‘ zuwan
yanayin daya tsinci ‘kansa ba mai dadi ba ne,
baya sha’awar abin da zai dawo '"da shi' duk da
bai son komawa gidan haka ya daure domin
matsalar kara kaiWa daren zata janyo masa;
matsala tsakaninsa DA bahijjah
Falourn ya ,cika taf da kartin almajirai ga kuma
na bakin taga suna leke suna hayaniya da shan
rake.
“Allah ya kyauta.” -Shi ne kadai. abin da ya iya
furta mata a sanyaye ya' nufi dakinshi dama ba
shi.da matsalar yunwa domin ya gama ;.,cika
cikinsa gidan Ummanshi ynna jiyo kauri kaurin
abinci a kichin yasan girkin yau yasha wuta.
Da mukulli ya kulle dakinsa domin baya bukatar
wasu maganganu na Bacin rai.
,Bahijja kuwa bakaramin tashin hankali ta ahiga
ba lokacin 'da ta murda kofar dakin Nuradden ta
tarar da shi a kulle da mukulli.
Nura bai taBa rufe mata kofa ba ta tabbatar kuwa
yana cikin domin ta ji zuwansa hankalinta ya ta
shi kwarai domin
kasa ishashsen barci ta yi saboda bata san
irin hukuncin da Nuran zai yanke akan ta ba, tun
da ya‘ soma mata da irin wannan salon.
.. Tana mutukar Kaunar Nuradden abin da take
gani kawai shi din mai tsauri ne da ‘dorawa
kansa damuwa a kan 'abin da take gani kankani
bai taka kara ya karya ba.
Barci ya kauracewa idonta juyi kawai take yi tana
jin mutukar kewarshi da tunanin hanyoyin da zata
bi ta mallaki Nura a tafin hannunta ta juya shi
son ranta ya yi sanyin hali kamar ruwa a wajenta.
Bayan ta idar da sallar asuba bata‘ ‘ koma barci
ba sanin ko ta koma‘ ‘barcil
n ba dauketa zai yi ba saboda tukukin da radadin
da zuciyarta ke yi, sai ta tsinci kanta da ‘ share
gidan dama ta san abinda Nuradden ke, so ke
nan sharar waje 'ta somayi tas amma' ta kasa
tsaida ita a kanta tana"ganin matsine kawai da
sa mutum aiki irin na Nura ya
tsinci kansa da faduwar gaba domin bai san da
abin da ta shigo DA ita ba yanda yaga murmushi
ashimfide a fuskart yasan yaya zuciyarsa har ya
karBa katon farantin dake hannunta shi ma da
murmushi a fuskarshi ya tsaya da idanunwansa a
kannt- yana yi mata shu’umin kallon nan mashi
wani irin son Bahijja yake fisgarshi kamar yau ne
ya soma ganinta komai nata sha’awa yake bashi
ya ajiye kayan a tsakiyar dakin hakurinsa. yakére
har sai da ya shafi gefe fuskarta a hankali ya
furta.
“Kin yi kyau amaryata. mena samu safiyar nan ta
yau.”
Ta riko hannunshi. ‘
“Farin cikin _samunka cikin koshin lafiya shine ya
sani cikin annashiwa ka hango kyaunane?
HirarrakinSu cikin faranta wa juna da nishadi suke
a haka Nura ya yi break past cikin annushuwa
komai ya shafe a zuciyar Nura-' dama shi mitar
Bahijja ce baya so kuma yaga bata yi masa ba. '
Ita ma ta fahimci‘ abinda baya so din kenan tana
shigar da wasu sirrikane a wajen‘shi sam
Showing 24001 words to 27000 words out of 79369 words