mamaki kamar _ ‘yanda ta
shayar da shi. . Yasa .hannu ya fizgo towel din
da ya rage saura a jikinta ta hade waje daya ta .
takUre jikinta. '
“Kin rokeni, zan kuma rufa miki asiri kamar yadda
kika bukata ,ba Zan BANKADA sirrin da kika
sanar da ni ba, sannan zan hukuntaki dai dai
laifin da kika aikata" min yan da a gaba ba zaki
sake tunanin shiryawa Wani abin da kika yi min:
ba.” “
Kafin ta yi wani yunKuri ya soma dukanta kafa da
hannu tana guduwa yana tarar da ita har ta
durkushe a gabansa tana ,.
fatan mutuwa ta, dauketa a daidai lokacin
kota huta da wannan bala’in daya yiwa rayuwarta
shigar sauri sai da ya“. gaji dankanshi sannan ya
deBo kayanta" ya yi watsi dasu a adaren amarcin
Sannan ya ce' ki fita ki barmin .gidana yanxu ba
sai’gari ya Waye ba, na .sake~ki ‘ saki‘uku.
_Wani uban ihu Amira, ta kurma wanda ita’”kanta
bata san lokacin datayishi ba tun a'farkon sa in
Sarsu. Ni’ima dake killance kan darduma
tanagabatar da sallolin nafila saboda rashin
'barci da ya addabeta. Tun lokacin da ta ‘ fahimci
Alhaji Saminu ya shiga dakin Amaryarshi wani irin
azababban kishi wanda bata taba"tsammanin
tana da shi ba ~ya ta so mata ya kuma hanata
rintsawa. , .. , Ta yi kuka iya‘yinta sannan ta
yanke shawarar dauro alwala tayi nafila
da addu’a k0 ta samu sassaucin zuciyarta tana
cikin sallar ta soma jin maganganu sama sama
duk da suna da tazara tsakanin Bangararoin ta
soma zargin tabbas ba lafiya lokacin da ta idar
da sallar ta ji kamar a na kuka har ta yanke
shawarar ta je wajen Amira taga me ke faruwa?
Domin tana da tabbacin daga Bangarenta wannan
ihun yake .~ tashi. a ‘Wata zuciyar ta gargadeta
mace a dakin mijinta tana tare da shi ke mai zai
kai ki cikin dare ki ganowa idanuwanki abin da
zai dameki
Tajuyo a hankali zuwa bakin gadonta sai dai bata
jima da zama ba ta jiyo wani irin ihu da ta
tabbatar ba lafiya ba
Ta mike da sauri Ta
mike da sauri har da sassarfa tana dada
karasowa Bangarcn nasu, :kukan yana dada cika
mata kunne ta sOma buga Kofar. .
‘A razane dai dai lokacin Alhaji Saminu ya
watsawa Amira kayanta. ‘ ' “Sai ki saka tun da
kin yi mana gayya,
uku bana bukatar ki sake yin k0 da minti. goma
sha biyar a cikin gidan nan ma kin ji', na fada
miki.” " ‘ '
A hanzarce take saka kayan ba a'daina' bugun
kofar ba sautin kukanta da zubar
hawayenta basu tsagaita ba. .“Wuceki bani waje,
ban lamunci ki
waye gari a cikin gidan nan ba, domin ban- san
irin Abinda zaki aikatamin ba kafin“ wayewar
gari.”
Tana gaba yana bin"bayanta da wadannan
kalaman har zuwa bakin kofar“
dakin' shi.’ Ya murda ya '_bude Amira na a'gefe,
ya murda kofar Ya bude Ni’ima‘ta ce
“Abban Ammar lafiya kuwa? ni duk hankalina ya
ta shi, kuka daga Bangaren nan ya cika gaba
daya gidan.”’
Amira ta fita da sauri bata jira amsar da zai bata
ba domin zuciyarta ta kekashe da soron duhun
daren da take Kokarin fuskanta a titi burinta kadai
ta fita .daga gidan kamar yadda ya bukata ganin
tozarcin da yake yi mata a daren amarcinta gara
ta fita ta fada hadarin da zai gama da
ragyuwarta ta huta da wannan ranar da tun da ta
mallaki hankalinta a ka sanya mata suna ranar
farin ciki rayyuwa, ranar da zata aure wanda.
zuciyarta ke so ta zame mata ranar bakin ciki a
rayuwarta wanda'bata taBa mafarkin shigar shi
ba.
Tana jiyo muryar Ni ’ima na CeWa “Tsaya mana
Amira ina zaki je haka.?” , Alhaji Saminu ya amsa
da cewa, “Sakinta na yi kuma bana bukatar ta
sake ko da minti talatin a gidan nan, kuma ke ma
ki koma Bangarenki bana son dogon
turanci.’ “Haba Alhaji yanzu saboda Allah .. Bai
saurari karashen bayaninta ba ya . yi shigewarsa
zuwa_dakinshi ya turo Kofar yana laluban
maigadi a lokacin ya sanar da shi ya budewa
yarinyar da zata fita yanzu.gate Ni’ima ta bita
kofar da sauri hade da sassarfa ta bi bayanta.
.Amira ta kusa bakin get don zuciyarta
ta soma‘ hangen abin da zata iya 'haduwa da
Shi, .a tsakar daren nan. duk da ,abinda
zuciyar ke dauke da shi game hatsarin da
take hangen zai sameta a wajen amma zuciyarta
ta cika da tsoro mutuka domin a. iya tsahon
rayuwarta' bata saba fita cikin dare zuwa Wani
waje mai nisa ba, k0 da kuwa bayan ‘sallar-
magriba ne, a Ka’idar Abbansu da zarar Magriba,
ta yi to fa babu" mai sake fita a cikin ‘yayansa
mata kuma duk inda za su je kafin magriba sun
dawo gidan.
Ga shi garin ya yi shiru banda kukan Karnuka
babu abinda take ji maigadi yana hango tahowar
ta ya bude kofa domin tuni mai gidan ya sanar
da shi zuwanta. .
‘ Amira ta taka Kafarta ke nan taji an rike
mayafinta ta baya.
“Tsaye Amira.” :
.tayi Koda bata wai ga ba tagane murya Ni’ma
ce.
“Haba Amira yanzu ké sai ki biyewa fushin
zuciyarki fita daga gidan nan a cikin irin wannan
lokacin.” -’Ni"ima ta fada tare da riko hannun
Amira. Amira ta janye hannunta da sauri. “Tun da
ya koreni zaman me zan yi.” , Ni’ima ta sake
riketa da kyau ganin : tana sake kokarin fita
sannan ta dubi_ maigadin da ya tsaya yana
kallon su ta ce. “Malam Bala rufo get .” Malam
Bala ya ce “Ai maigidan ne ya ce a bude mata
ta-fita.” Na’ima ta 'ce. ‘ ; “Kai kuma sai ka
budewa ‘yar mutane ta fita cikin wannan daren,
idan wani abu ya ‘ sameta fa.? Ka rufe kofar
nace.” . Sai lokacin ya fuskanci abin da yake
shirin faruwa da sauri ya rufe Kofar Amira babu
yanda . ta iya Ni’ima tana ,rike da‘
hannunta tana bin bayanta sai sautin kukanta
kadai dake fita. ‘
Ni’ima kuwa zuciyarta cike take da sake sake,
babban dalilin da zai sa Saminu ya kore sabuwar
amaryarshi a daren farko k0 ma menene ita dai
bata ji dadin' shi ba, gabada' . ya jagula lamarin
gaba tun da 'saki uku ’ya mata bare ta yi RoKan
sassauta lamarin” kafin wayewar gari. °
Amira na biye da ita’ tamkar rakumi da " akala
har zuya dakin barcinta ta yi mata masauki. a
kan ga donta tama rasa da wacce
kalma zata” rarrashi Amira tabbas lamarin da
ciwo, saki na wulakanci irin haka idan Amira
batayi kuka‘ba me 2a ta yi? Ta sake duban Amira
dake zaune bakin gadon babu alamun zata
sassautaWa kukan da take
yi
Wani irin tausayinta ne ya mamaye zuciyarta saki
har uku to me ya yi .zafi haka? Koma me Amira
ta yi bata cancanci irin wannan sakin. na
wulakanci haka ba
1ta kanta abar zargi ce game-da sakin na Amira
iya abin da ta sani cikin zuciyarta koda kissar
baki ba zata lalata auren Amira da ita ba, bare ta
yi tunanin ta ta je wajen wani boka ’ko malam
kamar yadda ‘yan uwanshi da sauran mutane ke
zargin ita ke
' hana shi aure. ' ' A iya fahimtarta neman matan
Alhaji ' Saminu da ra ayinshi na zama da mace
daya kadai sune suka hana‘shi aure, domin bata
taBa» tunanin hana shi aure ba, a iya rayuwar
zamansu burinta kadai ya tuba ya daina neman
matan banza, wannan dalili. ne "ya dada kashe
kishinta har také ganin gwarama ya karo mata
abokiyar zaman tun dai ta‘ ji
maganar aureen Amira addu’a take yi‘Allah ya
hada‘ kansu, ta yanda za su mallake mijinsu su
kadai ya daina neman mata ta Bangaren daya
kuma ‘yan uWanshi su daina zarginta da habaice
habaicen cewa ta hana shi Kara aure. Yanzu su
waye gari dare daya, ya za a yi. ta fita duk wani ‘
burinta ya rushe ke nan.? Bata san- lokacin ‘ da
ta rushe da‘nata kukan ba. ' ~ Amira tana jin
sautin kukan Ni’ima ta dago cike da- mamaki ta
tsaida nata kukan . ' tak Ta zubo mata ido tana
kallonta babu ko shakka kuka take yi. Tsoh
won minti goma tana kallonta babu ~ alamun
Zata tsagaita da kukan Amira ta ja jiki . har zuwa
inda take ta dafa kafadarta. ' “Haba Aunty Ni’ima
mai zai sa ki-irin wannan kukan a ‘matsayinki na
wadda’ta
girme ni, lallashina ya kamata kiyi da yimin
addu’ar akan ki dinga rusa kuka irin haka.
_ Ni’ima ta dago idanuWanta da suka yi - jawur
suka jike da hawaye tace
, “Amira'ya zama dole ne na yi kuka k0 na
samu sauqin 'abin da ya ke cikin“ raina ba a kan
abin da zan fada miki amma'zaki yar da cewa
abin da ka yiwa dan wani dole a yiwa naka ina da
zuri’a da Abban Ammar ba zan so ace‘ an yiwa»
‘yar‘ 'Shi abin da ya yi miki ba, sannan ta yaya
zan
' fita daga zargin jama’a a kan cewa bani bace
na kore ~ki ba, a baya ina cikin zargin ni ce nake
hana shi aure.” “
. Amira ta yi wani. mUrmushin da ake kira DA
yaqe
Wanda yafi kuka ciwo
“Aunty Ni"ima ni kan k0 da ba kice "komai ba na
tabbar da baki da hannu k0 kadan a kan
Kaddarar da ta same ni, kuma
maganar 'mutane kada ki damu‘da ita domin ba
a iya musu, mu yi addu’a dukkanmu muce Allah
yasa hakan shi ne mafi alkhairi a .,gare mu ’Baki
daya.” ' Maganganun Amira da ta yi sai da ta sa
‘yar nutsowa a cikin ranta tun da ta tuna 'da
cewa babu wanda' ya isa ya wuce ~qaddarar da
Allah ya dora masa; Amira ta janye jikinta a
hankali zuwa man . gado sai a lokacin ne ciwon
jiki ya dirar nata lokaci daya.
Tshohon Ni’ima ta dauka tana kuka da tunanin
rayuwar da mijinta yake ci ta neman mata *da
hadarurrukan da. hangar nasu 'gaba daya na
tsoro da takaici ‘a cikin zuciyartA da ta bari tun‘
bayan
shiryen bikin Amira ya dawo mata domin ta ‘
dauki auren ‘amatsayin .Zuwan Karshen wannan
matsalar tata. Ta hangi rashin fa’idar kukan da
take
'Ta shiga toilet- ta dauro , alwala ta ~ dauko
hijab dinta ta saka ta tayar da sallah ‘ har
lokacin Amira na 'kwance da tunani _ cikin ranta
ganin Ni’ima na sallah ya tunatar da ita abin yi. ‘
'
A dai dai wannan lokacin ita ma ta shiga- toilet
din ta dora alwala ta soma :gabatar da nafila cike
da‘ tuba da rokon ‘ ' Allah“ ,sauki da samun canji
'mafi;alkhairi ya kawo sauki cikin wannan
rikitaccen 'lamarin nata.
****
nuraddén ya fito daga wanka yasa jallabiya‘ mai
yankakken hannu.;
A yau baya shirin fita da wuri, saboda tun a
yammacin jiya ya tura kayan da ya shigo dasu
daga Dubai, zuwa Abuja tun daren " na jiya a ka
tabbatar masa da kayan sun iso lafiya, shi kuma
yana saka ran washe gari ya yi sammakon zuwa
abuja ya raba kayan a dukkan shagugansu na can
din.
Yana zaune da wayarsa a hannunsa yana tuttura
hotunan ’kalolin kayan da ya zo da su zuwa ga
abokan kasuwancinsa ya dago kai dan jin motsin
shigowa.
Bahijja ce ta shigo fuskarta a dame dam! Ta
zauna daya daga cikin kujerun dakin’ ya zubawa
fuskarta ido sai a lokacin ya tuna da rikicinsu na
daren jiya da yawan zirga zirgar yasa bai dawo
gidan da wuri ba, har sai zuwa Karfe goma sha
biyu na dare.
Abin da agogonsa ya nuna masa ke
nan lokacin da ya shigodakin Bahijja ya
ya qarasa kan gadonta sanye take da kayan data
wuni dasu hatta .daurin dankwalinta na daure a
kanta’
wannan dalili __ ya Kara tabbatar masa da ba
barci takeyi ba, yasa hannu ya‘dagota yana
dariya ya ce ‘ nasan ba bacci kikeyi ba ki tashi
Wani saKO zan baki.” Ta'turesa a fusace . “Nura
bana son abin da kake yi min kada ka sake
tashina.” ". ‘ Ta j uya zata sake kwanci-ya. Ya
riKota..‘Haba Bahijja ki tsaya mana ki tambayi;
dalilin ‘ da yasa na kai‘ 'wannan lokacin ban
dawo ba, kafin ki soma' fushin dani."
Ta fasa “ta tashi zaune tana aika masa da wani
..irin kallon da yasa hantar
cikinsa kadawa. bai karasa abinda yake fadanba
ta katseshi
“Abinda ya tsareka ya wuce wajen
‘yan iska ‘yan matan ka da kake. zuwa ne ina
wai zaka fadamin Nura ni na yarda da kai dukkan
kalaman‘ka na karya na gama‘ «karanta su, ka
barni“ ka komawa ‘yan iskan' ‘matanka tun 'da
rayuwar da ka zaba.kenan Kalamanta sun yi
mutuKar kona zuciiyarshi wai shin wane irin
bahagon zargi'
‘bahijjah take y1 masa, ko da yaushe
maganarta ke nan yana tare da ‘yan iska ta ta
maidashi mazinaci, kuma maganar tayi matuqar
yi masa~ daCi yana ji tamkar ya
"kamo ta ya shaketa sannan ya gaya mata
ubanta ne mazinaci sai dai ,ya kasa 'koda. daga
leBBansa dan furta mata wata kalma, duk abinda
ya taho da shi ya Bace masa sai kunci da Konan
maganganunta.
Kirjinsa har kagawa yake yi saboda bacin rai
haka ya mike a fusace ya fita daga dakin ya nufi
nasa dakin ya 'yi wanka ya ‘saka kayan barcinshi
ya kwanta.
A hankali laifukan Bahijja suka dinga.‘
shafewa daga Zuciyarsa yasan cewar zafin son
da take yi masa ne ya haddasa mata zafin
kishinsa da take ganin tamkar yana tare da Wata
ne.
: Tunaninsa ya tsaya, dai-dai lokacin da
idanuwansa suke ci gaba da nazarin
' fuskarta.
Ya lura da yanayinta har lokacin fushi
' take yi sosai dashi. Ya yi murmushi ‘
Bankada
Chapter7
Sannu sarauniyar mata, baki tambayeni‘ yanda na
kwana ba jiya. .. Ta murguda baki, -
“Na san lafiya Kala'u ka ta shi me‘zan tambaya.?
Ya sauke ajiyar zuciya zuciyarshi dankare da
mamakin halayyar da take nuna masa, yama rasa
a wanne sashi 'baudewar hali zai a jiye Bahijja
rashin tarbiya wani sashin na zuciyarsa ya bayya
mishi abin da ke damunta.
Idanunsa ya tsaya a kanta yanda ta cika tana
Bata fuska abin dariya ‘ ma ya bashi, amma ya
kanne gudun:kada yasake yin wani lafin ya
tausasa murya.
“Bahijja kin san ina gudun duk wani abu da zai
kawo Baraka a tsakaninmu saboda bana son
ganin Bacin rai a shamfide
a fuskarki amma ki kasa yarda dani,
da zata kawo zaman lafiya a tsakaninmu
matsalarki guda daya ce, zargi Bahijja 'shi ne
kika sawa ranki. wanda yake hana zuciya samun
kwanciyar'hankali, da nutsuwa, kike bata ranki a
banza alhalin dukkan abin da kike nema akaina
kina samu. Ina jin ciwon zargin da kike yimin
domin a. wajenki' ne ya dace na samu
kyakkyawar shaida domin kin fi kowa kusanci da
ni a yanzu, amma kullum cikin zargina kike batare
da kin ga wani abin zargi a gareni ba.” ‘
Maganganunshi sun ratsa ta har ta ji zuciyarta
na son ta amince da shi sai wani sashi na cikinta
ya 'tunatar da ita dadin bakin ‘ namiji, take ta ji
kamar busa yake mata. Ta
ce. “Ka ga malam kada ka cika ni da wani didin
bakinka har kana wani cewa banga wani abin
‘zargi ba, to darem da ka.yi kuma fa,
? A ina ka yi shi dan nasan ba agidan Inna ka
zauna ba, kuma ba awajen Malam ba, domin ko
shi sai ya yi maka fadan ka koma gida.” ‘ : ‘
'Zuciyarsa ta hasala mutuka wato duk- abinda ya
fada mata bata amince mishi ba.
Amma sai ya kasa . bayyana mata fushinsa
burinshi kadai ta amincewa gaskiyarshi.
Ya mike ya durkusa a gaban kujerar da take a
zaune ya kamo hannuwanta duka biyu ya soma
laluben nata idanuwan cikin hashi, bai furta mata
komai ba har sai da .yaga idanunta sun risina
daga yi mishi wani irin kallon mai kama da
harara ta mai da su kan hannuwansu da suke
cikin na juna. ’ Bahijja abin da ya kamata ki yi
kenan» ki soma'" tambayata dalilin rashin
’daWOwata. Wuri tun farko baki ‘biyewa
, abin da zuciyarki ta saka miki ba kika hau kika
zauna akai batare da 'kin tabbata -da zarginki
gaskiya Bane.” Bahijja ta janye hannayenta ta
dora su kan kafadunshi ta saki murmushi. ‘ “Na
yarda da kai aminina kishinka ne ya rufemin
idanuna, har na kasa fahimtar hakan tuni Wani
irin’ farin ciki yaji ya mamaye shi tabbas akwai
'alamun nasara akan lamarin da ya daUri niyyar
yiwa Bahijja idan har ya daure "Zai nusar DA ita
ya kuma fahimtar da ita yanda zata s tarbiyyantu
daga hannunshi ya juya akalarta yanda yake so,
wani irin
sonta yakeji yana ratsa dukkan jikinsa ya janyota
zuwa kirjinsa a hankali yake rada mata cikin
kunnenta.
“Bahijja ki ajiye kishi waje daya domin ke kadaice
tauraruwar dake haske
idona bana jin zan iya hada jiki da kowaCe diya
mace bayan ke duk yanda kika so da rayuwata
haka 2a a yi Bahijjanah.”
'. ****
Amira barci ta yi wanda‘ har ta makara; sallar
asubah, lokacin da ta farka har an idar a
masallatai masallaci da'sauri ta mike ta yi alwala
gamida sallar sai daidai wannan'lokacin ta fita
daga gidan Ta dubi Ni’ima da itama barcin takeyi
bata farka' ba, tana idar da sallah ta lalubi
mayafinta ta kira sunan' Na’ima ta mike ta ce‘
“‘Na gode Aunty Na’ima 'bisa- karamcin da kika
yi mink Allah ya hada , fuskokinmu da alkhairi.”
Daga nan ta juya Na’ima kuma kasa cewa komai
ta yi'domin ita ma tana gani . lokacin daya dace
kenan Amiran ta bar gidan don bata san' irin
kaskancin da zai yi
musu ba idan ya fahimci‘Amira a gidan ta kwana.
Wasu hawayen tausayin Amira suka ‘zubo mata
ta mike tana sharar kwalla ta shiga toilet dan yin
alwala.
Garin ya yi shiru sai sasanyar iskar dake kadawa
cikin yanayin sanyin safiyar banda radadin da
zuciyar da Amira ke dauke da shi har da tsami da
ciwon da jikinta yake yi, tun daren na jiya.
Alamun zazzaBi ke bibiyarta a yanzu da iskar
sanyin safiyar ke kadata sai gaba daya jikinta ya
soma rawar ,sanyi zazzaBin ya sauka gaba daya
a jikinta,‘ tana ji tamkar ba zata iya ci gaba da
tafiyar ba,‘ amma babu bukatar ta tsaya ta' ko
da hutane domin taf1 so ta isa gidan hajiya Kaka
kar garin ya gama wayewa ta hadu DA idon sani
a yayata a gari. sai dai kam abin hawa Sama da
guda uku ta
yi kokarin tsayarwa amma suka shigeta bata‘ da
wani zaBi’da ya wuce ta ci gaba da tafiya,; duk
da ta san abinné mawuyaci ta kai gidan‘ Kaka da
kafafunta.
Haka ta ci gaba da tafiya har ta yanke shawara
komawa gidan Aunty Ummi duk da‘ ta san bata
gidan tana can gidansu tun daga nesa ta hango
wani mai tasi ta soma addu’a‘i Allah yasa ya
tsaya aikuwa yana zuwa
dai dai inda take ya tsaya.
Ta gaya masa in da zata ya ce ta shiga‘ ta shiga
ta zauna ya soma cewa “Yan mata akwai hadari
fa wajen fitowa dai 'dai irin wannan lokacin in ba
tare da babban dalili? ba, ,shi ma na ciwo da ya
zama dole, ne a yanzu matar makocina na kai
asibiti kuma kin yi sa’a hanyar zan yi na dauka
kema
asibitin zan kai ki shi yasa na tsaya sai kuma
ki ka yi sa’a hanya daya zamu bi, shi yasa na
dauko ki.”
Ya yi shiru yana jiran abin da zata, fada domin
alamunta sun nuna sosai babu' lafiya a tare da
ita musamman yanda ya kula da fuskarta ta.
kumbura idanunta sunyi jajur, ga yan da take
takurar sanyi.
Ya yi shiru yana? son ya ji daga gareta . amma
kamar da ‘ dutae yake magana domin k0 uffan
bata ce. masa ba asalima bata fahimtar abin da
yake fada talula cikin zafaffan tunani jin ta yi
shiru ya ce.
Adai dinga kula ‘yan mata duniya ce yanzu ta
lalace da gurBatattun mutane duk abin da za ki yi
ki bari hasken rana ya fito
‘ jama’a su fito kafin ki fita daga gidan.”
Nan ma shiru yaga tayi dole shima
yadinke bakinsa domin karfe daya baya magana,
inji masu iyé magana.
rarrashinta da cewa komai ya yi farko yana da
karshe, ta siyawa kanta audugar toshe
kunnuwanta daga surutun mutane ta sani lokaci‘
kalilan labarin mutuwar aurenta zai warwatso a
kunnuwan makiya da masoyanta, kamar yan da
labarin aurenta ya watso a kunnuwan‘su, ta yi,
sa’a Kofar gidan abude take ba kamar yan da ta
zata zata yi bugun kofar
Showing 21001 words to 24000 words out of 79369 words